Free chapter · Read without an account

Page 13

by Halimatou Khabir · MUGUN NUFI!

*MUGUN NUFI*


     ©️ *Nana Haleema.*


*Page 13*


Ganin suna kallon ta sun kasa furta komai ya sanya ta takowa a hankali har lokacin jikin ta rawa yake ta dafa kujerar da take kusa da ita ta durk'usa kanta a sunkuye tace, "Kayi Hak'uri Dr, kayi hak'uri ka yafe min." D'auke kai yayi daga kallon ta hakan kawai zuciyar sa take hasaso adadin mazan da tayi tarayya dasu duk sai ransa ya b'aci komai ya fita daga ran sa.


Ganin dukkan su sunyi shiru ya sanya Omar ya kalle su yace, "Dr magana take maka." Kallon Omar yayi yace, "na fita daga cikin lamarin daya shafe ta, ba k'anwa ta bace haka ba Yaya ta bace ba ita. Koda jini nace iya abinda zan mata kenan, tell her ta fita ta bani waje I don't want to see her anymore."


Duk da bata fahimci English d'in da yayi ba amma taji me yace da farko ta fara girgiza kai tana hawaye tace, "Kar kace haka Dr duk abinda ya faru ba laifi na bane ba ka amince da abinda nake fad'a maka." A fusace ya kalle ta yace, "laifi nane in b laifin ki ba?, yanzu ba daga k'asar Spain kika dawo ba Husna?, har gidan ku naje mahaifin ki ya sanar dani kin tafi bai sani bai yana sanar dani yana hawaye, ko iya hakkin mahaifin ki bazai bar ki ba. Ki fice ki bani waje kar ki sake dawowa inda nake na fad'a miki na cire ki a cikin wanda nake son taimakawa na ajjiye a gefe sabida naga ba taimakon kike da buk'ata ba, har yanzu shaid'an yana kan ki kije kiyi duk abinda zakiyi ba kabarin mu d'aya ba ke kad'ai zaki girbe abinda kika shuka. Husna bana son sake kallon fuskar ki ki fita ki bani waje" ya fad'a yana lumshe idanu zuciyar sa na yi masa mugun k'una.


Mik'ewa tsaye tayi tana kallon Omar tana kuka tace, "Ka bashi Hak'uri bazan iya barin sa ba, komai yake so na daina na zan daina, amma kace ya daina cewa na fita ya tsaya ya saurare ni" ta fad'a tana kuka sosai. Sai ta bawa Omar tausayi ya kalli Ahmad zai magana yaji Ahmady yace, "nace ta fita kar kace min komai" ya fad'a cikin voice mai d'an k'ara yana nuna mata hanya.


"Bazan iya ba, wallahi bazan iya fita ba. Zan daina wallahi ina so na daina na kasa, da zarar nace na daina a gaban sa in na kwana na tashi sai naji san abin ya ninku a zuciya ta. Ba laifi na bane wallahi ban sani ba" ta fad'a tana zubewa a wajan tana kuka mai sauti.


Omar ya kalli Ahmad yace, "Please Ahmad ka tsaya ka saurare ta tunda ta baka Hak'uri yana da kyau ka hak'ura."

"I can't Omar, I don't want to continue take her worries suna saka min damuwa ba, I'm tired with her lies, always zan daina, zan daina, but she can't do it because ba shine a zuciyar. Na gaji Omar taje tayi duk abinda zatayi babu ni babu ita!, ta d'auka bata sanni ba nima ban santa ba period!."


"Bazan iya ba in na rabu da kai rayuwa ta zata sake lalacewa ne, ina son ka wallahi Dr ina qaunar ka bazan tab'a iya barin ka. Kai kad'ai ne mai nuna min dai-dai da ba dai-dai ba in kace babu kai babu ni ya zanyi? Wallahi mutuwa zanyi."


"Ki mutu sai me in kin mutu? Bai shafe ni ba kije kiyi duk abinda kike so amma ki goge ni a zuciyar ki."


"Nayi maka alqawari daga yau bazan sake abinda baka so ba amma ka daina cewa babu kai babu ni yana cutar dani fad'ar hakan da kake yi" ta kuma fad'a cikin kuka sosai fuskar ta duk ta jik'e da ruwan hawaye.


"Baki san mahimmacin alqawari ba shiyasa koda yaushe kice kinyi alqawari, bana zama waje d'aya da mak'arya ta masu sab'a alqawari kuma duka kin had'a. Ki tashi ki bani waje kije can ki k'arata duk abinda zakiyi bai dame ni ba."


Omar ta kalla da yake tsaye yana kallon su yace, "Ka bashi Hak'uri a wannan lokacin da gaske nake na daina koda hakan zai zama silar mutuwa ta, zan daina abinda baya so wallahi zan daina" ta fad'a tana had'e hannayen t duka biyun tana kuka.

Omar ya kalli Ahmad yace, "Kayi Hak'uri Ahmad ka bata last chances in ta kuma sab'a alqawari ni da kaina zance ka rabu da ita amma wannan kayi hak'uri please badan ita ba."


Numfashi Ahmad ya sauke ya zauna yana sauke numfashi sama-sama ganin hakan ya saka ta kallon sa idanun sa a lumshe yace, "Dama ta k'arshe." Kamar k'adangaruwa ta d'aga kai tace, "Na yarda in na sake kome ya biyo baya nice na jawo."


Bud'e ido yayi suka had'a ido yace, "Ba ina damuwa da lamarin ki bane da ke d'in wata ce a waje na A'a ina shiga ne sabida ina jin ki kamar k'anwa ta, in badan haka ba da yanzu na cire ki na ajjiye a gefe ko waye zai zo yace na sake sauraron ki bazan kuma koda kallon ki ba." Duk da bata ji dad'in abinda yace ba amma da yake neman shiri take ta gyad'a kai tace, "Kayi Hak'uri."

"Naji. Kafin muje ko ina so nake yanzu ba anjima na ki tashi ki koma gida kin tayarwa da mahaifin ki hankali in kin koma gobe ki koma makaranta hakan shine zai bani tabbacin abinda kika fad'a gaskiya ne."


"Kaduna!" Ta fad'a tana kallon sa. "Eh can nake nufi akwai inda yafi miki can ne?."

"Akwai" ta fad'a idanun ta na kawo ruwa. 


"Okay ina ne?."

"Wajan ka, ka kaini gidan ka wajan matar ka na zauna komawa ta Kaduna dai-dai yake da komawa ta abinda baka so, koda nace maka na daina in na koma Kaduna sai na cigaba kayi hak'uri kar ka saka na koma."


Da mamaki suke kallon ta dukkan su kafin Omar yace, "Ko meyasa hakan?." Kallon Omar tayi tace, "nidai dan Allah kar ku saka na koma Kaduna in ba haka ba wallahi bazan iya yin abinda kace ba."


"Baki ji me yace miki bane? Cewa yayi meyasa bakya so?" Ahmad ya fad'a yana kallon ta.


Shiru tayi tana goge hawaye Ahmad ya kuma cewa, "baki da abinda zaki ce dan haka dole ki koma gida kodan mahaifin ki, yana son ganin ki a kusa dashi zaman ki a wajan sa shine zai baki kariya daga abinda kike son bari."


"Wallahi komawa ta can ba kariya bane warsatsewa ne Dr, komawa ta can kamar kace na cigaba da abinda nake yi ne, ka amince da abinda nake fad'a zama na a nan shine samuwa abinda nake so."

"Ya zamar miki dole ki koma."

"A'a bazan koma ba, na koma can zan sab'a alqawarin da nayi maka ne ni kuma bana son hakan, ka barni n zauna a kusa da kai yadda zaka dinga nuna min dai-dai da ba dai-dai ba, bana son komawa Kaduna" ta fad'a cikin kuka sosai.


Omar ya kalli Ahmad ya juya harshe zuwa turanci yace, "Ahmad kamar fa abinda take fad'a har zuciyar tane, ana tilasta ta a can ne shiyasa bata son komawa." Ahmad yace, "An ce ta fad'a tak'i ta yaya zamu gasgata abinda take fad'a?."

"A gani na ka bar ta a nan d'in kawai."

"Baka da hankali Omar, gidan uban wa zan kai ta?" Ya fad'a yana zaro idanu.


Omar yace, "wajan Anty Lubna zamu barta na kwana biyu muga da gaske take zata nutsu, in ka kalle ta ka kuma duba yadda take magana jikin ta na rawa akwai abinda yake faruwa a can Kaduna d'in shiyasa bata son zuwa can d'in." Kallon Husna Ahmad yayi da take kallon su bata fahimtar duk abinda suke cewa yace, "kasan halin ta zata bari kuwa?."

"Na kwana biyu zasu zauna kuma in ka duba ita Husnan islamiyya zata dinga zuwa a kwana biyun, mu lallab'a Antyn zata amince in sha Allah."


"Mahaifin ta fa?." Omar yace, "Ka kira shi ka sanar dashi zai zo hakan ai tunda yasan baza ka cutar masa da y'a ba." Ya sauke numfashi yace, "Ina zamu samu Anty Lubna?."

"Muje office in bata nan muje gidan ta."

"Let me call her first" ya fad'a yana d'auko wayar sa.


Yana kiran ta ta d'auka tace masa tana gida ta gaji bata je office ba yace gashi nan zuwa, Ahmad ya kalle shi yace, "muje tare" ya fad'a yana mik'ewa shima ya mik'e Omar ya kalle ta yace, "Zan mu kai ki gidan Yayar mu ki zauna zamu baki kwana biyu in muka ga kin mayar da hankalin ga zuwa islamiyya da kuma kin abinda kike yi zaki cigaba da zama a wajan ta. In akasin hakan ya faru ki d'auka baki tab'a sanin mu ba."


Mik'ewa tayi ta goge idanun ta tace, "Na yadda."


"Muje" Omar ya fad'a yana nuna mata hanya ta fita suka biyo bayan ta.


Lokacin da suka sakko suka had'u da Mima ta kalle su suka kalle ta babu wanda yayi mata magana suka wuce ta bisu da kallo, mamaki ya kamata ta rik'e k'ugu tace, "Wai wacece yarinyar nan ne? Meye had'in ta da Yaya Dr nake yawan ganin su tare?." Babu mai bata amsa tayi k'wafa ta juya ta koma office tare da alwashin nemo ko wace.


Tunda suka shiga motar babu mai magana tafiya kawai Ahmad, yana isa gidan yayi horn aka bud'e musu shiga yayi parking suka fito sukayi gaba tana bin su a baya. Da yake lokacin islamiyya ne ita kad'ai suka samu a zaune a falo ta amsa sallamar su tana fad'in, "Manyan taro ko baccin gajiya baku samu kunyi ba kenan?."


Zama sukayi itama ta zauna a gefe Omar yace, "Bari kawai Anty abubuwa sun yi yawa ne sosai." Kallon Husna tayi da kanta yake a k'asa ta kalle su tace, "Wannan fa?." Omar yace, "Sunan ta Husna itace yarinyar da nake fad'a miki."


Kallon ta Anty ta kuma yi suka had'a ido da Husna tace, "Ina wuni." Ta amsa da lafiya ta dawo da kallon ta gasu Omar tace, "Sai akayi yaya?."

Omar ya canja harshe zuwa English yace, "Mun kawo ta wajan ki ta zauna na kwana biyu ta dinga zuwa islamiyya, ta nuna bata son komawa garin su kamar a can matsalar ta take kuma daman munyi dake zamu bar komai a hannun ki."


Anty Lubna tace, "Tabd'ijam wai kuna nufin na zauna da karuwa a cikin gida na?."

"Na kwana biyu kawai Anty, rayuwar ta tana cikin wani hali tana buk'atar taimakon mu ki daure dan Allah" Ahmad ya fad'a yana kallon Anty.

"Tunda bata san a taimaka mata ba sai mu a bar harkar ta ba dole ne taimakon?."

"Relax Anty, Allah muka ce" Omar ya fad'a yana kallon ta.


Kallon Husna tayi tace, "Husna." Ta d'ago ta kalle ta tace, "Na'am."

"Meyasa bakya son komawa gidan ku?."

"Komawa ta shine cigaba da lalacewar rayuwa ta."

"Meyasa kika ce haka?."


Tayi shiru ta kasa magan Anty ta sake maimaita mata Husna ta kalle ta tace, "Dan Allah kar ku tilasta min sai na fad'a ku taimaka min ku bar ni a garin nan kada ace na koma Kaduna" ta fad'a hawaye na sakko mata.


Numfashi Anty ta sauke ta kalle su tace, "Naji zata zauna na kwana biyu kawai, Daddyn su Alina baya nan kuma nan da four days zai dawo bana so ya same ta a gidan nan dan haka kwama biyu kacal, a kwana biyun kuma naga wani abun a lamarin ta wanda yake nuna bata d'auki hanyar gyara ba dukkan ku sai kun fita harkar ta ko na fad'awa Abbah."


Ahmad yace, "Mun yadda." Ta harare shi tace, "Daman dole ka yadda mana tunda so kake, a kan batun Mima naga daina kula ni kayi yanzu da yake abinda kake so ne gashi ka tako kazo har inda nake." Lumshe idanu yayi ya bud'e bai ce komai ba dan baya so ya tanka ta fasa karb'ar Husna.


Ganin hakan ya sanya ta sake kallon Husna tace, "Zaki zauna dani na kwana biyu zaki shiga islamiyya zaki kashe wayar ki ki daina amfani dashi ko ki canja sim card sabida kar abokan ki su neme ki, in naga kin mayar da hankali sosai zaki cigaba da zama a nan in naga akasin hakan zaki bar gidan nan ne haka zalika zaki bar rayuwar su" ta fad'a tana nuna mata su Ahmad.


"Duka na yadda na amince zanyi" ta fad'a tana goge idanun ta. Anty Lubna ta kira mai aikin ta ta bata umarnin ta kai ta d'akin su suka tafi da Husna.


Sai a sannan yayi ajiyar zuciya ya kalle ta yace, "Thanks you." Hararar sa ta kuma yi bata ce komai ba yayi dariya kawai basu jima ba suka mata sallama suka koma.


Shaf Ahmad ya manta zai kira mahaifin Husna ya sanar dashi abinda yake faruwa bai tashi tunawa ba sai gab da magrib ya shiga mota zai koma gida ya tuna ya zauna a motar ya d'auki wayar sa ya kira number sa, bata jima tana ringing ba aka d'auka da sallama Ahmad yayi magana kafin yace, "Baba Ahmad ne daga Abuja."


Daga can b'angaren yace, "Malam Ahmad ai na d'auki murya, ya aka ji da jama'a? Jiya naga kunyi babban taro Allah ya sanya alkhairi." 

"Amin Baba nagode."

"Husna bata dawo ba ko?."

"Akan ta na kira daman Baba. Ta dawo yanzu haka ta gidan Yaya ta."


Da mamaki yace, "To can kuma ta sauka?." Ahmad yace, "A'a ta nuna min bata san dawowa Kaduna a yadda na fahimci lamarin ta kamar yadda na fad'a maka tun farko akwai takurawa da tilastawa a cikin sa, ta nuna min komawar ta Kaduna shine lalacewar turbar gyara da ta d'auka tace indai ina so ta gyaru to na bar ta a kusa dani."


"Nikam Ahmad waye wannan wanda yake tilastawa Husna yin bariki? Ta fad'a maka waye shi?" Baba ya tambaya yana jiran amsa. Ahmad yace, "A'a bata fad'a ba ta kasa fad'a da alama ana tsora tata ne amma in muka bi komai a sannu zamu fahimta."


Baba yace, "To kana ganin zaman ta kusa da kai babu matsala? Kar ta jawo maka cin mutunci da zubewar k'ima fa." Ahmad yace, "Babu komai Baba daman yayar tawa da take a wajan ta itace shugaba a foundation d'in tamu kuma lawyer ce babu wani abu sai dai ka taya ta da addu'a kamar yadda aka saba."


"To Ahmad Allah ya saka k'arshen wahalar kenan. Har kwana nawa zatayi a nan d'in?."

"Amin. Zata fara zuwa makaranta ne a makarantar akwai wajan kwanan d'alibai itama zata dinga kwana a cikin su akwai mai kula dasu."

"Allah ya saka maka da alkhairi Ahmad ya saka farin ciki a rayuwar ka kamar yadda kake k'ok'arin sanyawa a tamu rayuwar."


Ahmad yayi murmushi yace, "Amin Baba a cigaba da taya ta da addu'a komai zai wuce."

"Ana yi Ahmad za kuma a cigaba, Allah ya dafa ya bamu nasara."

Ya amsa da Amin sukayi sallama ya kashe wayar.


Kunna motar yayi bayan ya ajjiye wayar ya ja motar zuwa gida zuciyar sa wasai, tunda yayi nisa wata number take kiran sa ya gani ya share sabida baya son waya in yana tuk'i, har yaje gida wayar ake ba'a fasa ba hakan ya saka yana fakawa ya d'auki wayar ya kara a kunne, kafin yayi magana aka riga shi aka ce, "Ahmad Abdulsamad ina maka gargad'i akan ka fita hanyar Husna tun kafin kazo kana dana sani."


Jin abinda akace ya saka Ahmad gyara zama ya nutsu sosai yace, "To kai kuma d'in waye?" Ya fad'a hankali a kwance dan muryar namiji yaji duk da an canja ta an k'ara kumbura muryar amma kana ji kasan namiji ne.


"Sanin ni waye ba shine abinda ya kamata ka tambaya ba abinda nake so shi ya kamata kayi, ka fita hanyar Asma'u in ba haka ba zakayi dana sanin da baka tab'a yi ba a rayuwar ka." 


Ahmad yayi murmushi yace, "In na fahimta dai-dai Kaine wanda kake tsorata ta take karuwanci ko?."

"Sanin nine ko ba ni bane duka ba naka bane fita daga lamarin ta shine naka."


Ahmad yace, "to in nak'i fa?." 

Yace, "Zakayi kuka, zakayi bak'in ciki, zaka zubar da hawaye, zakayi dana sani wanda baka tab'a yi ba a rayuwar ka. Sai na tozarta ka a idanun duniya sai na yaye maka rigar mutunci mutane sun koma kallon ka tsirara."


Ahmad yayi y'ar dariya kana yace, "Bazan fita ba lamarin Husna yanzu na fara shiga duk abinda zakayi kayi." Shima yace, "Dama nake baka matsayin ta k'arshe wallahi!, wallahi!!, in baka fita harkar ta ba sai nayi maka abinda har ka mutu baza ka manta dani ba."


Ahmad yace, "Nace mu zuba d'an halak ka fasa." Daga can b'angare shima yace, "Ga fili ga mai doki."

"Saura sukuwa da zamiyaaaa" Ahmad ya fad'a cikin wani irin salo na rainin hankali tare da kashe wayar ya bi ta da kallo.



Share it sabida Allah👏🤗

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol