Free chapter · Read without an account

Chapter 3

by HAFSAT USMAN WAZIRI · ALAQAR MU!

💋_ALAQAR MU💋_

         ~Our destiny ~


©️®️ _Hafsatouamjad_ 


Chapters 02 


    ✍️Ya kwashi ak’allah 30minutes azaune all this time Kallon ta yake bayaso ko kiftawa yayi , ahankali ta fara k’okarin bude idanuwanta da suka canza launi zuwa jaaa sun yi wani mugun kumbura ,hakan ze tabbatar maka da ba karamin kuka tayi ba , seda ta gama bude idanuwan nata akan celine din Asibitin ahankali ta waiga side dinta na hagu tana kara Lumshe idanunta , abunda ya faru ne ya fara dawo Mata cikin kwakwalwarta wani razanannen ihu ta saki daya janyo hankalin nurses din dake yawo a reception dakin suka nufo Da gudu ,Ganin Noorain akanta yasa nurses din suka bashi hakuri ya fita , Babu yanda ya iya dole ya fito adakin yana rike kanshi dake barazanar Cirewa .

Girgiza kanta take tana riko hannun nurse dinnan cikeda azaba da fargaba tace “Ka barni na tuba da zafi ,Dan Allah kayi hakuri karkayi “.

Abunda take ta fada kenan duk ta rikitasu ,lokaci daya tausayinta ya kama zuciyoyin su ,yarinya Karama da ita 

Da sauri suka kira babbar likatan ta shigo , allurar bacci ta Mata ganin taki dawowa hayyacin ta .

 Sauke numfashi sukayi atare lokacin da baccin ya fara dibarta ,ahankali ta Lumshe idanunta hawaye na gangaro Mata a side din idanunta . 


Doctor tana fitowa ta kalleshi tace “Munyi Mata allurar bacci ,ya kamata ka fadawa iyayenta halin da ake ciki saboda kula da ita dole se mace “.

Fitowa yayi daga asibitin zuciyansa duk babu dadi , koda ya koma gida be nufi part din Mommah ba ,seda yaje yakarayin wanka ya shirya sannan ya fito ganin lokacin xuwa office dinshi yayi . 


Seda ya fara tsayawa A kofar gidan su yai parking ya dade yana kallon gate din gidan sun yana nazari,Dole ya sanarwa da iyayenta sabida yasan komai rintsi zasu sani ,bashi da wani option dole ya fito daga Motor ya nufa kofar gate din cike da nutsuwa da kamalar shi .Knocking yayi a kofar tasu me gadin ya leko yana tambayar waye ,ganin Noorain Ne yasa me gadin ya fadada faraarshi yana cewa “Ranka shi dade ka shigo mana “

Babu musu ya shiga ya tsaya daga jikin kofar yace “Inason ganin Ammah Asmah ne “

“Toh Toh bara afada musu “

“Asmau mauuuu Ina kike “

Me gadin yake Dan raira wakar shi har ya shiga cikin dakin ,landline din dake jikin katangar dakin nashi ya latsa sannan ya kara a kunne 

Babu jimawa ya fito ya kalli Noorain yace “Ance ka shiga “

Godiya ya mishi yai cikin gidan gaban shi na faduwa ,harya manta Rabonshi da gidan .

Koda ya shiga parlour babu kowa tsit yake se Tv da take a kunne amman ko sounds babu , ga kuma sanyin da parlour ya dauka da kamshin Air freshner ,daya daga cikin kujerun parlour yayi ma kanshi maxauni ,ko minti biyu beyi ba Ammah ta fito sanye da babban hijjabin ta har kasa ,Ganin Noorain ne yasa ta fadada faraarta tana zama akan kujeran dake Dan nesa dashi tace “Noorain kaine yau agidan “?

Saukkowa yayi a kujeran yana gaisheta cikeda ladabi , amsawa tayi fuskanta awashe tana tambayar ya Maman shi dasu Mamah da Lafiya ya amsa sannan yayi shiru , sosai yake nazari bega wani alaman daze nuna mishi Ammah na cikin damuwa ba ,hankalin shi ya rabu gida biyu ,kallon shi Ammah tayi ganin kamar akwai alamun magana abakin shi tace .

“Ina sauraron ka Noorain “

Ammah ta katse masa Tunanin sa ,gyara zaman shi yayi sosai kanshi akasa yace “Dazu da safe na fito jogging naga mutum kwance akofar gidan nan ,naso na wuce amman ganin kamar mutumin yana cikin mawuyacin hali ne yasa dole na dawo abunda ya ban mamaki mace ce kuma Asmah ...”

Dagowa Ammah tayi da sauri tana kallon shi ,Murmushi tayi mishi tace “Aa Noorain Badai Asmah ba ,jiya ta tafi gidan kanwata dake kaduna zata Mata sati daya ta dawo gaskiya inajin kamace “

Ammah ta fada da confidence duk da hankalinta ya fara tshi ,duk wani abu da ze shafi Asmah yana damunta .

Sauke numfashi yayi yana nazari kafin yace “Ammah ba kama bace Asmah ce yanzu haka na kaita asibiti ,Zaki iya shiryawa muje ki ganta “.

Innalilahi wainnaillahi rajiun Ammah ta fada azuciyar ta , Da sauri ta tashi tace mishi tana zuwa daki ta koma ta daukko Wayarta da takalmi ta fito tana ce mishi su tafi , a compound suka hadu da Ansar da ya fito da shirin sa na zuwa aiki ,ganin Ammah a rude yasa ya karaso inda suke yana mamakin ganin Noorain tare da Ammah da sanyin safiyan nan .

“Ammah Lafiya kuwa “?

“Just follow me “.

Abunda ta iya fada kenan tabi bayan Noorain da ya kusa fita gate din ,Motor shi ya shiga yabi bayansu,duk yanda Ammah taso kada ta tada hankalin ta abun ya faskara gumi ne kawai yake zubo Mata Noorain yana lure da yanda hankalin ta ya tashi ,duk seyaji ta bashi tausayi .

Tafiyar 20minutes ne ya karaso dasu babban asibitin ,parking yayi ya fito itama Ammah ta fito ,Ansar ma da yayi parking Motor shi ya biyo su abaya .

Tun daga reception Ammah ta fara jin muryan Asmah tana kuka ,wani mugun faduwan gaba ne ya ziyar ce ta ,batabi takan Noorain ba tayi gaba da sauri tana bin direction din da takejin kukan , cikin dakin Ammah ta shiga hankalin ta a tashe abunda bata taba tunani ba da sauri tace “Asmah na “

Zabura Asmah tayi ta juyo tana kallon Ammah da gudu ta saukko akan gadon tayo kanta tama manta da ciwon dake jikinta burinta be wuce ta karasa wurinta ba , bude Mata hannu Ammah tayi ta fada jikin ta tana sakin wani Marayan kuka ,muryan ta ya dashe idanunta ko iya budesu batayi da kyau . 

Tsyawa Ansar yayi cak yana kallon Asmah ,Yaushe ta dawo daga kadunan? Me takeyi a Asibiti kuma ? 

Fita nurses din sukayi a dakin suka barsu su kadai , Ammah gaba daya ta kasa magana kukan Asmah yana ratsa Mata jinin jikinta , gashinta daya barbazu a fuskanta take ta matsar Mata dashi tana pating bayanta , 

“Ammah yaushe little ta dawo “?

Daga mishi Hannu Ammah tayi ,alamun yayi shiru .

A gefen gadon ya zauna yana zurawa Asma idanu har Yanzu kuka take . 

Sallamar likitan ne yasa suka dago ,Asmah na ganin likitan ta kara kankame Ammah tana cewa “Ammah mu tafi gida am scared “

Seda takai kunnenta saitin bakin ta taji abunda take fada 

Buga bayanta tayi tace “Oaky Yanzu zamu tafi don’t cry “.


Kallon ta Likitan tayi tace “Condition din yarinyar Ki is critical gaskiya ,you have to take good care of her nayiwa mijinta bayani daxu , mazajen yanzu ne sesuce zasu karbi hakkin su by force kuma ai ba haka tsarin addini yace ayi ba , Dan akaida se police sun shiga case din zaayi treating dinta tunda raping nata yayi ,bayan ya saka Mata desire tablet ga maganin bacci abun yayi yawa gaskiya “

Tunda likitan nan ta fara bayani Ammah wani razanannen tashi hankkai ya ziyarce ta ,innalilahi wainaillahi rajiun Ammah take fada Allah yasa abunda kunnuwanta suke fada mata ba daidai bane ,Allah yasa abunda takeji yanzun a mafarki ne Asmah ?Rape? Noo this is impossible yarinyar ta karama ?this can never happen to her love . 


“What what are you saying doctor ban fahimce ki ba ,Ni kanwata bata da aure fah “. 


Itama jiyowa tayi da sauri tana kallon Ansar jin abunda yake fada .

“Kaga look mutumin da kuka shigo tare shine mijin ta ,shiya kawota asibitin and yace Matar sa ce what are you saying now “?


Cikeda firgici Ammah tace “Yes mijin ta ne “.

Muryan ta na rawa akowani lokaci kuka xe iya kwace Mata . 

Kallonta Ansar yayi da sauri yana mamakin amsar da ta bawa doctor .

Ita kuma likitan cewa tayi “Okay Good amman she need to rest please and na rubuta magunguna na bawa mijin nata ze siyo nurse zatazo ta bata “

Gyada kai Ammah tayi likitan ta fita . 

“Ammah ban gane ba ,Bangane abunda kikacewa likitan nan ba and What’s wrong ? Nifa na kasa ganewa Naji tana maganar raping who and to who “?


“Look kiramin Hammad da Yusuf I need them yanzun”

Wayarshi ya dauka ya kirasun kamar yanda tace , shigowa Noorain da ledar magunguna nata ne yasa suka dago atare suna kallon shi ,karasowa yayi kusa da Ammah da take kuka yace “ga magungunan ta nizan tafi wurin aiki “.

Ajiye su yayi ya mike yayi hanyar waje “Noorain “

Juyowa yayi yana amsawa 

“Please let it be secret “.

Gyada mata kai yayi yace “Insha Allah “.

Sannan ya fita yanajin taysayin su gaba daya aranshi , in Banda abun Ammah taya ze iya tonawa Asmah asiri batasan iya adadin son da yake mata ba shiyasa ta fadi hakan .


Yana shirin fita yaga su Hammad sun shigo hankulan su a tashe basu lura da shi ba ,Dan Haka ya shige cikin Motor shi yabar asibitin cike da tunanin ta . 


Ansar ne ya fito ya shigo Dasu ,halin da suka tarar da Ammah aciki ba karamin daga musu hankali yayi ba ,agabanta suka durkusa dukansu suna tambayar abunda ya faru . 

Share hawaye Ammah tayi tace “Someone rape my daughter “

Kamar saukan Aradu haka sukaji maganr musamman Hammad ,azafafe ya mike yana huci yace “Ammah I didn’t get you “

“Hammad someone rape Asmah “

Ta fada a tsawace , Galala sukayi dukan su jirin da ya kusa dibarshi ne yasa ya nemi gefen gadon ya zauna da sauri yana kama kanshi . 

“Bansan wanene ba Hammad me Asmah tayi mishi da tayi deserving haka daga gareshi ? For the first time na kasa taimakon yarinya ta , I can’t control it ,I can’t help my daughter “

Abunda Ammah taketa fada kenan kukanta ya kara karfi , 

“Ammah yaushe ta dawo a kaduna ehh “?

“I don’t know Yusuf ,bansaniba “.

“I told you don’t let her go Ammah kikace waye waye yanzu look at what happen did she deserve this , koma waye behind this I promise to find him out Wallahi koda zan rasa Raina sena bima Asmah hakkinta this is not fear “.

Ya fada yana dukan table din da aka ajiye Mata magungunta atake kuwa suka rarrabe. 

“All this is not the case karku bari Abba ku yaji labari let’s solve it by our selfs,banson maganar nan ta fita kuma muddin kukace zaku dauki action akai mutuncin Ahalin mu ne ze zube shi kanshi wanda ze aure Yan fasawa zeyi my girl didn’t deserve this do this for her sake plaese “Jugum sukayi su dukan su kowa da abunda zuciyan sa yake fada mishi 

Duk abunda sukeyi Asmah na jinsu she just pretend to sleep but all she knows is kome zasu mata bazata fada ba 

“If you let anyone know this Wallahi Asmah sena kasheki har Lahira karnuka zan wullawa ke suyi yaga yaga dake sanann In haka rami in bunneki babu wanda ya sani it’s left to you in kinga dama go and tell that your brothers “.

Hawaye ne ya gangaro Mata tuna last maganar da ya Mata abunda take iya tunawa kenan warning dinshi ,bayan wannan she can’t remember anything.

Dagota Ammah tayi tana kallon yanda hallitar fuskarta ya canza tace “Asmah who did this to you “?

Girgiza kanta ta farayi cikeda tsoro tana kuka tace “Ammah I don’t know please let’s go home “

Tasowa Hammad Yaya ya karso kusa da ita yana riko mata hannu yace “Look princess you know we promise to take good care of you ? Gyada mjshi kai tayi yacigaba da cewa “Don’t cry i just want to ask you one question. “

Kuma gyada kanta tayi yace “Are you not in kaduna “?

Rufe idanuwanta tayi tana tuna lokacin da Sophia tace Mata ta rakata gidan sister ta zata karbi sako ,tunda tasha lemon da aka kawo agidan bata kuma tuna abunda ke faruwa ba . 


Gyada mishi kai tayi tace “Yes “

“Toh what happen ? Mesa kika dawo kano Anty Ni’ima tasan kin taho ne kedawa kuka taho “?

“I don’t know Yaya Hammad i just see me here “

Sakin ta yayi yana komawa jikin gadon ,jikin su duk yayi sanyi se Binta sukeyi da ido . Kowa da abunda yake sakawa aranshi . Tabbas someone is behind this but who ? 

“Ammah zanje gida “

Ta kuma fada da shakakiyar muryanta . 

“Hammad kacewa doctor ta bamu sallma she is not comfortable here “

Fita yayi babu jimawa se gashi ya dawo doctor na biye dashi , rubuta musu sallamar Tayi tana kara jama Ammah kunne akan a kuka Da ita a ringa shiga ruwan zafi kuma ta kula da Shan maganin ta If not everything will happen .

Insha Allah kawai Ammah tace Mata suka fito . Tana fara tafiya ta tsaya hawaye na saukko mata tacewa Ammah “I can’t walk Ammah “

Daukarta hammad yayi a hannu suka fita a asibitin ,Motor Hammad Ammah ta shig itada Asmah sukuma suka shiga nasu Motor suka biyo bayan su .

Koda sukaje gida Hammad dinne ya kuma daukarta,har cikin dakin Ammah ya kaita ya sauketa akan gado Ammah na bayansu da Yusuf da Ansar .

Ammah ce tace musu kowa ya tafi wurin aiki ,kar su wani tada hankalin su she will be okay .

Babu yanda suka iya haka suka fita ,kowa na tambayar Asmah mexe taho mata da shi kallon su take tana Murmushi tace “Ice cream “

Seda kowa acikin su ya Mata peck a Kumatu suka shafa kanta sannan suka tafi , bayan fitar su Ammah da kanta ta shiga toilet ta hada Mata ruwan dumi ,wani farin abu ta daukko acikin drawer ta ta zuba , kamata tayi suka shiga toilet din da kanta ta cire Mata Rigan asibitin tace Mata “Sit karkiyi kuka “.

 Gyada kai tayi tana zama acikin bath din ,ihu ta saki tana ruko hannun Ammah dannata tayi aciki tana tausarta seda tayi good 5minutes sannan ta kuma sake Mata wani ruwan Seda ta Mata sau uku sannan ta Mata wanka da ruwan zafi sosai Kallon cikinta Ammah take Ganin yanda yayi jaaa harda yagushi ga wurin nan yayi alamun ciwo,idanunta ta sauke akan madaidaitan boobs dinta da nipples din nata sukayi jaaa sun kunbura kai hannu Ammah tayi zata taba wurin yagushin da sauri ta zabura tace “Noo Ammah it hurts “

Wani tausayinta ne ya kara lullube Ammah koma waye wannan ya cika mara Imani da tausayi Allah baze barshi ba towel ta bata ta daura suka fito. Ajiyar zuciya ta sauke sosai taji dadin jikinta kuma ciwon nata ya dena Mata zafi se abunda baa rasa ba ,Ammah da kanta ta hada Mata tea me kauri ta bata sannan ta zubo Mata taliya da miyan hanta , taci abincin sosai duk da bakinta babu dadi . Seda ta shafa Mata magani awurin tace karta saka pant yanzu ,iya doguwar riga kawai ta bata ta saka da under siket. Sallahn asuba da batayi ba Ammah tasakata tayi ,ta dade tana addua tana hawaye sannan ta tashi Ammah ne ta nade sallayan tace Mata ta hau gado tayi bacci . 


Aikuwa kwanciyar ta keda wuya bacci yayi gaba da ita , 

Da Magrib duka suka dawo seda sukayi wanka dukan su suka shigo side din Ammah as usual kowa da tsarabn da yayiwa Asmah ,a parlour suka tarar da su itada Ammah Dan bataso tabar wata kafa da ze saka ta damuwa shiyasa bata barinta ita kadai , Seda suka yi hugging nata suna tsokanar ta tanata dariya kowa ya bata Tsaraban da yayi Mata .

Wayan Ammah ne yayi ringing ganin bakuwar number ne yasa tayi picking tana karawa a kunne,daga can bangaren Dadyn Sammad yace “Hello kina magana da Baban Sammad “

Murmushi Ne ya bayyana akan fuskan Ammah tace “Eyyah barka da dare mun wuni lafiya “?

Cikeda gadara yace “Lafiya ,ba wani magana me yawa bane yasa na kiraki “

Dan canza fuska Ammah tayi jin respond dinsa tace “Okay inajin ka “

“Yaro nane yazo min da wata magana yace shi fa ya fasa auren Asmah ,na tambayeshi dalili yace kawai ta fita a kanshi ne kuma ni gaskiya bana tauye ‘yayana kuma bana musu dole a dukan lamuransu musammman Sammad duk wani abu da yake so shi nake so saboda shine farin Cikina bazan iya mishi dole ba akan farin cikin yar ku,so shine nace let me let you know good night “.

“What”?

Ammah ta fada tana mikewa jikin ta Banda rawa babu abunda yake , 

Mikewa sukayi suma dukkansu suna kallon Ammah 

“What’s wrong Ammah “?

Da gudu sukayi kanta ganin ta tafi da baya zata fadi .



Wanene yayiwa Asmah fyade? Kuma menene dalilin shi ? Meyasa Sammad ya fasa auren Asmah ? Mexe faru idan Asmah taji labarin Sammad ya fasa auren ta ? Meze faru da Asmah anan gaba ? Duk amsoshin ku suna cikin Wannan littafi kamar yanda kuka sani wannan yasha banban da sauran ,ku biyo alqalamina Ina maraba daku masoyana.



Wannan littafin na kudi ne it’s just 500 for enquiries contact me via *** ina maraba da masu sharhi.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol