Free chapter · Read without an account

7

by Hauwa A Usman · BAK’AR SHUKA…!

*BAK'AR SHUKA...!*




       NA




*HAUWA A USMAN*

    ~ JIDDARH~



Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh

ArewaBooks:Hauwaausmanjiddarh



7️⃣



A zabure Abba yace "Kar dai kace min Nakowa?


"Shi Abba cewar Ajlaal , "to ikon Allah wannan ba sai anyi wani bincike ko b'ata lokaci ba, zan nemi mutane sai muje, murmushi Ajlaal yayi yana shafa kanshi yace " nagode sosai amma dan Allah aje da wuri,

" zamuje da wuri amma sai kayi min alk'awarin zaka koma kamar da zaka koma Ajlaal Basaan d'in dana sani zaka koma level 4 d'inka,

" in sha Allah Abba, har Ajlaal yakai bakin k'ofa Alhaji Basaan ya kira sunanshi cikin taushin murya "Ajlaal..!,

jin yadda ya kira sunanshi yasashi juyawa cikin nutsuwa, " Lokaci da rayuwa suna da matuk'ar mahimmanci dan idan daya daga cikinsu ya kufce maka bazai taba dawo maka ba, kayi kokari ka amfanesu, ba shekara ba, ba wata ba, ba sati ba, ba kwana ko yini ba, ba awa ko minti ba dai-dai da dakika daya idan ta wuce daga rayuwarka bazata kara dawowa ba harka koma ga Allah, dan haka kasan me kayi a kowacce rana ta rayuwarka da zai amfane ka Duniya da Lahira,

fata, buri da mafarki duk abu d'aya ne, kuma kowa yana da nasa, yawan burikanka yawan jajircewarka, karka bari shirme da shiririta su cinye kaso mafi yawa a rayuwarka,

ya kamata kayi abinda zaka amfana kuma al'umma zasu amfaneshi, wanda zaka ci moyarshi duniya da lahira,

murmushi Ajlaal yayi tare da jinjina kanshi yace " nagode sosai Abba in sha Allah zanyi amfani da abinda ka fad'a min.


Daya shigo makaranta farkon abinda yake fara yi shine nemanta, in banda ma tayi mishi gargad'i da fad'in " karka soma gangancin zuwa gidan mu duk ranar daka sake kaje gidanmu nasan daga ranar bazaka sake ganina a rayuwarka ba dan cire ni za'ayi daga makaranta ayi min aure.


Murmushi yayi yace mata " dako saina addabi ahalinki da mijin daya aureki, da kice mace ta farko a duniyar musulunci da zata fara kasancewa matar maza biyu dan kuwa ko kinyi aure ke tawa ce ni kad'ai Deeyanah, tana d'aukar kalamanshi da wasa dan haka bata tab'a basu mahimmanci ba.


Yauma yana shigowa department d'insu ya wuce tana zaune cikin aji ana yi musu lecture's yayi sa'a tana dai-dai window dan haka yaje jikin windon ya tsaya yana kallanta, cikin sa'a ta d'ago ta kalli windon suka had'a ido, tayi mishi murmushi shima ya mayar mata da martanin murmushi, a hankali cikin rad'a-rad'a yace " yaushe zaku fito?


Itama cikin rad'a-rad'ar ta bashi amsa da " nan da minti 30, dayake dama ya saba idan zata kwana tana lectures sayya jirata duk dad'ewar da zatayi baya damuwa, ya koma gefe ya zauna yana jiranta.


"Deeyanah me nace?


Malaminsu ya tambaye ta saboda ya lura da abinda take yi, " na'am Malam! Ni?


"Eh! Ke me nake cewa yanzu?


Kame-kame ta soma yi, "fito nan, Malamin ya fad'a yana kafe ta da ido, cikin sanyin jiki ta fito gaban allo, alli ya mik'a mata yace " ungo maza k'arasa mana bayanin tunda naga kamar kin riga kin sani, bata karb'i allin dayake mik'o bata ba tace " kayi hak'uri dan Allah Malam.


"Dama soyayya da kula-kulan maza iyayanki suka turo ki yi makaranta?


"Arahar taki har takai haka?


"Gaskiya banyi zaton kina da sauk'in samu haka ba wall......


Tasssss! Tassssss! Ajlaal ya d'auke shi da gigitattun marika masu k'arfi, ya shak'i wuyanshi yana huci ya d'aga shi sama " idan mahaifiyarka ko matarka da 'yarka ta cikinka da k'anwarka aka fad'awa ya zaka ji?


" Suma fa 'ya'yan wasu ne, k'annan wasu sannan wata rana zasu zama matan wasu har su kai ga zama iyayen wasu, ya buga shi da k'asa zai rufe shi da duka Deeyanah tayi saurin shiga tsakiya tana zubar da hawaye tace " ka kyale shi dan Allah.


Hannunshi ya dunk'ule had'i da nausar iska kana ya rik'o hannunta suka fice daga ajin, ko ba'a fad'a mata ba tasan Ajlaal akwai bak'ar zuciya ji yadda jijiyoyin kanshi sukayi rad'o rad'o idanuwanshi sukayi jajir kamar gauta, bayyi mata magana ba ya bud'e mata gaban motar ba musu ta shiga ya mayar ya rufe ya zagaya ya shiga, ya figi motar da k'arfi ya tada k'ura.


A bak'in get d'in Estate d'insu yayi parking bayyi mata magana ba ya bud'e ya fita ya zagaya ya bud'e mata, cikin sanyi jiki ta fito, tayi tsaye tana kallanshi kamar zatayi magana sai kuma ta fasa tasa kai zata shige ciki "kiyi hak'uri please! ya fad'a cikin sanyin murya, cike da mamakin hak'urin da yake bata na miye ta juyo, murmushi ya sakar mata yaja motar ya tafi batare da yayi mata magana ba, tabi bayan motar da kallo tana murmushi tace " rigimamme!.


Washe gari kusan a tare suka shiga makaranta, suna wajen me siyar da gurasa ita da Raleeya ya k'araso wajen, kallo d'aya tayi mishi ta kawar da kanta tana fad'in " zaka ci gurasa band'ashe?


"Kin cika baki kina yi man tayin rowa wai zaka ci, to ban ci, dariya tayi gami da kallan me siyar da gurasar tace " ka had'a mishi special. 


Ya soma cin gurasar kenan aka aiko kiransu shida Deeyanah, kallan juna sukayi kana ya mayar da kallanshi ga wanda aka turo yace " kace muna zuwa, hankalinshi kwance yadda kasan babu me jiranshi ya gama cin gurasar, "muje mana, a nutse ya mik'e suka jera har office d'in, Malamai suka gani birjik da gani meeting suke yi, da sallama a bakunansu suka shiga, ganin yadda Malaman suka tsatstsare su da ido yasa Ajlaal murtuke fuska murtuk kamar wanda akayiwa sammacin mutuwa, sai da ta d'an rusuna kana ta gaida Malaman suka amsa ba yabo ba fallasa, while shi yana daga tsaye yace " ina yini?


Daga haka bai k'ara ba, kad'an daga cikinsu ne suka amsa, HOD su yayi gyaran murya had'i da cewa " wai meke faruwa daku ne?


"Meke damunku?


"Meke yawo cikin kanku?


"Fisabilillahi abinda kayi ka kyauta kenan?


Cike da gwarin yace " me nayi Malam?


Cikin zafin rai ganin yana neman rena musu hankali d'aya daga cikin Malam yace " kai ka shiga taitayinka duk cikin mu nan babu sa'anka balle ka rena mana hankali, ido ya zubawa Malamin ya tsare shi da ido yana yi mishi kallan ka shiga hankalinka.


"Kasan wannan?


HOD ya fad'a yana nuna mishi Malamin su Deeyanah daya mara, "eh! yace kai tsaye cikin rashin tsoro.


"Meya had'aka dashi?


Tsayyuwarshi ya gyara kana cikin isa yace "Abun rashin kyautawa yayi ni kuma na gyara mishi, ya fad'awa 'yar wani, k'anwar wani, matar wani kuma mahaifiyar wani maganar da bata dace ba wacce idan aka fad'awa mahaifiyar shi ko k'anwarshi ko matarshi da 'yar shi sai inda k'arfinshi ya k'are, shiyasa nima na nuna mishi rashin dacewar hakan a aikace bada baki ba.


Kwafa d'aya daga cikin malaman yayi had'i da girgiza kanshi, Ajlaal yayi mishi kallan iyakacin nan amma bazan daku ba.


HOD yace " fad'a min abinda ya faru in details, tun daga farko har k'arshe ya komai ya fad'awa su HOD babu abinda ya b'oye har dukan da yayiwa Malamin sai da ya fad'a.


A zafafe d'aya daga cikin Malaman yace " kai ina ruwanka a cikin maganar?


"Meka had'a da ita k'anwarka kome?


A rene ya kalli Malamin yace " matata ce ko kai akwai wanda zayyi b'atanci ga matarka a gaban idonka kayi shiru?


"Lusarin namiji shashasha wanda bai san mutunci da k'imar kanshi ba shine wanda za'a ciwa matarshi mutunci a gaban idonshi tsoro yasa yayi shiru saboda tsabar rashin sanin ciwon kai......


Dakatar dashi HOD yayi ta hanyar d'aga mishi hannu kana yace " ka bashi hak'uri shikenan komai ya wuce dan kyautawa bai kyauta ba shima.


" In bashi hak'uri akan me?


"Me nayi na rashin dacewa da zan bashi hak'uri, shiya kamata ma ace ya bata hak'uri agaban mutunen daya muzanta ta, a d'an hasale HOD yace " nace ka bashi hak'uri ko?


"Kayi hak'uri Malaman ina ganin mutuncinka sosai amma gaskiya bazan iya bashi hak'uri ba, babu juyin duniyar da ba'ayi da Ajlaal ya bawa Malamin nan hak'uri ba amma ya lashi k'asa ya dire ya k'i fur.


"To shikenan tunda bazaka bashi hak'uri ba, kayi taurin kai kuma ka kafe duk da bamu ce saika koma cikin class gaban d'aliban daka mareshi a gabansu ba amma shine ka turje kak'i bin umarnin mu duk da munso muyi masalaha cikin salama dan haka mun yanke mu dakatar dakai har lokacin daka yanke ka bashi hak'uri, cikin tafasar zuciya ya bud'e baki zayyi magana tayi saurin rik'e hannunshi.


Hannunshi data rik'e ya kalla yana jin yadda bugun zuciyarshi ya k'aru da kaso 70 ido ya zuba mata batare daya iya furta komai ba, a hankali ta girgiza mishi kanta alamar a'a kana ta motsa labb'anta cikin sanyi tace " ka bashi hak'urin please.


Ido ya runtse da k'arfi, bashi da yadda zayyi bazai iya yi mata musu ba amma banda ita da idan duniya zata tashi bazai bashi hak'urin ba, idonshi a runtse yace " kayi hak'uri. 


Ido ya k'ifta gami da cewa " eye! banji me kace ba fa, hannunshi dake cikin nata ta k'ara damk'ewa tana rad'a mishi please a kunne, idanuwanshi ya bud'e ya sauke su akansu sai da gabanta ya fad'i ganin yadda suka canja launi zuwa asalin jajaye, " kayi hak'uri.


"Nifa bana jinka, in zakayi magana kayi da sigar rok'o ba kana magana kamar kana bani umarni ba, kayi magiya Malam ka rok'e ni.....



JIDDARH

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol