Free chapter 路 Read without an account

Chapter 24

by Azizat Hamza 路 Duk kyan Namiji

*馃挳DUK KYAN NAMIJI馃挳*

............. ....馃懗.... ..............


0锔忊儯2锔忊儯4锔忊儯


Tuntuni take duba agogon da ke bangon falonta, gani take kamar matar ba za ta zo ba. Sumy mai maganin mata kenan, wadda su ka ha蓷u a gidan ma茩ociyarta Maman Muhsin. Yadda ta ji Maman Muhsin na yaba maganin Sumyn ya sa suka exchanging contacts, yau ta ma ta al茩awarin zuwa gidan ta 茩arfe sha蓷aya na safe, amma gashi har shabiyu ta gota ba ta zo ba. A karo na ba adadi, ta sake gwada layin Sumy amma har lokacin a kashe ya ke. Ta ja tsaki ta ajiye wayar. Bayan minti uku ta ji ana buga gate 蓷in gidan, da sauri ta 蓷au mayafi ta fita. Ganin Sumy ce ya sa ta fara murmushi. Sai da ta kawo mata ruwa mai sanyi sannan ta ce " Anty Sumy kin shuka ni fa, ke da ki ka ce 11am za ki zo"

Sumy ta kur蓳i ruwan ta ce " kin san anguwan kun nan inada customers dayawa, ina shigowa a keke muka ha蓷u da Maman Farida wallahi ta tsaidani, sai da na fara zuwa gidan ta kafin na zo, wayata kuma ta mutu ba chaji"

"Ayya sannu da zuwa" Nafy ta fa蓷i tana tunanin ta ina za ta fara 蓳ullowa Sumyn.

Kusan minti biyar suna hiran duniya sannan Sumy tace " yawwa Amarya wanne ha蓷in ki ke so?"

Nafy ta yi ajiyar zuciya ta ce "Anty Sumy ni fa irin maganin da ki ka bawa Maman Muhsin ranan nake so"

Sumy ta kalleta da mamaki tace "maganin da na bata fa na Baban Muhsin ne. Kina auren yaro miye ha蓷aki da neman magani irin wannan?"

"Anty Sumy ba za ki gane ba ne wallahi, ai gara ma Baban Muhsin ya haura shekaru hamsin kuma matan sa uku. Amma ni nawa hmmmm....abar maganan kawai"

Sumy ba yau ta saba samun complains irin wannan ba dan haka ta san matsalar Nafy.

"Mijin ki ya kai shekara nawa?"

"28yrs" Nafy ta amsa mata

"Wanni irin aiki ya ke yi?"

To wanni aikin za ta ce Suhail na yi, bayan jiya ma yake ce mata call-up letter na shi ya fito an tura shi Jigawa. Ta washe baki ta ce "aikin office ya ke"

Sumy ta yi murmushi dan 蓷azu ta gama jin gulman mijin Nafy a wajen Maman Farida.

" gaskiya maza ma su aikin 茩arfi sun fi 茩arfin sha'awa, kaman 'yan 茩wadago, soldiers, aikin force dai, ko 'yan ball da sauran su. Idan kuma ma mutum baya aikin 茩arfi to indai yana yawan motsa jikin sa za ki ga yana jimawa. Mijin ki yana buga ball kuwa?"

Nafy ta yi tsaki ta ce " sai shegen kallon 茩wallo amma baya bugawa"

" baya 蓷an motsa jiki ko a gida haka? kaman irin push-up da maza ke yi 蓷in nan"

Nafy ta girgiza kai

"Toh!.... shikenan dai, amma gaskiya bai kamata tun yanzun shi ya fara amfani da maganin 茩arfin maza ba, yana nan saurayi mai jini a jika. Zan dai baki wani for now, amma ki sa ya dinga shan kayan marmari sosai musamman kankana da cucumber sannan ya dinga motsa jikin sa hakan zai taimaka ma sa sosai"

Da sauri Nafy ta kar蓳i roban maganin da Sumy ta mi茩o ma ta, ta kasa kunne tanajin bayani kan yadda za ta yi amfani da shi.

Transfer na ku蓷in maganin ta mata dan bata da enough cash a 茩asa. Sun 蓷an jima da Sumy su na hira kafin daga bisani ta ma ta sallama ta tafi.

茦arfe biyar na yamma Suhail ya shigo gidan. Da gudu Nafy ta zo ta rungumeshi tana ma sa oyoyo. Yai saurin zame jikin sa tareda daka ma ta tsawa. " Mi ki ke nufi?"

"Haba heartbeat, kuma ka dawo ba zan ma ka welcoming hug ba"

"Yau 蓷in kuma?, na 蓷auka ai da ni da ke duk 蓷aya mu ke a gidan nan. Tunda kince na koma saka skirt da zani"

Ta 蓷an langwa蓳e kai ta ce " haba My Suhail kai ba ka mantuwa ne, na fa baka ha茩uri"

Bai kulata ba ya shige 蓷aki ta bishi da sauri. Yana 茩o茩arin cire kayan jikin sa ta shigo 蓷akin ta ce " abincin ka na kan dining. Dan Allah idan ka gama ka fito ka ci"

"茦arfe takwas za mu je gidan Abba, yana son ganin ki"

Ta amsa da toh...

Sokali 蓷aya Sumy ta ce ta zuba cikin juice ko tea amma sokali uku ta zuba saboda samun biyan bu茩ata da wuri. Bai fi minti ishirin ba da 茩arisa cin abinci ya fara jin yanayin sa na chanjawa. Wata sha'awa mai 茩arfi ce ta taso ma sa. Nafy ganin yadda ya ke yi ya sa ta fara 茩o茩arin taimaka masa...

Shi kansa Suhail yai mamakin yau, saboda rabon da ya ji 茩arfin sha'awa irin haka tun daren farkon su da ya sha abinda Qasim babban abokin sa ya bashi. Sai dai bai kawo kome a ransa ba sai ya fi danganta hakan da jimawa da yai ba su sadu ba, dan tun ranan da ta kirashi da mace ya dena kulata.

茦arfe tara saura su ka shiga falon Abba. Shi ka蓷ai ne a falon yana kallon news a tashar BBC. Suhail ya risina ya gaishe shi ita ma Nafyn ta 蓷an risina. Sai da su ka gaishe shi sannan ya tambayi Nafy ko akwai wata matsala, ta girgiza kai.

Wata envelop Abba ya mi茩awa Nafy yana fa蓷in " idan bai isa ba feel free ki dawo. Gobe za a kawo mi ki kayan abinci" Nafy ta kar蓳i ku蓷in tana ma sa godiya duk da cikin zuciyarta wani 茩unci ta ke ji. Gani ta ke kamar sadaka aka bata. Abba ya katse tunanin ta da cewa " za ki iya zama ke ka蓷ai a gidan ko a tura mi ki yara su dinga tayaki kwana?"

"Dama akwai 茩annena da za su zo mu zauna tare"

"Shikenan" Abba ya fa蓷a tareda maida duban sa ga TV...

Kamar yadda Abba ya fa蓷i washe gari 茩arfe goma aka aiko mu su da kayan abinci.  茒okin tafiya Camp da Suhail ke yi ya sa ta ke jin haushin sa, miye a zuwa Camp da zai yi ta rawar 茩afa. Bai ma tunanin rabuwar da za su yi har na sati uku, shi ko ajikin sa...

..............................

Yadda ta ke jeka ka dawo a hall 蓷in ya sa ta fara jin jiri, ta yi saurin dafe bango saboda yadda kanta ke wani juyawa. Cikinta ya mur蓷a, lokaci guda ta saki 茩ara wanda ya jawo hankalin wasu da ke wajen su ka yi kan ta da sauri...

Wayar Lubna Helen ta 蓷auka ganin numbar Mama ne last call da ta yi yasa ta yi dialling 蓷in numbar. Mama na tareda Alhaji tana serving na shi breakfast wayarta ya fara ringing. Alhaji ya 蓷au wayar ganin sunan Lubna ya sa shi cewa " ki ga 'yar halak yanzu mu ka gama hiranta fa" ya 蓷au wayar ya sa ta a handsfree "Hello Auta, ni ne ba a kira kenan"

"Good morning ma, i'm Helen Lubna's colleague"

Jin muryan inyamura ya sa hankalin Alhaji da Mama ya tashi. Mama ta yi saurin cewa "yes Helen, what happened?"

" Lubna just had a miscarriage"

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, where are you now?"

"Ni'ima hospital"

"Ok we'll be there soon" Mama ta fa蓷a yayinda Alhaji tuni ya tashi yana neman key 蓷in mota.

Hankalin Alhaji da Mama a tashe su ka fita daga gidan.

............................

Lokacin da su ka isa asibitin sun samu anyiwa Lubna allura tana bacci, da shike dama Ni'ima hospital 蓷in ne iyalen Alhaji ke zuwa ya sa kai tsaye Alhaji ya fara neman likitan su dan ya mu su 茩arin bayani duk da kuwa Helen ta briefing na su akan abinda ya faru da kuma abinda likitan ya ce.

Likita ya 茩ara tabbatar mu su 蓳ari Lubnan ta yi...

Numbar Hudu Alhaji ya fara kira ran sa 蓳ace amma kuma ba a 蓷auka ba. Mama ta yi saurin cewa "Yalla蓳ai barin kira Ummar sa 茩ila baya kusa da wayar"

Bugu 蓷aya da ta yi Umma ta 蓷auka. Nan ta sanar ma ta abinda ya faru. Umma ta ce gasu nan zuwa.

Tareda Inna Mairo su ka hau keke su ka taho bayan ta kira Baba ta gaya ma sa abinda ya faru.

Hudu na shago yana aiki baisan wainar da ake toyawa ba. Da ke wayar sa na silent shiyasa duk kiran da ake ma sa bai 蓷auka ba. Yana tsaka da aiki wani yaro ya zo wai Baba ne ya aikeshi akan wai maza-maza ya wuce Ni'ima hospital.

Hankalin Hudu a tashe ya zaro wayar sa daga aljihu ya fara bin missed calls da ya gani. Alhaji da Baba ne su ka fi kiran shi sai Umma da ta kira shi sau biyu. Ya fara kiran numbar Baba.

"Ina ka shiga ana ta kiran ka tun蓷azu ba ka 蓷auka?"

" wayata na silent ne. Baba miya faru ka aiko wai na je asibiti"

"Matar ka ce ta yi 蓳ari, su Umman ka na can asibitin" ai bai jira ya ji 茩arshen ba ya kashe wayar ya nufi wajen da ya ajiye machine 蓷in sa.

Lokacin da ya iso ya kira Umma ta ma sa kwatancen 蓷akin da su ke. Su hu蓷u ne a 蓷akin, Mama, Umma da kuma Inna Mairo sai Lubna da ke bacci. Ya du茩a ya gaida Mama sannan ya tambayeta ya mai jiki.

Mama ta ce da sau茩i sun ce zuwa yamma za a sallameta.

"Ba a bu茩atar wani abu?" Ya tambaya yana 蓷an sosa kai, Mama ta ce ba komai.

Sai da zai tafi Mama ta ce idan ya samu dama ya je gida Alhaji na neman sa. Ya amsa da toh...

...............................

Ko chanja kaya bai yi ba ya wuce gidan su Lubna, da ka ganshi ka ga carpenter dan duk jikin rigar shi zuwa gashin kan sa 茩uran katako ne, ga pencil da ya 蓷an ma茩ala a bayan kunnen sa. Sai da ya isa ya kira Alhajin. Alhaji ya ce ya shigo falon sa.

Maganganun da Alhajin ya ma sa ya sa kan sa ya 蓷au zafi. Ba makawa maganganun Alhajin sun fi kama da tuhuma, taya zai ma sa irin wannan zargin. Ba abinda ya fi 蓳ata ma sa rai irin hukuncin da Alhajin ya yanke, wai Lubna za ta zo ta yi jinya a gida na sati biyu. Da 茩yar ya iya kai kan sa gida, yana zuwa yai wanka ya chanja kaya sannan ya wuce asibitin bayan ya 蓷auka wa Lubnan wasu kaya. Lokacin da ya je ta farka, ya ma ta ya jiki ta ce da sau茩i. Allah na gani ba dan Mama da ke wajen ba da ba abinda zai hana ya rungumi matar sa.

Bai jima ba ya tafi saboda sallar la'asar da aka fara kira...

......................

Tunda su ka iso gidan Inna Mairo ke ta surfa masifa. Umma sai bata ha茩uri ta ke amma ta 茩i ji. A haka Baba ya shigo ya samesu, ta fara yiwa Baba bayanin rashin mutuncin da Alhaji ya mu su da su ka je asibiti.

Baba ya ce" Mairo ni banga laifin sa ba, 'yarsa ce dole ya nuna damuwa a kan ta"

"Yaya wallahi wannan rashin mutunci ne, a kanta aka fara 蓳arin ciki ne. Da zai ce wai aikin wahalan da ta ke yi ya sa cikin ya zube. 'Yar buhun uba kwana na uku da na yi agidan nan kullum ta fita da safe sai yamma li茩is ta ke dawowa. Wani aikin ta ke?"

Shigowar Hudu ya sa ta maida zancen kan sa.

"Ai kai ma Allah ne ya kamaka, ka nemi cikin 'yan uwanka ka aura ka 茩i. Ka je ka auri 'yar ma su ku蓷i, wanda ba su 蓷auke ka da wani daraja ba"

Hudu bai ce komai ba ya wuce sashin su. Inna Mairo dama ba maganan Alhaji ka蓷ai ya bata haushi ba, har yau tana jin haushin 茩in auren 'yar ta Uwani da Hudun ya yi...

Acan gidan Alhaji ma dai rikine ya 蓳alle tsakanin Alhajin da Mama domin shi Alhaji kalmar 'STRESS' da likita ya fa蓷i a matsayin dalilin miscarriage da Lubna ta yi ya ma sa fassaran 'WAHALA'. Shine dalilin da ya sa ma ya dage sai Lubna ta zo ta yi sati biyu a gida.

"Fatima kina so ki ce bana jin turanci kenan?, a gaban ki likita yai mana bayanin komai fa"

"Alhaji ba haka na ke nufi ba. Ina so ka san cewa ba wani aikin wahala da Lubna ke yi a gidan Hudu. Asalima stress 蓷in da Lubna ta samu daga aikin office 蓷in su ne, saboda kwana ukun da su ka wuce ta gaya min su na wani program kuma Lubna na 蓷aya daga cikin team leaders. Alhaji, Hudu ya fi mu hakki akan Lubna yanzu, kuma ba adalci bane mu ce Lubna ta zauna a gida na sati biyu, hakan na nufin munyi ma sa katsalandan a lamarin gidan sa. Wannan abu da ya faru dai 茩addara ce haka Allah ya rubuta. Wata macen ranta ka蓷ai idan ya 蓳aci matu茩ar tanada 茩aramin ciki to za ka ga sai ya zube, akwai dalilai dayawa da ke sa Mace ta yi 蓳ari "

" A ta茩aice dai ban fahimci bayanin likita ba kenan?"

"Allah ya huci zuciyar ka Baban Abdallah" ta fa蓷i a hankali.

Hular sa ya gyara sannan ya fice a falon ran sa a 蓳ace. Ta sani indai akan Lubna ne to zuciyar sa a kusa ta ke. Gara ta bari idan ya huce ta cigaba da fahimtar da shi....

茦arfe tara na dare Hudu ya kira Lubna. Da sauri ta 蓷auki wayan ta sa a kunne dan ta yi kewar sa sosai. Yana tambayarta ya jiki ta fashe ma sa da kuka.

"Haba Hayaty, miye na kuka kuma, ko so ki ke nima na yi kukan ne?"

"My baby....i-i lost my bbbbaby" ta fa蓷i tana sheshshe茩ar kuka.

"Our Baby, Our Baby Lubna" ya fa蓷i a hankali

Haka dai yai ta rarrashinta har ta yi shiru. Sai da su ka sha hira sannan ya ce "idan kina son mu sake samun wani baby 蓷in da wuri, sai ki dawo gobe"

Ta yi dariya ta kashe wayar...

Kwanan Lubna biyar a gida kafin ta koma gidan ta. Tare da Mama su ka zo, cikin hikima Mama ta bawa Umma ha茩uri kan maganan da Alhaji ya mu su ranan a asibiti. Umma ta nuna ma ta magana ai ta wuce kuma Alhaji na da gaskiya domin dole ne ya nuna damuwa akan abinda ya samu 'yar sa. Wannan ya sa Mama ta 茩ara ganin darajar Umman kuma ta 茩ara amincewa Lubna ta yi dacen uwar miji...

...........................

Hankali kwance su ke gudanar da rayuwar su, wanda ta ke cike da soyayya da 茩auna ta asali. Kowanne 茩o茩arin farantawa 蓷an uwan sa rai ya ke.

A 蓳angaren Nafy kam tunda Suhail ya tafi camp sau biyu ya kirata, ko ta kirashi baya shiga idan ta samu ya shiga kuwa ba 蓷auka ya ke ba. 茦arin haushin kuma kusan kullum sai ya sa hotunan sa da 'yan mata a status na shi. Ta san mijin ta mai kyau ne, kuma kyaun sa ke ru蓷an duk wata mace da ta ke ma茩ale ma sa su yi hoto. Ba inda ta ke zuwa daga makaranta sai gida inda Zahra da Batool ke tayata kwana, rigimar su da hayaniyar su ka蓷ai ke 蓷ebe ma ta kewa. Ita kam a 'yan kwanakin nan tana tamtamar ko dama can Suhail na sonta. Taya zai yi tafiya har na sati uku ace sau biyu kawai yai magana da matar sa kuma bai damu ba. Ko ta tura ma sa message ma sai ya ga dama ya ke reply kuma reply 蓷in sa baya wuce, ' I'm busy, zan kira ki idan na samu dama' 

Sati biyu da tafiyar Suhail ta ce bari ta je ta gaida Lubna, dan tun da ta yi 蓳ari ba ta je ba. Ko ba komai Lubna 'yar uwar ta ce. Tareda su Zahra su ka tafi yammacin ranan asabat...

Ta yi tsaki sau ba adadi tun dawowar su, ita Hudu zai wala茩anta. Ko da ya ke laifin ta ne, da ba ta je gidan su ba da ba za ayi ma ta cin fuska ba...

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol