Free chapter · Read without an account

12

by Nazeefah Nashe · TAKAICIN UBA

Takaicin Uba…



Na



Nazeefah Sabo Nashe




Elegant Online Writers



12.

Hameeda ganin S.Turaki har a lokacin bai yi niyyar tursasa ‘dan nasa ya dawo ba, da kanta ta kira shi a waya murya ba alamun wasa ta ce “Turaki wannan ce magana ta ta k’arshe da Kai a kan maganar auren nan, na gaya maka dole ne ka dawo a yi auren nan da Kai sannan kuma ka turo da sadaki da ku’din Kayan lefe kafin isowar taka.” Turaki cikin b’acin ran takaici da gajiya da Jin maganar auren nan ya ce “Toh Ummeey, Amma me yasa dole sai nazo? Ku yi abinda ya dace kawai?” “Ba zamu yi abinda ya dace ba Turaki saboda aurenka ne Kai zaka zauna da matarka ya zama dole ka zo ku fahimci juna, in banda haka wane irin aure ne wannan ko ce maka aka yi sadaka suka Baka y’ar?” Turaki kamar ya amsa ta da “Eeh mana ai kamar sadakar ne yarinyar da ban Santa ba ban tab’a ganin ta ba ace an bani ita ai sadaka kawai aka bani.” A fili kuwa sai ya ja ajiyar zuciya kafin ya ce “Shikkenan Ummeey zan turo duk abinda ya dace, then I will try my best naga na zo don kawai farin cikinki.” “Yauwa ko kai fa? ‘D’an Albarka, da har kasa na fara tunanin ko an canja min Turaki ne a can k’asashen masu jajayen kunnuwa.” “Mhnn” kawai ya ce murya a shak’e alamu k’arara Sun nuna Ummeey ta gama tik’e shi, don dai ba yarda zai yi ne a matsayinta na mahaifiyarsa, Amma da ya ce ta jira ta ga Uwar da ya zab’a y’ay’ansa shekara da shekaru yake dakon soyayyarta, kamanninta kaf ba su ‘dauke daga idanunsa ba, duk sau ‘d’aya tak ya tab’a ganinta tun bayan mutuwar matarsa Har yau bai sake ganinta ba, sai soyayyarta da yake ta dako. “Yauwa sai na jika.” Hameeda ta fa’da tana katse wayar cikin murmushin samun nasara. 


Gidan Talatu take son zuwa ta ji menene abinda Ayran ta fi buk’ata ta tambayo colours da sizes ‘din takalmin Ayran da ubder wears ‘din ta. Burinta a yi auren nan duk a zatonta Matsalar Turaki ta zo k’arshe gani take Turakin ya sake dacewa da mata kamar matarsa ta farko. Bata San abinda Ayra take shukawa ‘d’an nata ba da ta sani tabbas da farin cikinta ya tak’aita.




Gaba ‘daya ahalin Amma suna baje a parlourn Ma sha Allah y’ay’a da jikoki birjik a zube Ayra ce kawai take bedroom ‘dinta saboda hayaniyarsu da ta fara damunta.


Ummeey ta yi sallama ta shiga falon da fara’arta take fa’din “Aa A’a, yau bataliyace a gidan namu haka.” Kasancewar sun je har gida Sun gaisheta hakan yasa suka ganeta da sauri suka baje suna gaisheta. Ummeey ta dinga amsa musu tana rarraba idanun yarda zata ga surikarta ta so take yau ko a fakaice ta yi mata hoto ta turawa Turaki ya ga canca’de’diyar matar da ta samo masa. “Na ga kowa ban ga daughter ta ta ba.” Amma tana murmushi ta ce “Ai Allah ya ha’daki da misklar yarinya sai kun yi hak’uri da halinta. Dijah kirata tana sama ‘dakinta.” Dijah ta tafi da sauri ta bar Ummeey tana fa’din “Ai gwara haka sau tari yawan surutun ba shi da amfani.” Amma ta ce “Kamar yarda rashin maganar ma ba shi da amfani ba. Yauwa ni kuwa mu je daga can falon akwai maganar da za mu yi da ke…” Ummeey ta mik’e ta bi bayanta suka bar su Zainab suna maganar kirkin Ummeey “Wallahi Ayra banda shak’iya ce ai ta dace da Surika ta k’warai” Zainab ta fa’da tana jinjina girman rashin kirkin Ayran Wanda idan ya tashi rufe idonta take ta mata da duk wata alak’a da take tsakaninku.



A falo Amma ta ‘d’an dubi Hameeda kafin ta ce “Dama tambaya zan miki anya shi Turakin ya amince da auren nan?” Ummeey ta na murmushi ta ce “Me kika gani?” “Gani na yi har yanzu ko waya ban ce Sun tab’a yi ba.” Ummeey ta ja ajiyar zuciya “Turaki Talatu yana da taurin Kai da kafiya idan na biyewa ta son ransa ba zai yi aure ba shi yasa sam ban damu da amincewarsa ba kamar yarda na tabbatar itama Ayran ba wai ta amince ba ne don haka ki k’yalesu idan suka je su ci kansu sa daidaita kansu a can.” Amma ta ja ajiyar zuciya Sam ba amsar da ta so ji ba kenan, amma ya ta iya burinta sada Ayra da ‘dakin mijinta. “Amma Hameeda mai yake raba shi da wa’dancan matan?” Hameeda ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce “K’addara duk da dai yanzu ya gaya min wai ba masu kamun Kai ake Kai masa ba sai Sun gama gantalewa a titi. Kin ga amsar tambayar dai shine ba sa Kai budurcinsu……….”


Zuciyar Ayra da take niyyar shigowa ‘dakin ta wani irin bugawa tamkar zata tarwatse daga jikinta, ta rasa me zata yi murna ko farin ciki? kafin ta saki wani zazzafan murmushi ta jingina da bango “Idan kuwa haka ne Turaki wannan karan…..”

“Waye nan?”

Maganar Amma ta katse mata tunaninta hakan yasa da sauri ta fa’da falon tana furta “Ni ce fa Amma!” Amma ta saki tsaki tana jinjina maganar Hameeda ta kalli Ayra ta ce “Lab’e kuma kika koma yi?” Ayra ta girgiza Kai nik’abin da yake fuskarta ne ya sa Amman bata ga dariyar da fara’arta ba. Da k’yar ta durk’usa a gefen Ummeey tana gaisheta Ummeey ta dafa bayanta ta ce “Yau ‘din ma rowar fuskar za’a min? Ai shikkenan idan da Hotonki turo zan nunawa angonki..” da sauri ta girgiza Kai cikin takaici ta ce “Ummeey bana hoto ko a waya.” Amma ma ta sake tabbatar mata, “Ai ina ji Ayra rabonta da hoto tun na graduation na Primary, ita ko irin hotonnan na Zamani na y’an mata ba yin sa take ba, wai duk don wani ya ganta ya d’orawa kansa son ta.”

Ummeey cike da mamaki ta gyara zama “To saboda me? Ko da yake duk ba matsala bace ki je yanzu waje wata daga y’an uwan ki ta d’aukeki sai a turo min, sannan ki bani sizes na ki.” Ayra ta dinga ha’diyar wani yawu mai ‘daci a zuciyarta tana Jin haushin Ummeey da ta bi ta shigo rayuwarta ta yamutsata. Dabara ta fa’do mata ta ce “Ummeey na rok’i alfarma please!” Ummeeyn kallonta take sosai kafin ta dafata cikin kulawa ta ce “Ba wannan tsakani na da ke Daughter just go straight to the point, ki fa’di ko me kike so zan miki.” Ayra ta ji da’din jin hakan sosai don haka murya a sanyaye ta ce “Kada ku bari mutumin da zan aura ya san zahirin kamanni na don Allah.” Ta fa’da tana ha’da hannayenta alamar rok’o. Amma da sauri ta ce “Saboda me kenan?” Ummeey ta yi saurin dakatar da Amman tana murmushi “Ba ruwanki, ba mu sako ki cikin zancenmu ba, na amince Ayra na ‘daukar Miki wannan alk’awarin na San kina da babbar hujjar da tasa za ki aikata haka.” Ta sunkuyar da kanta sosai ta ji da’din samun Ummeey a yarda take so ta yi godiya sosai kafin ta ce “Sannan please ba zan bi shi ko ina ba zan zauna anan garin, saboda ni nake kula da companyn mu.” Ummeey ta yi jum tana tunanin yarda zata amincewa Ayran da hakan, sai dai bata son Ayran ta ‘dauketa a matsayin mace mai son kanta don haka ta ce “Shikkenan, zan duba wannan In sha Allah tunda anan ‘din ma yana da gida ai ya tab’a zama da matarsa ta farko Amma da Abbansu Abuja Ya ce za’a kai ki.” “Abujan zata je ita zata zab’a wa kanta abinda take so.” Amma ta fa’da cikin hassala da jin haushin Ayra na wannan titsiye da ta yiwa surukarta. Ummeey ta girgiza kai “Ko ‘daya, yarda take so haka za’a yi tunda ba mu zamu yi mata zaman auren ba, yanzu ki tashi ki je ki rubuto min abubuwan da ki ke buk’ata a lefenki da sizes na komai na ki.” Da sauri ta mik’e ta cikin hijab take kallon hararar da Amma take watso mata. Ta ‘d’an saki murmushi a karo na farko shirinta ya fara tafiya yarda take so.



A bakin gado ta zauna hannayenta zube a fuskarta, takarda da biron a hannunta idanunta na zubar da k’walla takaici take ji wai ita ce zata yi aure duk da alwashin da ta sha a kan ‘da namiji, wai yau da kanta zata rubuta abinda take so na aurenta ashe kuwa ba zasu kawo mata lefen ba. Ko sunan lefen bata son ji, angon ma bata San sunansa ba kuma bata buk’atar ji, buk’atar ta shine samun hanyar da zata gujewa auren nan…

Ina ma zata iya tafiya ta bar Amma tabbas da ta tserewa auren nan ko da kuwa ta hanyar barin k’asar ne, duk da dai ta San burinta zai cika musamman sanin cewa ance shima angon baya maraba da auren? 


Shigowar Dijah da dariyar da ta shigo tana yi ne ya dawo da ita cikin hayyacinta. Ta zubawa Dijahn ido da ta shigo ‘dauke da wasu kaya a hannunta tana fa’din “Bikin autarmu ai dole mu kece raini, wajen event mafi tsada za mu kama mu dagargaji Dinner, sati guda za mu yi muna cashewa abinda muka da’de muna fata Allah dai ya nuna mana, ga ankonki ma a hannuna ki turo Drivernki ya karb’a” ta fa’da tana kashe wayar idanunta cikin na Ayra da itama ta ke kallonta cikin mabayyanin b’acin rai, Da gaske ji take kamar ta tashi ta rufe Dijah da duka su tuna lokutan baya. “Idan da Wanda ya isa ya jani ya kai ni gurin bikin ai sai mu gan shi. Dijah ki fita daga harka ta abubuwanki Sun fara isata.” “Kamar yarda na ki suka fara isata ba, biki kam ai dole ki je shi Allah ya nuna mana lokaci. Yanzu ma Amma ce ta ce na gaya miki mai miki gyaran jiki ta zo zata ga yanayin fatar taki.” “Kan bala’i, au Har wani gyaran jiki kuka shirya yi min? To wallahi kada ma a fara idan ba so kuke na fasa auren ba..” Dijah ta bita da kallo tana nazarinta ‘Tabbas akwai abinda Ayra take b’oye musu bata shirya zaman auren nan ba, ta amsa ne kawai gudun b’acin ran Amma don haka jikinta a salub’e ta fice ya zama dole ta tattauna da y’an uwanta kada a zo matsala ta faru….”





____________



A kitchen suke shi da yaron sa Aman, da ya samu hutu a ranar, yaron yana da rashin ji ga shi sosai ya sangarta shi ganin shi ka’dai Hibba ta bar masa yarinyar da ta Haifa wajen haihuwa ita ma ta bita. Turo baki yaron kawai yake cike da sangarta yake furta “Ni Ummeey zan je Abbu.” Tsaki ya ja yana k’ok’arin tsiyaya masa fresh milk a cup. Aman duk da shekarun da yake da su shekara goma cur har a lokacin baya iya yiwa kansa komai saboda shagwab’a shi da suka yi. Cup ‘din ya karb’a ya sha sosai kafin ya ce “Abbu, Please Ummeey.” Ya zuba masa ido kafin cikin b’acin rai ya ce “Aman zan zaneka fa, nace maka Ummeey na Nigeria ni kuma ban shirya zuwa Nigeria yanzu ba…” Yaron cikin takaci ya fice da sauri yana kuka sosai. Jikin Turaki ya yi sanyi saboda Sam baya son b’acin ran Aman ‘din don haka don dole ya fara nema musu ticket na tahowa Nigeria, da shirin idan ya zo dole ya ruguza auren da ake son masa, sabida har a lokacin zuciyarsa bata gama amincewa da auren ba. Zai bi duk hanyar da zai bi yaga ba’a yi auren ba.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.