Free chapter · Read without an account
ZAZZAFAR KAUNA 21&30
*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*
*BOOK THREE*
_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_
_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_
_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! ***_
***
*21-30*
Karfe goman dare jirginsu ya sauka a Aminu kano airport,bayan yan lokacin passenger suka fara fitowa,a hankali take taka matakalar benen jirgin ta na ida saukowa a filin jirgin ta lumshe Ido tana sauke ajiyar zuciya,shakar iskan wajen tayi tana furzarwa a hankali ta bude idonta a hankali ta sauke a saman fuskar AK da yake tsaye tana sakar mata da murmushi,itama murmushin ta sakar mashi tana cewa.
"Yau gani a kano."
D'aga mata kai yayi yana kamo hannunta a hankali yace.."Yaushe rabonki da taka kafarki a wannan wajen.?" Langwabar da kai tayi tana wasa da yatsan hannunshi tace.."four years back."
Jan hancinta kawai yayi suka bi bayan su Ammie dan har an gama zuba kayansu a booth suka shiga mota su ka dauki hanyar GRA,Dan a nasarawa zasu kwana washe gari sun dauki hanyar jigawa saboda yanzun dare yayi ga kuma matsalar tsoro da ake fuskanta balle su doshi hanyar dutse a cikin dare.
Koda suka isa gida masu gadin gidan suka kwashe kayan suka shigar masu da shi ko zama basu yi ba kowa ya shigewarshi dakinshi dan watsawa saboda gajiyar da suka kwaso...Koda ta shiga room din Ammie tace ta shiga need ta tadda dakin sai kace ana rayuwa a cikinshi komai gyare yake a cikin dakin,ga dakin yayi masifar bala'in kyau komai na cikin dakin milk ne ba karamin kyau dakin yayi ba,bayan ta gama k'arema dakin kallo ta fada toilet tayi wanka ta dauro alwallah bayan ta fito ta shafa cream ta shirya cikin doguwar rigar bacci ta zura hijab tayi sallah sannan ta fashe turare ta kwanta dan bacci ne fal a idonta ga kuma yar yunwa tana jin amman baccin ya danne yunwar.
Bayan sun fito parlo suka zauna a dining zasu ci abinci, Jidda suka tsaya yi shuru bata fito ba,5mn Ammie taga tayi ba taga Jidda ta fito ba, ganin bata fito ba sai ta tashi ta shiga taga ko lafiya.
Tsaye Ammie tayi tana kallonta sai kuma ta saki murmushi tana karasawa a jikin gadon ta zauna,tana kallon yanda take bacci duk gashi ya rufe mata ido bacci take cikin kwanciyar hankali dan a hankali take fitar da numfashi take wani murmushi Ammie tayi tana yaye mata gashin da ya rufe mata fuska tana Kara gyara mata kwanciyarta a hankali tace.
"Allah yayi maki albarka."
Kashe mata hasken dakin tayi ta kuma tofe ta da addu'a tana fitowa ta dawo wajensu kallon Dad tayi tana cewa.."Ashe bacci take." Murmushi Dad yayi yana cewa. "Ina ruwan Hauwa'u,ai dole ayi bacci angaji sosai balle ita ba sabawa tayi da tafiya mai tsawo irin wannan ba." Murmushi AK yayi yana cewa.."Gaskiya kam Dad dan tunda taje Ukraine bata sake matsawa ba kullun dai tana cikin rabon da ta hau jirgi wai shekara hudu kenan."
Zaro Ido Ammie tayi tana dariya tace .
"Kaiiii Luv Anya kuwa babu sheri a maganar nan taka.?" Kwabe baki yayi yana saka tsokar nama a bakinshi a hankali yake taunawa kamar ana mashi dole dan shi a duniya ba abunda yake mashi wahala kamar tauna abinci..ba abincin bane bai son ci ba A'a kawai dai taunashi yake mashi wahala shiyasa sai ya hakura Koda yana jin yunwa sai yasha milk ko kuma yogurt.
Sai da ya hadeye sannan ya kalli Dad yace.."Dad kaga Ammie ko?bayan ita ta gaya man da kanta kuma sai Ammie tace haka." Dariya Dad yayi yana cewa.."rabu da ita naga alamun so take su hademana kai su nuna mana banbanci." Kwabe fuska kawai ya Kara yi yana turo baki murmushi kawai Ammie tayi tana cigaba da cin abincinta tayi kamar bata san suna yi ba.
Tunda ta kwanta bata san inda take ba baccin gajiya kawai take dan bata san Ammie ta shigo ba balle kuma yaji addu'ar da tayi mata da fitar ta,can wajen karfe ukkun dare yunwar cikinta ta tadata tashi tayi tana murza ido, dump lamp din gefen gadon ta kunne tana maida hular baccinta ta sauko saman gadon tana bissimllah,direct toilet ta shiga ta wanko fuskarta ta dauraye bakinta ta fito tana neman wayarta duba time tayi taga ukku har da rabi ,mamakin baccin da tayi take sai kuma ta kwabe baki tana nufar hanya dan sama ma cikinta abinci dan wata irin yunwa take addaba mata a ciki.
Koda ta fito direct dinning ta nufa tana bude warmers din da suke a dinning din, jallof cous-cous ne da yaji kayan lambu da kuma tsokar nama sai da miyaunta ya tsinke dan couscous din yayi mata kyau sosai,kuma baiyi sanyi ba da yake ba a karamar kula aka zuba couscous din ba , kula ce wanda zata kai duba dari biyar ko ma sama da haka.
Sosai ta zuba couscous din ta zauna taci ta koshi sai da taji har ba waje a cikinta sannan ta ture plate din tana tsiyaya ruwa a glass cup mai kyau da daukar ido ta sha sai kuma ta tsiyaya pineapple juice mai sanyi tasha tana lumshe ido,sai da ta sauke ajiyar zuciya tana jin wata natsuwa na saukar mata a ko wane lungu na jikinta.
Kwashe kayan tayi ta maidasu a kitchen sanann ta dauko bottle daya na ruwa ta nufi room dinta dashi dai dai zata shiga room dinta ta sauke idonta a kanshi, murmushi tayi tana weaving din shi shima weaving dinta yayi yana cewa.
"Hope kin tabbata kin koshi sosai.?" D'aga mashi kai tayi tana cewa.."Yeah." Huro mata kiss yayi yana bude kofar room dinshi ya shige lumshe ido kawai tayi itama tana ida shiga nata room din...Koda ta shiga ajiye ruwan tayi a saman lakar gado sanann ta shiga toilet tayi alwallah ta fara sallah,ganin har hudu da minti ashirin tayi asuba tana gabatowa..kuma yanzun har ta saba da yin sallar dare saboda tunda ta dawo da kwana a gidan su AK take tashi sallar dare saboda yan gidan sun saba da tashi har tashin ya zaman mashi jiki.
Bata koma bacci ba sai wajen karfe shidda na safe sai da ta gama har azkar sannan ta koma bacci ,ta dade bata tashi ba dan sai wajen 1 na rana ta tashi tana tashi wanka tayi da alwallah wata doguwar rigar ta atamfa ta saka ta daura hijab tayi sallar azahar...tana gama sallar ta zauna saman stool tayi shafa ta daura dan kwali sannan ta fashe turare ta fito,zaune ta tadda Ammie a babban parlon tana magana da wata mata Koda ta karaso a parlon zaunawa tayi kusa da Ammie tana daura kanta a saman kafadarta tace.
"Gud Afternoon Ammie."
Shafa kanta tayi tana cewa.."Afternoon Too Jiddah,fatan kina lafiya." D'aga mata kai kawai tana Kallon matar da ke gaidata tayi murmushi tace.."Ina wuni ya gida." K'asa matar tayi da kanta tana cewa.."lafiya lau Hajiya ya kuma gajiyar tafiya.?" Alhamdullahi tabi jiki." Cewar Beauter tana komawa dayan parlon ta kunna kallo ta basu waje su ida maganar su duk ta lura kamar matar gateman din gidan ne Ammie take magana da ita.
★★
*ABUJA🥀*
Kallon Zubaida tayi tana murmushi tace.."Sis maiye sirrin?Kinga yanda kika koma kuwa?daga yin aure ko sati biyu ba'ayi ba." Murmushi Zubaida tayi tana kama hannun Zulaihat suka shiga room dinta da ita sai da suka zauna ta kulle kofar room din ta kalli Zulaihat tace.
"Sis."
D'agowa Zulaihat tayi tana murmushi tace.."Na'am gaya man sirrin dan Allah wallahi baki ga yanda kika yi kyau ba kikayi fresh kin zama wata Hajiya."
Murmushi Zubaida tayi tana cewa.."kwanciyar hankali da kuma samun miji na gari ga soyyyar da yake nuna man ba dare ba rana." Dan shuru tayi tana kallon Zulaihat itama ta chanza ta Kara haske da kuma kyau sai daukar Ido take amman batayi wata kiba ba tana yanda take bata rame ba kuma batayi kiba ba,amman tayi haske sai glowing fuskarta take dan tunda akayi aurensu basu hadu ba sai yau,yau din ma Zulaihat din ce tazo da kanta ita ba yanda batayi da Moha ba ya barta taje sai yace a'a ta barshi karda taje ta takura masu suna cikin amarci,yanke shurun Zulaihat tayi tana cewa.
"Hakane kuma Sis kinji dadi Allah ya baki Allah ya baku zaman lafiya da zuria daiyaba daman Dr Moha bai da damuwa kuma baida matsala so simple haka yake."
Murmushi Zubaida tayi tana cewa.."kema ai kinyi dace yanda Habibi yake simple haka Dr Najeeb ma dan shi da bai da magana ma kuma bai da yawan hayaniya ba kamar Habibi ba da ko gaji da surutu baya yi."
Furzar da iskan bakinta kawai tayi tana cewa.."Allah ya rufa asiri kina waya da Umma dai ko sosai." Harararta Zubaida tayi tana cewa.."ai kinsan wannan ajiye take,ya muna magana zaki chaza wata.?" Kwabe baki tayi tana cewa.
"Saboda bani bukatar maganar shiyasa."
Kallonta kawai Zubaida take tana mamakin bakar zuciya irin ta Zulaihat takan rasa Ina ta samu wanann zuciyar dan da ba haka halinta yake ba,ta chanza ta zama wata jarabar biya kadan take jira ta dunga zabga masifa da bala'i.
Dafata Zubaida tayi tana cewa.."kina nufin har yanzun ba abunda ya shiga tsakaninki da Dr.?" Tsaki tayi tana cewa.."wai maiye haka?wannan wata irin tambayace daga zuwa mu gaisa sai ki tareni da wannan maganar."
"Allah ya baki hakuri,amman nasa ba laifi bane dan nayi maki wannan tambayar nasan akwai irin wannan maganar a tsakaninmu."
Dan shuru tayi sai kuma tace.."hakane Sis sai dai wallahi ni sam bani son maganarshi,ni ko kallon shi bani son yi bansan mutumin nan ko kadan ba zaki gane yanda nike ji ba akan shi akan mai zan bashi jikina bayan ba sonshi nike ba.?"
Kama baki Zubaida tayi tana cewa.."Amman Sis baki kyauta ba,bai cancanci irin wannan tsanar daga gareki ba ki tuna irin son da yake maki mana." Hararta tayi tana cewa."Yaushe yayi dake yana sona?ya tab'a ce maki yana sona?kina bani mamaki inda kina cewa yana sona,wai tsaya na tambayeki dan Allah kema haka Dr Moha yake maki?haka yake maki fisgar kai da kuma d'aga kai da wulakanta ki a Koda yaushe kuma duk sone haka ko.?"
Girgiza kai Zubaida tayi tana cewa.."gaskiya maganar gaskiya ba haka ake soyayya ba, ai ita soyayya ba'a yi mata haka taitali ake a so kuma a taraiyyashi ba'ayi ma so haka kuma ba'ayi mashi gadara indai haka yake maki har yanzun bai chanza halinshi ba gaskiya karya yake ba sonki yake ba."
Gyara zamanta tayi tana cigaba da cewa.."To Sis shi haka yake mani,tunda naje gidanshi a matsayin mata bai tab'a yi man maganar arziki ba sai ta tsiya ke kallon arziki ma bai tab'a yi man balle azo da yin magana kinga yanzun sati daya kenan da yin bikinmu dai ko?to dan ma nima ina ramawa ban yarda,da yayi man nike ramawa dan na lura yana da son girma bai son raini shi mutumi ne mai son girma da a girmamashi,ni kuma da na lura da haka sai nike mashi rashin kunya dan na dunga b'ata mashi rai dan wallahi yanda yake b'ata man nawa rain nima sai na b'ata mashi yaji idan da dadi."
Dafata Zubaida tayi tana cewa.."Ba zan hanaki ba dan k'ato yancinki a wajenshi da kuma martabarki sai dai na Kara dauraki a hanya dole ya kwashi kashinshi a hannu,dan wannan halin nashi ya fara isata gaskiya idan ba'a gyara mashi zama ba to ba zai daukeki a bakin komai ba Sis."
Kallar tausayi tayi da fuska tana cewa.."Ni wallahi Sis ban san ya daukeni a bakin komai dan nima ba zan dauke shi ba tun da baya gabana Kinga ba bukatar shi ya daukeni amman inason na koya mashi hankali Ina son na sauke mashi duk wani girman Kai da wani d'agawa da kuma miskilancin banzan da yake fama dashi kuma shi ba kowan kowa ba ni wanann ce kawai matsala ta ba komai ba."
Murmushi Zubaida tayi tana cewa.."Taya zai shiga taitayinshi ki koya mashi hankali da duk abunda kika lissafo ba tare da yasan darajarki ba ya kuma san matsayinki a zuciyarshi.?"
Shuru Kawai tayi tana kallon Zubaida sai kuma ta girgiza ma Zubaida Kai kawai bata sake cewa komai dariya kawai Zubaida tayi tana cewa.
"Kinga aikin da zamu fara yi a schedule dinmu shine ko yana sonki ko bai sonki to ke kiyi yanda zakiyi ki tusa mashi sonki idan muka ya kamu yanda muke so sai mu shiga next plan."
Furzar da iskan bakinta tayi tana cewa.
"Amman Sis taya zan iya tusa mashi sona,bayan ni ba sonshi nike ba haba mana Sis ki duba dai." Dariya Zubaida tayi tana cewa.."nasan baki sonshi ko baki fadi ba fuskarki tana nuna haka ,kedai kawai maiye fatanki?baki koya mashi hankali ba?to ki san yanda zakiyi ki saka mashi sonki ki saka mashi sonki yaji kamar zai mutu idan yayi Koda 1mn bai ganki ba and Ina son ya susuce akanki ya zama Wawa akan sonki ya kasance zai iya nuna ki a matsayin masoyiyarshi matarshi a ko Ina yake ya zama lokacinshi naki ne komai naki idan har hakan ta faru a cikin ruwan sanyi zaki koya mashi hankali duk da yana sonki kuma yana kaunarki amman har yanzun Inaga basu Kai inda ya dace ba a zuciyarshi idan kuma girman Kai ne da miskilanci yake hanashi nuna maki son to zai ajiyesu a gefe ya rungume ki hannu biyu shine kawai."
Murmushi tayi sai kuma ta tsuke fuska tana cewa.."naji amman duk da haka na rasa gane ya zanyi ,kin san waye Najeeb ba sai an tsaya gaya maki ba,kinsan shi murdarden hali ne dashi ba'a gane gabanshi balle bayanshi taya wannan gagarumin aikin zaizo man da sauki."
D'aga Kai Zubaida tayi tana cewa..."hakane kuma, sannu a hankali zakiyi komai yanzun ki cigaba da tafiya dashi a yanda ya zab'a a hankali zaki fara chanza salon tafiyar har kiga muyi successful din plan din mu sai mu shiga plan B,ai ba sauri ake ba."
Tashi tayi tana cewa.."hakane kuma and bari na tafi nasan sai munyi ta dan bai san na taho nan ba tun da ba maganar arziki muke ba balle na gaya mashi." Itama Zubaida tashi tayi tana dariya ta dauko mata wasu turaruka ta bata har bakin kofa ta rakota ta koma dan daura dinner.
Tana fitowa ta gansu zaune akan plastic chair shi da Dr Moha suna hira sai dariya Dr Moha yake shi kuma Ogan sai murmushi kawai yake,dan murmushi tayi tana kallon Dr Moha tace.
"Ina wuni."
Murmushi yayi yana cewa.."Lafiya lau Amarya ya gida ya kuma hakuri da wannan mijin naki.?" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba tayi tafiyarta da kallo ya bita yana mamakin daman bata cikin gida?tun yaushe ta fita taje gidan Moha bai sani ba?tabbas ya yarda yarinyar ta raininshi raini mai girma haka,har ta iya daukar kazaman ƙafafunta ta fita ba tare da tayi noticing din shi ba,wani bakin cikine ya mamaye mashi zuciya dole ya hukunta da wannan laifin nata.
Girgiza shi Dr Moha yayi yana cewa.."wannan kallon fa ango, tashi ka bita kusha kauna nima daman so nike naje wajen Darling ta dan tausayi man na dan rage zafi Kafin a kira sallah."
Harararshi yayi yana buga tsaki ya bar mashi wajen bai ce mashi komai ba,dan shi mamakin halin Moha yake yabi ya chanza ya zama karamin dan iska tunda akayi masu aure yake wani abu kamar ba shi ba,dariya Dr Moha yayi yana dan d'aga murya yace.
"Karda azurma da yawa dai saboda lokacin sallah yana yi idan ba za'a iya d'aga kafa ba a fito sallah."
Waigowa kawai yayi yana kallon Moha can kuma yayi murmushi yana tafiya yace.."Ai ni ba Kai bane." D'aga haka bai sake bin ta kan Moha ba ya wucewarshi so yake ya ritseta a parlo yaji dalilin fitarta ba tare da tayi notice din shi ba.
Koda ya shigo bai tadda ta a parlon k'asa ba kitchen din k'asa ya leka yaga wayam,sai kuma ya Kara'sa haurawa sama nan ma bata nan sai dai ya jiyo motsinta a kitchen murmushin mugunta yayi yana shigewarshi room din duba lokacin sallar mangariba tayi karda ya tsaya ta b'ata mashi lokaci ya rasa sallar ma.
Koda ya fito baibi ta kanta ba ya tafiyarshi amman yana addu'ar Allah yasa ya har ya dawo daga sallah bata koma cikin room dinta ba, dan idan bai hukuntata akan laifinta ba tabbas tasha dashi.
Yunwa take ji daman tunda tazo gidan bata girka abinci dashi,zata dafa duk abincin da ranta yake so ya kuma gadama amman bata daurawa dashi dan tace ita ba baiwarshi bace,ba zata zauna ba taita girka mashi abinci yana ci amman ba godi bare na gode.
Indomie ce ta girka taji pies da carrot da kuma kifin gwangwani (sardine) sai kamshi take juyewa tayi a plate tana dauko mangon juice din tayi dazun kafin ta fita a freeze ta daura Saman babban tire ta zo ta ajiye a saman center table, ganin indomien da zafinta sosai yasa ta shiga room dinta danyi sallah kafin ta fito ta dan huce sai ta ci hankali kwance dan bata son cin abinci da zafi Kona mata baki yake kuma ko plate nawa zataci to ba zata koshi ba saboda zafin da yake dashi,shiyasa ta barshi dan yin sallah tana shiga room dinta sai kawai ta tube kaya ta fara yin wanka tana fitowa ta saka wata halfgown mai armless din hannu ko cinyoyinta rigar bata rufe ba,zane ta daura tayi salla ta samu tayi azkar turaren da Zubaida ta bata ta dan shafa a wajen wuyanta da kasan boobs dinta sai kuma ta shafa kwali ko hula bata daura ma kanta ba ta fito dan wata irin yunwa take ji.
★★
*KANO🥀*
Bayan Ammie ta sallami Samira ta matsama Beauter akan taje taci abinci zuwa anjima zasu koma gida jigawa..arewa24 take dan wani shiri suke haskawa mata a yau,mundu'i suke mai mahinmamci da daukar hankali dan suna magana akan soyayyar wannan zamanin wanda ta lalace tazo karshe daga kan samarin har yanmatan basu da alkibila ba'a gina soyayyar akan gaskiya mata suna aure dan dukiya mazan kuma suna auren yarinya dan kyau da surar jiki,da anje akaga ba haka ba sai auren ya lalace baya kulla Koda wata biyar balle azo shekara.
Motsi mai karfi Jiddah bata son yi saboda sherin yayi mata kyau bama tasan ana yin shi ba saboda rabon da ta kalli tashar har ta manta...ita kallo baya gabanta Sam daman koda tana gida ba yinshi take ba sosai idan anga tana kallo to recipes ne taga ana gwadawa a wani channel din zata zauna ta kalla.
Duba da yanda tayi concentration akan kallon kuma abunda suke fada mai ma'ana ne da kuma mahinmamci yasa Ammie ta rabu da ita ta tashi da kanta ta zuba wata abincin shinkafa ce da taji kifi sai coslow ta ajiye mata ta kawo mata juice ta ajiye tana cewa.
"Sauko to ki zauna ki ci Daughter kina ci kina kallon ban san ulcer ta kama man ke."
Tashi tayi tana dawo kasa ta zauna tana kallon Ammie tace..."Thank you Ammie I love you ." Murmushi Ammie tayi tana cewa.."Allah yayi ma rayuwarki Albarka." Amin tace tana bissimllah ta fara cin abincin takan rasa wani irin sone mutanen nan suke mata,kullun Kara ganin sonta da tausayinta take a kwayar idanunsu.
Su dai mutane ne masu mutunci da kuma karamci masu maida damuwar wani tasu, dukiyarsu bata tab'a rufe masu Ido ba suka ga sunfi karfin magana da wannan bama kace wa sune masu wannan makudan kudaden , komai nasu burgeta uake rayuwarsu abun burgewace da kuma kwatance da kuma abar koyi ce ga kowa.
Kullun cikin taimakon mabukata suke so suke suji anzo ance a taimaka su bada aikin Kenan,dan zaman da tayi dasu a Ukraine taga wannan halin a wajensu suna taimaka wa Christian din kasar sai dai inda basu zo,balle kuma ace musalmai yan uwansu ai sai abunda hali yayi wajen badawa...tunda ta tashi bata saka Dad da AK ba a idonta da ta tambayi Ammie ce mata tayi suna kofar gida suna gaisawa da mutane ko yanzun Samira da ta.shigo sukayi magana da Ammie tana jinsu makudan kudadene Ammie ta tura a account din Samira sama da 6m ta raba ma makubata sannan kuma tayi sayaiya ta Kai gidan marayu da makarantun allo gaskiya halinsu abun sone da koyi.
Bayan ta gama cin abincin suka zauna sukayi fira da Ammie wajajen 3pm suka tashi dan zuwa shiryawa zasu dauki hanyar tafiya jigawa wanka tayi ta shirya cikin laces light purple mai ratsin pitch a jiki sai da tayi sallah sannan ta daura dan kwali ta yafa veil ta dauki bag dinta ta fito,tana fitowa ta taddadu parlo duk sun fito ita suke jira gaida Dad tayi tana mai kallon AK ta langwabar da kai a hankali tace.
"Afternoon Beb."
Kureta kawai yayi da Ido yana kallon kyaun da tayi,ya ma manta a gaban suwa yake duba da irin kallon da yake mata fuskarshi kumshe da murmushin kauna,ganin d'an nasu ya manta da tsayuwarsu Dad yayi gaba Ammie tana bin bayanshi tana murmushi tana kuma mamakin yaran zamani da kunya bata ishesu ba.
Gyaran murya tayi tana yin weaving din hannunta a fuskarshi tace.."Beb karfa su Ammie su tafi su barmu." Sauke ajiyar zuciya yayi yana kama hannunta ya kureta da Ido yana cewa.."Partner please be my wife,Ina kaunarki ina Kaunarki sosai dan Allah be my wife I beg you."
Jan hancinshi tayi tana cewa.."Me too please be my Husband." Dariya yayi yana yi ma hannunta kiss sannan suka fito rike da hannun juna suna labari sai murmushi suke zabga ma juna...Koda suka fito har su Dad sun shiga mota tayi gaba wata motar suka hau wani drive din yazo ya daukesu sai jigawa dutse.
★★
*ABUJA🥀*
*AMATULLAH DATA SERVICES*
*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700
9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000
VIA✓***
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank
*** for call or whatsapp