Free chapter · Read without an account
Chapter 6
Abdul salam Musamman yaje ya sami Inna Mariya Akan ta nema mishi wacce zata taya Zaliha zama sabida kar Haihuwa tazo gashi babu kowa shikuma yana Makaranta, shiyasa ta kira wata Yar_uwarta tun daga Gombe tazo domin taimaka musu, wato Inna Hussaina.
Wata Rana Zaliha tana zaune tana sakar kaya data saba Abdul ya shigo gida Hankalin shi A tashe, kana ganin fuskarshi kasan yana cikin wani yanayi mara dadi, yanayin shi data gani yasa jikinta yin sanyi.
Daki ya nufa ta bishi A baya jiki A sanyaye, Murmushi yayi mata wanda ya tsaya iya fatar baki, tare da bata Umurnin zama kusa dashi, Nasiha yayi mata sosoai Akan tawakkali da irin juriyar da Akeso Musulmi yayi idan wata Masifa ta kunno mishi, sai da ya tabbatar ta karbi jawabansa hanu biyu kafin ya shaida mata Allah yayi Rasuwa wa Mahaifinta.
Abdul_Salam yana gama isar da wannan Mummunar Sako' taji kamar An muskuleta A cikinta, kafin tayi wani yunkuri ciwo ya kara tsananta, ganin haka yasa Abdul mikewa A kidime ya tallafota tare da kwala wa Baba Hussaina Kira, babu bata lokaci suka nufi da ita Asibiti.
Inna Mariya ya kira Akan tazo su taimaka mishi su zauna ita da Baba Hussaina koda Abinda za'a bukata, domin yana so ya sami jana'izar Surukin nashi, da Gaggawa ya nufi tasha ya hau Motar Azare, yana hanya suka kirashi Akan Zaliha ta sauka ta sami Yarinya Mace.
Murna sosai yayi, bayan Ankai Mahaifin Zaliha Gidan shi na gaskiya! nan yake shaida musu Aita sauka, An sami Yarinya, Addu'a sosai sukayi Ubangiji ya daiyyaba ya kuma bata lafiya.
Zaliha kuwa tana Haihuwa ta fashe da wani irin kuka tunowa da tayi da Abinda ya sameta, Hakuri Inna Mariya suka cigaba da bata daga bisani Aka sallamesu sabida babu wata Matsala data samu.
Bayan sun dawo Gida ta daga hankali Akan za taje Azare, Inna Mariya ce ta kira waya ta shaidawa Abdul Abinda yake faruwa, hakuri yayi ta bata Akan ta bari zuwa gobe kafin ta huta, Amma ina gaba daya ta rikice mishi shiyasa ya Amince da bukatarta.
Babu bata lokaci Inna Mariya ta kimtsata suka fito tare tayi tasha su kuma suka nufi gidan Hajiya Mairo, A haraban Gidan ta sameta tana shan Iska, Nan take shaida mata zancen Haihuwar Zaliha da Mutuwar Mahaifinta.
Kallon Raini ta bita dashi, daga bisani tacigaba da fada' inda take shiga ba tanan take fitaba, domin A cewarta Ai Munafurci ne wannan, Matar Abdul ta Haihu Ace A bakin Inna Mariya Akaji.
Shiyasa taki kiran Abdul tayi mishi Barkatu bare ta'aziya, ko Alhaji Ali ma itace ta hanashi zuwa Azare, domin sun kirashi A waya sun shaida mishi Zancen Mutuwar, shikuma yace musu yana tafe Insha Allah.
Bayan Anyi kwana Uku da Rasuwar Baban Zaliha, shi yayi dai_dai da Kwanakin Haihuwar Yarinya, Nan Abdul ya rada mata sunan Mahaifiyar Zaliha wato Sadiya, sosai sukayi murna da wannan ba zata daya musu, musamnan Zaliha dako hiran baitaba yimata ba, A Ranar ya kama Hanya ya dawo domin cigaba da Karatu.
Ta bangaren Mai jego kuwa' ko taron suna ba'ayiba saka_makon Mutuwar da Akayi, duk da Babu taron Suna haka Hajiya Mairo ta hana kowa Na gidanta zuwa duba Zaliha da Yarinyarta, Abin yayi wa Abdul ciwo Amma ya daure ya shanye.
Bayan sunyi kwana 40 Zaliha ta dawo Gidanta ita da Baby Sadiya, Bayan dawowarta da kwana biyu ta zauna da Abdul ta sanar dashi irin yawan dukiyar data samu, sannan suyi shawarin yaya za'ayi su juyata ya habaka suma su dogara da kansu, Hakuri ya bata Akan ta bari yayi nazari sosai domin sanin wata irin sana'ah zasuyi.
Hakan kuwa Akayi sai da Sadiya tayi kusan wata Bakwai kafin Abdul ya taso da Maganar, Kasuwancin Abinci yace tayi tunda Allah yayi mata Ilimi Akan hakan, da yardan Allah kuwa Abubuwa suka karbu, Ya kaima ko biki Ake ko suna za'a nemeta domin ciyar da jama'a.
Kafin wani lokaci Kasuwanci ya karbu sosai, nan danan dukiya ta cigaba da Yawaita, Hajiya Mairo kuwa sam ta fita harkansu saka_makon Abinda Abdul yayi mata na fifita Inna Mariya Akanta.
Ko Gidan yaje bayi ganin Fuska, shiyasa daya gaisheta zaifito Abinshi, kusan A tare su Iman suka kawo Mijin Aure ita da 'Yan_matan Alhaji Ali, shiyasa Aka tsaida lokacin Bikin tare, kuma lokaci kankani, dake Mazajen nasu duk Yaran Masu hanu da shuni ne, babu batun Rashi A ciki.
Biki Nagani na fada Aka gudanar, Zaliha kamar ba zata taje ba, Abdul ne ya takurata, haka ta dauki Sadiya suka nufi gidan, tun shigarta Hajiya Mairo take binta da Mungun Kallo, durkusawa tayi har Kasa ta gaidata, nan Hajiya Mairo ta cigaba da surfeta ta yanda take shiga ba tanan take fitaba, Akan tazo bikin Gaiyyar sodi.
Hakan yasa Zaliha kasa jurewa ta rufe idanu tayi rashin Kunya wa Hajiya Mairo, harda Goranta musu Akan Ai Dukiyar Mijinta ne suke wadaka dashi, kuma su jira sakayyar Ubangiji.
Ba karamin Sanyi Jikin Hajiya Mairo yayi ba, haka Zaliha ta dau Yarta suka bar Gidan Rai A bace, Hajiya Mairo kuwa har Aka gama bikin Hankalinta bayi kwance, burinta taje A buga mata A kasa A sanar da ita ta yaya Zaliha tasan wannan boyayyen Al'amarin.
Zaliha kuwa sam taki sanar wa Abdul wannan zance, iyaka tayi karyan ciwo Akan bazata iya karasa zuwa hidimar Bikin ba.
Hakan kuwa Akayi bayan Ankai Yaran gidan Mijinsu, Hajiya Mairo ta niki gari ta tafi har Kasar Niger, nan ta sanar da Mallaminta duk Abinda Ake ciki, ya jima yana surkulle kafin ya sanar da ita, kan cewar A Gidanta Aka labarta mata wannan zance, Amma ya kasa gane Macace kona Miji.
Cike da kunar Rai ta dawo Bauchi, nan zarginta ya sauka Akan Inna Mariya, domin babu wacce xa tayi wannan Barakar sai Ita.
Aikuwa ta nufi dakinta ta hauta da fada, Akan Ita Munafuka ce, waye ya sanar da ita dukiyar Abdul suke Anfani dashi dahar xata sanar da Zaliha.
Tsoro da Mamaki shiya kama Inna Mariya domin zaliha bata kyauta mataba, sai da tace kartayi hira ma wani, Ashe A banza har Agaban Hajiyar ta fada, wani Abin takaicima tace mata itace ta fadi.
Haka ta durkusa har Kasa tacigaba da neman gafara, Amma Ina haka Hajiya Mairo taki saurara Mata, nan danan ta bata Umurni cikin Minti 10 ta kwashe komai nata tabar Mata Gida kafin ta tara Mata jama'ah.
Cikin tashin hankali ta mike ta hada dan tarkacenta ta fito tana Kuka mai tsuma zuciya, ko Naira daya Hajiya Mairo bata Ajiye mata Akan ta sami na Motor ba, tace Munafurcinta ya kaita Gida.
Haka ta fito cikin tashin hankali tama rasa ina zata je, Unguwar su Abdul ta nufa ta tsaya jikin wani shago ta rakube tana jiranshi yazo shiga, domin takaicin Zaliha bazai barta ta shiga Gidan ba, sai wajen karfe Biyar kafin Abdul ya dawo, Aikuwa da gudu ta nufo inda yake.
Cike da Mamaki yake kallonta domin bai taba ganinta cikin wannan yanayi ba, sannan kuma ga kaya A hanunta, kukan data fashe dashi yakara gaskatar masa da babu lafiya, bakinsa yana rawa yafara tambayarta maiyake faruwa, ganin ba zatayi maganaba yasa shi jan hanunta zuwa cikin Gidan.
Zaliha da Sadiya suna zaune A Falo suna cin Abinci sukaji shigowar su Inna Mariya, gabanta ne taji ya fadi ganin Inna Mariya tana kuka shar_shar da Hawaye, A kidime ta mike ta rikota izuwa kujeran dakin.
Dakyar suka iya jan hankalin Inna Mariya harta tsagaita da Kukan da takeyi ta basu labarin Abinda ya faru.
Jikin Abdul har Rawa yake sabida tashin hankali, Zaliha kuwa kasa Magana tayi, baki na rawa ta tsuguna ta fuskanci Inna Mariya tare da Rantsuwa Wa Inna Mariya tare da shaida mata gaskiyar yanda sukayi da Hajiya Mairo.
Ajiyar zuciya kawai Inna Mariya ta cigaba da saukewa, ba karamin fada Abdul yayi wa Zaliha Akan shiga Abinda bai shafetaba, gashi ta jawo wata Matsala ta daban, duban Inna Mariya yayi tare da rokonta Akan ta zauna dasu idan ba zata damuba.
Amma ina ta turje Akan sam hakan bazai yuyuba, babu yanda za'ayi ta kara musu nauyinta bayan tasan bayi dashi, kuma ya zama dole ta koma wajen 'Ya'yanta, dama can suna kewarta babu yanda zasuyi ne kawai suka hakura.
Sosai Zaliha taba Inna Mariya Hakuri, bata bar taba har sai da ta tabbatar da cewa Inna Mariya ta sauko kuma ta fahimce ta, Sai da Inna Mariya ta kwana biyu kafin Abdul yadauketa tare da Zaliha suka Rakata Gombe.
Karba na Karramawa Akayi musu, nan Aka gama karewa Hajiya Mairo tanadi, tare da Addu'ar Allah ya tona Asirinsu, sai yamma lis suka kamo hanya suka dawo Bauchi.
Haka Rayuwa tacigaba da kasancewa, sati yazo ya wuce! wata tazo ta wuce, shekara tazo ta wuce, A wannan yanayin Abdul da Zaliha suka sake haihuwar Yarinya
Nan taci Suna Maryam za'ana kiranta da Fadila, A lokacin Abdul ya kammala Karatun shi, da ikon Ubangiji kuwa ya samu Aiki karkashin wani Bawan Allah dake Companyn shinkafa, har zuwa wannan lokacin babu Abinda yake hada Abdul dasu Hajiya Mairo kowa ta kanshi yake, ya kaima yanzu ko zuwa Gidan ba yayi sabida mungun karban da Akeyi mishi.
Abdul ya samu karbuwa A wajen Maigidan nashi, Alhmdullah kafin kace meye dukiya sai kara hauhawa take, ga Zaliha tana kan kasuwancin Abinci, A haka har suka biya kudin Aikin Hajji suka tafi domin sauke Farali, zaliha da Sadiya kuwa Gidan Mannir Aka kaisu dake yayi Aure shima A garin Bauchin, sabida kar A katse musu Makaranta da cewa sukayi Azare zasu tafi.
A Saudi Hajiya Mairo taci karo da Zaliha, ba karamin tashin hankali ta shigaba, ganin Zaliha A Saudi, gashi da ganinta tana cikin kwanciyar hankali, tayi kiba tayi fari, Abundai sai wanda ya gani, bata tsorata ba saida ta gansu da Abdul watarana, nan hankalinta yayi Mungun tashi.
Bayan Sun dawo takira Mallaminta ta shaida mishi meye Ake ciki, nan ya shaida mata kaf Abida yake Akwai, Abdul mai Qashin Arziki ne matukar suna tare da wannan Ubangidan nashi tofa nan gaba saiya basu tsoro, domin jinin shi mai karfine Akan Mutane.
Jin wannan bayani yasa Hajiya Mairo tsayawa sosai har saida ta gano komai game da Abdul da Ubangidan shi, Nan tacigaba da Aikinta na Munafurci da shiga da Fita wajen Mallamai har sai da ta hada Abdul da Ubangidan shi ya koreshi, tare da yi masa Mungun Asiri, babu ta yanda zai sake samun Aiki makamancin wannan bare yayi tsammanin kara Azurta.
Abu kamar wasa, duk inda Abdul yaje neman Aiki baya samu, da kyar da Addu'a Allah yasa yasamu wani Karamin Ma'aikata ya fara zuwa, duk da Albashin babu yawa Amma bai hanashi daukar dawainiyar iyalanshi ba, dake Allah yasa mishi Albarka.
A haka Rayuwa tacigaba da kasancewa har Su Sadiya suka shiga Secondary, A wannan lokacin ne Allah ya jarabci Sadiya da ciwon Zuciya, ba karamin wahala suka sha da ita ba, kamar baza tayi Rai ba, Amma da taimakon Allah data Hajiya Zali Aka samu Aka fita da Sadiya kasar waje domin neman lafiyarta, Watan su Biyu suka dawo, cikin hikimar Ubangiji kuma ta sami lafiya dai_dai Gwargwado.
Nan Aka daurata Akan Magani da ganin likita duk bayan wata guda, tare dabin ka'idojin hana damuwa shiga Zuciyar tata, Ba karamin Kashadi Alhaji Abdul_Salam yake wa Fadila ba, Akan ta kiyayi duk wani Abinda zai bata Ran Auntyn Nata, shiyasa take nan_nan da ita don ganin Farin cikinta, ko Aina bata bari wani yaci zarafin Sadiya ta barshi.
Haka Rayuwa tacigaba da kasancewa har su Sadiya suka shiga Ajin Karshe, wato SS3! A lokacin Fadila tana Aji Hudu! wato SS1, A wanna lokacin suka hadu da Sadiq Masoyinta.
Wata Rana sun fito ita da Fadila suna neman Abin hawa A kofar Makaranta suna hira basu kula da Motor A gabansu ba, kiris ya rage A kadesu, nan ya fito daga Motor yafara Zazzaga musu Tsiwa kamar zai cinyesu! Akan Rashin kula da basuyi A gefen Hanya, yanda yake musu yasa Sadiya fashewa da Kuka sosai, ganin haka yasa Fadila cire Hijabi tasha dammara tacigaba da Surfa tijara iri da Kala, tare da shaida mishi! Matukar yayi sanadin tashin ciwon Auntyn nata, to sai Allah ya saka musu.
Mai makon yaji haushin fadan da Fadila takeyi! saima yaji tausayin Sadiya dukya kamashi, take yaji Kaunarta ta shiga Zuciyarshi, Musamman jin Abinda 'yar_uwarta take fada game da ita.
Ya jima yana Kallonta kafin yayi Ajiyar Zuciya, Ahankali ya furta, Allah Sarki gata da karamin shekaru Amma Allah ya jarabceta da ciwon Zuciya Mai tsanani.
Durkusawa yayi har Qasa ya cire Hanky ya share mata Hawaye tare da bata hakuri gamida zuba Mata idanu kamar zai cinyeta.