Free chapter 路 Read without an account
Chapter 27
*馃挳DUK KYAN NAMIJI馃挳*
............. ....馃懗.... ..............
0锔忊儯2锔忊儯7锔忊儯
Zaunar da Lubna yai yana kallon ta, har lokacin ya kasa saita kan sa.
"Ni kam kallon ya isa haka" ta fa蓷i tana ma sa fari da ido.
A hankali yai sujjadar godiya a tsakiyar falon, da ya 蓷ago ya ce "Lubna ki tayani godewa Allah, ni'imar da ya min acikin shekara 蓷aya ba zan iya misaltawa ba. Ya bani ke a matsayin matata, ya 蓷aukaka darajata ya karramani. Sannan uwa uba ya bani kyautar da na jima ina mafarkin samu. Allah ya saukeki lafiya wifey" ya 茩arasa maganar tareda kissing goshinta.
Hawaye ta gani yana zuba a idon sa ta yi saurin sa hannu tana goge ma sa.
"Za ka sani kuka nima"
"Kukan farin ciki ne Hayaty, ki bari na yi kawai"
"Baby ka ga Daddy na kuka ko"
Hudu ya kai kan sa saitin cikin ta ya ce "princess Daddy loves you kin ji"
Sallamar da 茒ahir ke ta yi ya fargar da su.
Hudu ya 蓷an 蓷aga murya "茒ahe minene?"
"Yaya Abba, Baba ya dawo"
"To ina zuwa"
Sai da ya mata kiss mai kyau sannan ya je ya bu蓷e 茩ofa ya fita....
Sun jima suna tareda Baba ana hiran bayan rabuwa, sai da aka kira sallar magariba sannan ya shiga ciki yai alwala ya chanja kaya, ya saka jallabiya, ya samu Baba a 茩ofar gida suka wuce masallaci tare. Daga masallaci kuwa bai samu shigowa gidan ba sai 茩arfe tara nan ma da dabara ya samu ya taho, abokan sa ne su ka sashi a gaba da hira. Ba abinda ke ran sa irin ya ke蓳e da matar sa ya nuna ma ta tsananin kewarta da ya yi.
Yana shiga yai wa su Umma sai da safe sannan ya kashe wayar sa ya shige sashin su. Abinci ka蓷an ya iya ci saboda abinda ke damun sa ya fi 茩arfin abinci. Tare su ka yi wanka inda tun daga ban蓷akin ya fara aika ma ta da sa茩onni ma su zafi, shi da kan shi ya 蓷auketa cak duk da tulelen cikin ta, bai direta ko'ina ba sai kan gado. Dukkan su sun nuna kewar junan su a daren ranan sai dai daga 茩arshe, Lubna sai da ta sare ta barwa Hudu ragamar komai. Tausayin ta ya ji ya sarara ma ta amma ba wai dan ya gaji ba...
Da safe sai 茩arfe goma ya fito saboda bayan sallar asuba sai da su ka gaisa da babyn sa.
Dawowar sa da kwana biyu su ka je gidan su Lubna dan gaida Alhaji. Alhaji ba 茩aramin jin da蓷in ganin su tare yai ba. Can 茩asar zuciyar sa yana godewa Allah da ya sa ya aurar wa Lubna za蓳in ta, domin a koda yaushe yana ganin farin ciki, nitsuwa da kwanciyar hankali a tattare da ita sa蓳anin abinda bai ganiba a fiskar Nafisa. Ba zai iya tuna yaushe Suhail ya zo ya gaishe shi ko ya kirashi a waya ba, hakanan tun auren Nafy sau 蓷aya su ka zo gaishe shi tareda Suhail, duk zuwanta gida ita 蓷ayan ta sukutum ta ke zuwa ta tafi. Amma Hudu duk bayan kwana biyu zai kira su gaisa haka nan indai Alhaji yana gari to duk Jumma'ah sai ya zo ya gaishe shi. Ko lokacin da ya ke 茩asar waje baya sati ba tareda ya kira shi sun gaisa ba.
Lokacin da Alhaji ya ga video da hotunan Hudu ana karramashi, ya 茩ara godewa Allah da bai hana Hudu auren Lubna ba, saboda kallon 茩as茩anci da ya ma sa da farko a matsayin ba zai iya kula da Lubnan ba. Lallai ko da wasa ka da ka raina matsayin mutum, domin Allah ke 蓷aga darajar mutane, kuma a kowani lokaci ya kan 蓷aga wanda ya so ya kuma 茩as茩antar da wanda ya so. Abinda ya 茩ara bawa Alhaji mamaki kuma ya sa shi farinciki bai wuci yadda Hudu bai da girman kai ba ko ka蓷an, wannan matsayi da ya samu bai sa ya nuna wani isa ko jiji da kai ba.
Daga wajen Alhaji su ka shiga babban falo inda su ka gaisa da matan gidan. Mama da Anty, kasancewar Hajiya ba ta gida a lokacin.
Bayan sun gaisa Hudu ya fita da zimmar zai dawo ya 蓷auketa bayan Isha. Sai da ya fito yai kici蓳is da Hajiya da Abdallah sun fito daga mota da alama tare su ka fita. Ya mi茩awa Abdallah hannu su ka gaisa sannan ya 蓷an risina ya gaida Hajiya, ta amsa ma sa ba yabo ba fallasa.
Shikan Hudu ya rasa wannan shan mur da Hajiya ke ma sa a duk lokacin da ya zo, Lubna ya aura ba Nafy ba amma har yanzu kallon 茩as茩anci ta ke ma sa. Ko da ya ke bai shafeshi ba tunda Mama da ta ke uwar gimbiyar sa tana ganin sa da daraja...
..........................
Kwana tara da dawowar sa ya siyawa Baba Mota, Baba yai ta ma sa fa蓷a akan haka , wai da tsufan sa mi zai yi da mota yanzu.
"Baba ka fi 茩arfin mota, na jima ina son siya ma ka ka hanani, anbani kyautar mota na baka ka ce ba ka so, na ajiye motar saboda ba zan iya hawa mota kai kuma kana fama da tsohuwar machine ba. Wannan motar Baba ka amsa ka samin albarka kawai, da ku蓷ina da halaliyata na siyeta. Idan ka 茩i 茩ar蓳a kaman ka rena ni'imar da Allah ya min ne"
"A'a Baba na,ba haka bane. A kullum ina 茩ara godewa Allah da ya baka baiwa da fasaha a 蓳angarori daban-daban, kuma ya ke baka nasara a dukkan lamuran ka"
Ya 蓷auki key 蓷in motar ya ce " Allah ya maka albarka Hudu. Ha茩i茩a ina 茩ara godewa Allah da ya bani 蓷a mai tausayin iyayen sa. Kamar yadda ka taimake mu ka ji tausayin mu, Ubangiji Allah ya sa na ka 'ya'yan su yi ma ka fiye da haka"
Hudu ya amsa da Amin. Baba ya jima yana sawa Hudu albarka kafin daga bisani ya ce " Babangida na ji hiran ku da Haruna shekaranjiya"
Gaban Hudu yai ras ba dai Baba ya ji komai ba.
"Kana ganin hukuncin da ka 蓷auka ka yi dai-dai? Ba za ka ji haushin za蓳in daka yi ba watarana?"
"Baba zama na kusa da iyayena ya fi min komai, duk wani aiki da zai zama ba a 茩asar nan ba, zan ha茩ura da shi koda kuwa yana tattare da samun ku蓷i da dukiya, saboda aiki ne da zai sa na yi nisa da ku. Ni ne babba, idan na yi nisa da gida ya zan yi na san halin da ku ke ciki. 茒ahe yai 茩arami ya kula da gida, Baba kai kuma ba isashshiyar lafiya gareka ba"
Baba ya ji da蓷in maganar Hudu. Ba kowani 蓷a bane a zamanin nan zai samu gurbin aiki a 茩asar waje kuma ya ha茩ura da aikin saboda ya fi son zama kusa da iyayen sa. Balle aiki mai tsoka kamar wanda Hudu ya samu.
Sai da zai wuce Baba ya ce " yaushe za ka tare a gidan na ka ne?"
"Dama na fi so sai Lubna ta haihu tunda ta kusa haihuwa"
Baba ya ce "Allah ya sauketa lafiya" Hudu ya amsa da Amin...
...........................
茦arfe biyar na yamma a 茩ofar wani gida ta mu su a anguwan Sarakuna. Ita kanta Lubna ba ta san inda za su je ba, kawai cewa yai ta shirya za su je yawo. Ado mai Napep ya 蓷auke su saboda tun ranan da su ka je gidan su Lubna a machine 蓷in sa da su ka dawo Umma ta masa magana akan kar ya kuma 蓷aukan Lubna a machine. Shi ma sai da ta yi maganar ya ga rashin dacewar hakan tunda cikinta ya tsufa...
Ga mamakin Lubna taga Hudu ya fito da keys a aljihun wandon sa, ya bu蓷e gate 蓷in gidan ya kamo hannunta ya ce "mu shiga da Bismillah".
Binsa ta dinga yi da ido har ya kulle get 蓷in su ka fara takawa cikin gidan hannunsu sar茩e dana juna.
Ta yi 茩o茩arin tambayar sa inda su ke amma ya ce ta yi shiru zai ma ta bayanin komai.
Upstair ne gidan, a bakin 茩ofar gidan ma ya sa key ya bu蓷e su ka shiga falon gidan. Falo ne babba wanda ya sha furnitures na gani na fa蓷a, akwai 蓷akuna biyu a jere a gefe kowanne da ban蓷aki a ciki sai chan gefe wani babban 蓷aki ne mai ha蓷e da 茩aramin falo. Shi 蓷akin ba komai a ciki bayan wallcloset da ke ciki. Akwai madaidaicin dining area wanda ke 蓷auke da dining table mai 蓷auke da kujeru takwas, sai kitchen da store. Shima kitchen 蓷in babba ne. Sai da su ka haura sama Lubna ta ga nan kuma 蓷akuna biyu ne, 蓷ayan babba ne kamar master bedroom ya ke, shima ya sha furnitures sai 蓷ayan kuma madaidaici, shima da furnitures a ciki. Daga nan sai study room wanda ya ke 茩unshe da wani 蓳angare 蓷auke da bookshelf da littafai a ciki sai wani 蓳angare kuma desktop computer ne da kayan tarkacen electronic gadgets wanda yai kama da mini office 蓷in Hudu.
Sai da su ka sauko 茩asa Hudu ya ce " do you like the house?"
Baki bu蓷e ta ke kallon shi cikin sar茩ewar murya ta ce " yyyyou mean......this.... bbbbba dai gggggidan da ka ggggggina ba kenan"
Yai murmushi ya ce " yes Hayaty, gidan da Hudu Carpenter ya gina kenan. Za ki zauna a nan mu gina rayuwar mu cikin so da 茩auna tareda 'ya'yan da za mu haifa?"
Ta gya蓷a ma sa kai tareda rungume shi ta ce " I Love you Hood"
Ba 茩aramin jin da蓷in maganarta yai ba. Ba kasafai ta ke furta ma sa kalmar so ba, duk da kuwa shi kam anashi 蓳angare indai su na tare baya minti talatin ba tareda ya fa蓷a ma ta kalmar "I Love you" ba.
Shima 茩ara rungumeta yai ya ce " tun kafin auren mu dai Hood ki ke kirana, haba Luluwa ba za a upgrading 蓷ina bane"
Dariya ta yi ta ce " i love you my shining star"
"Kai kai, wannan sunan sai na bashi tukwici" daga haka ya 蓷aga ta, shi bai ji nauyin ta bama haka ya haura da su stairs 蓷in zuwa 蓷akin sa. Inda su ka nunawa junan su so.....
Kafin su bar gidan sai da ta duba ko'ina lungu da sa茩o na gidan, daga 茩arshe ya kaita wajen da motar sa ta ke a 蓷an 茩aramin parking lot 蓷in gidan. Anjima da ma sa kyautar motar tunma kafin auren su, sai dai ya ce ba zai iya hawa motan ba bayan Baban sa machine ya ke hawa. Ba su bar gidan ba sai 茩arfe tara na dare...
Kasancewa za azo a mata jeren kayanta ya sa washe gari ta kira Mama ta sanar ma ta. Cikin kwana biyu aka gama ha蓷a komai, abubuwanda su kai 茩ura duk aka karka蓷e aka fito da su. Mama, Anty Amarya da wata aminiyar Maman sai Rahma wanda itama suna hutu a lokacin da Aisha da Zahra aka je jere. Already dama su Amina suna gidan suna jiran su. Harta Mama tai mamakin gidan domin Lubna ba ta gaya ma ta tsarin gidan ba. Tundaga gidan Rahma ta kira Nafy tana bata labari. A yadda ta ke zuzuta gidan ya sa ba shiri Nafy ta zari gyalen ta ta nemi abin hawa ta taho. Ba ta sha wahalar gane gidan ba. Ai kuwa idonta ya raina fata, ko ha蓷i babu gidan Lubna ya ninka na ta a kyau. Sai ma da aka gama jere gidan ya ha蓷u ya fito sosai, sun shiga ko'ina sun gani banda 蓷akin Hudu wanda ya ke a kulle.
"Anya Hudu gina gidan nan yai kuwa, ko dai 茩asar waje da ya je ne ya samu ku蓷i ya sayi ready made gida haka, dan na ji ance ya samu ku蓷i sosai"
Da Amina ta ke maganar amma Husna ce ta bata amsa saboda dukkan su sun san Nafyn kuma sun san wala茩ancin da ta yiwa yayan su.
"Gida dai shi ya gina, kuma shekara hu蓷u kenan da ya fara ginin, dama an 茩i shi saboda ance talaka ne. To yanzu Allah ya bu蓷a ma sa kuma ya bashi mace ta gari, mai son shi tsakani da Allah"
Sosai maganar ta daki zuciyar Nafy. Ta so tai magana sai dai kuma mi za ta ce tunda gulman da ya kawota ya ja mata 茩aramar yarinya ta ke gaya ma ta magana.
Rahma ta 茩ara tunzura zancen da cewa " dama haka Allah ya ke 蓷aukaka darajan mutum ai, kaman ba ayi lokacin da kowa a gidan mu ya san da Hudu Carpenter ba, ana ganin sa ana ma sa dariya. Sai gashi yau harta turawa sun yaba da basirar sa"
Mama ta yi saurin da茩ile zancen da cewa "to ya isa haka, kowa ta fara tattara kayan ta zamu tafi tunda an gama shirya ko'ina"
Nafy ce ta fara fita a gidan, Mama na cewa ta tsaya su rage ma ta hanya amma ta 茩i. A Mota Mama ta fara yiwa Rahma fa蓷a. Sai dai Anty ta ce " Mama ni banga laifin Rahma ba fa, gaskiya ta fa蓷a. Gulman da ya ciwo Nafy ta zo gidan ai taga abinda ya dameta"
"Ko da gaskiya ne bai kamata ta yi ma ta magana a gaban yara ba" Maman ta fa蓷a tana maida hankalinta kan tu茩i da ta ke yi...
........................
Zuwanta gida ta zauna tana tunani. Har abin ya kai Rahma 茩anwar bayanta ta gaya ma ta magana. Balle 茩anwar Hudu 'yar ficilar nan. Kiran LK da ta gani a wayanta ya sa ta manta da komai ta 蓷au wayar fiskarta shimfi蓷e da murmushi. Idan akwai wanda ta ke ji da shi a yanzu to LK ne...
Da farko Umma ta so su tare tun kan Lubna ta haihu sai dai da Lubnan ta nuna idan ta je chan ka蓷aici zai dameta ga ciki ya sa Umma ta ha茩ura ta haihu a nan gida. Cikin ikon Allah sati biyu da kwana hu蓷u da zuwa ma ta jere ta haihu. Tun asuba ta fara na茩uda ranan Jumma'a ba ta haihu ba sai bayan sallar la'asar. Hudu na dawowa daga masallaci ya tarar da kyakykyawar 'yar sa, kamannin Lubna sak sai dai ba ta kai uwarta ba茩i ba.
Da ya ke cikin sauki ta haihu zuwa 茩arfe takwas na dare an sallame su.
Alhaji tsabar 蓷oki da aka sanar da shi haihuwar bai iya ha茩uri ba sai da ya zo asibitin ya ga jaririya. Cikin zuciyar sa fal farinciki, yana godiya wa Allah da ya sa da Khadija da Lubna 'ya'yan marigayi ya aurar da su bisa za蓳in ran su kuma su na zaune lafiya. Ya ga 'yar Khadija ga shi yanzu ya ga na Lubna. Ina ma Hussain na raye ya ga Autar sa ta zama uwa...
.............................
Walimar suna da bikin tarewa duka aka yi rana 蓷aya. 'Yan uwan Lubna ta wajen Alhaji da wajen mommy a chan Yobe sun taka rawar gani a wannan shagali. Hudu da nashi 'yan uwan ma ba a barsu a baya ba, sun nuna ta su bajintar.
*AISHA* sunan Umma aka sawa yarinya amma za'ana kiranta da *HIBBATULLAH*
Da farko duk labarin gidan Lubna da su Rahma su ka bayar ranan da su ka je jere Hajiya ba ta wani 蓷auke shi ba, sai dai zuwanta suna ya tabbatar da ganau ba jiyau ba. Gidan Lubna ya fi na Nafy ba 茩arya, hakanan shigan da Lubna ta yi a wajen suna ya girgiza Hajiya duk da kuwa zuciyarta na gaya ma ta Alhaji ne yai ma ta kayan ba mijinta ba. Idan Suhail na ta茩ama da karatu a 茩asar waje shi Hudu aiki aka bashi a 茩asar America ya ce bai yi. Abinda mutane ke ta gulmatawa kenan a wajen suna. Auren Nafy da Lubna da aka yi rana 蓷aya aka sa a teburin gwaji ana ganin wacce ce ke cikin jin da蓷i kuma wacce tafi samun cigaba. Nitsewa ne kawai Hajiya ba ta yi ba a wajen amma maganganun da aka fa蓷a akan auren Nafy da Suhail sun girgizata, da 茩yar ta samu ta sulale daga gidan sunan.
Nafy kam dama ba ta je ba, abin mamaki har 茩awayenta Zubaida da Harira sun je sunan, inda anan ma su ke gayyatar Lubnan Bikin Zuby da za ayi nan da sati uku...
Soyayya mai tsanani ya ke nunawa Hibba da mamanta, hakanan yana 茩ara himma wajen ganin ya kula da su ta kowani 蓳angare. Sati uku da sunan Hibba ya je Abuja interview na wani aiki, abin mamaki duk da tarin basirar sa da experience da ya ke da shi amma aka hanashi aikin simply because HND ya ke da shi ba degree ba sannan ya fita da Upper credit ba distinction ba. Infact, cewa su kai da ya daure ya yi Pgd yai masters da ba abinda zai hana su 蓷auke shi aikin. Shi abinma dariya ya bashi, indai haka za a dinga bawa takarda mahimmanci a Nigeria to da sauran mu. Kamfanin Google da ta nemi bashi aiki ba ta damu da mi ya karanta ba, ko ina matakin karatun sa, abinda ta damu da shi shine basirar da Allah ya bashi. Ya tuna aikin daya fara yi da wata kamfani a Pakistan, lokacin bai ma fara HND ba, kamar wasa ya cika aikin lokacin da ya ga advert na su a facebook. Abinda su ka tambayeshi a interview shine ya iya programming? ya ce ya iya, su ka ce za su gwadashi. Sau uku suna bashi aiki yana musu kafin su ka aminta da ilimi da basirar sa. Kullum zai yi mu su aiki na awa hu蓷u a rana a cikin 3 out of 5 working days, 茩arshen wata su turo ma sa albashin sa. Da ya ke abune na computer, daga inda ya ke a Bauchi ya ke aikin ya tura mu su. Bayan yai one year probation yana mu su aiki sai su ka nemi ya zo pakistan ya samu full time job saboda sun gamsu da bajintar sa, ya ce ba zai iya barin iyayen sa ba. Ganin aikin sa na kyau su ka sake yin yerjejeniyar aiki da shi na shekara biyu wanda bayan ya kammala shekara biyunne su ka bashi award tareda kyautar dalleliyar mota wanda aka ma sa shipping 蓷in ta zuwa Nigeria.
Yanzu haka kamfanin Google 蓷in ma bawai sun barshi bane, akwai deal na aiki da su ka tsara ma sa wanda daga inda ya ke za su dinga morar sa ba wai sai ya zo California, USA ba.
Abinda aka ma sa a Abuja ya sa ya ha茩ura ma da yin aiki da gomnati, sana'arsa da kuma buga-bugan da ya ke yi a 蓳angaren abinda ya karanta ya isheshi ya kula da iyalin sa da iyayen sa.
漏AzizatHamza2020