Free chapter · Read without an account
Chapter 8
@fatymasardauna
*PART OF OUR DESTINY*
*Free page*
*CHAPTER 8*
Daidai ta parking din motar yayi, gami da zare key din motar yasa a aljihunsa, kamar yanda ya saba waya da kuma briefcase dinsa kawai ya d'auka, tare da bud'e murfin motar ya fita.
Atsanake ya nufi cikin hospital din, yana tafiya yana amsa gaisuwan da mutane ke kai masa kamar yanda ya saba, ahaka har ya isa office dinsa, wanda duk girman hospital din da kuma yawan office's din dake ciki, ba wani office daya kai nasa kyau da had'uwa kasancewar shine babban jagoran hospital din.
Yana shiga ya soma gudanar da ayyukan dake kansa, kasancewar yana da patients da yawa, dake jiransa awaje and akwai surgery din da zasuyi yau din, domin wasu patients din tun sassafe suka zo suna jiran zuwansa, bawani b'ata lokaci ya soma duba su.
Yau kam saida ya d'auki lokuta me tsawo kafun ya kammala da patients din nasa, wanda zuwa lokacin har 12pm ta wuce, 12:28 daidai kuma aka fara kiran sallan azahar, agurguje yaje yayi alwala ya wuce masallaci, domin 1pm daidai zasu shiga surgery din.
Koda suka idar da sallan, atare suka fito daga cikin masallacin shida Dr. Rayyern da kuma Dr. Mufeed, sai Dr. Kamal wanda atare zasuyi surgery'n.
Suna k'arasowa cikin hospital din kowannensu yaje ya shirya, kaitsaye suka wuce d'akin surgeryn.
Iya adadin lokutan da suka b'ata wajen yin surgery'n ba kad'an bane, amma saidai kasancewarsu k'warrrun likitotin da suka samu horo ak'asashe maban banta, yasa komai yana tafiya musu success ba wata matsala ahaka suka kammala, kamar yanda suka saba atare suka nufi d'akin sauya kayan, bayan an fitar da patient din da sukayiwa surgery'n, an kaita d'akin hutu.
Dr. Rayyern dake sauya rigar jikinsa ne ya dubi Dr. Khamal, dake cire hand gloves din dake hannayen sa, cikin sakin rai yace.
"Am off work today, I have so many patients but I can't see any of them, my wife is at home waiting for me."
Murmushi Khamal d'in yayi wanda shima duk ya k'osa yabar hospital din, hakan yasa ak'agauce yace.
"Me too, I left the rest of my patients to Dr. Mufeed, he's the one with night duty, my Amira is also waiting for me, even though we are not married yet, it's only six days away, zama ango is not easy, wallahi duk na k'osa marana har wani zafi yakemin i can't wait naji Amira ta akusa."
Dariya Dr. Rayyern yayi cikin yanayin tsokana yace.
"That's Good ai kai kafi wanda ma ko babe din baida ita, not even talking about being a groom."
Ya k'are maganar yana me kallon Dr. Emraan da ya riga ya gama canja kayansa, sarai yasan dashi yake amma ko kallonsu baiyi ba dukansu, haka yasa kai ya fice kamar baiji ma me suke cewa ba.
Da kallo duk suka bi bayanshi, Dr. Mufeed yana dariya yace.
"Nifa na farajin tsoron lamarin Emraan anya kuwa ba aljanune suka aureshi ba?"
"Ba wani aljanu, bai samu choice dinsa bane har yanzu, amma kuma maybe aljanun ne dan su kad'ai suke iya haka, but zamuyi maganinsa ne soon, we will get him married by force."
Dariya duk suka sa, tare daci gaba da abunda sukeyi, yayinda shi kuwa Dr. Emraan daga d'akin sauya kayan kaitsaye office dinsa ya koma, yana shiga nurse Farydah na k'arasowa, a rikice take knocking door din, wanda hakan yasa shi fusata da yanayin d'aga murya yace.
"Who's this?"
"It's me sir."
Farydah ta fad'a a d'ad'are saboda yanda taji yayi maganan, tasan baya buk'atar kowa adaidai lokacin.
"Come in."
Ya fad'a tare da d'auke kansa ga k'ofan, ahankali ta bud'e kofar ta shigo, jikinta na k'yarmar tsoro tace.
"Sir patient dinnnan da akayi rapping d’inta ne, jikin nata ya kuma tashi sosai, she's crying and screaming, mun sa mata drip ma amma ta tuge shi, she is reacting like she isn't on her senses, she is so depressed .
Idanunsa ya dan lumshe, domin zai iya cewa ya manta gaba d'aya da wani abu daya shafi zuwa ya duba ta, duk da cewa bawai zuciyarsa ta daina bugawa a dangane da ita bane, amma yanzu jin abunda Farydan ke cewa ya dawo masa da wani abu sabo, hot breath ya fesar, batare daya juyo ba murya adak'ile yace.
"I'll be there."
Da sauri ta fice, ko mintuna 2 ba ayi ba ya fito ya nufi side din da dakin yake.
Akaron farko na rayuwarsa da yake jin kansa cikin rashin kuzari da k'warin guiwar da baisan daga ina suka taho ba, ji yake jikinsa yayi sanyi musamman daya kasance saura baifi taku uku ya k'arasa cikin dakin ba, wanda daga nan inda yake tsaye yana iya jiyo sautin kuka da kuma ihunta.
Ahankali ya d'aura hannunsa akan handle din kofar tare da tura kansa ciki.
Kwance ya hangota tana ta birgima akan gadon tare da fusge fusge, yayinda Khalty ke rike da ita tana faman fidda k'walla na tsantsar tausayinta, domin babu yanda basuyi ba ita da Omer dake tsaye agefe wajen ganin sunyi controlling Yacine din amma abun yaci tura.
Ganinsa yasa Khalty karasowa garesa da sauri ta riko hannayensa.
"Likita ka taimaka ka dubamin ita, kuka take tayi da ihu, har yanzu tsoro takeji tana ganin kaman wani zai sakeyi mata wani abun, dan Allah dubamin ita likita, na farajin tsoron kada wannan abun ya kawar mata da tunani, tun d'azu abu d'aya kawai take fad'i, kamar me sabon ciwon aljanu, sai cewa take batason nan, mu tafi da ita, wani yazo zai kamata batason nan, mu kuma duk maganar nan da take yi bama ganin kowa.”
"She’ll be fine, don’t worry.”
Ya fad'a yana me k’arasowa inda take kwancen.
Hannunta ya kamo domin gyara mata zaman cannula din da tariga ta fige shi, da sauri ta janye hannunta tare da matsawa baya alaman bataso.
Kallonta yayi na dan wasu seconds kafun ahankali yace.
"Farydah give me the injection."
Da sauri Farydah dake bayansa ta miko masa allurar rage zafin ciwo wanda dama tuni an had'a ta za ayi mata ne taki tsayawa.
Jin ya ambaci allurane kuma yasa ta bud'e idanunta da suka k’ank’ance, hakan kuwa yayi daidai da kamo hannunta da yayi da k'arfi danyi mata alluran.
Kanta ta fara girgizawa, tare da bud'e baki cikin muryar kukan dake kama da sambatun zazzab’i tace.
"Dan Allah kar kayimin allura dan Allah, bana so...."
Idanunsa ya d’an tsura mata kafun ahankali, cikin tausasa murya yace.
"Ba kya so?”
Kai ta d'aga masa alaman eh, lokaci d’aya tana me yarfe y’an yatsun hannunta.
"Is okay, but ki daina kuka, fadamin me kike so, saboda idan bakya so na miki allura saikin daina kuka."
"Bana son nan, ku fitar dani daga nan, banason ina ganin wannan d’akin, komai zafi yake min, zafi da rad’a d’i nake ji anan dina, ina jin maganganunsa masu yawa acikin kunnena, zai sake kamani ne, Idan na zauna anan mutuwa zanyi!!!”
Ta k'are maganan cikin matsanancin kukan dake nuna gajiyarwata, hadi da zahirin abunda take fada, da gaske batason hospital din, duk abubuwan da take ji kuwa firgici ne, wanda akan samun irin haka, ga wasu mutane sometimes idan sun tsorata ko kuma wani mummunan abu ya faru dasu, ba kuma iya tsoro ba, wasu ko fuskar way'anda suka sani basa son gani, sukan samu kansu cikin yanayin fargaba me tsanani, kamar dai ita ayanzu da ta riga ta kamu da ANXIETY, dole tana buk'atar kulawa na musamman, kamar yanda yake abayyane, mafi yawancin mutanen da suka kamu da ANXIETY suna matukar son yin nesa da inda aka sansu, son kad’aicewa, suna buk'atar keb'abben waje da kuma sabin mutane danyin rayuwa, to haka yake awajenta itama, domin ya kasance pain biyu ne ke d'awainiya da heart dinta, kasancewar ta me k’ananan shekaru yasa ba zata iya d'aukan wasu damuwowin ba, brain dinta k'arama ce shiyasa take abu kamar wacce ta kamu da mental problem.
"Is okay, kinaso kibar nan, kina so na tafi dake wani waje na musamman?"
Kai ta jinjina masa alaman Eh, still batare da ta daina kukan ba, wanda hakan yasa Dr. Emraan din sake tausasa muryarsa cike da kulawa yace.
"Shikenan zamu tafi yanzu, amma sai kin tsaya na miki wannan alluran, ko bakya so ki daina jin pain din da kike ji?"
Kwab'e fuska tayi sai kuma ga wasu sabin hawaye shaaaaa kamar famfo sun soma k’waranyowa daga idanunta, magana takeso tayi amma sai taji harshenta yayi nauyi, hakan yasa ta rumtse idanunta k’am, tana jin ya kama dantsen hannunta da sauri tasa d'ayan hannun nata ta rik'o shi, sosai ta damk'esa har ya kai ga long nails din da ta bari a yatsun hannunta sun d’an fara k'warzanan fatarsa, domin adaidai lokacin da yake tsira mata allurar, daidai lokacin nails din nata ke cakan nasa hannun.
Idanunsa ya d’an rumtse saboda jin yanda nails din nata ke k’ara nutsewa acikin fatarsa.
Kuka ta sakar masa alokacin da yake zare alluran daga cikin jikinta.
"Is okay, daina kukan yanzu zamu tafi ai, ba kince baki son nan ba, zaki bini mu tafi?."
Yayi maganar yana me kallon yanda idanunta ke lumshewa, da alamar rashin kuzari.
"Eh, banson nan."
Ta amsa cikin yanayin mayen da allurar nasa ya haifar mata.
Wanda ganin haka yasa Khalty da Omer zuba musu ido cike da mamaki, juyowa yayi ya kalli Khalty da ta zuba musu ido cike da tarin damuwa.
Idanunsa ya dan lumshe mata alaman kada ta damu, kana ya maida kallonsa ga Omer, murya atusashe yace.
"Zamu tafi da ita gida, domin zamanta anan bazai bada abunda akeso ba."
"Farydah d'aurata akan wheelchair ku fita zuwa wajen da nake parking inazuwa."
"Okay Sir."
Farydan ta fad'a jikinta na b'ari saboda yau d'aya magar arziki ta shiga tsakaninta dashi kuma har ya bata babban umarni, wannan yasa ta d'aura Yacine din akan wheelchair d’in, da cikakkiyar azama take turata har suka fice daga d'akin.
"Ina za a kaita ne doctor? daka barmu anan din domin komawar mu gida tamkar sabunta ciwon nata ne, yanzu idan mun koma ma dole sai mun kuma dawowa.”
Cewar Khalty dake matsar kwallar da taki karewa har yanzu.
Numfashi me k’arfi yaja, tare da tauna maganar da yake son fad’i, d’an Jim yayi na d’an wani lokaci kafun ahankali yace.
"Idan kun amince zan kaita gidan mu, domin samun sauyin wajen zama, ko kuma yin nesa da inda ta sani da kuma inda abun ya sameta zai taimaka k’warai wajen dawo mata da tunaninta da kuma hayyacinta, yanzu tana cikin wani level din da kulawa na hakika take buk'ata, amma matukar zata ci gaba da sanya abubuwan dake tuna mata abunda ya faru da ita, lallai kwakwalwarta zata iya samun matsala."
Wani irin bugawa zuciyar Khalty tayi, da k’yar cikin tsoro ta soma kokarin yin magana, da sauri ya katseta yana me ci gaba da cewa.”
"Dan Allah karkuce a’a, ko saboda lafiyar ta, bani kad’ai nake zaune ba, ina zaune ne tare da iyayena, Idan kuna so zamu tafi tare daku, idan gidan baiyi muku ba na yarda ku tafi da ita duk inda kuke ganin yafi, amma yanzu lafiyarta shine komai, kada kuce a’a, ina da tabbacin cewa mahaifiyata zata kula da ita tamkar yanda zata kula da d’iyar da ta haifa, Idan kun yarda dani ku biyoni muje.."
Ya k'are maganan yana me wucewa gaba, yayinda Khalty da Omer kuwa suka shiga yiwa juna kallon kallo, abayyane tsoro ne fal azuciyar Khalty, amma saidai tashi d’aya ganin confidence din dake idanun Omer yasa tajin sanyi, hannunta Omer din ya kama suka rufawa Dr. Emraan din baya, wanda saida ya fara biyawa Office dinsa ya dauko abubuwan da yasan zai buk'ata, bayan yasa wasu daga cikin nurses din sun kawo masa magungunan da yasan Yacine din zata buk'ata, sannan ya nufi wajen motar duk su Khalty na biye dashi, ita kam Khalty sai b’arin tsoro take, yayinda ta damk’e hannun Omer k’am acikin nata, daga can k’asan zuciyarta take karanta.
“La ilaha illa anta subahanaka inniy kuntu minazzalumin.”
Ahaka suka k’araso parking space din, inda suka samu Farydah tsaye kusa da Yacine din wacce tuni bacci me k’arfi ya fara daukarta.
Key ya danna ya bud'e motar Farydah da Omer ne suka sanya Yacine din acikin motar nan b'angaren baya.
Bayan ya shiga ya zauna, yayiwa Omer umarni daya shigo gefensa b’angaren me zaman banza, domin Khalty kam baya ta shiga ta rik'e Yacine, gaba d’aya duk a tsorace take musamman ma da ta samu kanta acikin motar, da tsananin sanyin dake tashi acikinta yasa duk jikinta ya d'auki karkarwa.
Wannan wace irin motace haka, duk da baza tace bata tab'a shiga irin motar ba, amma rabonta da shiga ire irensu, tun shekaru 18 baya.
Shiyasa yanzun ta takure jikinta, tare da k'ank'ame Yacine dake kwance, wacce bata ma san ina hankalinta yake ba.
Dr. Emraan kuwa cikin kwarewa yake driving motar nasa, har suka fice daga cikin hospital din, acikinsu babu wanda ya iya cewa komai, hanyoyin da suke bi kawai suka zubawa ido, musamman Khalty da take ganin kamar Dr. Emraan din saidasu zaiyi, duk atsorace take, abubuwa da yawa take sak'awa aranta.
Ashe bata masan tsoro ba saida suka keto cikin unguwar, tare da samun kansu abakin wani wawagegen gate da isowarsu yasa aka wangaleshi, motar ta kutsa kai cikin gidan da kaitsaye zata iya kiransa da aljannar duniya, saboda kyau da tsaruwarsa.
Acikin babban compound din gidan ya daidaita parking din motar, tare da juyowa ya kalli Omer daya zubawa cikin gidan nasu ido.
"Ka fito da ita."
Ya fad'a yana me bud’e murfin motar ya fita, wanda ganin hakan yasa, Omer din shima fitowa duk da ayanzu shima ya fara jin tsoro saboda ganinsu da yayi acikin makeken gidan, amma saboda shi namiji ne dole tasa ya dake, wheelchair din dake boot din motan ya fito dashi, tare da zagayowa ya bude murfin motar, da hannayensa ya jawo Yacine din ya daurata akan Wheelchair'n domin zuwa lokacin ko iya bud'e idanunta batayi, alluran da dr din yayi mata duk ya galabaitar da ita, baya ga haka ga wani irin yunwa da takeji na tsakulan yayan hanjinta, duk da alluran da yake mata suna kara kuzari amma cikinta na bukatar asa masa wani abu na abinci.
"Khalty ki fito mana."
Omer ya fad'a yana me kallon Khalty dake hangale da baki, tana k'arewa cikin gidan kallo daga nan inda take zaune dab'as ba'alaman zata fito, saboda gaba d'aya atsorace take da kyaun gidan.
Ji takeyi kamar sun kawo kansu inda bazasu fita ba ne, domin awannan gidan sai a yayyanka sassan jikin ka ayi gunduwa gunduwa da namanka babu wanda ya sani, gidane kamar a k'asar France, ko ina korayen shuke shuke ne, hadi da wani babban tafkeken swimming pool dake tsakiyar gidan.
Ad'ad'are ta jefo k'afafunta waje ta fito, tana me sake murza idanunta da take ganin gizo yakeyi mata, saboda har yanzu bata gama aminta da zuciyarta ba.
Dr. Emraan kuwa fahimtar hakanne yasa shi yin murmushi, ahankali da yanayi irin na girmamawa yace.
"Muje ko."
Shiya shige musu gab'a, sai kuma Omer dake tura Wheelchair din da Yacine din ke kai, da idanunsa yakeyi wa Khalty magana akan ta b'oye wannan tsoro da k'auyancin nata, domin kuwa agarin kalle kallenta ta buga tuntub'e, saura kad'an taci dungure ta afka cikin tafkin ruwan dake tsakiyar gidan.
Ahaka suka k'arasa mashigan babban falon, anutse Dr. Emraan ya daura hannunsa akan handle din kofar, ya tura kofar ciki tare da matsa musu akan su shigo.
Da k'yar Omer ya iya tura wheelchair'n ya shiga cikin falon, wanda jefa k'afarsa aciki yasa zuciyarsa tsinkewa, saboda wani tsoro da yaji.
Khalty kuwa abakin Kofar ta daskare cike da tsananin mamakin ganin inda suka Kawo kansu, ashe basu ga komai ba duka abubuwan da suka tarar na k'awa a compound din gidan wasa ne akan wanda idanunsu ke gane musu acikin wannan parlor'n da kyaunsa yakai mak'ura.
"Khalty Bismillah mana."
Emraan ya fad'a cikin sakin fuska saboda sarai ya hango tsoro akan fuskar su.
Ad'ad'are ta jefo k'afafunta cikin falon Wanda babu kowa acikinsa, sai tv kawai dake ta faman aiki.
Da kansa yayi musu iso, saboda ganin yanda duk suke tsorace yasa shi fad'ad'a murmushinsa.
Ahankali yace.
"Khalty na tsoron kada gidan masu yanka kai na kawota ita da jikokinta ko, ku kwantar da hankalinku, bari na kira Mahaifiya ta."
Yayi maganar yana me jijjiga shoulder din Omer, wanda yasan sai yafi fahimtar komai fiye da Khaltyn, batare kuma da yaji tacewarsu ba, ya juya ya nufi part din Aamma.
Saidai koda yaje bai tarar da ita anan ba, hakan yasa shi sauk'owa kitchine ya duba nan ma batanan, wani tunani da yazo masa yasa shi nufan d'akin Ammabuwa, ai kuwa tun kafun ya k'araso ya soma jiyo muryoyinsu, musamman na Ammabuwa dake ta faman surfa fad'a kan bazata ci abincin da Aamman ta kawo mata ba.
Tura k'ofar d’akin yayi, wanda shigowarsa yasa duk hankalinsu dawowa gareshi.
Aamman nasa dake zaune ya kalla ahankali yace.
"Aamma muna da bak'i a falo."
"Bak'i kuma Emraan, daga ina? bamuyi da wani bak'o zai zo ba."
Aamman ta fad’a cikin mamakin bakinda suka zo batare da saninta ba.
Numfashi ya d'an fesar tare da shak'an daddad'an k'amshin turaren wuta na asalin Shuwa arab dake tashi acikin d'akin.
Asanyaye cikin yanayin karyar da kai yace.
"Haba Aamma ba nace zan kawo patient ba.”
"Oh I forgot ban yi tunanin da wurwuri haka zaka kawo patient din ba, yanzu ya kakeso ayi? Because...."
"Shiiiii please Aammana muje, don't say anything."
Ya fad’a yana me jan hannunta suka fice daga d'akin Ammabuwan, wacce ta saki baki tana kallon ikon Allah, domin da fari ta dauka wasa Bikir din keyi, amma yanzu ta tabbatar da abunnashi azimun ne, inama da ace k’afafunta lau suke, yau da ita kam taje ta ganewa idanunta, wannan gayyar sod’in.
Tun daga nesa Khalty ta zubawa kyakkyawar matar dake tahowa itada Doctorn idanu, domin kuwa mace ce wacce takai akalleta ak'ara, saboda nagarta had'i da kyaun dake tattare da ita.
Yayinda ab'angaren Aamman itama kyakkywar farar dattijuwar matar take kallo, har suka k'araso akan kujera Aamma ta zauna tare dayi musu sannu da zuwa, cikin harshenta na cikakkun Lebanese da suka saba da larabci, shi yasa hausan nata ya zama daban.
Ad'ad'are Khalty ta amsa domin tamkar zinariya me walwali haka taga matar acikin idanunta.
Yayinda Omer kuwa gaishe da Aamman yayi cikin girmamawan da yasa Aamman sakin murmushi, adaidai lokacin da take sauk'e idanunta akan ky'akky'war yarinyar dake zaune bisa wheelchair idanunta arufe kirib da alama bacci take yi.
Dr Emraan daya zauna kusa da Aamman ne ya d’an gyara zamansa, tare da duban Khalty dake zaune, muryarsa asanyaye yace.
"Khalty wannan itace Aamma, mahaifiyar data haifeni, nan kuma shine gidanmu, awajenta nake son Yacine ta zauna, saboda ina da tabbaci akan Aammana, zata taimaka k'warai wajen kulawa da ita."
Ya k’are maganan yana me juyowa ga Aamman, cikin yanayinsa daya saba yi mata idan yana son abu, atausashe yace.
"Aamma wannan itace Khalty, wannan kuma Omer, and then my patient YACINE, please Aamma ki taimaka mu kula da ita."
Murmushi Aamma tayi duk da tana iya hango wani abu na daban me rud'arwa dake kwance acikin k’wayoyin idanunsa, amma saita kawar da tunanin dake yi mata kai komo acikin zuciyarta, ta hanyar cewa.
“In sha Allah."
Mik'ewa tsaye tayi ta k'araso inda Yacine din ke zaune akan wheelchair, hab'ar ta ta tallafo wanda shi ya bata daman k'arewa fuskar yarinyar kallo, hakanan taji kyakkyawar yarinyar ta shiga ranta, tare da jin matsanancin tausayinta, sam batayi tunanin haka yarinyar take da kankantan shekaru ba, saidai daga wani sashi na zuciyarta ganin tsananin kyawun yarinyar yasa tajin fad'uwar gaba.
"Bacci takeyi ne?”
Tayi maganan tana me kallon Emraan dake kokarin cire safar k'afarsa.
"Eh injection nayi mata, but zuwa anjima kadan zata farka, saidai akwai yunwa ajikinta sosai, tana buk’atar abinci idan ta tashi.”
Kai Aamma ta jinjina tare da kama saman Wheelchair din da Yacine din ke zaune.
"Bari mu kaita d'aki to Khalty muje ko."
Tayi maganan tana me wucewa gaba rik'e da saman wheelchair din, yayinda Khalty da duk jikinta ya mutu ta rufa musu baya, direct wani k'aramin d'aki dake nan k'asa ta nufa tare da bud'e sa suka shiga ciki, ma daidai cin d'aki ne da cikinsa ke d'auke da d'an madaidaicin bed da kuma k'aramin 3 pieces drawer' da agefensa aka sak'ala wani dogon mirror.
Bayan wannan babu wani abu dake cikin d'akin sai lallausan Turkish carpet din dake kwance lub lub ak'asa.
Akan d'an madaidaicin gadon Aamma da kanta ta shumfud'e Yacine d'in dake ta bacci, wanda kana kallo kasan bawai dadin baccin takeji ba, saboda yanayinta ya nuna tana cikin galabaita k'warai, musamman yanda fuskarta ke d'auke da k'ananan tabo har zuwa kan lips dinta.
Hakanan Aamma taji duk abun baiyi mata dad'i ba, tausayin yarinyar ne matuk’a ya kama ta, Wanda hakan yasa ta dawo da kallonta ga matar da taji Emraan ya kira ta da suna Khalty tayi, wanda tana da tabbacin matsayin kaka take awajen yarinyar, ahankali cikin tausasa murya tace.
"Ina ganin mu barta ta samu bacci ko, karki damu in sha Allah zamu kula da ita sosai, d’a ai na kowa ne, duk da nasan kinajin abubuwa da yawa aranki amma nan kamar gida ne, Emraan bazai tab'a cutar muku da yarinya ba ina da tabbacin hakan.”
Ta k’are maganar cikin tausasa muryar da yasa Khalty share hawayen daya zubo mata, araunace tace.
"K’warai nasan haka y'ar nan, ba kuma inajin fargaban barinta awajenku bane, saidai ina mamakin yanda baku sanmu ba amma kuke son taimakon mu, waye zai biyaku idan ba Allah ba? bamu da kowa saishi haka ma Yacine bata da kowa sai Allah sai mu, dan Allah ku rik'e ta amana, domin ajikina nake jin cewa ku ba mutanen banza bane, kuna da kirki k’warai saidai zakuyi mana alfarmar zuwa duba ta akoda yaushe."
Murmushi Aamma tayi, kana cikin sakin rai tace.
"In sha Allah! Duk lokacin da kuke son ganinta zaku iya zuwa, Allah dai ya bata lapia."
"Aameen."
Khaltyn ta amsa tana me sake matsar k’walla da mayafin gyalen dake jikinta, zuciyarta duk tayi laushi tsananin tausayin jikar nata yasa ta kasa iya controlling kanta, wanda fahimtar hakan yasa Aamma kamo hannun Khaltyn suka fice daga d'akin.
Falo suka dawo inda suka tarar da Emraan da kuma Omer na magana wacce basu san kota mecece ba, domin suna isowa Omer din ya tashi ya kamo hannun Khalty da har yanzu take kuka.
"Mu tafi gida ko, mungode sosai Allah ya saka muku da alkhairi, ya baku ladan taimakawar da kuka yi.”
Ya fad'a yana me fad'ad'a murmushin dake kan fuskarsa.
Aransa yake jinjina maganganun da suka tattauna da Dr. Emraan din, tare kuma da irin kirkin su da bashi da na biyu.
Ahaka suka nufi hanyar fita daga falon, Khalty na ta faman kukan rabuwa da jikanta, tamkar wanda akace mata sun rabu kenan.
Har compound din suka fito tare da Dr. Emraan, wanda ya yiwa Sa'ed driver bayani kan yaje ya ajiyesu agida.
Har bakin motar ya rakosu, kafun ya juya da niyar komawa ciki, amma sai yaji an riko hannunsa, yana juyowa sukayi ido hud'u da Khalty, wacce keta faman matsar k'walla, hannayenta biyu ta had'e alaman rok'o, kana da muryar kuka tace.
"Yacine bata da kowa sai Allah, dan Allah ka kula da ita, mun kuma gode sosai da taimakon da kayi mana, in sha Allah tana samun sauk'i zamu zo mu tafi da ita."
Murmushin daya zama kamar dolensa ya k'ak'alo ya aza akan fuskarsa, cikin girmamawa yace.
"In sha Allah!!!"
Daga haka bai sake cewa komai ba, har suka shiga motar Sa'ed driver yaja su suka fice daga gidan, ganin fitansu ya sashi komawa aciki.
A falo ya tarar da Aamma da kuma Ammabuwa zaune, wacce ta lallab’a ta fito da k’yar.
d'an tsayawa yayi turus saboda ganin irin kallon da Aaamman keyi masa.
Hakanan yaji wani irin fargaba ya daki zuciyarsa, amma saiya share tare da k'arasowa ya zauna.
"Oh ikon Allah kenan, sannu shugaban masu kalan dangin dudduniya."
Cewar Ammabuwa da takeyi masa kallon mamakin daya kasa k'arewa.
Yayinda Aamma kuwa ta kasa cewa komai sai idanu kawai da ta zuba masa, cike dason karanto hakikanin gaskiyar abunda ke cikin idanunsa, amma hakan ya gagara, domin ya kasa bata daman hakan, wanda gudun kada ta kureshi ne ma yasa shi mik'ewa tsaye, batare daya tankawa Ammabuwa ba yace.
"Aamma nifa yunwa nake ji, me kika dafa mana yau?"
Ya k'are maganar yana me bud'e food flasks din dake jere saman dining.
Yau Algerian dishes Aamman tayi musu, Chorba frik, Tajine Zitoun, da kuma shakshouka, fuskarsa ya d'an kwab'e domin abincin sam basu wani dame shi ba, bai cika son traditional foods ba, hakan yasa shi d'aukan small cup, ya zuba tatacciyar madarar da Aamman ta saba had'a musu ko yaushe.
Hannunsa rik'e da cup din ya nufi sama.
Da kallo duk suka bishi daga Aamma har Ammabuwa da ta wangale baki da hanci tana kallonsa.
Kasa iya hakuri tayi ta bisa da k'wafa, yayinda acikin ranta kuwa take fad’in.
"Namiji har namiji amma fankon banza fankon iska.”
Amma kam kawar da idanun ta tayi daga garesa, tare da mik'ewa ta koma d'akin da ta kwantar da yarinyar, wacce tun ganinta ta tsaya mata arai, bata dan me take ji adangane da yarinyar ba, amma saidai tanajin zuciyarta na sak'a mata abubuwa da yawa, kowa na da irin tasa baiwar, amma ita nata baiwar itace hasasho K'addara.
Amma a wannan karon batasan ta inane k'addarar zata soma ba, saidai tayi imani cewa lallai wani abu zai faru domin tanajin hakan acikin jikinta.
Babbar abun tambayar kuwa shine.
MENENE WANNAN ABUN?
(Karku manta wannan littafin Na kudi ne, domin samun damar ci gaba da karantasa bayan an kammala free page, hanzarta ku biya 500 naira kacal ta wannan account number din 2268498748 Fatima Abubakar UBA bank, zaku iya tura shaidar biya ta WhatsApp number na kamar haka ***)
#fatymasardauna