Free chapter · Read without an account

21 end of book1

by Halimatou Khabir · MUGUN NUFI!

*MUGUN NUFI*


      ©️ *Nana Haleema.*


*Page 21*


A guje ta sauka zuwa reception amma bata gan shi ba hankalin ta y kuma tashi ta dafe kai ta fito compound na asibitin amma ko k'yallin mutumin bata gani ba ta dawo ciki da sauri tana tambaya amma kowa yace bai gan shi ba.


"Mima qalau kike kuwa?" Omar ya fad'a yana kallon ta ganin yadda take a gigice. Mima tana waige tace, "wani ne ya bangaje ni waya ta ta fad'i k'asa shima tasa haka garin na d'auki tawa na d'auki tasa, Dr ka taimaka min ka nemo min shi dan Allah."


Omar yace, "nutsu Mima, a ina kuka had'u dashi?."

"A k'ofar office d'in Yaya Dr."

"Muje mu duba camera room" ya fad'a yana yin gaba. Juyowa yayi ya ganta a tsaye yace, "Tawo mana."


Tana waiwaye ta bishi suka shiga cameras room d'in ya k'arasa gaban computers d'in ya rik'e mouse yana duba inda tace abin ya faru, sai gashi yaga lokacin da Husnah ta shiga office d'in Ahmad kuma bai ga ta fito ba yaga Ahmad ya shiga sai ga Mima bayan an jima tazo tana video tana juyowa wani namiji ya saka facemask yazo gifta ta ya bangaje ta, "wannan yarinyar me tazo yi wajan Ahmad?" Omar ya fad'a a hankali yana sake kallon tv.


Mima ta fashe da kuka tace, "Na shiga uku Yaya Omar waya ta." Ya kalle ta yace, "Karb'i waya ta ki saka account number ki kiyi blocking banks d'in ki in ba haka ba zasu kwashe miki kud'i."

Cikin kuka tace, "Ni ba kud'in ba Yaya Omar wayar nafi buk'ata wallahi."


Baice komai ba ya fara bincike compound d'in asibitin sai ga fitar mutumin a k'asa ya fita daga gate yana sauri, camerar waje ya kuma bincikawa yaga ganshi ya shiga taxi daga can nesa da asibitin sun tafi. "Kiyi hak'uri da wayar nan taki sai da kiyi hak'uri kawai, ki karb'i tawa kiyi blocking accounts d'in ki kafin su kwashe miki kud'i."


Kuka take sosai ta karb'i wayar ta danna codes d'in tayi blocking accounts d'in yadda babu kud'in da zai fita daga cikin su ta bashi wayar ya fita da sauri dan burin sa yaje wajan Ahmad.


Yana shiga office d'in Ahmad ya same shi yana k'ok'arin yi mata allura tana yunk'urowa kamar mai nak'uda tana shure-shure, ganin Omar ya shigo ya saka ya kalle shi yace, "Zo ka taimaka min please." Ba musu ya k'araso ya rik'e ta sosai suka mata allura a lokacin jikin ta ya fara saki amma har lokacin bacci bai d'auke ta ba.


Ajiyar zuciya Ahmad yayi ya ja baya ganin jikin ta ya saki babu k'arfi ya koma gefe yana sauke numfashi duk gumi ya jik'a masa jiki, Omar ya kalle shi yaga rigar sa tayi squeezing ga ma6allan saman rigar tasa a cire duk ya firgice kamar ba shi ba, kallon Husnah yayi ya ganta ba d'ankwali gashin kanta a watse ga gaban rigar ta ya yage har saman k'irjin ta ana gani siket d'in jikin ya tattare har guiwar ta a waje take.


Omar ya kuma kallon sa yace, "Lafiya Ahmad? Meya faru a wajan nan haka?." Bai amsa ba sai idanun sa da ya lumshe ido ya kasa furta ko wacce kalma dan bai san me zai ce ba?.


Kujera ya ja ya zauna ya bud'e ido ya kalli Husnah da take bacci ya kalli Omar yace, "Omar wanne irin feeling Husnah take fama da ita haka? Kasan irin alluran da nayi mata kuwa amma bacci yak'i d'aukar ta?." Omar ya k'arasa inda empty d'in kwalbar alluran suke ya duba y kalli Ahmad da mamaki yace, "Wai kana nufin duk da kayi mata wad'an nan bata dawo dai-dai ba."

"Hmmm" shine abinda Ahmad yace kenan yana saka tissue ya goge fuskar sa yana furzar da iska.


"Amma me tazo yi office d'in nan?."

Kallon sa yayi ya wara masa ido yace, "ya za'ayi na sani nima ganin ta nayi kawai."

"U know what Dr? Yau zuciya ta kuma gasgata min yarinyar nan akwai abinda take qullawa, u have to be very careful."


"Oh my god, Omar ni na kira ta? Bani nace tazo ba a gaban ka tazo na kore ta na dawo na tarar da ita a nan ya zanyi?, look at her condition d'in da take ciki is reality ba k'arya take ba ko pretending, ban tab'a ganin condition irin wannan ba."


Omar yayi murmushi kawai yace, "Ahmad kenan, yanzu ka saka a kai ta ward ta bar zaman office d'in nan barin ta nan problems ne" Baiyi musu ba yakira nurses biyu suka tura gadon da take kai zuwa ward zuwa lokacin tayi bacci sosai.


Omar ya kalle sa yace, "Ka tashi ka gyara kanka wani yazo ya ganka sai ya d'auka dambe kayi." Baice komai ba ya mik'e kawai ya shig band'aki jikin sa a sanyaye sosai zuciyar sa cike da tunanin yanayin ta.

Omar ya girgiza kai ya fice ya koma k'asa inda ya bar Mima, bai ganta a 2wjan ba bai kuma neme ta ba ya wuce office.


Har aka yi magrib yana asibitin har lokacin bacci take bata farka ba daman yasan zata jima tana bacci dan alluran da yayi mata bana wasa bane, gabad'aya jikin sa ya mutu ya kasa motsin kirki sai ajiyar zuciya da yake saukewa.


Wayar sa ce tayi k'ara yayi banza bai duba ba aka kuma kira ya d'auka a k'ufule ya saka a kunnen sa, baiyi magana ba yayi shiru daga can b'angaren yace, "Likita wannan ya kasance kira na k'arshe da zan maka akan Husna, in baka daina shiga lamarin ta ba zakayi dana sani."


"Nayi dana sanin mna sai me? Mtsw" zai datse wayar kenan yace, "Ka jira abinda zai biyo baya" yana fad'a ya kashe wayar shima ya ajjiye yana jan tsaki dan yadda ransa yake a b'ace bazai iya doguwar magana ba.


Gabad'aya ji yayi komai baya yi masa dad'i shiyasa ko ta kan kiran bai bi ba ya mik'e ya kwashi kayan sa ya fita daga office d'in, ward ya lek'a yaga bacci take har lokacin ya bada ajiyar ta ga wata nurse ya tafi gida jikin sa a salub'e.


Mima ma haka take sukuku ta kasa sakewa ko kad'an ko yaya ta juya tunanin videon yake fad'o mata ko ta kan sim card d'in ta bata bi kawai ita videon take ji, duk dana sani ta cika mata zuciya ji take ina ma batayi videon ba gashi voice d'in ta ya fito shiyasa hankalin ta yak'i kwanciya Gabad'aya.


B'angaren Ahmad yanayin Husna ne ya hana shi yin abinda yake gaban sa da ya juya abinda yake zuwar masa rai kenan shiyasa ya kasa sakewa baccin kirki ma ya kasa, ya jima yana tunanin yanayin ta na d'azu domin tunda yake a matsayin likita bai tab'a ganin irin yanayin ba, a daren y kira nurse d'in yafi a kirga tace masa har lokacin bacci take amma ya kasa samun nutsuwa har gari ya waye. 


Kasancewar asabar ce yasan iyayen su maza suna gida da wuri ya shiga ya shiga ciki sukayi karo da Tasleem tana breakfast, tana ganin sa tayi murmushi shima haka ya bata hannu suka tafa kamar koda yaushe tace, "Good morning Yaya Dr."

"Morning fav, yau ina lesson teacher d'in bai zo ba?."

"Ya yiwa Abie waya yace yau yaje unguwa bazai zo ba."

"Sai ki huta" ya fad'a yana jan kumatun ta a lokacin iyayen nasa suka fito har da Mima ma.


Kallon su yayi duka kafin yace, "Barkan ku da fitowa" ya fad'a yana d'an sakin fuskar sa kad'an. "Barka Ahmad za'a tafi?" Abie ya fad'a yana zama a kan kujera.


"Likita kenan baku da lokacin hutu ku sam" Mummy ta fad'a tana kallon sa. 

"Kaji jiya an canjawa k'anwar ka waya ko?" Abbah ya fad'a yana kallon sa.

"Wace kenan?."

"Mima ce sukayi canjen waya da wani bata san shi ba kuma ya gudu daman dai wayar tata aka yi nufin kwacewa, abin mamakin meyasa aka canja mata wayar? Dan in badan ana sane ba da yanzu an dawo da ita." Mummy tace tana kallon sa.


"Ayya" shine abinda yace kafin yace, "Cake d'ina ya k'are Mummy a yi min wani." Mummy tace, "Mima ce take yi daman ai sai tayi maka tunda tace ita baza taje aiki ba, ka siyo mata waya in zaka dawo sim card d'in kuma dole sai dai ta jira Monday tayi swapping."

Kai kawai ya d'aga fita ita kuma ta koma ciki suka bar iyayen nasu a wajan.


Gudu yake sosai a mota burin sa ya k'arasa yaga jikin Husnah, yana ajjiye motar ciki ya shiga direct ward ya nufa. Yana shiga cikin ward d'in ya kalli gadon da take a kwance jiya yaga empty babu kowa a kai, gaban sa yaji yayi mummunan fad'uwa ba tare da yasan dalilin hakan ba. "Good morning sir" aka fad'a daga bayan sa ya juyo ya kalle ta yace, "Morning, ina patient din wannan bed d'in?" Ya fad'a yana nuna mata gadon.


"Da safe wani mai kama da ita yazo naga sun fita ban kuma ganin ta ba" ta bashi amsa cikin girmamawa. "Oh my god, ina Zaliha take?."

"Night duty take jiya da zata koma shine ta bar min patient d'in tace na kula da ita."


Cikin fad'a yace, "Shine kika kasa kika bari ta tafi ko?."

"I'm sorry Sir."

Tsaki yayi ya juya ya fita ya d'auko wayar sa da niyar kiran number yaga message ya shigo da number Husna, kasa bud'ewa yayi domin bai san abinda zai tarar ba, ajiyar zuciya yake yana kallon notification na message d'in amma ya kasa bud'ewa, dak'yar ya daure y bud'e yana karantawa. _bazan iya zama ba Dr ka kasa bani maganin ciwon da yake damu na, na tafi zan dawo nan bada jimawa ba amma duk abinda kaga ya faru kayi hak'uri ba laifi na bane, tabbas akwai abu babba da zai faru ka yafe min dan Allah._


Kamar ya zubar da hawaye haka yake ji ko zuciyar sa zatayi sanyi domin k'unar da take masa har bakin sa yake jin tiririn ta.


_In sha Allah Husna na bar lamarin ki, indai suna na Ahmad yau na fita daga duk abinda ya shafe ki, bazan sake neman ki bazan sake waiwayon ki ba har abadah._ abinda yake fad'a kenan a zuciyar sa haushi da wani abu mai kama da tsanar ta n shiga cikin jikin sa da zuciyar sa.


Bud'e k'ofar akayi kamar yadda ya zata Omar ne ya kalle shi ya murmusa yce, "ta kuma guduwa ko? Ni daman nasan yarinyar nan wahalar da kai kawai zatayi Ahmad amma ka kasa gane haka, wallahi matuk'ar baka barta ba sai ta tarwatsa maka zuciya."

Numfashi ya fesar yace, "Daga yau na bar lamarin ta komai zai biyo baya babu ruwa na."


Murmushin rainin hankali Omar yayi yace, "In soyayyar ta da take zuciyar ka ta barka ba." Kallon sa yayi shima ya kalle shi yace, "Yes soyayya Ahmad, kana son tane shiyasa take duk abinda taga dama kake k'yale ta ka hak'ura. Yadda na sanka baka da juriya in badan soyayar ta ba da yanzu ka manta da shafin ta."


Ahmad yayi k'aramin tsaki yace, "Raina a b'ace yake kana neman ka sake saka min b'acin rai, babu soyayyar ta a zuciya ta namaimaita maka wannan yafi sau goma baka ganewa ne?."

"Kaine dai baka ganewa amma soyayyar Husna ta riga ta kama zuciyar ka, jira muke muga ta yaya Abbah zai amince kayi soyayya da karuwa."

"Mtsww baka da hankali."

"Kaine dai babu hankali a tare da kai duk kabi ka tayar da hankalin ka akan wata banza karuwa motar kowa, kalli yadda ka rame duka akan damuwar ta kamar wanda aka yi ma asiri."


Banza yayi masa bai kula shi ba ya kuma cewa, " Sai kai tayi ai kai kaga zaka iya indai karuwa ce gaka gata nan, Akwai patients biyu a waje suna son ganin ka." Girgiza kai yayi yace, "Bazan iya ganin su ba."

"Sai kasan yadda zakayi dusu ni kaga tafiya ta" ya fad'a yana ficewa ya barshi zaune idanun sa a lumshe.


Babu yadda ya iya haka yaga mutum biyun daga nan ya mik'e y fita, industry sa ya shiga yana ta aiki duk da ya manta da Husna amma abin yaci tura haka ya kwashe awanni a ciki da y fito ya tafi ya samu abinci yaci kad'an ya koma gida.


Da yamma ya shiga gida cikin gidan ya fara shiga Mummy take tuna masa maganar wayar Mima yace ya manta zai saka a kawo, a take yayi waya gudun sake mantawa yace a kawo masa ya tura musu kud'in.


Washe gari lahadi tunda ya tashi yake jin gaban sa na fad'uwa sosai ya rasa dalilin faruwar hakan ga jikin sa a sanyaye baya jin dad'in komai, bai yi niyar fita bama sam yana kwance a d'aki bai samu ya fito ba sai sha d'aya na safe ya shiga cikin gida shima dan ance ana kiran sane.


Ganin yayyen sa maza a zaune dasu Abbah yasan wani abun za'a tattauna ya nemi waje ya zauna yana sauke numfashi, "Ya dai Ahmad?" Yaya Sulaiman ya fad'a yana kallon sa.

Kallon sa yayi yace, "yau da fad'uwar gaba na tashi ban san dalilin hakan ba."

"Kai ta maimaita Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ko meye zai kau in sha Allah" Mamy ta riga Sulaiman fad'a. Kai kawai ya d'aga Mima a lokacin ta fito itama ta zauna.


Abbah yace, "Yaushe ce tafiyar ka Germany akan wannan project d'in?." Ya kalli Abbah yace, "Cikin week d'in nan zanje na gama komai can zanje nayi depending in yayi suyi approving."

"Allah ya taimaka, ya batun ginin gidan naka da nayi maka?."

"Wallahi Abbah na manta gabad'aya bana cikin nutsuwa ne."

"Meya hana ka nutsuwar?" Abie ya fad'a yana kallon sa.


"Wata karuwa ce Abie yake son taimakon ta tun farko sabida rayuwar ta abin a taimaka ce amma ita tak'i bada had'in kan hakan, in tace masa ta daina kamar abin kirki ta fara zuwa makaranta to fa a satin zata manta ta cigaba da sabgar ta bayan kwana biyu sai ta kuma zuwa tace wai yayi hak'uri. Ya rasa nutsuwar sa a kanta gabad'aya kamar wacce ta yiwa asiri da nayi magana yace yana jin ta kamar Tasleem kuma na tabbata ko Tasleem d'in ce tak'i barin abinda baya so har zuwa wannan lokacin da yanzu ya share tunda bashi da juriya" Omar ya fad'a yana shigowa yana kallon Abie.


Abbah da Abie da duka mutanen wajan suka kalle shi kafin suyi magana yace, "Ina so na taimake tane kawai bayan wannan babu komai."

"K'arya yake Abie son ta yake" Omar ya fad'a yana kallon sa.


"Son ta? Karuwar yake so?" Abbah ya fad'a yana kallon Omar da mamaki. Omar yace, "baya so a kira ta da karuwa ai Abbah."


Ahmad yace, "Omarrrrr!" Ya fad'a yana lumshe idon sa. "Barni na fad'a ai ba k'arya nayi ba, lamarin naka yayi yawa in Abbah da Abie suka tsawatar maka wata k'ila ka daina."



Zai kuma magana wayar Abbah tayi k'ara ya d'auka ganin sunan Lubna ya saka ya kara a kunne baiyi magana ba yace to kawai ya kashe wayar ya kalli Mima da take kusa da TV yace, "Kunna TV nan ki kai min BBC hausa." Ba musu ta kunna ta d'auki remote ta canja zuwa BBC hausa.


Fuskar Husna da aka hasko ya sanya gaban Omar fad'uwa yace, "Abie ka ganta itace yarinyar da nake magana, amma me ya kaita nan?." Shiru sukayi inda y'ar jaridar ta fara tambayar ta tace, "Meye kika ce sunan wanda kike neman a bi miki hakkin ki?." Ta d'ago idanu ta kalli y'ar jaridar tace, "Dr Ahmad Abdulsamad."

"Likitan b'angaren da ya shafi mata kuma masanin ilimin kimiya, shi kike nufi?."


Ta d'aga kai almun eh ta kuma cewa, "Shugaban kungiyar say no rape foundation shi nake nufi."


Gabad'aya mazaunan d'akin suka kalli Ahmad da shima ya kalli tv k'irjin sa na bugawa a guje.


Y'ar jaridar tace, "Me yayi miki har haka da zaki zo nan kai tsaye?." Kuka Husnah ta fashe dashi tace, "Yayi min fyad'e daga nan ya mayar dani tamkar matar sa duk sanda yake nema ban isa nayi masa musu ba, nace na gaji yadda yake taimakawa wasu su daina su shiga makaranta nima ya taimaka ya barni amma sai yak'i ya dinga min barazana da in na rabu dashi sai ya kashe ni. Abinda ya sanya ni zuwa na sanar daku naje na same shi nace ina da ciki yace sai an zubar kuma wannan shine na hud'u an tabbtar min in na zubar bazan kuma iya d'aukar ciki ba, sai na k'i dana nuna bazan ba yace kar na kuma zuwa inda yake" ta fad'a tana fashewa da kuka sosai.


Y'ar jaridar tace, "Amma kowa yana shaidar halayen sa masu kyau ne kuma yak'i yake da masu fyad'e ta yaya zai iya aikata haka?."

"Son zuciya, a zahiri halayen sa masu kyau ne amma a bayan fage tantirin gaske ne, koda zai musa akwai videon da na d'auka lokacin da naje ya kore ni sabida nasn za'a iya yin haka shiyasa nayi video dan ya zama hujja. Ina da tarin hotunan mu a hotel Wasu a cikin gidan su sun san muna tare kamar yayar sa da abokin sa da wata Mima."


Ta share hawayen ta tace, "Bai kyautu na saka hujjar a nan ba amma n saka su a duniya kowa zai iya gani. Ina rok'on hukuma da layoyi da hukumar kare hakkin d'an Adam da su shiga maganar nan dan a karb'a min hakki na a wajan sa, Barr Lubna wacce ta kasance mai jajircewa wajan ganin an yiwa irin su hukunci kar tayi san kai dan ya kasance k'anin ta taimake ni ta jajirce a bi min hakki na a wajan sa, ya cutar dani ba kad'an ba ya raba ni da kowa nawa" ta fad'a cikin kuka mai tausayawa.


D'uff aka kashe tv babu wanda yake motsi a cikin su sai Omar da yayi k'arfin halin shiga Facebook dan yaga abinda yake faruwa, abinda ya fara karo dashi shine videon lokacin da yake mata tsawa yana cewa ta fita sai aka canja kalman ta, na biyu kuma Mima ta d'auka ga maganar Mima rad'au a videon, na uku kuma hotuna ne a hotel tana tsaye shima yana tsaye.


Babu wanda ya lura da Anty Lubna ta shigo sai da suka ji tana kuka tana fad'in, "Ahmad kaga abinda muke guje maka tun farko nida Omar ko? Kaga dalilin da yake sakawa nake cewa ka dakata da shigewa yarinyar nan ko?, me gari ya waya Ahmad me zamu cewa duniya?."


Shi dai Ahmad ya kasa furta komai sai numfashi da yake saukewa a hankali idanun sa a lumshe, kwatanta irin tashin hankalin da yake ciki b'ata baki domin Allah kad'ai yasan yanayin da zuciyar sa take ciki. Hatta naman jikin sa zafi yake ji a ciki balle zuciyar sa da ruhin sa.


Mamy kuka, Mummy kuka, Dada kuka, Anty Lubna kuka, Mima da Tasleem duka kuka suke. "K'arya take masa, wallahi Allah K'arya take ni shaida ne, duk abinda tace yayi mata babu d'aya da ya faru taimako shine yake had'a su da ita" Omar ya fad'a a rud'e yana kallon mutanen falon kamar ya kurma ihu.


"Dukkan mu nan mun san hakan Omar amma mutane fa? Maganar da nake maka human right suna gab da zuwa gidan nan su kama Ahmad. Kalli kaga irin zagin da akewa Ahmad a social media, yarinyar nan ta kashe Ahmad da ransa" Anty Lubna ta fad'a da kuka sosai.


Sauran mutanen duka sun kasa magana kowa yayi shiru yana kallon Lubna da Omar, "kinji kunya Mima dake za'a had'a baki wajan tozarta d'an uwan ki? Meye ribar ki akan hakan?, in kika tozarta Ahmad ai kan ki kika tozarta, meye naki nayi masa video kina magana? Kin san lokacin me ya faru Mima?, taimakon ta yake a lokacin ke kuma kikayi video kina fad'ar kalamai marasa dad'i ita kuma tayi amfani da hakan aka canja miki waya" Omar ya fad'a yana kallon ta rai a b'ace. 


Girgiza kai take tace, "Ranar juma'a naje bakin office nasa sai na ganta a ciki ni kuma dan na fanshe marin da yayi min nayi videon dan nazo na nuna dan yaji haushi shima, kuma wallahi tunda nayi video na fasa nunawa nace shi zan nunawa ya bani hak'uri, canja min waya akayi manta ma kaine ka bani wayar ka nayi blocking accounts? Bada niya nayi ba wallahi" ta fad'a cikin kuka sosai ma kuwa.


Mai gadi ne ya shigo yace, "ranka ya dad'e anyi bak'i a waje."

"Sun iso" Anty Lubna ta fad'a tana zama tana kuka sosai.

"Jeka kace su shigo" a lokacin Abbah ya samu bakin magana ya na kallon Ahmad.


Ba jimawa suka shigo d'aya daga cikin su yace, "Suna na Asp Bukar jami'i daga hukumar kare hakkin d'an Adam, mun zo mu tafi da Ahmad sabida ya amsa mana wasu tambayoyi sakamakon k'arar da aka shigar a kansa."


"Babu abinda Ahmad ya aikata babu wanda ya isa ya tafi dashi" Dada ta fad'a tana kuka Mummy da Mamy ma haka suka ce.


Mik'ewa Ahmad yayi tsaye yace, "Duk abinda aka ce nayi nayi d'in, ku barni ayi min hukunci dai-dai dani."

"Baka da hankali Ahmad? Kasan me kake cewa?" Omar ya fad'a yana kallon sa da a zafafe.


"Kar ku damu komai zai wuce, Anty kiyi aikin ki kamar yadda kika saba kar ki kiyi min kara ki karb'a mata y'ancin ta" ya fad'a cikin wani irin yanayi yana yin kamar d'an maye.

"Bazan ba! Bazan je na tsayawa k'arya a kotu ba!."

"Dole kiyi Anty, dole kiyi kodan ni" ya fad'a idanun sa a lumshe. 


Mummy ya kalla yaga tana kuka sosai ya k'arasa kusa dasu yace, "Mummy, Mamy Dada ku daina kuka dan Allah, komai zai wuce" ya fad'a muryar sa na shaking. Fad'awa jikin Mummy yayi ya rungume shi k'am tana kuka tana girgiza masa kai. Kukan yaji shima yana niyar yi yayi saurin mayar da k'wallar sa Mummy tace, "Duk inda kake Allah yana tare da kai Ahmad." Janye jikin sa yayi ya kalle ma'aikatan yace, "Muje."


Dada tace, "Kar ku tafi dashi k'arya take masa wallahi, bai aikata ba ku dawo min dashi" tuni sun fice ma Dada tayi baya zata fad'i suka taro ta gabad'ayan su.


*********


Duk abinda Husna take fad'a yana gaban tv yana kallo har k'arshe kana yayi murmusa fari ciki mai tare da zallar nishad'i na shiga cikin jikin sa yace, "Ahmad komai yazo k'arshe na tabbata wannan abin zai sanya kai da dangin ka ku tsani Husnah balle son ganin ta, bayan wannan kuma ya kamata komai yazo k'arshe kowa ya san matsayin sa."


Mik'ewa tsye yayi ya zaga falon yace, "Ya kamata y'ata Aishatou dake gaban ku tasan nine mahaifin ta, Husna kuma kusan Abdulhamid shine mahaifin ta ba ni ba, ya kamata ku san ta yadda komai ya faru ku bani d'aukakkiyar y'ata likita kuma matar Ahmad ta dawo gare ni, gurb'atacciyar y'arka ta dawo hannun ka Abdulhamid, Abdulhamid lokacin bak'in cikin ka yayi kamt yadda ka saka ni a baya."



"Na lalata muku zuri'a na saka muku lalatacciya kuma gurb'atacciya a cikin sa, lokacin yazo!!!."



End of book1⛹‍♀️⛹‍♀️⛹‍♀️



_Tofa fan's ya abun yake ne? Ga Ahmad a hannun hukuma ga sunan sa ya b'aci a duniya ga kuma Husna, meye ribar Husna na b'ata masa suna? Duk da tarin taimakon da yayi mata a baya. to ga Baba yana fad'in Mima ce y'ar sa ya kenan bayan mun shaida kamar da Baba yake da Husnah? Ta yaya kamar ta samo asali in ba y'ar sa bace.....?🤔😳 idan Husnah ta kasancewa da gaske har Abie ce fa...? Mima kuma y'ar Baba ya kenan....? Ya matsayin auren Mima da Ahmad...? Zai d'ore kuwa?. Anya Ahmad zai kub'uta daga hannun hukuma....? Anya Ahmad zai yafewa Husnah...?._



_mu had'e a book2 ku samu amsar tambayoyin ku duka fan's 💃😍 akwai rikici, makirci, dana sani, tausayi, soyayya, duka suna nan suna jiran ku a labarin nan, biya naira 300 kacal ki samu ayi tafiyar dake kema in ya zama complete document zai k'ara farashi🤸‍♀️ tuntub'e a kan wnn number domin mallakar naki *** only whatsapp pls._




Share it sabida Allah.🤗🤗

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.