Free chapter · Read without an account
ZAZZAFAR KAUNA 81&90
*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*
*BOOK THREE*
_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_
_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_
_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! ***_
***
*81-90*
"Sister Zulaihat gaskiya kin burgeni sosai yanda kikayi mana wanann bayanin cikin natsuwa da hankali ki gode ma Allah da ya baki baiwar kwakwalwa gaskiya." Murmushi Zulaihat tayi tana cewa."Nagode sosai nima kin burgeni sosai kuma kema kina da hankali har da kwakwalwarma."kallon Zulaihat tayi tana cewa."nagode Sosai,sunana Khadija ana kirana da Baby." Murmushi Zulaihat tayi tana cewa."your are welcome Baby." Tasowa Zubaida tayi ta dawo wajen su sai fira suke gwanin burgewa da yake Baby itama bata da bakunta tana da saurin sakin jiki da mutane.
Bayan sun fito wajen cin abinci Baby ta nufa dasu Koda akaje ba abunda Zulaihat ta bukata duk da kuwa tana jin yunwa amamn haka nan taji bata bukatar cin komai sai coffee da ta bukaci kawai a kawo mata kuma karda a cika mata sugar dan basu had'a hanya da sugar sam.
Bayan an kawo masu abunda suka bukata har sun fara ci ma,Baby ta d'ago Kai tana cewa.."Sis Zulaihat kin san mai.?" Girgiza kai Zulaihat tayi tana ajiye mug din coffee tana cewa.."A'a sai kin fad'a ." Wani murmushi Baby ta saki tana lumshe ido can kuma ta bude su tana cewa.
"Inason wanann Dr Najeeb din dama dama."
Kallon kallon aka shiga yi tsakanin Zubaida da Zulaihat furzar da iska Zulaihat tayi tana kallonta sosai tace.."ke kam mai kika gani a wajenshi da har kika ji kana son shi.?" Murmushi tayi tana goge bakinta da tissue tace.
"Class." Dan shuru tayi tana yarfa hannunta tana mai cigaba da cewa."Guy din yana da aji yana da kyau ga iya gayu uwa uba ga kuma ilimi komai nashi a cikin ilimi yake yin shi Ina son shi sosai Ina fatan na kasance a matsayin matarshi mu rayu a inuwa daya har *DA'IMAN ABADAN* ."
Rintse idonta Zulaihat tayi da karfi tana budewa dan kalamanta na karshe su rayu a inuwar aure har *DA'IMAN ABADAN* wani abu taji ya kare mata zuciya ga wani zafi da take mata take taji tana jin haushin Baby har bata son ganinta haka taji,kutt haka ta hadiye wani abu mai d'aci tana sakin murmushin yake tace.
"Hakane duk da ni ban ga abunda kika lissafo taitare da shi ba,amman ya zakiyi da son shi.?"
Zaro Ido Baby tayi tana ajiye bottle water din hannunta tana kallon Zulaihat can ta maida kallonta wajen Zubaida da ta zuba masu Ido tana kallon ikon Allah, dan taga wani abu taitare da Zulaihat akan maganar da Baby tayi murmushi tayi dan tayi noticing din wani abu da ita Zulaihat har yanzun taki ta kwantar da hankali ta gane matsayin Najeeb a zuciyarta hauka kawai take amman abunda bata sani ba sonshi da kaunarshi suna makale a cikin zuciyarta ba tare da ta san da zamansu ba,ko kuma ta sani take pretending oho.?
Ce ma Zubaida Baby tayi t "Sister Zubaida wai kinji bata ganin class din new lecture din nan har da kyaun shi ma." Cikin mamaki Baby tayi tambayar dan ita dai tasan ko makaho ya laluba sai yace Najeeb Handsome ne balle kuma mai Ido,amman Koda yake ance abincin wani gubar wani.
Murmushi Zubaida tayi tana cewa.."aikuwa abincin wani gubar wani,but nima yayi man da dan duk abunda kika lissafo yana da su maybe ma baki ga wasu ba."
Dan b'ata fuska Baby tayi tana cewa.."kar dai ace kema kina son shi.?" Yanda tayi magana tana nuna kishinta a fili ya k'ara ba Zulaihat mamaki wato ita bata ji kishi ba sai ita,a gabanta take yabon mijinta har take cewa tana son su kasance a inuwar aure,amman tayi mata uzuri daman ance rashin sani yafi dare duhu.
Dafa Baby Zubaida tayi tana dariya sosai sai da tayi mai isarta sannan tace.."Mai da wukar kawata,ni Ina da mijina na manta ban gaya maki bane da aure a kaina." Waro Ido tayi tana cewa."wow happy marriage life." Murmushi Zubaida tayi tana cewa."Thank you."
Cigaba da cewa Baby tayi.."soon zaku ga muna soyayya da Dr Najeeb believe me." A tare suka ce mata.."Taya kenan.?" Murmushi kawai tayi tana cewa.."nifa macece,kuma nasan hanyoyin da zan bi dan gaya mashi sirrin dake raina a kan shi,kuma ai Ina da kyau balle yace baya sona." D'aga Kai Zubaida tayi tana cewa."hakane kam amman kibi sannu karda ki shige mashi da yawa dan na lura guy din yana da disgi sosai"
D'aga Kai kawai Baby tayi tace.."I know hakan ba damuwa bane,nidai bukata ta kawai ya soni ba ruwa da disginsi ni hakan ma yayi man ba kowa wace mace zata kawo mashi nonsense ba."
Tashi Zulaihat tayi tana wani cin cin magani tace.."Baby ni zan wuce gida." tashi itama Babyn tayi tana cewa.."okay muje na ajiye ki." Girgiza kai tayi tana cewa.."No bar shi nagode byee." Tafiya tayi ta bar su tsaye suna bin ta da kallo can kuma ta d'age kafad'a tana kallon Zubaida tace.
"Komai ke damunta?"sai kuma ta cigaba da cewa." Ko dai itama son Dr Najeeb din take?ai idan son shi take ba sai ta gaya man ba maiye sai na bar mata dan ni Zulaihat tayi man farkon ganinta zan iya bar mata komai ta nema a wajena."
Murmushi Zubaida tayi tana cewa.."Anya kuwa maybe dai kanta ke ciwo kiyi mata zato mai kyau mana,ki cigaba da son Dr Najeeb zan tayaki da addu'a." Dan b'ata fuska Baby tayi tana cewa.
"A'a ba zan iya cigaba da son shi ba gaskiya na tabbata akwai wata a kasa,zaune muke da ita lafiya fa sai labari muke amman lokaci guda tabi ta chanza hawaye nagani fa suna neman zubowa a fuskarta."
Yanda Baby ta damu yasa Zubaida ta zaunar da ita tana kallonta can kuma tayi kasa da murya tace ce mata.
"Do you now what?"
Girgiza kai Baby tayi cikin damuwa dan ta damu sosai da yanda Zulaihat ta tashi ta barsu wai zata tafi gida bayan suna da lecture da zasuyi guda d'aya kuma ta sani ta tafi gida cigaba da cewa Zubaida tayi.
"Zan so ace ki cigaba da fadin kina son Dr Najeeb a gaban Zulaihat kuma kina yabon kyaunshi da kuma class din shi."
Kallon Zubaida tayi tana cewa.."saboda mai kika ce haka.?" Furzar da iskan bakinta tayi tana cewa.."saboda mijinta ne." Wani irin tsorata Baby tayi tana tashi tsaye tana dafe kirjinta sai zaro Ido take waje cikin karma da rawar baki tace.
"What.?"
"Kwarai kuwa Dr Najeeb mijin Zulaihat ne,ita Yayata ce rana d'aya akayi aurenmu da nasu." Zama Baby tayi tana kallon Zubaida sai ga hawaye sun zubo mata sharrr a fuska tana sharewa cewa tayi.
"Amman maiyasa basu nuna sun san juna,fact ita bata ce man tana aure ba."
Murmushi kawai Zubaida tayi ta gaya mata auren da sukayi da irin tsanar da take mashi bayan kuma tana son shi tsanar ta danne son ,cigaba da cewa tayi..."ta wanann hanyar ce kadai zamuyi achieve,ba daman kin ce idan itama tana son shi zaki sadaukar mata dashi ba?"
D'aga Kai tayi tana cewa.."tabbas hakane kuma zan bada gudumunwata ta wannan hanyar in shaa Allah,kuma na cire shi a zuciyata dan da gaske nike son Zulaihat nike ta zama kawata kuma daman sun yi matching wallahi."
Murmushi Zubaida tayi tana cewa.."sauran shawara akan plan din zan yi tunani gobe zamuyi magana, amman karda ki nuna mata kin san alaqarsu ,ki cigaba da pretending akan kina sonshi ki ta yaba shi a gabanta har sai ta gane mai ye so da kuma kauna Ina son ta wannan hanyar ce kawai zata gane son da take mashi balle kuma naga ta kasa boye kishinta."
Murmushi kawai Baby tayi tana jindadi sosai ashe matarshi ce shiyasa yayi mata wanann question din a class kenan ,har zuciyarta take jin dadi duk da gaske take son Najeeb amman yanzun zatayi kokari taga ta dalilinta ta gyara soyayya dan sunyi matching sosai.
Tun da Zulaihat ta fito ba inda ta dosa sai office din Najeeb,nocking tayi bata tsaya aka bata umirni shiga ba ta shigo sai wani turo baki take tana tamke fuska,samun waje tayi ta zauna ta daura d'aya saman d'aya tana shakar fuska.
Tun da ta shigo bai d'ago Kai ya kalleta ba,dan kamshinta ya sanar mashi da itace ta shigo,daman yasan ba wanda zai mashi haka a school din sai mutun biyu daga ita sai Moha bama kamar ita.
Ganin bai da niyar kallonta ta tashi tana cewa.
"Nidai ka taso ni ka kaini gida."
Ajiye pen din shi hannunshi yayi yana kallonta sai kuma ya girgiza kai yana cewa.."akan mai zaki tafi gida tun yanzun bayan kuna da lecture kuma.?" Turo baki gaba tayi tana cewa.."haka kawai bani bukatar tsayawa wannan din ne."
Tsaki yayi yana buga mata tsawa yace..."na lura hauka da rashin tunani da wayau yana damunki,idan baki dawo a cikin hankalinki ba wallahi sai na dun ga zaneki na lura ke baki son a saka maki Ido ba sai ana tab'a lafiyar jikinki sanann zaki yi hankali ko.?"
Sunburo baki kawai tayi bata ce mashi komai ba,duba lokaci yayi yana cewa.."ooo yi maza tashi ki b'ace man da gani ki shiga class karda kiyi lating,kuma ban hanaki kin maida hankali ba,future din ki ne ba nawa ba, useless wanda bata san inda ke mata ciwo ba,rashin wayau yayi maki katutu da kuma rashin kunya abunda kika iya kenan."
Kin tashi tayi sai ma turo baki da tayi tana cewa.." nidai gaskiya gida zani ba zan yi attending din wannan lecture din ba sai next week kuma naji ba komai kace man duk abunda zakace ba haushi zanji ba kuma ba mamaki zanyi ba tunda nasan matsayina a wajenka,ba sona kake ba kuma ba kaunata kake ba dole mugayen kalamai su dunga fito a bakinka a kaina ba abun mamaki bane."
Kallonta kawai yake yana mamakin yanda ita a kulle take cewa bai sonta aikinta kenan daga fadin gaskiya har yayi mata mugayen kalamai,shi dai bai san ya zanyi mata ba ta gane son da yake mata ba,da ace tasan irin so da kaunar da yake mata da sai ta dunga tausaya ma zuciyarshi amman ita aikin Kenan bai sonta,furzar da iskan bakinshi yayi yana ce mata.
"Okay shkn tunda baki zuwa tashi shiga rest room din nan ki kwanta kafin na gama abunda nike sai na yi maki magana okay.?" D'aga mashi kai kawai tayi tana daukar jikarta tana shigewa room din da ya nuna mata tana gunguni,da kallo ya bita sai kuma ya saki tsaki yana cewa.
"Allah ka Kara man hakurin zama da wannan yarinyar." Cigaba da hidimarshi yayi yana duba lokaci dan shima yana da lecture din da za yayi.
★★
*JIGAWA 🥀*
Yau tun da ta tashi gabanta yake faduwa sai dai kawai tayi inalillahi wa'innalaihirajiun,dan rabon da taji faduwar gaba irin wannan har mantuwarta ta manta,bayan ta fito daga wanka zaunawa tayi a hankali ta fara shiryawa.
Shiryawa kawai take amman ita hankalinta ma baya gabanta tunanin da take d'aya ne idan sun je gusau shin mai zata iske?wata irin tarba su Baba zasuyi mata?bama kamar Baba da yake da zafi dan shi bai da wasa kuma bai daukar shirme da shashanci.
Duba time tayi taga lokaci yake tafiya ga shi kuma jirgin karfe biyu zasu bi da zai sadasu da gusau.. murmushi kuma tayi tana zura doguwar riga tana hango irin farincikin da zatayi idan ta saka Mama da su Nana a kwayar idonta.
Ita kanta tasan tayi kokari kuma tayi laifin babba marar musaltuwa da har ta iya daukar waya tabar gida,tabbas tasan bata kyauta ba kuma batayi ma kanta da iyayenta adalci ba,har da su Nana dan abun zai masu yawa da wane zasu ji?da gorin rashin uba ko kuma da gorin uwarsu karuwa ce? tabbas yaran abun tausayi ne.
Hawaye ta share tana mai yafa veil din ta tana cewa.."karku damu in shaa Allah ba zaku tab'a kukan rashin uba ba and karku damu da wai uwarku karuwa ce haka tawa da taku qaddarar take much luv my twins."
Fitowa tayi tana zama gefen Ammie tace."Sorry Ammie na barku kuna ta jirana ko.?" Murmushi Ammie tayi tana boye damuwarta na barinta da Jidda zatayi dan sun saba sosai bata son ko nisa tana mata sam cewa tayi.
"Bakomai Jidda tashi kije kici abinci har yanzun akwai sauran lokaci." Duba time din ta kara yi sai kuma ta kalli Ammie tana cewa.."AK fa.?" "Har yanzun bai fito ba maybe bai gama shiryawa ba ko.?" Dan shuru tayi tana cewa.."Anya kuwa Ammie? wannan wace irin shiryawa ce haka sai kace wanda zai shafa poder nida da nike shafa poder din har na rigashi fitowa."
"Rabu da shi yana nan zai fito maza kije kici abinci karda kema ki b'ata naki lokacin." Murmushi kawai tayi tana wucewa dinning din,zama tayi ta zuba gasasen biredin da yaji bama da sardine kadan ta dan fara ci ko d'aya kasa ci tayi ta ture tana dan shan tea.
Dan hankalinta baki d'aya yana wajen AK tasan abunda ta hana shi fitowa bai wuce tafiyar da zatayi yau ta koma Gusau da zama,tasan irin so da kauna da yake mata,tasan ba zai iya jurar rashinta ba ko na second d'aya ba
Tasan ba tun yau ba ya fara kewarta ta sani dan tasha kamashi yana kukan zuci akan rashin da zai yi na ta ,watarana ta nuna mashi ta ganshi su hadu suyi kukansu tare watarana kuma ta nuna mashi ganshi ba taje tayi nata kukan ita d'aya.
Tana tashi yana fitowa jiki a saki a sanyaye murmushi ya sakar ma Ammie yana cewa .."Morng Myluv." Kallonshi kawai Ammie take sai kuma can ta girgiza kai dan tasan hakan zata faru koma fiye da haka shiga damuwa ba da hana Ido bacci duk sai yayi duba da irin son da yake ma Jidda.
Itama ta shiga halin damuwa akan tafiyar da Jidda zatayi Ina ga shi? da yake sonta,so ba na wasa ba ai dole ya kasance a irin wannan statuation din koma fiye da haka.
Duba time yayi yana cewa.
"Sorry for keeping waiting " murmushi kawai Ammie tayi tana cewa.."Abinci fah.?" Girgiza kai yayi yana cewa."Am full." Harararshi Ammie tayi tana cewa.."okay Oya Oga maza kaje kayi breakfast karda kayi wasting time dinmu kasan dai Dad dinka baya son jira."
Marairaice fuska yayi yana nufar dining ganin ya nufo dinning ta koma ta zauna tana jiran isowarshi yana isowa taja mashi kujera ya zauna sai itama ta zauna tana kallonshi tace.
"Morning Beb."
Kureta kawai yayi da Ido yana kallo can ya furzar da iskan bakinshi yana cewa..."fatan kin tashi lafiya Partner. " Langwabar da Kai tayi tana cewa.."partially." kallon karin bayani yayi mata dan turo baki tayi tana cewa."just zanyi kewarka sosai and kasan yanda nike sonka Ina tsoron karda na koma Gusau wata tayi man kutse a zuciyarka ta ta ruguje gidan da nike ta famar ginawa Ina bashi ruwa." Dan shuru tayi tana furzar da iskan bakinta tana juya idanu ta cigaba da cewa.."ba zan iya jurar hakan ba,zuciya ba zata iya dauka ba sonka kaunarka kishinka sun mamaye zuciya Beb."
Tunda ta fara maganar ya kwafe ta da Ido yana kallon yanda take motsa karamin bakinta da yanda pitch lips dinta duke d'agawa kamar ana masu dole,shi kusan dariya ma taso bashi how come?as how?taya wata zata iya shiga cikin zuciyar da tuni ya mallakata ga wanda take so?Taya wata mace zata iya rushe gidan da aka gina da rodi da karfuna akayi ya'bon ginin da kwalta har za'a iya samun wanda zata iya rushe wanann ginin?never abunda ba zai tab'a faruwa ba har abada.
Shine yake a cikin irin damuwar da take sai dai mai tashi ta linka tata,yaushe duka duka ya samu karbuwa a wajenta?wata irin wahala ce bai sha ba akan samun sonta daga shi har iyayenshi sun sha wuya sun sha tunani da hasashen hanyoyin da zasu bi akan sonta.
Tabbas da ace akwai yanda zai yi da yayi da ace yana da iko ba zasu dira a garin gusau ba sai da igiyoyin aurenshi a kanta,yana tsoro kuma yana fargaba karda ta subuce mashi.
Tabbas ba zai iya jura ba,kuma jikinshi na bashi akwai abunda zai faru indan har suka je gusau a yau,yana tsoron karda iyayenta su ba da ta ga wanda suka gadama sukayi ra'ayi,tsoronshi kenan idan har yana wannan tunanin yana tausayin kan shi har da iyayenshi.
Idan ya duba yaga shi d'aya jal Allah ya basu bayan shi babu wata ko wani tunda Hafsat ta rasu,shi dai yasan duk randa aka wayi gari akace an bada Jidda ga wani ba shi ba tabbas tasan a ranar sai ya bakunci lahira.
To ya iyayenshi zasuyi?duk da daman mutuwa ta zama dole ba wanda yazo duniya dan ya dauwama kowa sai ya mutu amman sai kawai ya furzar da iska yana cewa.
"Zuciyar dana mallaka maki ta zama taki." Furrrrrr haka ya furzar da iska dan yama rasa mai zaice mata,baki ba zai iya masalta mata girman so da kaunar da yake mata ba,tabbas da ace tasan girman son da yake mata tabbas da ba zatayi tunanin zai iya kula wata mace bayan ita ba.
Ganin ba zai mata magana ba,duk da taga akwai magana a bakin shi wahalar fadinta kawai yake sai kawai ta fara bashi breed din tana dan bashi labari sai da yaci biyu ya kuma sanye tea din da ta hada mashi sanann suka dawo parlo.
Ko zama basu Kai da yi ba Dad yace su fito ko su tafi saura 20mn jirginsu ya tashi kuma dai sun san jirgi ba jira yake ba,da to suka bi shi suna tashi suka bi bayan shi har airport drive ya Kai su suna zuwa aka fara shiga jirgi basu dade ba jirgin ya lula zuwa jahar Zamfara Gusau.
Cikin minti talatin suka dira a airport din Gusau,bayan sun sauko daga cikin jirgin take kallon airport din sai kawai hawaye suka fara zubo mata tana sharewa.
Ganin airport din kawai da tayi sai ya tuno mata da abubuwa da yawa,wani waje ta kalli sai kawai ta saki murmushi mai ciwo,dan Kara kallon wajen tayi tana tuno ranar da suke zaune ita da Haidar a wajen sai soyayyarsu suke suna jiran a fara Kiran passenger.
Sun dade a wajen suna fira kafin a fara Kiran passenger din,bata yarda AK ya gane a yanayin da take ciki ba,sai ma murmushin yake da take zabga masu amman ita d'aya tasan inda yake mata ciwo ita kadai tasan irin zafin da rad'adin da take ji a zuciyarta.
Taxi suka samu suka zuba kayan su a boot sannan suka shiga suka gaya mashi unguwar da zai kaisu wato tundun wada...tun da suka dauki hanya take kallon Gusau tana lumshe ido tana share hawayenta,dan ta fidda rai da sake dawowa jahar gusau ta da a ranta har abada ba zata sake waiwayo jahar ba .
Amman sai gashi ta dawota ta dalilin mutanen kirkin da ta hadu dasu ,sun dawo da ita hanyar da tayi bakwana da ita sun cireta daga cikin duhu sun maidota cikin haske...sun haska mata hanya sun cirota daga cikin halaka tabbas bayan iyayenta bata da kamar su a duniyar nan.
Tafiya suka yi mai dan nisa daga airport zuwa anguwarsu suna shigowa cikin unguwar gabanta ya fara faduwa ji take kamar ta balle marfin motar ta doro daga cikin mota tai ta gudu.
Lura da yanayin da take ciki Ammie ta rike hannunta tana dan bubuga ta a hankali a hankali sai sauke ajiyar zuciya take tana mai addu'a a cikin zuciyarta dai dai kofar gidansu tasa taxi din ta tsaya... Bayan sun fito daga cikin motar sun sauke kayansu tayi tsaye tana kallon gidan zuciyarta sai bugawa take kamar ta fito daga kirjinta,kama hannunta Ammie tayi suka tura gate din gida suna shiga.
*AMATULLAH DATA SERVICES*
*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
VIA✓***
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank
*** for call or whatsapp
Share pls ✓