FreeArewaPen original
WASU MAZAN
- 1views
- 41chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuciya manazarciya.
Sample · Page 1
WASU MAZAN!written byBILLY S FARI💎©️HASKE WRITERS ASSOCIATION💡Duk'e take a qasa tana kuka irin kukan dake bayyanar da tsantsar tashin hankalin da take ciki, tsananin kukan da takeyi ne ya haifarwa da muryar tata daqushewa izuwa shaqaqqiyar muryar daba lallaine ka iya jiyo kome take fad'a ba, duk dako qoqarinta wajen ganin ta jiyar da sautin nata izuwa ga wanda shine ya zamo silar faruwar kukan nata akoda yaushe,"Haba Abban shurieym, wannan wace irin masifa ce haka?, wace irin rayuwace kake neman jefamu a ciki ni da yaranka?, Kaji tsoron ALLAH Abban shurieym katuna cewa ni amanarka ce kuma tsakanin ni dakai akwai ranar da ALLAH zaiyi hisabi ga duk wanda ya cuci wani acikinmu, na roqeka a matsayina na matarka kuma uwar 'ya'yanka kaje tausayin mu ni dasu koda kad'anne acikin zuciyarka,Wani irin wurgo kwanon tasa daga can cikin d'aki wanda take kira da Abban shurieym yayi har takusa dakar mata goshi yana ci gaba da watso sauran kayan nata dake cikin d'akin har ya gama watsosu waje tsaf tare da jawo qofar ya kulle da makulli yana fad'in,"Kin gama Batulu? Nace kin gama?" Yaqare maganar yana shuri da wasu kayan dake gabansa cikin zafi da kuma b'acin rai, a tsorace taja baya tare da mammaqe jikinta waje d'aya tana k'walla, kafin ta ankara taji saukar wani abun a goshinta sakamakon shuri da wasu kayan nata da yayo ashe tasar dake cikine ta daki goshin nata ya fashe saiga jini ya fara zuba, 'yar qara ta saki saboda tsananin zafin data jiya tana fad'in,"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Abban shurieym ka fasamun goshi" ba tare daya damu da halin da take ciki ba yaja tsaki had'e da nunata da yatsa Yana fad'in,"kad'an ma kika gani Batulu, Wallahi tallahi yau ko mutuwa zakiyi dole sai kin bar mani gidana tunda bana mahaifinki ne ba!, banda baqin Hali da baqin naci irin naki, nifa ke auren nan kuma nace na gaji bazan iya ba amma kin zauna kina faman yimun magiya tare da b'ata lokacinki a banza a wofi, sai kace anfad'a maki cewa dole sai dake ne zan rayu, ko kuma anayi dole" Cikin kuka tana dafe da goshin nata tace"A'a, ko d'aya ba'ayi dole Abban shurieym, amma ina so katuna alqawurran da kayi mani acan baya, katuna irin so da kuma qaunar da wannan batuluwan taka tayi maka, katuna tsantsa halacci da irin zamantakewar da mukayi dakai! Yanzu idan kace na tafi na barmaka gidanka a ina kake so naje? Ina zan tafi nabarka da yarana fisabilillahi?, Wazai kula mani dasu idan bana nan?, Ya rayuwarsu zata kasance idan ka saka nayi nesa dasu?, Meye zai faru da tarbiyarsu a bayan idonuwana? Shurieym, Sudeis, Bilal, Hisham da kuma Jawad har yanzu dukansu qananan yara ne, gaba d'aya basu gama sanin ciwon kansu daidai ba balle su iya kula da junansu yanda yakamata idan na tafi na barsu, Abban shurieym na roqeka don ALLAH kabarni na zauna da 'ya'yana na rayu dasu koda kuwa...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.