Free chapter · Read without an account
23
23
Humairah da take ta barci a bayan mama tunma kafin a fara rigimar ta fara kuka mama ta sauketa daga bayanta,daga ita sai pant jikinta nan mama ta fara bata nono,Gwaggo dasu Aunty Zainab suka kalleta "lafiya haka Aisha ba kaya jikinta"
Gwaggo ta 'dora"ko Bata da lafiya ko wani abun ya ha'da ki da surikan naki gama dai ansaba,hala qannan nasa suka ci miki mutunci ke sakarai Kika kasa ramawa Kika taho mana nan ki tayar wa da mutane hankali,shiyasa sam banji da'din dawowarku nan ba kinacan asirinku rufe muma namu haka Atika Kuma na 'dan taimaka muku,da koda aka koreku kunje gidanta ai zatasan yadda zatayi a samo muku wani gidan ko a unguwar ne,sai abu ya faru a kasa tunanin da ya dace to kundawo nan din,in dukan kawo wuqa zasu miki nidai da sanina qannanki bazasu je ba,inma rigimarce dasun kada Miki da 'yar taji ciwo da paracetamol bazasu taimaka muku ba, wannan jarabbabbun mutane hukuma ma sunfi qarfinta ,haka suke rigimar su dukansu da surikansu da qannan miji da yayye su Mubaraka da Maimuna haka sukeyi danma sun ha'du da daidai su ne abun ke zuwa da sauqin wulaqancin su Kuma duk laifin surikan naku ne da basasan laifin 'ya'yansu"haka Gwaggo ta cigaba da sababi,
Ita dai Mama haquri ta bata da cewa"Mama ni bama dani suke ba da 'dan uwansu sukeyi shine ganin ko kar haushin ya qarasa qarewa kaina ya ce na taho nan tunda yara suna nan",mama da jajayen ido take cigaba da maganar,"Gwaggo wallahi na gaji da zama da mutanan nan ko a can ban tsira ba su barmu ma da talaucin dake damunmu da ubangiji ya sa kasancewar mu haka maimakon su tausayama na ,shine dalilin da Allah ya Samar da Mai ku'di da talaka saboda mai shi ya taimaki mara shi koda da shawara da kwantar da hankali ne,amma babu dukkansu ba mai taimakon mu sai jifanmu da mugun alkaba'i basu ba 'yan uwanshi hatta da iyayenshi,wallahi sainaji kamar na zube musu 'ya'yan ko kotu naje a raba auren nan,indai nice matsalarsu" ta qarasa maganar tana rushewa da kuka mai ban tausayi dan Mama abar a tausaya mata ce,cikin yanayin tausayi su Gwaggo suke bata haquri harda Aunty Zainab Gwaggo ta ce"inkin kashe aurenki Hauwa'u kikazo nan wa Kika bawa ajiyar dauke miki duk dawainiyarki su Sha'aban suma buga bugace kina gani ba wanda ko maganar aure ya Fara ma da ya dace ace sun fara shekaru tafiya suke tayi,kuma kinada tabbacin zasu kula 'ya'yan naki sun riga basa qaunartaki kuma bama kece basa qauna ba Abdullahi 'dinne basa so har su iyayen nashi,dan da suna sanshi murna zasu yi dake da Allah yasa ya samu yayi auren,ya auri matar rufin asiri ai ita mace a wajen miji kamar katanga ce,kuma daraja da haiba take qarawa namiji kamar yadda itama yake zamar mata,in bakaso matar 'danka ba ba kasanshi kenan matar rufin asiri,in kinga ana qin surika anawa ganin sai baqin halin nata yakai iyaka,shima ace tana munanawa 'dan naka shine kake qinta,amma dan surika ta ta mai sauki ce sai taje inda suke ko ta sauraresu za'ayimata,saidai ko fitsararta ta takai qarshe,ni yanzu su Jabir nawa suke amma ji nake kamar ko da kaina na samu ku'din da Zan aurar dasu na huta naji da su ommu da Zainab,amma su sunfisan 'daga ma 'dansu hankali bare ke kisa ran naki zai kwanta shine basa so ba ke ba"
Jin maganar Gwaggo yasa ni fara magana"wallahi Gwaggo hakane basa qaunar Abbah ne kawai"labarin komai da ya faru ni da akayi komai zai iya cewa a gabana na shiga basu,ransu in yayi dubu ya 'baci haka suka cigaba da mamakin su Abbah Imran 'din amma Gwaggo fa'di take Abbah dukda haka bai kyauta ba da ya farfa'dawa Hajiya maganganu su Aunty maimuna da Aunty Asma'u ya kamata ace ya zanesu duk abunda zai faru ya faru zata fi jin ciwan hakanma ,Ni dai shiru nayi Mai faruwa ta riga ta faru,haka muka cigaba da labaran duk na gidanmu ne,bamu muka bar gidansu Mama ba sai dare har Abbahsu Mama Saida yadawo Gwaggo ta shiga bashi labarin abinda ya faru shima duk labarin gidansu Abbahn yana dashi ko tantama baiyi ba yasan fiye da hakan zasu iya ma dan Abbansu shi cewarshi harshi Abban namu sai ya samu warwara za'a tantance shi nashi halin dan zumunci yanzu yana samu zasu shirya shima ya manta aibunsu tunda 'yan uwanshi ne,itadai Gwaggo ta ce wa Malam anya kuwa haka zata faru kuwa,haka muka tattaro da su Rumaisa muka taho gida,da sallama bakinmu muka tura kofar gidan muka shiga a tsaye kofar dakin Hajiya muka samu Abbansu Abbah yana kallon kofar gidan da alama shigowarmu yake jira tsaiwar da tsumayenmu tayi kama hasken wutar nefa ya haska mana fuskarta shi da take cunkushe ba alamun fara'a
Mamarmu da muke koqarin shigewa ciki saboda ganin hakan mama bata masa magana ba dan tasan ba abu mai da'di zai biyo baya ba tsawar da Abbah ya dakawa mama mukanmu saida muka tsorata
"Ke Hauwa'u "ya ambata cikin daga murya da karaji,Mama a firgice ta tsaya muma muka ja muka tsaya ta 'dago ta kalleshi jikinta na 'bari ta kasa cewa komai ya cigaba da magana cikin zafin zuciya
"Na sallamawa Abdullahi ke kin zama uwarshi to inaso ki zama ubanshi,babu ni babu shi,bazan ce ya rabu dake ba saboda girman kuskuren da yayi mana da butulcin haihuwarsa da mukayi da yayi saidai mu barshi da ke,alfarmar kwana 'daya a gidannan nayi muku in ba haka ba,zan muku abinda acan gidan hayar ba'a yi muku ba sainasa an muku taron dangi an fasa muku jiki an wurgar muku da kayanku waje,duk da hakan banji na wuce abinda Abdullahi yayimin bare Kuma nace uwarshi ta wuce ni kika sa ya wulaqantani da tarbiyyar da na masa,kika mayar masa da 'ya karuwa saboda kema halinki kenan"
Cin zarafin naji yayi yawa ciki qeqashewar zuciya na kalli Abbahn su Abbah din babu alamun tsoron mai bakin yake fa'da da abinda za'a mayar masa ko kuma abunda furucinsa zai ja masa ko da a gaba ne take maganar da kaurarata ya tsaidamin uwa yana maganar san ranshi,Mama na kalla tare da cewa "mama ki taho mu shige ciki idan yana da magana da mu ya biyo mu ciki,in bahaka ba zan masa rashin kunyar karuwai,saboda na lura babu imani bare tsoron Allah a furucin mutanan nan,baki zama Abbah ba kuma ba suda alaqa dake saboda basu mayar da 'dansu 'da bare ke ki sa ka rai za'a maida ke 'dan wani abu a ransu"
Banma jira sake jin muryarsa ba da nake jinta tafi komai munin ji a wajena ba dan komai ba sai jifan da akemin da kalma mafi muni banji ba bangani ba
"Ku taho mu shige in kun ga zaku cigaba da sauraran shashancinsa ku cigaba"suku ku suka bi bayana har Mama da nasan banda ranta ya 'baci sai ta mareni kalmar da nake fa'dawa Baban musamman ta qarshe har muka shige ciki ban ko sake jin tarin shi ba alaqa damu dama ya yanke ni kaina kan qaya zan kwanta gidan na kwana 'daya sallama mukayi da Ahmad yayi qoqarin yi mah shirun da muka ji muka qarasa shiga muka fara leqa falo anan muka samu Abbah da alama gyangya'di yake dukanmu da tausayawa muka shiga ciki muka sameshi muka fara "Abbah mun dawo"firgigit ya tashi a rikirkice ya kallemu"Kun da'de sai kace ba zaku dawo ba,ku nake ta tsumaye, Hauwa'u nayi zaton ko Gwaggo ta hanaki dawowa ta inda yaran zasu 'bullo nafi zaman jira da fargabar abunda zan ci karo da shi na Fara gyangya'di danni da nake cikin jarrabawar da jiran hukunci da qudirar ubangiji a kainah zan kasance shine nayi imani da shika shikan imani yadda da qaddarar jarabawa mai kyau ko akasinta inajin a raina ubangiji yana kusantani da alkhairi ko da bayan raina ga iyalaina,dan kune komai na,duk labaran da nake ji banta'ba jin kalar nawa ba,ace abun ya tsaurara haka ban ci musu ba sha musu ba,na rasa ina ma zan saka kaina ne,Musa yazo bayan tafiyar ku ya maidomin ma wayar nan yace tayi tsadar da zata zama zargi akan yadda akayi aka sameta wani ma zai iya sharrin tashi ce aka sata mutane ba tsoron Allah,ko Kuma a tayata ku'di banza saboda zasuga ko an matsu da sai dawa,yace Sumayyah ta cigaba da anfani da ita a gabanshi Baba ya cimin mutunci ya ce gobe gobe mu bar gidannan,shine bayan tafiyarshi Musan yace akwai wani gida inda yayi haya kafin ya qarasa gininshi to bakowa ciki yace zaizo da mota a kawoshi kayanmu ko da asuba mukeso mu koma zamu iya saboda gidan a hannunshi yake shima rigingimu da qannanshi da matarshi yasa ya bar gidansu ya Kama hayar wannan gidan amma shi abun nashi baikai kwatar wannan ba"
Tunda Abbah ya fara magana har ya kammala hawaye nakeyi zuciyata a cunkushe take,a cikinmu inajin Khalil ne kawai bazai iya fahimtar abinda ke faruwa ba,nama kasa yarda akan talauci ake qiyayya damu saina kalli abun muddin hakane a matsayin jahilci babba,saboda suma da suke da shi specific abunda zasu kalla suce ya samar mu su dashi qarya sukeyi,Abbahnmu yayi karatu tuquru yanada ilimin da ya wuce na kwalayenshi hakan yasa banjin ko ka'dan karatu ne arziqi, arziqin ka dashi ka samu kyakkyawar rayuwa da yawa daga manyan shaharrun masu ku'dinmu na jiya da yau ba suyi ilimi ana wasu da ga cikin na yau qwalin SSCE ba su ha'da har zuwa yau 'din banaji ko familynsu Abbah sun san haka ko fahimtar gaskiya ta rufe musu ido,kalaman Mama ya katseni
"Muma yanzu Baban ya taremu kasa cewa komai nayi sai Sumayyah ta masa magana itama 'din banyi zaton zata iya ba"
Abbah yayi murmushi "Ai ko zaginsu tayi bazan musa ba saboda kalamun su musamman akanta yanzu sunyi tsauri fiye da nacan baya, Hauwa'u dan kana babba baka da izinin tauye qarami,ba zaka ce zakaita shimfida isarka ga qarami kuma na zalunci kace bazaiyi magana,ko da 'danka ne ka d'abi'ance shi da kyakkyawar da'bia hakki ne akanka ga dukkan mutane duk yadda kake kallonsu a qasqanci bakasan alaqar bawa da ubangiji ba wani bazai 'daga hannu yana roqon Allah ayi ruwa ba face bai sauke hannu ba Allah ya qaddari hadarin ya ha'du anyi ruwan akwai abubuwa da yawa da zasu sa mu hankalta amma bamayi,Allah ya kawo mana mafita kawai"
Mu ka amsa da "Amin"
Shi dai Ahmad tunda aka fara zancen bai sanya baki ba bansani ba ko ys rasa mai zaice ne ma,da haka mukayi shirin kwanciya barcin sam ni kasa samuwa yayi a tare dani na ma rasa maike min da'di ma abubuwan kamar a almarane zance rushewar takai qarshe dukdai kan Mama ne zan iya cewa ni kam tausayinsu nake musamman ma Maman da ko rabuwa tayi da Abbah ba zasu iya amsarmu ba saidai su dauki nasu kawai tunda abun nasu haka ya nuna,ji nake zuciyata ta qeqashe inajin zan zama ne mace kamar namijin da zan kawar da mikin dake tare dasu,kuka nake mara qarfi duk dalilina abun ya taso haka kuma dalilin zuwana Katsina ne,sai yau na tabbatar da illar zuwa hurumin da bai dace da Kai ba ko da janka akayi aka kaika kai yakamata ka gudo ne da qafafunka kabar rayuwa da San birge wanda yake gani ya fika bazaka ta'ba burgeshi ba inajin ko a 'yan uba aka samu irin wannan matsalar za'a jinjina amma uwa kuma uba 'daya hawaye suke bin saman fuskata inajin sharewar ba shida anfani saboda wani ne zai sake biyowa,bansan iya lokacin dana dauka ba a haka har barci 'barawo yayi awan gaba dani,tashin da Mama tayimin yasa ni fahimtar asuba ko safiya tayi idona na bu'de na kalli waje haske har ya fara fitowa mama ta kalleni
"Lafiya Sumayyah haka kikayi nauyin barci haka,sai Ahmad ya tashi su Rumaisa ke ko yama tasheki baki tashi ba"
Muryata a shaqe ta alamun wadda tasha kuka "wallahi Mama barcin ne ya kasa daukata saikace mai dannau"
Maman ta ce"Dannau din kuka ba,wallahi Sumayyah ki kyale mutane ubangiji ma baya iyama yawancinmu ki bar kowa da fahimtarshi ko da bahagon tunanin qiyayyarsa akanmu akan abin duniya da bamu dashi,Allahn da ya raba yaba kowa zai raba ya bamu idan yaso idan be so ba haka zamu faru mu tafi ba tare da hakan ba Kuma insha Allah dukkan jinkiri alkhairi ne"
Na jinjina maganar Mama dan kaifin basirar ta kasance mace mai shi kalamanta ga masoyi abun yadda ne da san jin tayi su,nidai nasan bata ta'ba nuna mana aikata mummunan aiki ba muna fama da yau da gobenmu ne muna barci da zullumin ya gobenmu zata Kaya zamu samu abinda zamu ci ko a'a ko sau daya zamu samu kawai shiyasa ba ma muda lokacin qulla wa wani wani abun bare musa ran dan aiken ya dawo kanmu kana girbar abinda ka shuka ne nake kallon abunda duk zaka shuka ne 'din,na ajiye tunani na ce"Mama kukan ai yana zama sauqi a kowacce zuciya ne akan quncin da ta riski kanta a ciki kuma da kunayi zaku samu sauqi a zuciyarku nasan kuna cikin shi duk da miqa lamura ga Allah ko ya ya za'a samu wani miki a zuciya ne na tunani"
Mama dai ta ce"cigaba da kukan ki idan hawayenki ya qare zaki bari,kuka ma aikine babu wanda yasan kinayi kuma ga mutanan da qiyayya ta shafe komai akanmu ba zaki samu sassauci ba"
Na ce ina miqewa"Mama Kuma ranar da kuka fara naku ba zan hanaku ba abunda kukeson yi tsawan shekaru kuka kasa sai a lokacin nasan zaku rage ra'da'din da zuciyarku takeyi" daga nan na fice yin alwala dan Kam gari ya waye ne danma bisa barci nayi rashin sallar lokacin duhun asuba,a dakin na dawo na sameta a falon da muke kwanciya ta zuba tagumi da hannu biyu ne har na dawo nayi sallar na idar bata ji ba sai da muka fara jiyo sallama naganta firgigit ta miqe tana dube dube tsayawa nayima kallonta ganin duk ta ki'dime na ce"Mama lafiya kuma?"sai sannan ta daidaita kanta ta ce"yawwa tashi su Rumaisa su fara fitar da kayan naji sallamar kamar ta Abbah Musa"Ni dai kallan ta nayi tana ficewa na girgiza Kai kawai wannan fitinar kam dole ta gigita mama din tashinsu nayi kawai na fara tashinsu.