Free chapter · Read without an account

Page 4

by Faiza auwal · ALKAMA BISA DUTSE

*ALKAMA* *BISA* *DUTSE*


*ANFA*


*4*


K'arfe takwas taji Ana sallama a bakin k'ofar kwangon dasuke ciki.

Dasauri tabud'e ido tatashi zaune tana mamakin wane irin baccine sukayi haka.

Mayama datake tashin wuri yau tunda takwanta Bata farkaba tunda ba wani sanyi akeyiba .

zanin tayafo tafito bakin k'ofar taga isiya atsaye da d'an fara'a afuskanta tace.


"Isiya muntashi lafiya?ya iyalin ,harkafito kenan.

"A nafito wlh anty ELA inasone mufara zuwa asibitin mudawo sai inbud'e shago.


"toshiken Bari mud'an kuskure Baki sai mufito mitafi.


"To Bari inje inkawomuku ruwan bunu da biredi daruwa ko bokiti d'ayane saikud'an watsa ,Amma inda zaasami ruwan zafi dazakud'an had'a kuyi wankan saboda ad'ankwai sanyi duk da basosaibane.


"A a karka damu isiya ruwanma ahaka yayi ,ai basabon abubane wanka da ruwan sanyin balle muce zai mana illa.


"Toshikenan Bari inje inkawo.

Daga haka yajuya yatafi .

Ciki Takoma tatadda Maya tatashi saka makon d'an kwanan da Isa yasa aka bugamusu saboda ruwa saman gefenshi ya d'aga ,ranan datashigo ta haske fuskanta yasa tatashi.


"Yauwa beauty tunda kintashi zo inwanke Miki Baki muyi wanka mutafi asibiti.

Baki ta turo idonta yayi narai narai da hawaye Alamun kuka takesonyi.


"To haka zamuje bamuci komaiba bake kikace mutum beshan magani beci komaiba ?


"To idan likitan yabaki magani yazakiyi Kisha bamuci komaiba.


Ahankali tamatso jikinta tace"kawo kunnenki kiji .

Duk'owa tayi takawo kunnenta bakin Maya saijitayi tace.


"Muje shagon isiya irinnajiya mugaisheshi yak'arabamu abinci tunda ai jiya barok'onshi mukayiba ,kince Kar insake indinga rok'o Amma inan bani indinga amsa Amma indinga kawaici ko?"


Kallonta ta tsayayi batasan sanda murmushi ya sub'uce mataba Wai ita Maya zatama wauyau.


Suna haka isiya yayi sallama ,dagudu Maya tayi k'ofar kwangon tana ganin isiya ta kofin d'an jug ahannunshi da biredi da bokitin ruwa sai murna da tsalle.


Dariya isiya yayi yace,Maya y'ar kyakkyawar mamanta zoki amsa biridin kikai ciki Dan bazaki iya d'aukar ruwan bununba .


Amsar biredin tayi ELA tak'araso tana cewa.

"Sannu isiya baka kajiya dawahala munatasaka hidima .

"Bakomai anty ELA Bari inje bakin shago wani na jirana inkungama saiku k'araso tawurin muwuce.


"To isiya Allah yataimaka saimunfito ,jiyowa yayi yama Maya magana Ina harta wuce ciki ,murmushi kawai yayi yajuya yatafi Yana bala'in San yarinyar baitab'a ganin yarinya maishiga Rai irin mayaba.


Komawa ciki ela tayi tasameta harta bud'e biredin tanaci ,zama tayi kusa da ita tad'auki jug d'in ruwan zafin tazuba ak'aramin cup d'in daya had'o musu dashi acikin ruwan wanka.

Ruwan zafin tazuba, Maya zata d'auka tace "kibari yahuce dazafi karki k'ona bakinki.


shagwab'e fuska tayi ta b'ata rai zatai kuka ,da ELA taga haka saita sa Baki tana hura mata ,Yana d'an Shan iska ta mik'a mata itakuma tafarashan nacikin jug d'in.


Suna gamawa taciremata riga tajawo d'an k'aramin sosansu dasabulun wanka tarik'o hannunta suka fito cikin langalangar tamata wanka ta lullub'eta da zanin datake yafawa takaita cikin y'ar rumfar tashafa mata Mai tamaida mata rigarta.


Zanin ta d'auka itama tazaga cikin bayan kwangon tayi wankanta sharp sharp tafito itama tamaida kayanta tarik'o hannunta sukayi shagon isiya."



Suna Isa tasameshi zaune abakin shagon Yana jiransu ,Yana hangosu ya mik'e da biscuit a hannunshi Yana y'ar dariya yace.


"Maya ga biscuit d'inki ,dasauri ta amsa tana washemishi fararan hak'oranta both sides na cheeks d'inta na lotsawa .


"Kuma Baki iya godiya in anbaki abuba ko?

Dasauri tace "nagode uncle isiya Dan mom d'inta tahanata Kiran sunan duk Wanda yagirmeta Dan hakan rashin girmamawane.


ahaka suka k'arasa bakin titi suka tari napep d'in dazai kaisu asibitin mariya dake cikin hayin malan bello.


Suna sauka isiya yaciro kud'i yana me adaidaitar suka shiga cikin asibitin 


wurin siyan Kati suka nufa yace anty ELA kizauna muje mubud'e kati.


 Yana rik'e da hannun Maya yanufi record office d'in ya yatadda mutum uku Saida suka d'an jira sannan layin yazo kansu yaciro dubu d'aya yabayar yafad'i details d'in unguwansu yabada phone number nashi yayi aka bud'e musu katin.



Saida sukayi zaman awa d'aya da y'an mintoci sannan layin ganin consulting ya iso kansu .

Ana kiranta tatashi tacema isiya yarik'e Maya barita fito.


Kujeran ganin doctor ta zauna tana facing d'inshi .


"Good morning doctor.

"Good morning, meyake damunki?


" da daddare nikan d'an kwanta da fever.

Sannan ina ganin jiri musamman idan nawuni zaune band'an mommotsaba.


Tana magana doctor narubutu,d'agowa yayi da kyau yakalleta yace."


 

"Have you noticed your heart beating quickly than normal?


Kai ta d'aga kishi ahankali .


"Gaskiya kinkamu da heart palpitation,Amma bawani abun tashin hankali bane zamu d'oraki kan medication inkikakiyayi zakiji sauk'i kidawo nolmal kamar Baki tab'ayiba harda depression dayamiki yawa.


"so pls koma meyake damunki kirageshi for your healthy life .

Kodan y'an uwanki da yayanki dazasu shiga damuwa idan suka rasaki please u should seriously take note about dis ba abunda yakamata kiyi wasa dashibane life d'inkine.


"Insha Allahu zankiyaye doctor nagode sosai.


Magani yarubuta mata ta d'auka tafito tana mishi godiya.


Tana fitowa isiya yace "anty ELA me doctorn yace ke damunki?


"Bawani abubane isiya zazzabine nadare danake fama dashi,shine yarubutamun magani.

Amsar takardar yayi yanufi pharmacy ya Basu ,amsa sukayi sukaduba sukacemishi dubu goma .


Ela dake gefe tanaji ta k'araso tace.

"Dan Allah isiya abar siyan maganin Nan yayi tsada dayawa .


"Bakomai anty ELA ciwo ai yawuce wasa konawane Dole akashe anemi lafiya ,bansaniba kotaimakonane Baki so .


"Shikenan nagode sosai isiya Dan bataso suyita ja'inja tunda Basu Saba hakan dashiba.


Kud'in dazaije kasuwa ya mik'a musu ya amsa ledar maganin yarik'o hannun Maya suka fito daga asibitin sukasami adaidaita tamaidasu d'anbushiya inda suke zaune.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.