Free chapter 路 Read without an account
Page 6
by BIL-SAN 路 WASU MAZAN
FREE
_Page 6_
*WASU MAZAN!*馃挃
_written by_
*BILLY S FARI*馃拵
*漏锔廐ASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕*
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A
______________________________
Ganin yaqi saurarenta yasa ta fashe da kuka cikin d'aga murya tana fad'in,
"Don ALLAH Yaya Ali kada kaje, tuni nariga dana miqawa ALLAH duka lamurrana akan yaran nan, hatta Shurieym ma ya zab'a masu kulawar ubangiji fiye da tawa, don haka ka qyalesa tunda zab'in da yayiwa rayuwarsa damu kenan"
Runtse idanuwa yayi yana jin kukan nata har tsakiyar ransa had'e da juyowa a fusace yayo kanta kamar zai daketa, ya ce
"Idan kika cigaba da wannan nan kukan naki komai zan iya zuwa nayi masa, qarshe ma zan iyasa qararsa kotu har sai ya bada yaran nan ko yana so ko baya so"
"A'a Yaya Ali, ai bama biye mashi ba, duk abunda zai yi ai mahaifinsu ne shi kuma 'ya'yansa ne, yana sane da yanda nake matuqar son yarana da kuma basu tarbiya shiyasa ya riqi wannan son da nakeyi masu a matsayin makamin da zai yi amfani dashi wajen tarwatsa rayuwata, ni kuwa na d'aukarwa kaina alwashin saina nuna masa cewa don nabar yarana a hannunsa bazai hanani cigaba da rayuwa kamar kowa ba, haka ma bazai kashemun zuciyar kasa yin walwala da farinciki ba, duk abunsa dole dai nice mahaifiyarsu, kuma duk inda za'a je adawo nasan zasu nemeni da kansu watan wata rana, Yaya Ali don ALLAH kabani damar nunawa WASU MAZAN kuskuren tunanin da sukeyi akan cewa don macce nada 'ya'ya bazata iya haqura tabar gidansu ba ko samun natsuwa idan bata tare dasu"
"Bazaki iya ba Batulu"
"Zan iya Yaya Ali, wlh zan iya, zan jure sosai na kuma zamo abur d'aukar darasi ga 'yan uwana mata"
"Shikenan, amma kiyi shiru hakan, kin sani tun kina qarama bana jurewa ganin kukan nan naki Batulu balle yanzu da kika girma har da tarin 'ya'ya, in Sha ALLAH zan lallab'asa kamar yanda Adda tace koda Shurieym d'in ne da Jawad ya baki, hakan yayi maki ko?"
"Eh Yaya Ali, nagode da kulawarka sosai" ta fad'a tana share hawayen dake kwance saman fuskarta, ajiyar zuciya yayi tare da sakar mata murmushin da yafi kuka ciwo, don gaba d'aya wannan abun ya bala'in qona masa zuciya fiye da tsammani,
Sake juyowa sukayi suka dawo suka zauna inda Adda take ta rabka uban tagumi sukaci gaba da tattauna yaushe ya kamata aje kwaso kayanta, inda ta roqi Adda akan aroqa mata Ahmadi ya bawa yaran d'ayan d'akin da yake ajiye mashin d'insa da sauran komatsai a saka masu katifarta ta gado da kayan kallonta da sauran abubuwan da zasu iya buqata, sauran kuma sai a kwashikke su.
Haka kuwa akayi, washe gari Adda ta tura maqwaftanta da wata 'yar gwaggonsu da tazo daga qauye da ya Ali akaje kwaso kaya, cikin sauqi Ahmadi da sai faman gyaran d'aki akeyi ana fenti ya amince da zancen baiwa yaran d'ayan d'akin yace zai maida mashin d'insa a store don dama baya so su takura amaryasa, Amma fa d'akin akwai inda ba'a rufe ba, in ruwa yazo zai iya shigowa kuma shi yanzu baida kud'in gyarasa don bata tasu yakeyi ba, wannan maganar ta qarshe ce ta qona zuciyar ya Ali amma duk da haka ya daure cikin taushin murya ya sake bijiro masa da roqonsa na biyu akan ya taimaka yaba Batulu koda Hisham da Jawad ne, ai kuwa kamar jira Abban shurieym keyi ya lailayo ashar ya tule yana zage zage wai shi babu ub**n daya isa ya rabasa da 'ya'yansa tunda ba rasa mai kula masu dasu yayi ba, gobe gobe za'a kawo wacce zata kula masa dasu fiyema da yanda mahaifiyarsu keyi don haka babu wanda zai bada acikinsu, shi ba shashasha bane balle yazama mijin tace sai yadda macce ke so zeyi mata.
Wud'annan maganganu su suka harzuqa ya Ali shima ya bud'e masa wuta had'e da gaigaya masa maganganu masu d'aci suka rabu baran baran kowane cike da haushin d'an uwansa, wannan abun kuma ya b'atawa kowa rai dake anguwar ciki kuwa har da masu kwashe kayan suka bar gidan cikin b'acin rai da tausayin halin da rayuwar yaran zata kasance, inda wasu ke ganin ya Ali bai kyauta ba wasu kuma ke ganin rashin kyautawar ta Abban shureym ce, dama abunda Adda ke gudu kenan kuma gashi ya faru.
Bayan sun koma gida Adda taji abunda yafaru fad'a tayita yiwa ya Ali sosai tare da nuna masa illar rashin sauraren abunda ta fad'a masa da yayi, don kuwa Ahmadi bai raga masa ba ko susar akaifa, ya fad'a masa maganganu masu zafi akan cewa shi ba lalatacce bane irinsa da zai zauna ba aure ba 'ya'ya don mace ta mutu tunda ba bakin uwa ne dashi ba, koda mutuwa Batulu tayi ita da yaran hakan bazai hanasa aure ba don ya samu wasu 'ya'yan,
Ba abunda yafi qonawa Adda Rai irin kalmar tinda ba bakin uwa ne da shiba, kenan yana nufin shi Aliyun nata bakin uwa ne dashi?, hakan yasa fad'anta ya qara tsananta akan rashin auren da ya Ali ya qiyi, gashi yau har yaja ana goranta masa had'e da jifarsa da miyagun kalamai, fashewa tayi da kuka tare da cewa,
"Shi kenan Ali sai kayita zama hakan ana cigaba da goranta ma, tunda kaga bana son takura maka, yau da inada wasu yaran nasan ko kayimun hakan su bazasu yimani ba, zasuyi iya qoqarinsu wajen faranta mani"
Da yake zuciyar mazan tahau baice komai ba sai daya sauka zuwa marece bayan sallar magrib yazo ya bawa Adda haquri tare da yimata alqawarin zai nemo matar aure nan da qanqanin lokaci, idan kuma baiyi hakan ba to yabata dama ta nemo masa duk wacce taga ya dace, zai sota kuma ya zauna da ita, fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa masa tare da roqa masa ALLAH ya zab'o masa tagari wacce hankalinsu zai daidaita ya amsa da amin,
Ya jima agidan suna d'an tab'a hira kafin can ya miqe yaje cikin motarsa ya d'auko naman kazar daya siyo masu da lemu ya kawo masu sannan ya wuce gidansa dake can anguwar samaru don ba wani nisa ne tsakaninsu ba.
***. ***. ***
A b'angaren Abida kuwa da Baban Jamila kullum tozarci da qasqanci sai dad'a qaruwa yakeyi agareta, haka ma yaranta gaba d'aya anbi an takurasu, zagi da hantara kai kace ba gidan ubansu bane,
Kukan yau daban na gobe daban ga cikin jikinta sai dad'a qara girma yakeyi abunda ke ciki na neman fitowa waje, yauma kamar kullum tana kwance kan gado ita da 'yan biyunta Hasin da Hasina ta tasasu agaba sai sharqar baccinsu sukeyi hankali kwance, yayin da Shakur da Shukura ke kwance a can qasa saman katifarsu suma suna baccinsu, ita kuma kwance kawai take baccin yaqi d'aukarta saboda azabar ciwon naquda dake damunta, tun tana jurewa har ta soma gajiya, tashi tayi ta shiga safa da marwa a tsakiyar d'akin bakinta na jero addu'o'in da tasani tana mai neman agaji da kuma taimakon ALLAH akan ya dubeta da idon rahama ya sauketa lafiya acikin d'akinta, tunda take haihuwa bata tab'a shan wahala irin wannan ba, hatta tasu 'yan biyu ta samu sauqi sosai fiye da wannan don batafi awa d'aya tana naquda ba ta haifesu, amma wannan tun wayewar safiyar yau take abu d'aya gashi har yanzu qarfe uku na dare ba batu ba tsammani kuma tana jin haihuwar zangu zangu tamkar za'ayi amma abun ya cutara,
Ganin haka yasa cikin qarfin hali tana cizar baki tafito daga cikin d'akinta ta nufi na Dije, a hankali ta shiga qwanqwasa qofar don ta sheda masu halin da take ciki amma sai da tayi mintuna biyar tana qwanqwasa basu bud'e ba, ko motsinsu ma bata jiyowa balle tasa ran zasu taso su bud'e, cikin wata irin azabar zafin naquda ta doki qofar da qarfi tana fad'in,
"Dije, Baban Jamila, don ALLAH ku taimakeni"
A firgice duk suka miqe har baban Jamila na birgimowa daga saman gadon had'e da fad'owa qasa, duk da dama kowanensu na jinta tun d'azu sukayi kunnen uwar sh**gu da ita dole su firgita yanda sukaji ta doko qofar da qarfi ba tare da sunyi tsammanin hakan daga wajenta, basu ba hatta maqwabta sai da sukaji sautin qarar qofar tare da shiga firgici,
Tsaki Dije taja cikin b'acin rai had'e da cewa,
"Wannan wane irin bala'i ne haka!, to wlh kaje ka dakatar da ita don ni in naje ba maikyau za'ayi ba, yo ni na aiketa da zata zo ta isheni ta takura rayuwata a cikin wannan tsohon daren? To kasa tabarmun qofar d'aki kafin taqarasa hasalani" Ta qare zancen had'e da komawarta kan gado tayi kwanciyarta tana ci gaba da balbala masifa,
"Yi haquri Dije" ya fad'a tare da zuwa bakin tagar d'akin ya hankad'e labulen dake wajen cikin kaushin murya da rashin tausayi yace,
"Wai meye haka Abida, baki san dare mahutar bawa ne ba da zaki zo ki ishemu ki ishi maqwabta, Ina dai haihuwar nan ke kika saka kanki ba wani ya saki ba? Don haka kijeki har ALLAH ya saukeki lafiya tunda kince kin ji kin gani"
"Haba Baban Jamila, don girman ALLAH ku taimaka mun ku kaini asibiti, a wannan karon gaba d'aya qarfina ya gaza ina buqatar taimakon likitoci kafin na iya haihuwa da kaina"
"Abida likitoci? Asibiti? A ina?, Badai a gidana ba ko? Ai kema kinsan bazata sab'uwa ba bindiga aruwa, kije ki haqura in zaki haqura ni bacci nake ji" ya ja labulen tagar had'e da barin wajen, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata had'e da fashewa da kuka tace,
"Kaji tsoron ALLAH Baban Jamila, ya zakayi da haqqina Dana d'an dake cikina idan muka rasa rayuwarmu, ALLAH fa zai tambayeka!"
"Kyaji dashi, ni dai babu wata asibiti da zan kaiki ayo mani tatare-tataren kashin kud'in daya fi 茩arfina ina zaunena lafiya" ya fad'a daga cikin d'aki yana gyara kwanciyarsa a saman gadon daya koma ya kwanta.
*ALLAH KAJIQAN IYAYENMU 馃憦*