Free chapter · Read without an account
51&60
*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*
*BOOK TWO*
_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_
_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_
_Ban yarda yan audio su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! ***_
***
*51-60*
Jum!Wasi tayi tana kallona tama kasa yin Koda motsi,wai Ahmad nike so,so fa to wani irin so nike mashi?shin anya kuwa ba hannu Ahmad ya saman ba,ya za'ayi zance Ina son Ahmad bayan nasan waye shi,nasan k'asungumun dan'iska ne mazinace dan tasha,gaskiya ruwa baya tsami banza akwai wata a kasa ,banza bata kai zomo kasuwa girgiza ta nayi Ina kwabe fuska nace.
"Haba mana Wasi ya na kawo maki damuwata kin kuma sani gaba baki ce komai ba sai kace kin samu tv." Sauke ajiyar zuciya tayi tana cewa.
"Dole na zarara maki Ido Hauwa,abun naki ne ai naga kamar bana hankali ba gaskiya."
"Kamar ya ba na hankali ba?ni karda nayi kuka dan Allah ki bani shawara mafita nike nema,wallahi ji nike Ina sonshi fa." rintse idonta tayi tana bude shi tana cewa."Hauwa kanki d'aya kuwa."? D'aga mata kai nayi Ina cewa."kwarai kuwa ras nike."girgiza ni tayi tana cewa."Anya kuwa kanki d'aya Hauwa'u Abdullah jibir." Full name dina ta fada,sake d'aga mata kai nayi kawai bance mata komai ba,itama bace man komai sai da ta kusa 10min sannan ta fara cewa.
"Tambaya d'aya zan fara yi maki anan,Hauwa mai kika gani a wajen Ahmad da har kika ji kina son shi."? Dan shuru nayi Ina duba character dinshi,sai kuma nace.",Gaskiya ni babu nidai kawai hakanan naji sonshi fa." Murmushi tayi tana kama hannuna tace."Dan Allah Hauwa ki rufamana asiri ki fidda son bawan Allah nan a zuciyarki,Kinga dai bai da hali ke infact ba sai na tsaya gaya maki waye shi ba kinsan dai waye shi baku dace da juna ba sam,karda ki biye ma so ki dawo kina da na sani,ki zab'a ma yaranki uba nagari dan Allah."
Shuru nayi kawai Ina kallonta,jikina mutuwa yayi da tace na zab'a ma yarana ubana ma gari karda na biye ma son zuciya,yanzun idan na auri Ahmad ya dawo yana aikata halinshi ko kuma yayi fiye da haka.duk abunda kayi sai anyi ma naka kenan duk wanda Ahmad yayi ma fyade sai anyi ma yaran da na haifa dashi!?zuface ta keto man take naji ya fice man a rai,dan inason yarana suyi alfahari da uban da ya haifesu,ba suyi kuka da dana sanin haihuwarsu ba.
Cigaba da cewa Wasi tayi.."tun wuri kiyi ma kanki karatun ta natsu ki watsar da soyayyar Ahmad tun dare baiyi maki ba wallahi,bance kiso Yaya Auwal ba tunda baki sonshi ba'a dole shima nasan ba zaiso ki aure shi baki sonshi ba, dan haka sai ki natsu kiyi mashi magana ta hankali ki nuna mashi ba zaki samu damar aurenshi ba dan baki sonshi ba,yayi hakuri Allah ya bashi wata,kema yayi maki addu'a Allah ya baki wani haka ya dace kiyi a gani na."
Murmushi nayi Ina cewa."Allah ya zab'a mana abunda yafi alkhari,Wasi ki sani zan bar Ahmad ba dan ban son shi ba,zan barshi da zab'a ma yarana ubana na gari,shi kuma Yaya Auwal maganar gaskiya Wasi na kasa jin sonshi a zuciyata da gaske nike maki,dan haka bayan bikin Yaya Teemarh zanyi magana da shi zan gaya mashi gaskiya kawai karda a kama wasa babu murmushi."
Furzar da iska tayi tana cewa. "Allah ya zab'a mana abunda yafi alkhari,sai dai ba zan boye maki gaskiya ba Hauwa,naso ki da Yaya Auwal naso ace kin zama mallakin shi *DA'IMAN ABADAN* ,ba dan komai ba sai dan kyaun halayenshi da natsuwarshi da kirkinshi,Hauwa wallahi banson kizo daga baya kina cizon yatsa na rashin mutumin kirki,nidai da zaki bi shawarata da kin kara bashi dama kin gani ko zuwa gaba za'a dace banson ayi lost din mutumin kirki irin Yaya Auwal gaskiya."
Kina da gaskiya Wasi,nima bansan mu rasa Yaya Auwal,amman maganar gaskiya na kasa nayi nayi na saka sonshi a zuciyata,amman zuciyata taki amincewa da hakan in shaa Allah Wasi hakan zai zama alkhari dan inaji a jikina,dan kullun cikin rokan zabin Allah muke daga mu har iyayenmu dan addu'ar iyaye bata faduwa kasa banza."
In shaa Allah Hauwa,bakomai na fahimceki Beb na kuma gane inda kika dosa Allah ya baki wanda ya fishi Beb ,shima Allah ya bashi Wanda ta fiki." Murmushi kawai nayi Ina kallonta tabbas nayi sa'ar Kawa Wanda ta damu da dani,Wanda ta damu da rayuwata ta keson cigaban rayuwata,tabbas nima sai na saka mata da hallaci sai na sakata kukan farinciki da yarda Allah,yanda take man fatan dace duniya da lahira nima haka nike mata.
Na dad'e a gidan su Wasila Muna fira,nida ita mukayi girkin gidansu shinkafa da miya da kifi mukayi,sai salad da muka yanka tare muka ci sanann na wuto gida,dan bansan mangariba tana man a waje gashi mangariba din ta kawo Kai.
Bayan nayi sallama da Mami sannan na fito ta rakoni tsada nayi daga bakin zauren gidan Ina cewa. "Barshi iya nan,rakiyar ta isa haka na yafe dai yau ba sai ankaini har gida ba."murmushi tayi tana cewa."Aa dan Allah Hauwa ki bari to ko wajen gidan su Tata na kaiki to." Girgiza kai nayi Ina yin gaba nace."aifa!sai fa kiyi bye sai mun hadu Monday dan gobe ba zan shiga school ba gaskiya tunda daman ba wani abu za'ayi serious ba."
"Ok amman maiyasa ba zaki je ba."?waigowa nayi Ina ce mata."saboda gobe Yaya Muhammad zai dawo kuma gobe Yaya Auwal zai shigo zance."
"Okay fine,Allah ya kaimu goben lafiya a gaida Mama." "Zataji in shaa Allah Bye."
Koda na koma gida ban taddasu a parlo ba,da yake lokacin sallah yayi nasan sun shiga ciki dan yin sallah,mazan kuma sun wuce massalaci dakinmu na shiga Ina shiga ta tadda Meenat ta fito wanka sannu da dawowa tayi man,na ansa Ina shigewa toilet nima wanka nayi na fito na shirya cikin gown english wear ce har kasa,hula na saka sannan nayi sallah Ina gamawa na zauna nayi azkar na daura da karatun quri'ani ban fito parlo ba sai da nayi sallar isha'i sanann na fito,Ina fitowa sai da na fara wucewa kitchen na zubo abincin dare,tuwon shinkafa sukayi da miyar danyar kubewa da naman sa.
Zama nayi Ina cewa."barka da hutawa Mama." Kallona tayi tana cewa."ai nasa can zaki kwana, ban hanaki kai dare waje ba."? girgiza kai nayi Ina cewa."wallahi tun kafin maganriba na shigo gidan nan,lokacin da na shigo kin shiga ciki na kowa a parlorn amman tambayi Meenat ita ai ta ganni ko."?
Daga Kai Meenat tayi tace."eh Mama,Ina shirin yin sallah ta shigo itama."
"Okay ai nasa shigar yin sallar isha'i ne kika shigo,da sai ranki ya b'aci wallahi." Sauke ajiyar zuciya nayi Ina cin tuwo na,sai da na cinye na maida plate din kitchen sannan na kalli Mama ina cewa.
"Mami na gaidaki."
"Ina ansawa,fatan kin barosu lafiya."?
"Lafiya lau Alhamdullahi,Mama gobe da kamar yaushe Yaya Muhammad zai iso."?dan shuru tayi,sannan tace." Gaskiya sai cikin dare,Kinga yace karfe shidda na maraice jirginsu zai sauka a kano sannan kuma tara na dare jirginsu zai tashi daga kano zuwa nan gusau,Kinga at least ya iso goma ko."?
Daga Kai nayi Ina cewa."hakane Allah ya maidoshi lafiya,Ina ta missing din Yaya Teemarh wallahi ana dai birinn kebbi." Murmushi Mama tayi tana cewa."aikuwa ana birnin kebbi daga zuwanta har Hajia Aisha ta fara yi mata dilka, daman nasan za'a rina dan Hajia Aisha ba daga baya ba wajen gyaran jiki."
Dan tabe baki nayi Ina cewa."gaskiya ne Yaya Teemarh a jikata asha,Momy da kanta take mata gyaran amaraici gaskiya ne haka nan take borin bata zuwa,ashe Momy ma ta shirya ma zuwan nata."
Girgiza kai Mama tayi tana cewa."ai daman kune baku fahimci halinta ba,dan Hajia Aisha tana da kirki bata da matsala barta kawai da shariya wanann halinta ne,amman bata da damuwa Sam."
Hakane kam,Allah ya Kara hada kanmu,yauwa Mama gobe in shaa Allah Yaya Auwal zai zo in shaa Allah."
Kallona Mama tayi tana cewa.."kuma shine baki gaya man ba sai yanzun."?kasa nayi da kaina ina cewa."yi hakuri Mama Ina son gaya maki wallahi na manta sai da naje su Wasi na tuna shiyasa." Daga Kai tayi tana cewa.
"Okay Allah ya kaimu goben lafiya,Ina ruwan Auwalu yaron kirki ba dai ruwanshi." Murmushi nayi Ina cewa."Aiko dai Mama,Allah dai ya zab'a mana abunda yafi alkhari."
Murmushi Mama tayi tana cewa."Amin!Kulu kenan ,kedai har yanzun baki son Auwalu ko?Allah sarki Auwal wallahi har tausayi yake bani bawan Allah yana son maso wani,dan Allah Kulu gaya man wai wa kike so har haka da har kika ki Auwal."?
Girgiza kai nayi nace."ko d'aya Mama,ni banson kowa da dai Ahmad naji inaso kuma na barshi saboda wasu halayen nashi mararsa kyau,amman wallahi nidai bansan ya zanyi da Yaya Auwal ba bani sonshi da aure gaskiya da zaiyi hakuri da ya daina zuwa wajena nikam dai."
Kuraman Ido Mama tayi,sai kuma can ta girgiza kai tana cewa."Allah sarki kurrici dangin hauka,kowa ya gama yarinyata lafiya aimai barka,shikenan ba zan maki dole ba Kulu sai dai da ace Saddiqa babba ce ta isa aure wallahi sai na ba Auwal ita a madadinki Kulu,saboda yaron kirki ne shi da kuma ace ba'a bada Meenat na ga Abbas da na ba Auwal ita a madadinki Kulu,sai dai ni yanzun banda budurwar da zan bashi sai dai zan cigaba da yi maku addu'a ku dukanku Allah yayi maku zab'in kwarai."
Jikina yayi sanyi sosai, tabbas Mama tana son hada zuri'a da Yaya Auwal,banga lefinta ba ko gangancinta saboda shi mutune na kwarai da kwarai yana da kirki kam da natsuwa,amman ya za'ayi qaddara ai ta riga fata da ace zan iya da na aureshi ko dan farincikin Mama da ma su Meenat da Wasi,sai dai wallahi ba zan iya ba sam,nidai bansonshi haka nike ji a raina bani sonshi ban iya aurenshi ko dan na aureshi ba zan mashi biyaiyar aure ba gaskiya.
Nidai shuru nayi bance komai ba,sai kasa nayi da kaina kawai dan bansan mai zance ba,Yaya Bash ne yace.
"Jiddah."
Dagowa nayi Ina kallon shi can nace."Na'am." Cigaba da cewa yayi. "Ba zamuyi fosing dinki ba muyi maki dole,duk yanda zamu so ki auri Auwal idan har baki so hakura zamuyi mu daura maki wanda kike so Jidda,sai dai Ina son na ankarar dake wautar da kike kokarin tamkawa Jidda zaki yi ganganci idan har kika sallami Auwal ,wa zaki kama idan kika Kori Auwal?duk cikin samarinki banga kamar Auwal ba,naji kince Ahmad Bala ko."?
Nidai bance komai ba sai Meenat da tace."Nima haka naji tace Yaya Bash." Murmushi yayi yana cewa."ai Ahmad ba sonki yake ba,daman zuwa yayi ya cuceki kuma kika tsallake rijiya da baya baya,da ace yana sonki Koda ba da gaske bane zai aureki ya cima wani guri nashi wallahi sai ya sako manyanshi sun nema mashi izini kamar yanda dokar gidan nan take,da yake babu Allah a ranshi ta bayan fage yake maki magana,shin ya tab'a ce maki zaizo gidanku zance."?
Girgiza mashi Kai kawai nayi.cigaba da cewa yayi."Kinga dan haka tun wuri ki cire Ahmad a ranki dan ba mijin aure bane and ki kara bama Auwal lokaci ki zauna kiyi karatun ta natsu Jiddarh karda kiyi kuskuren barin Auwal dan Auwal mutun ne har da rabin mutun.Shuru nayi bance komai ba sai kuma can na d'ago Ina cewa masu.
"Hakane kam Yaya Bash,kuma in shaa Allah zanyi kokari naga komai ya tafi yanda kowa ake so,dan maganar gaskiya Yaya Auwal mutumin ne kam,Allah ya zab'a mana abunda yafi alkhari." Murmushi Yaya Bash yayi yana cewa."karda ki cuci kanki Jadda kuma ki sani ba zamu yi maki dole ba akan lamarin nan ,aure ba wasa bane ke zakiyi zaman nan ba wani zaiyi maki ba dan haka mudun kika ji baki son Auwal ki fito fili ki gaya mana mu kuma zamu aure maki wanda kike so,amman banda Ahmad dan maganar gaskiya ba zamu had'a zuri'a da Ahmad ba,dan Ahmad bai da tarbiya da kamun Kai Kinga ba amfanin hudda da irinsu."
D'aga masu Kai kawai nayi ban sake cewa komai ba,dan banda ta cewa nikam kuma har na gaji da magana d'aya sai magana d'aya ake sun kasa fahimta ta ko kawai kansu suka sani a wanann lamarin.kawai na auri Auwal na auri Auwal na gaya masu bani so sunce dai na duba zanji Ina sonshi taya haka zata faru bayan ni dai nasan bani so ,amman ila auren Auwal din shine alkhari a gareni shiyasa suka kafe akan Auwal din dai,ni kuma zan bashi dama kamar yanda ya bukata ,amman sai bayan bikin Yaya Teemarh kamar yanda nace mashi zamuyi magana.
Muna cikin magana labarinmu Baba ya dawo daga campany sannu da zuwa mukayi mashi mu duka, sannan muka tashi muda Meenat muka shiga kitchen muka hado mashi abinci muka kawo mashi,Muna k'ara yi mashi sannu da zuwa k'ara ansawa yayi yana saukowa kasa ya fara cin abincin bayan yayi Bismillah.
Maida hankalinmu makayi wajen kallon wisal hausa Ina yin wani wa'azi mai dadi shuru parlon ya dauka,idan akayi abun da za'ayi comment a wajen wa'azin sai muyi haka.har Baba ya gama tashi Meenat tayi ta dauke foodflake din da plate din da yayi using dasu ta maida kitchen sannan ta dawo,gyaran murya Baba yayi yana cewa.
"Kakata."
D'agowa nayi Ina kallonshi sanann nace."Naam." Murmushi yayi yana cewa."gobe idan Allah ya kaimu keda Meenat kuje ku zab'a ma Teemarh kayan daki tunda ita ta tafi bata je ba, sanann kuma ku fara parking din kayanku masu mahinmamci ku kaisu bayan gida cikin dakunan da aka gina."
"Baba nasa ai sai ana saura sati daya bikin zamuyi parking ko."? girgiza kai yayi yana cewa."ai bikin saura sati daya."kallon juna mukayi mu duka parlon,Mama tayi gyaran murya tana cewa."kodai wata d'aya kake son cewa Alhaji."girgiza kai yayi yana cewa."sati d'aya ne ,yanzun Yaya Bishir yake sanar mani yan maido bikin nan da sati saboda shi Sadiq din zaiyi wata tafiya america kuma.yana son tafiya da ita Teemarh din kuma.tafiyar ta kama urgent anyi bikin da sati zasu tafi."
Murmushi nayi Ina cewa."Allah sarki,gaskiya na taya Yaya Teemarh murna america aa gaskiya Yaya Sadiq ya duba da yace a matso da bikin ba a daga shi ba sai ya dawo,Allah ya kaimu goben,amman Baba ita Yaya Teemarh din yaushe zata dawo."?
"Ana saura kwana biyu zasu zo in shaa Allah,haka Yaya Bishir yace man."murmushi nayi Ina Allah ya kaimu lafiya."
"Amin Amin."
Washe gari tunda safe na tashi nayi gyaran gida har da breakfast sai da nayi sanann na tada Meenat,na matsa mata sai da ta tashi ta shirya sannan.na rabu da ita na koma parlo lokacin da na fito parlo har Baba ya fito yama fara breakfast din shi sai labari Mama take bashi yana dariya,samun waje nayi na zauna Ina gaishesu nima na zuba kosai da Kunu da yake kosai nayi.mana fara ci nayi Ina sauraren labarin da Mama take bashi nima wani wajen dariya labarin yake bani ,can sai ga Meenat ta fito ta gaidamu ta zauna sai da muka gama break din sannan muka tashi muka tafi.
Gado ukku kujeru biyu Baba yace mu zabar mata sai kuma sauran tarkacen daki wanda mukasan ana sawa a dakin amare,aikuwa mun zabar mata da kaya masu kyau da tsada daga campany Baba ba daga baya ba wajen kawo da kaya masu yan waje ,Dan shi a kasa biyu kawai yake yin order kayan daga turkiya dai Dubai anan kawai yake yin order.
Kuma campanyn daga karami ya fara, lokacin da Baba yana cikin halin babu sai dai gojiyar Allah,ga kuma yara lokacin mu bakwai ne ba'a Kai da haihuwar Sulaiman ba da Saddiqa da Rukky,a lokacin Yayanshi na birnin kebbi wato Alhaji Bishir shine yace ya zabi duk.abunda yake so yayi kasuwanci kanshi shi kuma ya bashi jari,a lokacin Baba yayi shawara da Mama tace ya fara sayar da furniture,haka akayi ya gaya mashi da kanshi ya bude mashi babban shago ya kuma zuba mashi kayan yan wajen yace ya bashi halak malak Allah ya kawo kasuwa,daga nan Baba ya cigaba da kula da shagon shi sannu a hankali yayi suna a cikin garin gusau da kewayenta dan har daga sokoto neja Katsina zuwa ake sayen kaya a wajen Baba.
Sannu a hankali har ya gina babba waje duk glass ya dawo ya kuma bada hayar wancan shagon wanda yayanshi ya fara bude mashi first,da yake Baba shine dan Auta a wajen yaiyenshi su biyar ne Mamarsu ta haifa.
Bayan mun gama zabar ma Yaya Teemarh kaya sannan muka fito,muka shiga kasuwa nan muka sawo laces dinmu da atamfa bamu zarce gida ba sai wajen tela muka bashi dinki har da na Yaya Teemarh da na kuma Mama.dan mun bashi kaya sun Kai kala 50 ni kaina ina da kala goma,Meenat ma tana da goma, Saddiqa shidda,Rukky shidda,sai Mama na da goma sai Yaya Teemarh tana da goma itama,yake tela dinmu mun kuma gaya shi mashi bikin saura sati dan an matso dashi bill yayi mana mukayi peyment din rabi,sauran kudi kuma sai munzo ansa,yake babban shago ne harda yara gareshi sunfi goma ko kowa ne yaro yana da keken dinki Shima take ya raba masu dinki gabanmu yace nan da kwana biyu muzo mu ansa.
Daga nan muka tsaya wajen yan cefa ne mukayi cefene sannan muka wuto gida,lokacin da muka shigo gida la'asar ta wuce kayan kawai muka ajiye kitchen muka shiga room dinmu,wanka mukayi da sallah sannan muka fito muka koma kitchen.
Brown rice with chicken soup sai kuma mango juice da kuma watermelon lemonade da kuma bow tea meatballs,bamu bane muka gama girki ba sai takwas flakes ukku muka dauko muka zuba ma Yaya Muhammad nashi dan sun taso sai kuma muka zuba ma Yaya Auwal sauran kuma mu zamu ci yan gida.
Wanka na shiga nayi sallah sannan na fara shiryawa Ina cikin shiryawa ya kira yace ya iso to nace mashi sanann nasa Rukky taje ta shigo dashi na koma daki na cigaba da shiryawata.
Kwaliya nayi dan harda jigira sai da nayi da yake na iya sosai makeup duk na iya har da kayan makeup din duk ina dasu yine banyi sai dai naita ma yan gidanmu da yan unguwa,amman ba kowa nike mawa ba sai na gadama,harda Jan baki na shafa,kallona Meenat tayi tana girgiza kai tace.
"Dan Allah Yaya Kulu ki goge red gloss din nan da kika shafa." Kallonta nayi Ina cewa."saboda." ", Saboda bai hau da lips dinki ba." Ni dariya ta bani wai bai hau da lips dina ba,daman kenan ba kowa color yake hawa da bakin mutane,kallonta nayi cewa." Maiye dalilinki na cewa bai hau da bakina ba."
"Haba Yaya Kulu kefe bakinki daman can jan bakinki aka haifeki,da Allah ya tashi sai ya baki pitch lips ma,wallahi duk wanda ya kalleki idan bai sanki ba sai yace pitch gloss kika shafa kuma yana kara fiddo da kyaunki sosai,pls Yaya Kulu ki goge kisa lips gloss kawai karda mu ki barshi shi d'aya zaune a parlo."
Girgiza kai kawai nayi Ina goge jan bakin na shafa lips gloss sannan na fito da sallama dauke a bakina.
Murmushi nayi inayin kasa da kaina dan wani irin kallo yake jefeta dashi mai ma'anoni daban daban,shi dai Yaya Auwal ya iya kallon kurila dan lokaci guda yake kalleka tas kafin ka farga da kallon da yake maka har ya gama sai ya nuna shi bai kalleka ba,haka yake da yake ni nasan waye shi a wajen kallo shiyasa da ya fara kallona sai na dunga turo mai baki Ina kwabe fuska sai kawai yayi murmushi ya girgiza kai sai ya sake salon kallon Wanda ba zan gane ba.
Zama nayi Ina cewa.
"Yaya Auwal Ina wuni." Baice komai ba sai ma kureni da Ido da yayi yana murmushi mun kusa 5min a haka sannan yace."kin hadu kinyi kyau Jiddarh komai naki yayi bari na gaya maki wata magana duk da nasan abokan karawata suna gaya maki ita nima zan gaya maki ke full option ce komai yayi,Allah dai ya bani ke a matsayin mata Jiddarh da nafi kowa dace." Murmushi kawai nayi Ina cewa.
"Yaya Auwal."Ina rufe fuskarta Shima murmushin yayi yana cewa "eh fah Jiddarh gaskiya ce na gaya maki kin hadu,fatan na samu Gimbiyata cikin koshin lafiya."?
"Lafiya lau Alhamdullahi,ya kuma kokari."?
"Da godiya Jiddarh myluv."
Murmushi kawai nayi ban sake ce mashi Komai ba,Meenat ce ta shigo da abincin da muka girka mashi tana gaisheshi,ansawa yayi yana jinjina mata murmushi kawai tayi tana bar mana waje,saukowa nayi na fara zuba mashi brown rice din na daura mashi chicken soup din a sama,sanann na ajiye a gabanshi wani plate din na dauko ma zuba bow tea meatballs sake dako cups nayi na zuba mashi mango juice da kuma watermelon lemonade na ajiye gabanshi Ina cewa.
"Sauko kaci abinci Yaya Auwal."
Kallon abincin yayi yana kallona sai kuma ya kalli cikinshi yana cewa."Babe duk a cikina zan duba wannan delicious din."?
Daga mashi Kai nayi Ina murmushi na tashi nace."kwarai kuwa Yaya bari ma na bar maka fili yanda zakaji dadin ci,dan ban yarda a barman saura ba duka za'a cin yeshi."
Shafa cikinshi yayi yana cewa."please Babe karda muyi haka dake, amman wallahi cikina bai anshe wannan kayan dadin ba."
Tashi nayi Ina turo baki nace."nidai ai na gama magana gaskya kuma itace ba chanzi." Inajin yana man magana ban waigo ba na shigewata.room dinmu,girgiza kai kawai yayi ya sauko ya fara cin abincin.
Ban dawo wajenshi ba sai da na bashi 20min sannan na fito Ina kallon plate din ba laifin dan yace ba kamar da ba idan yazo yaki cin abinci sosai,amman yanzun yaci ba laifin dan Brown rice sai da ya yafi rabi sai meatballs shima yaci ya kusa ukku da yake biyar na saka mashi sai ya bar biyu, juices kuma yasha duka bai rage ba har kasan raina naji dadin yanda yaci abincin amamn sai na shagwabe fuska Ina kallon plate din Ina kallonshi na cinno baki nace.
"Nidai nidai gaskiya ban yarda ba sai cinye duka."
Hada hannayenshi yayi waje daya ya langwabar da kanshi gefe yace.."Babe dan Allah ayi man afuwa na cika cikina har ba space idan kuwa na kuskura na k'ara Koda one spoon ne maybe fashewa cikin kawai zaiyi."
Zama nayi bance komai ba Ina ta kallon plate matso hawayen karya nayi Ina cewa.
"Shikenan tunda bakya ci nasan abincin bai maka dadi ba, shiyasa kaki ci."
Rufe baki yayi yana cewa."wallahi abincin nan yayi masifar dadi Babe,dadinshi ya fisgeni har nayi over feeding ban sani ba."
Turo baki kawai nayi ban sake cewa komai ba, murmushi yayi yana cewa."Babe rigima, rigimarki na tafiya dani Jiddarhna,komai naki special ne komai zakiyi sai na ganshi daban da na sauran pls ayi ma Yaya hakuri a bar yi mashi asarar wanann hawayen masu tsada."
Kara turo baki nayi Ina cewa.."yo ba Kai bane." Kama kunne yayi yana cewa.."nasan nine masoyiya,ayi man afuwa ba zan sake ma Rayuwata."
Murmushi kawai nayi ban sake cewa komai na Ina share hawayen,shima murmushin yayi yana lumshe yace.
"Jiddarh."
Dago Kai nayi Ina kallonshi bance komai ba, murmushi ya sakar Mani yana cewa.
"I love you Jiddah,Ina kaunarki sosai Jiddarh Ina fatan ki kasance tare dani har karshen rayuwata,dan kece rayuwata da gasken gaske."
Nan ma murmushi nayi ban ce mashi komai ba, cigaba da gayaman irin son da yake man da yanda yake jina a zuciyarshi,wani wajen na bashi ansa wani wajen kuma nayi.shuru mun dade muna fira sai tara da wani abu na dare sanann ya tashi yana ajiye man wata leda mai kyau a parlo ya tafi a bakin gate na rakashi Ina godiya na jiyo gida,Ina dawowa na dauki ledar na kaima Mama,nan Meenat ta fara fiddo abinda ke cikin ledar.
*AMATULLAH DATA SERVICES*
*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700
*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500
*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500
9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000
VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank
*** for call or whatsapp