Free chapter · Read without an account

Page 14

by Halimatou Khabir · MUGUN NUFI!

*MUGUN NUFI*


     ©️ *Nana Haleema.*


*Page 14*


Zuciyar sa ce take bashi tabbacin akwai b'oyayyen abu a lamarin Husna tunda gashi har an fara kiran sa ana masa barazana, "Amma waye wannan yake lalata mata rayuwa?." Bashi da mai bashi amsa ya kunna wayar ta kawo haske ya shiga cikin numbobin wayar sa ya lalubo wanda yake nema ya danna masa kira.


Bata jima tana ringing ba aka d'auka bayan sun gaisa yace, "S boy akwai wata number da zan tura maka yanzu kayi min bincike a kanta please." Daga can b'angaren ya amsa Ahmad ya kashe wayar ya tura masa number.


Kiran sallah da yke ya sanya shi bai shiga gida ba yayi alwala a wajan masu gadin gidan ya fita zuwa masallaci. Bayan an idar ya shigo gida ya shiga part d'in sa yayi wanka ya canja kaya ya zauna yana Nazario akan lamarin Husna.


Fita ya kuma yi yayi i'sha sannan ya dawo ya shiga cikin gida dan abinci kawai yake so yaci ya huta a gajiye yake sosai. 


Dukkan su basa nan yasan suna can kowa yana sallah ya shiga kitchen da kansa ya dafa noodles ya soya kwai ya fito ya zauna yaci sosai dan kad'an ya rage ya ajjiye plate d'in ya shiga ciki. Sallama duka ya musu kawai ya fito ya koma nasa b'angaren dan ya huta.


Dukkan su d'akin Mima suka shiga lokacin da Tasleem take sanar dasu bata da lafiya hakan ya saka su shiga gabad'aya.


Jikin Mima rawa yake sosai sabida zazzab'i tana kwance ta rufe kanta da bargo tana k'yarma. Mamy da Mummy da kuma Dada suka yi kanta ko wanne yana tambaya lafiya.


"Taurin Kaine ne dake Mima wallahi, ba tun yau ba nasha fad'a miki kije a duba ki in ke baza ki bawa kan ki magani ba amma kika k'i ji yadda zazzab'i ya rufe ki fa" Mummy ta fad'a tana zama a kusa da ita tana kai hannun ta wuyan ta.

Mamy ta kalli Tasleem tace, "Maza kira Ahmad yazo ya duba ta." Mima da take cikin ciwo jin abinda Mamy tace tayi saurin cewa, "A'a Mamy gobe Dr Hanifa zata duba ni."


Mummy tace, "Shige ki kira shi tun da meyasa bata duba ki ba sai yanzu?, Tasleem jeki kice yazo yanzu." Tasleem bata musa ba ta fice aka bar su a d'akin Dada ta kalle ta tace, "Sannu takwara ta, ni bana so ma yazo yace zai miki allura dan nasan da mugunta ma yi miki zaiyi dan ya saka ki kuka." Ba wanda ya amsawa Dada kowa shiru yayi ba jimawa Tasleem ta shigo Ahmad na bayan ta fuskar nan a cushe.


Mummy ta kalle shi tace, "K'araso kazo ka duba ta" ta fad'a tana kallon sa ba musu ya k'arasa ya tsaya a kanta yace, "Me yake damun ta?." Mummy tace, "Ki bashi amsa yana tambayar ki."


Shiru tayi bata amsa ba yaja tsaki yace, "Mummy in badan ku ba in nazo inda yarinyar nake ba sunana Ahmad ba" ya fad'a a fusace yana kallon Mummy. Cikin fad'a Mamy tace, "Wai baza kiyi magana bane?."

"Nace muku Dr Hanifa zata duba ni fa Mamy" ta fad'a kamar zatayi kuka tana sake rufe jikin ta.


Bai ce komai ba ya juya zai fita Mummy tace, "Yi hak'uri Ahmad dawo, ke fad'a masa abinda yake damun ki ko ranki ya b'aci" ta fad'a ba wasa tana kallon ta fuska a had'e. Da baya ya dawo ya kalli Mamy kamar zai magana sai kuma ya fasa ya k'arasa inda take kawai ya zauna a kan bedside bai ce komai ba.


Dada ta fusata itama tace, "Wai Mima lafiyar ki kuwa? Baza ki bud'e baki kiyi magana ba?." Mummy tace, "So take na mare ta ai Dada." Mima kamar zatayi kuka tace, "Zazzab'i da ciwon kai." Kamar bai ji ba shima yayi banza da ita yana kallon k'asa.


Mummy tace, "Kaji ciwon kai da zazzab'i amma fa ni naga ta rame ma sosai ko dai damuwa ce?." Shiru yayi kamar baiji Mummyn ba sai daga baya yace, "Mummy malaria na saka fever, abubuwa da dama na saka fever, ta yaya zan abinda yake damun ta?."


Mummy ta mik'e ta bashi wajan tace, "Zauna ka duba." Motsawar da Mummy tayi ya ska Mima tayi k'ara kad'an tace, "Washhh Mummy k'irji na."

"Meya samu k'irjin?" Mummy ta tambaya tana kallon ta.


Bata bada amsa ba Mummy ta kalli Ahmad tace, "ka duba min ita sabida ni ba dan ita ba." Jin abinda Mummy tace ya sanya shi lumshe idanu ya bud'e a kan fuskar ta da idanun ta suke a lumshe a hankali ya kai hannun sa kan goshin ta.


Bud'e ido tayi jin sanyin hannun sa a goshin suka had'a idanu bai d'auke ido daga cikin nata ba, Mamy ya kalla bayan ya janye idanun sa yace, "Mamy ta zauna." Mamy ta kalle ta tace, "tashi ki zauna." Motsawa tayi ta tashi zaune dak'yar tana sauke numfashi ya kalle ta ya kalli Mamy da take tsaye Mummy ta fita yace, "Ta cire rigar ta Mamy."


"Kaji fa kai illar ka Ahmadu duba mara lafiyar ne yanzu sai ta cire riga?, bafa na san iskanci" Dada ta fad'a tana hararar sa. Bai kula ta ba yace, "Mamy bacci nake ji tayi abinda nace." Kallon da Mamy tayi mata ya ska ta kwab'e fuska tace, "Dan Allah Mamy ki bari Hanifa zata duba ni."

"Dallah malama kiyi abinda yace wallahi ranki ya b'aci."


Kuka ta fashe dashi ta saka hannu zata same rigar yace, "Bar ta" ya fad'a yana saka hannu ya zame bargon jikin ta milk d'in vest d'in da take jikin ta ta bayyana mai k'aramin hannu ya d'ora hannu a kan vest d'in daga sama ya zame kad'an ya danna saman breast d'in ta da k'arfi, abinda yje so yaji shi ya jiyo ya murmusa kad'an"Wayyo Allah Mummy" ta fad'a da ihu tana runtse idanun ta.


Janye hannun sa yayi a mik'e tsaye a lokacin Mummy da Tasleem suka shigo har dasu Abie Dada tace, "Gwada da Allah ya kawo ku ku gani da idanun ku, a gaba na a gaban uwar ta yaron nan ya zura mata hannu a riga yana latsa ta. Me yaron nan yake so ya koma ne? Ku duba yadda take kuka wannan cin zarafi da me yayi kama, in shi jamilun yaji zai ji dad'i kenan?."


Abie yace, "Me ya faru Dada?."

"Hannu fa ya saka mata a riga yana matsa mata na shanun ta, ranar nan tace muku ya rungume wata baku d'auki mataki ba yau gashi ya yiwa k'anwar sa nan gaba fyad'e zaiyi mata" ta fad'a har da hawaye na gaske masu yawa.


Abie yace, "Ahmad ya haka?" Ya fad'a da mamaki Yana kallon sa. 

"Abie kai ka kula wannan rikitacciyar tsohuwar, kaina ciwo yake min tana k'okarin saka min damuwa. Yarinyar nan Abie bata da hankali ko kad'an bata san ciwon kan ta ba, tana zaune da ciwo ta san illar sa amma ko a jikin ta."


Dada tace, "Kaine baka da hankali ba ita ba, ga mari ga tsinka jaka? Ka zurawa yarinya hannu a riga ka latsa ta kazo kana cewa wai bata da hankali, uban me yake damun ta to a nonon nata?." Kallon Dada kawai yake wallahi ji yake kamar ya shak'e ta sabida takaicin abinda take fad'a.


Mummy tace, "Kayi mana bayani mana ka bar mu a tsaye kana kallon mu." Yace, "Mummy yarinyar nan tana fama da breast lump ne shine ya saka ta wannan ramar da kike fad'a, duk da baya saka ciwo amma ita ya saka ta zazzab'i sabida ya fara girma a jikin ta, Mummy in fa ya girma shine yake komawa breasts cancer amma da yake bata san abinda take yi ba ta zauna da ciwo ko a jikin ta."


Abie yace, "Kamar yaya kenan Ahmad?." 

"Abie breast lump wani ciro ne da yake fitowa a kan fatar breast yana da tauri sosai kamar dutse haka yake, baya jin magani komai aka saka masa baya kashe shi kuma ganin sa yana d'aya daga cikin alamomin sankarar mama sabida indai ba'a rabu dashi ba shine zai cure waje d'aya ya had'e ya zama cancer k'arshe sai dai a cire breast din gabad'aya. Abinda take fama dashi kenan amma ba nemawa kanta magani ba" ya fad'a yana nuna ta hankalin sa a kwance yake jawabin.


"Ni jikar mutum hud'u. Ahmad sankarar mama fa kace?" Dada ta fad'a tana dafe k'irji. Bai bata amsa ba yayi mta banza Abie yace, "To yanzu Ahmady meye abin yi?."

"Tunda bata son lafiyar ta meye namu da zamu nema mata mafita? A barta kawai tunda haka take so."


Mummy tace, "Wannan ai shirme kake fad'a ka tab'a ganin inda aka bar mutum ciwo? Ciwon ma irin wannan mai had'ari?." 

Mamy tace, "Ba dole yace haka ba in banda shirme da rashin hankali tana jin ciwo a jikin ta tasan illar sa ba bata sani ba amma shine zata zauna dashi? Ta fa san matsalar sa amma bata d'auki mataki ba."


Mummy tace, "Ahmad amma akace masu k'iba da wanda shekarun su suka ja sunfi kamuwa da wannan ciwon, Mima dai ba jiki ne da ita ba kuma babu shekaru meya kawo shi?."


"Mummy ake haihuwar yaro da ciwon zuciya dan ta samu breasts lump ba abu bane mai wahala ba."


Abie yace, "Yanzu duka ba wannan ba Ahmad ya za'ayi?." Ahmad yace, "Dole sai dai ayi surgery a cire su." Dada ta k'araso kusa dasu tace, "Meye sajari?." 


Abie yace, "Yana nufin a yanka a cire ciwon." Dafe k'irji tayi tace, "Na shiga uku ni Ayshatou, nonon za'a yanka? Budurwa ce fa in ya lalace fa?." Ahmad ya kama k'ugu yace, "Sai a bar shi ai in yaso sai a yanke su gabad'aya."


"Yaushe za'a yi aikin?" Mummy ta tambaya tana kallon sa. Juya idanu yayi yace, "Sai abinda surgeon din da zai mata yace." 


"Gaka waye zai mata kuma? Kawai ka saka lokaci muji" Abie ya fad'a yana kallon sa. Yace, "Sai zuwa nan da kwana biyu nake da lokaci." Mummy tace, "A'a gobe za'a yi mata a cire kar ya cigaba da k'aruwa."

"Ina da ayyuka sosai kuma bazai yu ayi gobe ba zata sha magani ta sha yau ta sha gobe."

"To jibi za'a yi mata in Allah ya kai mu" Mummy ta kuma fad'a zaiyi magana ta hana shi dole yayi shiru.


Dada tace, "Kun mayar dani mahaukaciya kenan ko? Duk kun had'a kai kenan yanka ta za'ayi?." Mamy tace, "Dada in ba aikin akayi ba ai baya mutuwa ciwon."


Shiru tayi bata ce komai ba Mummy tace, "Yanzu ina maganin?." Ahmad ya yatsine fuska alamun ya gaji yace, "Mummy ina zanga magani? Bani dashi sai a clinc."


"To ka hau mota yanzu kaje ka d'auko mata ka kawo ta fara sha." Da mamaki yake kallon Mummy zaiyi magana Abie yace, "A'a ya fa gashi da yawa in kika duba tun shekaran jiya bai huta ba, yanzu Tasleem ta bishi ya rubuta maganin sai a siyo kawai." Ajiyar zuciya yayi yace, "Thanks you Abie" ya fad'a yana ficewa Tasleem tabi bayan sa.


Abie ma fita yayi Mamy da Mummy suka dinga mata fad'a kamar wacce take lafiya lau, ita dai tayi shiru duk ji take ta muzanta akan abinda akai mata ga kalaman Dada suna bata takaici. Ita tab'a mata jiki da yayi yafi komai b'ata mata rai shiyasa taso Dr Hanifa ta duba ta yanzu gashi surgery d'in ma shi zai mata duk sai ya gama kalle ta kafin mijin ta.


Kamar yadda akace aka siyo maganin aka bata tasha nan da nan bacci ya kwashe ta da wannan takaicin a zuciyar ta.


********


Baba kuwa tunda suka gama waya da Ahmad ya kasa nutsuwa sallah ma bai samu ya yita a nutse sosai ba gabad'aya hankalin sa yayi mugun tashi ganin da gaske Ahmad yake taimakon Husna zaiyi tund har ya ki ta wajan yayar sa.


Zagaya yake a falon sa yana tunanin irin hukuncin da ya cancanci Ahmad yana yi yna cizon yatsa, "Ya zama dole na d'auki matakin gaggawa a kansa tun kafin ya kai ni ya baro ni, ya zama dole ya tsane ta ta haka ne kawai zai fita daga cikin lamarin ta amma to ta yaya?, ta wanne b'angare ya kamata a jefa masa tsanar ta?."


Numfashi yaja ya sauke ya koma kan kujera ya zauna yana bubbuga k'afa cikin neman mafita, "barin Husna tare dashi babar illa ce a gare ni nan gaba tsaf zai iya cewa zai aure ta" sai kuwa ya zabura ya mik'e tsaye yace, "Inaa! Hakan baza ta tab'a faruwa ba Husna bata ta tab'a jin dad'i a rayuwar ta ba, dole a raba su dole a nemo hanyar da zai tsane ta, dole na san abin yi Ahmad bazai zama mallakin ta ba" ya fad'a yana fad'awa d'aki jikin sa na that's tsatstsafo da gumin tashin hankali.


*********


"Sholly! Sholly!! Kina ina ne?" Mahmud wanda suke wa laqabi da Mah ya ke kwala mata kira yana kalle-kalle. Da sauri ta fito daga band'aki d'aure da guntun towel tace, "Wai mah lafiya kake kwala min kira kamar na ciyo maka bashi?."


Nuna ta yayi da yatsa yace, "Waye wanda kika had'a Husna dashi ya tafi da ita Spain?, Sholly ban miki warning akan Husna ba? Ban hana ki had'a ta da wani ba bayan ni?."


Tsaki taja ta harare shi tace, "Wannan babban mutum ne sun juma tare kuma ba yanzu suka fara tafiye-tafiye tare ba." Har wuci yake yace, "Amma meyasa baki sanar dani ba lokacin da kika ji labarin zasu tafi?."

"Nima ban sani ba sai kawai kira na tayi tace min suna chan. Kai ta wani kumfar baki a kan ta kamar wata matar ka ka manta matar bariki matar kowa ce, kamar taxi ce kowa shiga yake ya fita lokacin da yaga dama."


Kyakykyawan mari ya sauke mata a fuskar sa ya nuna ta da yatsa yace, "Ni Husna tawa ce ni kad'ai bayan ni babu wanda ya isa ya rab'e ta, in kika kum kiran Husna da taxi sai na fasa miki baki wallahi."

Sholly da take dafe da kunci tace, "To in bance mata taxi ba me zance mata? Tun safe ta dawo daga Spain d'in ta fita ta tafi wajan wancan likitan can na kira ta yanzu take sanar dani tana gidan sa kar na kuma kiran ta. Shi a tunanin ka ya kai ta gidan sa ne kawai dan ya kalle ta?."


Sak yayi yana kallon ta yace, "Kina nufin tana gidan Ahmad Abdulsamad?." 

"Kaji ai abinda nace, dan haka dole nace mata taxi domin motar kowa ce kowa shiga yake ya tuk'a yadda yaga dama."


Girgiza kai yake yana jah baya yace, "K'arya kake Ahmad Husna tawa ce ni kad'ai babu wanda ya isa ya rab'e ta bayan ni, ka jira ni gani nan zuwa a gare k dole ka dawo min da matata" yana fad'a ya bud'e a fusace ya fita Sholly ta tab'e baki ta mayar da k'ofa ta kulle ta koma band'aki.


Ana wata ga wata⛹🏼‍♀️


Share it sabida Allah🤗

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol