Free chapter · Read without an account

Chapter 1

by Sadiyamuhammadnasir · Mugun gani


Wata Kyakykyawar Budurwa ce kwance Akan Makeken Gadon ta, wacce bazata wuce shekara Ashirin da Uku A Duniya ba, kunnen ta makale da waya! kana ganin fuskarta kasan Tana jin dadin hiran da take..


Karan murda handle din kofa taji, A hankali ta maida idanuwarta wajen "Baby ina zuwa please. katse wayar wayar tayi gamida duban Wacce tabude kofar.


"Fadila lafiya? ya naga fuskarki A turnuke? maiya faru haka?"


Wacce Aka kira da Fadila, nan take fuskarta ta kara nuna tsananin damuwa, waje ta nema ta zauna gamida share kwallah.


"Aunty Sadee sam Abba yakasa fahimtar Maganata, Wannan dama ce da idan ta kubcemin wallahi bazan sake samu nan kusaba.


Karatu A nesa ba shine yake nufin idan naje bazan rike tarbiyata ba, Pls Aunty Sadee ke kadaice nake da tabbacin idan kika tunkari Abba da wannan Maganar zai Amince"


Karashe maganar tayi tare da goge Hawayen daya fito mata, wanda yasa Farin fuskarta ya canza launi izuwa Jaa, Ajiyar zuciya Sadiya tayi "Shikenan Fadila kidaina kuka insha Allah zanyi iya bakin kokarina don ganin Abba ya Amince da wannan kudirin taki, maza share hawayenki"


Murmushi tayi "nagode Aunty Sadee shiyasa nake Kaunarki A Raina"


"Bakomai muje dama nagama Abinda zanyi A dakin, so nake na shiga Kichen na shirya wani Abu, Sarkin naci yana hanya bayan Magarib, yacemin Abincin shi yana wajena" mikewa sukayi gaba daya suka fito Babban Palon Gidan.


Fadila kuwa cikin Ranta haushi taji, domin sam bata Kaunar wannan Sadeeq din, domin daga ganin shi zaiyi rawan Kai, gashi Aunty Sadee ba cikakken lafiya gareta ba, tsoronta karya Aure Auty sadee yaje yayita kuntata Mata, har yayi sanadiyyar karasa mata zuciyar.


Wata Matace zaune A daya daga cikin Manyan kujerun da suke Palon, Matar zata iya Kai kimanin shekara 50, Hanunta rike da wayar Saka, tana kokarin kammala Hulunan sanyi na Yara da takeyi.


Gaba daya suka zauna A gefenta tare da dubanta "Ummi ke Kullum baki gajiya da wannan wahalar? haba Ummi so kike idanunki su sami Matsala ne?" dago ido tayi ta dubesu.


"Meye Abin wahala kuma A jikin saqa? naga dai A zaune nake" dafa Kafadarta sukayi "Ummi duk da haka kina hutawa" dariya tayi "toshikenan bakomai naji" mikewa Sadiya tayi "Ummi barin shiga Kichen Sadeeq zan dafawa Abinci, yana Azumi kuma Anan zaisha ruwa"


"Okey to shikenan bakomai" wucewa tayi ta bar Fadila da Ummi suna hira, Abinci mai sauki ta dafa mishi, sai wajen karfe 5 kafin ta kammala, dakinta ta shige ta nufi toilet tayi wanka, Wata Material Marown Colour ta saka, wanda Akayi mata doguwar Riga, yalwataccen gashinta ta tufke ta dauki Mayafi ta yafa.


Sai da ta tabbatar dagama shirya komai kafin ta dauki wayarta, Dialling number Sadiq tayi, Ringin biyu ya dauka "Hello honey...fatan kina lafiya?" cikin sigar shagwana tace "Alhmdullah Baby, zaka iya zuwa nariga na kammala komai"


"Okey Honey shiyasa nake Kaunarki, kina kulawa da Al'amura na, gani Akan hanya insha Allah"


"Shikenan sai kazo take care" kashe wayar tayi tare dayin murmushi.


Sadeeq kuwa saida ya tsaya yayi Sallah kafin ya nufo Gidansu Sadiya, Maigadi da sauri ya bude mishi Motor "Ranka shidae barka da zuwa" dan Murmushi Sadeeq yayi "barka Baba, ya iyalan?"


"Alhmdullah Mungode Allah" kudi ya zaro A cikin pejeon_hole ya mika Wa Baba, godiya sosai yayi sannan ya wuce da Motor, saida yayi parking kafin yayi dialling Number Sadiya, A hankali ta dauka "Honey gani A harabar Gidanku"


"Okey Baby gani zuwa" cikin takunta ta nutsuwa tafito waje, tun daga nesa Sadeeq yake sake mata Murmushi, jin zuciyar sa yake fes, domin Yana tsananin ji da sadiyar shi, sannan yana Mutunta soyayayyarta.


"Muje ko?" binta yayi A baya kamar Jela, yana mai kare mata kallo, A haka har suka nufi Karamin Saet Room da Abba yake zama da Baki, da kanta tayi sarving Sadeeq, zama tayi ta kura mishi idanu har ya kammala cin Abincin.


Saida yasha Ruwa kafin ya dubi Fuskarta "My Wife ina sonki, bazan iya Rayuwa ba tare dake ba, A kullum kwanan duniya Soyayyarki kara rikitani take, Saukowa yayi gamida durkusa A gabanta, kura mata idanu yayi, wanda yasa Sadiya saukar da kanta Qasa, sakamakon irin Kallan da Sadeeq yake mata, gaba daya fuskarsa ta zama Abin tausayi.


Furxar da wani iska mai zafi yayi tare da sake kura wa Kyakyktawar Fuskar Sadiya idanu "Please Sadiyatee ki dago idanuwarki ki kalleni, hakan shizaisa ki tabbatar da Abinda yake cikin zuciyata, A hankali ta dago ido ta dubeshi, Please Sadeeyati ki tausaya wa Rayuwata ki Amince min A wannan Karo na turo su Dady suzo su nema min Aurenki, idan ba hakaba ina gab da Haukacewa, please Honey" 


Kura mata idanu yayi yana mai sauraron Abinda zatace "Baby mike ka zauna please, A hankali ya zauna yana fuskantarta, Baby nima ina so na Aureka kaima shaidace, kasan lalurar da nake fama da ita, ina gaban su Abba Amma hankalinsu yana tashe, to inaga idan nayi Aure? kana tsammanin zasu sami nutsuwa?"


"Sadiyatee ke kanki shaidace bayan Ummi da Abba duk duniya baki da masoyi kamata, ina da tabbacin yanda su Ummi zasu rikeki nima haka zan rikeki, sabida lalurar da take damunki shiyasa kullum burina bai wuce naga kin zama mallaki na ba, please kiyi nazari Akan Maganata"


"Shikenan Baby bakomai zanyi tunani" hira suka cigaba dayi har wajen karfe tara kafin ya mata sallama ya tafi, saida taga kulewarshi kafin ta shiga cikin Gida, Ganin Abba ya dawo yasata karasawa cikin Palon, yana hangota ya saki Murmushi.


Zama tayi A Qasa gefen Kafarshi "barka da dawowa Abba nah?" shafo kanta yayi "Barka Sadiya kina lafiya?"


"Alhmdullah Abba"


"Masha Allah, shuru tayi nadan wani lokaci, Abban ne ya juyo ya dubeta, lafiya kalau kuwa Sadiya?" 'Dan gyara zama tayi "Abba na ina neman wata Alfarma A gareka, Abba Dun Allah kayi hakuri kabar Fadila taje Makarantar nan, Fadila Yarinya ce mai nutsuwa da kamala, bana shakku Akan bazata iya rike kanta A Makarantar ba, please Abba"


Kallon idanunta yayi da suka kada sukayi jazur, Ajiyar zuciya ya sauke "Sadiya bawai bani farin ciki da Abinda Fadila ta samu bane, ni kaina zanso tasami wannan Kwali, Amma tafiya karatu har Cairo? duk fadin Nigeria Ace babu Makarantar da Fadila za tayi sai tabar Kasa?"


"Abba kayi hakuri, shekara 3 ne, kuma na tabbata baza kayi nadamar tura Fadila wannan waje ba, Abba Karancin Ilimin yara Mata tayi yawa A kasar mu, Mu samman wannan Course da Fadila zatayi, babu Mata, idanma Akwai to ba Yaran Hausawa bane.


Kuma sabida hazakarta shiyasa Govnoty ta dauki nauyinta domin zuwa wannan Kasa don karin fasaha, Dun Allah Abba kayi hakuri"


"Shikenan Sadiya zanyi tunani idan na yanke hukuncui zaku jini" Kama kafafunshi tayi "Nagode Abba Allah yasa muji Alheri, mikewa tayi Abba na saida safe" Murmushi yayi Mata "saida safe Sadiya, ina fatan kinsha Magani?"


"Abba zansha da zaran na koma dakina"


"Shikenan mukwana lafiya" Dakin Ummi ta wuce, tana Zaune A bakin gado rike da remote tana kallo "Sadiya kin shigo?"


"Eh Ummi nama tsayane wajen Abba shiyasa kikaga jumawata"


"Eyya to yayi kyau ya Sadeeq din?"


"Lafiya kalau Ummi yace ingaisheki"

" Allah sarki to ina Amsawa"

"Ummi barinje na kwanta saida safe"

"Shikenan Sadiya Allah ya miki Albarka ya kuma baki lafiya" Murmushi tayi "Ameen Ummi" 


Dakin Fadila ta nufa tana rike da systerm tana dube_dube "Aunty Sadee kin dawo?"


"Eh Fadila nadawo, karatu Akene?"


" Eh Aunty ina neman wani Abune"


"To Allah ya taimaka, zama tayi A bakin gadon, Fadila munyi Magana da Abba yace zaiyi nazari Akan bukatarki, Amma inaga baza'a sami matsalaba" rufe systerm tayi tare da duban Sadiya "Kai Aunty sadee Amma nagode miki ban san meye zance ba, Allah ina so naga na zama daya daga cikin Manyan masu Tonon Anfanin dake cikin Qasarmu, shiyasa tun ina Secondary school nake burin na karanci Geollogy"


"Allah Sarki to Allah ya baki nasara Akan Abinda kikasa Agaba, ni barinje na kwanta Gobe Tuesday kinsan ina daganin Doctor"


"Hakane to Allah ya nuna mana" ficewa tayi A dakin ta nufi dakinta, sai da tayi shirin barci kafin takira wayar Sadeeq, Kusan sau Biyu tana kira bai dagaba shiyasa ta kashe. murmushi tayi "Allah sarki May be ya gaji hala yayi barci" Rufe idanunta tayi cike da tunanin Masoyinta har barci ya dauketa.


Sadeeq kuwa bayan fitarshi daga Gidan su Sadiya, Masallaci ya nufa yayi Sallah, bayan ya dawo Motor ne yaga misscall biyu na Khalil, tsaki yayi gamida kiranshi "Haba Sadeeq ina kaAje wayar ne? sai kira nake ba'a dagaba"


Tsaki Sadeeq yayi "kaifa kana da matsala wallahi, shikenan bani da Abinyi sai danna waya? to Ina sallah ne, maiya faru?"


Okey dakyau, kaima kasan zancen Gizo baya wuce na koqi, Zuby ce ta dagamin hankali da waya, Akan nakiraka tayita kiran wayarka baka daukaba, ta cemin tana kofar Gidanka yanzu haka" 


Dogon tsaki Sadeeq yayi "Khalil Yarinyar nan fa bata da hankali, wai tsaban wulakanci ni zata kalli idona tacemin muyi Aure? to meye zan Aura Anan? Yarinyar data gama watsar da kanta A wajena" Dariya Khalil yayi "Kai kuwa Abokina meye A ciki? inhar tana yi maka yanda kake so ka Aure ta mana?"


"Mtsww Kai dai bazaka taba gane meye Ake fada maka ba, sauran wani zan Aura? kaima kasan A lalacenta muka hadu, Allah kadai yasan yawan Mazan da tayi Mu'amala dasu kafin ni, don haka kabar wannan zance, Abinda take so dai bazan daina Bata ba, tunda nima ina So"


Dariya Khalil yayi "Kai Abokina wallahi baka da dama"


"Kaga Mallam barin karasa Gidan na sameta, dama A koshe nake dam..." Bushewa da Dariya Khalil yayi "Abokina kana Abinda kaga dama, sai da safe Asha soyayya lafiya" Kashe wayar Sadiq yayi ya kara Gudun Motor.


A kofar Gida ya sami Zuby tana zaune ta zuba tagumi kamar wacce Aka Aiko mata da sakon Mutuwa, tana ganin Motor Sadeeq ta mike jiki na rawa ta isa wajen, bude mata kofar gaba yayi ta shiga! kafin ya fito A ciki ya wangale Gate din Gidan...

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol