Free chapter · Read without an account

CHAPTER 12 IDAN ME WURI YA ZO, DOLE ME TABARMA YA NAƊE

by Hassana Abdullahi Hunkuyi · SUN KASHE TA

BABI NA GOMA SHA BIYU

GIDAN RAMLA

Ramla, ta ci gaba da sauraron abin da mijinta ya ke faɗa ma ta a waya. "Wai ko bakya farinciki da dawowata ne? Sai na ga kamar ba ki yi zumuɗi kamar yadda kike yi a baya, idan na faɗa maki zan dawo ba."

Ramla ta yamutsa fuska, "My love, ka yi kuskuren fahimta, me ya sa za ka ce ba na farincikin dawowarka?"

"To ai ban ji zumuɗi ba ne a muryarki."

"Eh, lallai ba ka rajina yanzu, kamanta jiya na faɗa maka bana jin daɗin jikina. Allah kuwa ji na nake somehow."

"Eyya! Sannu gimbiyata, ki sha kuruminki idan na dawo gobe akwai albishir."

Suka aje wayar cikin barkwanci. To amma a ɓangaren Ramla, duk maganganun da ta faɗa wa mijinta, daɗin baki ne kawai, yanzu ya ya za ta yi da Izzatu? Dole ne Izzatu tabar gidanta a yau ɗinnan. To ina za ta je? Ta tambayi zuciyarta. Da wannan ƙalubalen ta sunkuci mabuɗin mota sai KASU.

A wajen mai siyar da abinci ta faka motarta, ta fito cikin sauri ta shiga shagon. tana ƙoƙarin tambayar Izzatu don ta kira wayarta ba ta shiga ba, to a lokacin ne Angela ta ba ta saƙon Izzatu. wato wasiƙar ƙaryar mutuwa. "Tun yaushe ta ba ki saƙon?” Ramla ta tambaya a Fusace. "Ɗa zu da safe, ta ce na faɗa maki ta kira wayarki ba ta shiga ba, amma da yamma za ta dawo." Inji Angela.

Ramla ta duba agogon wayarta, ta faɗa a ranta. 'Babu mamaki ƙila Izzatu ta koma gida ne.' Da sauri ta shiga mota ta dawo gida, to amma da ta tambayi mai gadi batun dawowar Izzatu, sai ya ba ta tabbacin Izzatu ba ta dawo ba. Don haka ta shiga cikin gidan gwiwa a saluɓe. Ta kalli falonta wanda, da ka shigo hoton Izzatu ne zai yi maka maraba. A da kuwa, hoton Aƙilu Maude ne wurin. Don haka ta ke Ramla ta cire haɗi da maye gurbinsa da na Izzatu.

To ga shi gobe Aƙilu zai dawo, dole ne kuwa idan mai wuri ya zo, mai tabarma ya naɗe. Ramla ta aje mayafi ta shiga aikin kawar da duk wasu abubuwan da Izzatu ta barbaza a gidanta don ta cire shakku da zargi daga ciki zuciyar Aƙilu. Duk wasu hotunan Izzatu da ta maƙala a falo da ɗakin barcinta sai da ta cire shi ta mayar da na Aƙilu a wurin.

Bayan ta gama kawar da komai, ta tsaya shiru tana tunanin mene ne kuma ya yi saura wanda ba ta kawar ba? Yawwa ta tuno da akwatin kayan Surayya Mustafa da Izzatu ta taho da shi. Ta faɗa a ranta.

'Dole ne in haɗa komai waje guda na bar gidan nan da shi, to ina zan kai ajiya?' ta saki ajiyar zuciya haɗi da ɗan sakin murmushi. Nan take ta kira mai gadi. Bayan ya zo ta nuna tsubin kayan dake gabanta ta ce.

"Amana zan baka ka ajiye mun, ka ga waɗannan tarkacen?” Mai gadi ya gyaɗa kai. "To, ka je da su gidanka ka aje a can ɗakin da kake ajiye hatsi, zan nema nan gaba. Sannan amana ce ba na son ka buɗe balle wani ya gani."

Mai gadi ya kwashi kaya jikinsa yana rawa ya bar gidan da su. To sai a lokacin Ramla ta ɗan samu natsuwa kaɗan, ta zauna tana ci gaba da neman wayar Izzatu, waje guda kuma ta ci gaba da saƙe-saƙen zucci. Haɗi da ƙirƙiro abin da za ta kare kanta da shi idan har aka yi rashin sa'a Aƙilu ya yi arangama da Izzatu a gobe.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol