Free chapter · Read without an account
3
Bayan fitowarsu daga massalaci ne Abba ke sanar dashi zasu shiga Abuja jibi akwai meeting din da zasuyi acan, kuma Abba bazai iya shi ɗaya ba sai da Junaid ɗin, nan danan wani irin zufa Junaid ɗin ya riqa haɗawa lokaci ɗaya.
Kuma ya tabbatar gida ɗaya zasu kwana da Abba, tunda acan Abujan ma suna da gida, taya zai iya kwana biyu batareda macce ba? Abinda ya fara zuwa kanshi kenan, suna tafe har suka qaraso cikin gida, Abba nayi masa zancen muhimmanci meeting ɗin a wajensa.
Gaba ɗaya shi dai dai Junaid jin Abba kurum yake a wannan lokacin badan yana fahimtar me Abban ke nufi ba, suna shiga sallama yayi wa Abba ko part ɗin Mamma bai samu komawa ba ya nufi nasa part ɗin sa, shi gaba ɗaya hanyar da zai zille tafia da Abba kawai yake nema. Har yayi shirin kwanciyya barci wayarsa dake gefensa ta fara ring, Mamma ce mai ƙiran nasa, ɗagawa yayi a hankali gami da yin sallama cikin sanyi murya, tambayar farko da Mamma tayi masa shine meke damunsa dan jin muryarsa wani iri, shiru yayiwa Mamma na kusan sakan goma “Karka yimin miskilanci Junaid tell me meke damunka?" Tamkar wanda akayiwa duka yake faɗin “Abuja zamu shiga jibi nida Abba, ɗan murmushi Mamma tayi wanda yana jin sautin murmushin nata ta cikin wayar “Kaine magajinsa Junaid dole ka riqa taimaka masa da wasu abubuwa ƙarfin Abbanka ya ragu yanzu.” Ya mutse fuska ya shigayi tamkar Mamma na agabansa yake faɗin “Toh ya barni na wakilcesa mana Mammah ba dole sai yaje ba." Aran Mamamh tace ja iri saboda kaje ka sheki ayarka ko? Allah ya shirya min kai Junaid. idan tace kaddarar Junaid bata damunta zatayi qarya idan tace kaddarar Junaid tana hanata barci ana din ma ƙaryar zatayi, a duk safiyar Allah har fargabar take yaron nata yafita batasan yaran mutane nawa ya lalata ba, kalar qaddarar tasa nayi mata wani irin nauyi a kirji “Ka tabbata kayi shafa’i da wutri kafin ka kwanta?” Mamma ta faɗa cike da kulawa “Insha Allahu Mamma, ki kula da kanki ina kaunarki fiye da komai a duniya." Murmushi Kurum Mamma tayi gamida sauƙe wayar, ƙiran Khairiyya ne ya shigo a wayar tashi tamkar bazai ɗaga ba dan fushi yake da ita sosai akan wani vedio nata da ta saka a duka kafafen sada zumunta, wanda tsaraici ne zallah a cikinsa, wata irin ajiyar zuciya ta shiga saukewa jin ya ɗaga wayar "Mine meyasa kake azabtar da zuciya tane? So nawa xan baka hakuri akan wannan vedio ɗin, kuma kaje ka duba tun ranar da naga ranka ya ɓaci naje na gogesu duka." Still kin magana yayi, tamkar zatayi kuka take faɗin "Dan Allah kayi min magana idan ba so kake nayi hauka ba."
"Khairiyya zan kashe wayar idan kin gama barci zanyi," ya faɗa da wani yanayi mai tattare da fushi a muryarsa, me zanyi ka yadda dani dan Allah."kittttt taji ya katse wayar, kashe wayar yayi duka bayason takura yasan nacin khairiyya bazata daina ƙiransa ba,
Shi kuma still fushi yake da ita sai ya gaji dan kansa sa'annan zai sauko,wani murmushi yayi wanda iyakarsa a fatar bakinsa "Tayaya Mamma take hango masa khairiyya zata zama matar aurensa har ta zama uwar yayansa tayaya? A kullum tambayar da yake yawan yiwa kansa kenan, da gaske yana bukatar aure cikin rayuwarsa kodan Mamman sa ko zai samu zunubban da yake manne dasu zasu rage.
Washe gari bai tashi ba sai wuraren qarfe 11 na safe, ya na tashi kai tsaye toilet ya nufa dan yin wanka, daman daga shi sai boxer ne ajikiinsa dan baya kwana da kaya ajikiinsa, idan kaga Junaid Dikko da pyjamas a jikinsa to a parlornsa yake yana aiki da laptop ko zai shiga cikin gidansu da kuma ya fito zai ciresu, komai sanyi baya kwana da kaya ajikiinsa, a hankali ya saki shower ajikinsa tururin ruwan zafi na shiga cikin jikinsa, kasancewar lokacin hunturu ne.
Yafi awa ɗaya a toilet ɗin sai kace wanda zai canja fata .ya fito ɗaure da qaramin towel a waist ɗinsa sai kuma wani akansa da yake tsane gashin kansa dashi wanda ya cika masa kai asalin gashin hausawa, wanda sabida mayyunka masu tsada da yake shafa ma kan yasa ya nannaɗe ya koma kamar na larabawa.
Asali su….
Aliyu Dikko haifaffen garin Dikko ne dake cikin jahar Katsina, matan aurensa guda biyu uwar gidansa mai sunan Hajiya larai Dikko, yaro ɗaya Allah ya mallaka masu a duniya wato Junaid Dikko, daganan haihuwar ta tsaya masu kusan shekaru talatin da bakwai babu asibitin da basu shiga ba amman ko wane asibiti abu ɗaya ake faɗa masu daga uwar har uban lafiarsu kalau, a haka Abba ya auri Hajiya Rafia itakuma asalin yar Bauchi ce, suna da ya'ya biyu a tsakaninsu Amatullah itace yarsu ta farko mai shekaru goma sha bakwai a duniya yanzu ne ta shiga jami'a aji na farko a jami'a, babu yadda Mum batayi ba da Alhaji dikko ya kai Amaah ƙasashen waje tayi karatu har ya yadda Junaid Dikko ya ɓata komai, anan yake faɗawa mahaifin nasu macce ce idan ta tsallaka ta tafi waye zai kula da tarbiyarta?? Bakaramin ciwo Mum taji ba daga ita har Amaah, gashi dama wasu kawayenta da sukayi secondary school a tare kasancewar iyayensu nada hali duk ƙasashen waje aka turasu karatu, a karo na biyu Mum ta qara neman alfarma a wajen Abba, akan yabar Amaah ɗin taje Bauchi tayi karatu tunda iyayen Mum ɗin na a raye sai ta zauna a gidansu, buɗar bakin Abba a lokacin yake sanar da ita Junaid ya riga da ya samar mata gurbin karatu a (Umar Musa Yar'adua) haka Amaah ta hakura ba dan taso ba ta fara karatu inda take karantar (Accounting) daman can jininsa bai wani haɗu da Amatullah ba, tsanani yake yimata a duk inda zata shiga security ne a tare da ita har a makaranta.
Sosai abun ke damun mum akwai ranar da ta kasa hakuri ta kalli cikin idon Junaid ɗin tana faɗin an faɗa maka yadda kake ɗan iska haka kowa yake ɗan iska? Sannan ba ta fatar zunubin Junaid Dikko ya shafi ƴaƴanta yabari idan ya tara nasa ƴaƴan sai su raba zununbin a tare, Mammah na gun lokacin a tsaye bata san lokacin da hawaye suka fara Rolling akan fuskarta ba tun daga kurciyarsu har girmansu basu aikata wani abun da zai mannewa Junaid Dikko ba, basu taɓa aikata wani zunubi na saɓon Allah ba daga ita har Aliyu Dikko, kawai dai sunyi imani da Allah qaddarar Junaid ɗin ce a haka suna masa addu'a a kullum ba tareda sun gaji ba dan sunyi faɗa sunyi hantara abun ya faskara tun Junaid na ɓoyewa iyayensa halinsa har abun yazo ya bayyana.
"Meyasa bazakayi aure ba Junaid idan mata kakeso Allah ya baka ikon ka aje macce har hudu a karkashin kulawarka, meyasa sai mata kazamai? Matan bisa titi kana jin zaka yiwa Allah wayau ne na taka tsantsan da kakeyi da Rayuwar naka kannen? Kasan kannen mutane nawa ka ɓata ka san iyaye nawa kasa bakin ciki akan lalacewar ƴaƴansu?" Ya ɗaga kai ya kalli Mamman sa a lokaci wani irin abu ta ke hangowa cikin idanun Junaid Dikko “Da gaske ina son na bari Mamma, ke shaida ce da nace zan bari koda na sati ɗaya ne sai na yi zazzaɓi, kuma Mammah matan nan da ake magana akan su bani ke kawo su ba da kakafunsu suke zuwa, ni babu maccen da na taba samu a Virgin a empty suke kawo kansu." A lokacin Mamma ta ɗaga kai tana kallon yaron nata tana mamakin rashin ta idon Junaid.
Aysha Dikko yanzu ne take ss 2 a secondary school, itace kuma fav sis ɗin Junaid Dikko bayaga Mamma da Abbansa, Assha Dikko itace mutum ta ukku wacce yafiso a rayuwarsa. Gabaki ɗaya karatun Junaid Dikko a Oxford University yayi sa degree na farko da na biyu, degree na farko under business Administration yayisa sai digree sa na biyu medical science, sabida Mamman sa wacce itama a ɓangaren lafia ta karanta (political science) Tana aiki da (Dikko special hospital) ko kaɗan Junaid Dikko baya da ra'ayin business da ƙarfi da yaji mahaifinsa ya turasa cikinsa, tunda shi kaɗai ne ɗa namiji tal wanda ya mallaka a duniya, Aliyu Dikko yana ɗaya daga cikin masu kuɗin Nigeria wanda sukayi suna yana da kamfanonin da bai san adadinsu ba anan gida Nigeria da kasashen ketare, yana da gidajen manfetur, gas, plaza's, hotel's, Companyn sai da motoci da machine. Yafi ƙarfi akan kasuwanci fiye da likitanci, Amman duk da haka shine family doctor na Dikko's family.
Mum itama ƴar kasuwace tana da shops sun kai goma kuma tana siyar da different abubuwa acikinsu, itama tana da ma'aikatan dake ƙarƙashinta, idan kaga kiyayyar Mum to ɓangaren Junaid Dikko ne wanda keyi mata iko da ya'yanta fiye da uban da ya kawo su a duniya,
Aliyu Dikko shima a wajen mahaifansa shi ɗaya suka haifa har suka bar duniya sai ƴaƴan ƴan uwan dake zagaye dashi, wanda wasu ma a karkashinsa suke aiki kuma yana taimakon ƴan uwansa sosai, qaddarar Junaid bada garesu bane daga Allah ne, Allah ne ya ɗorawa Junaid Dikko neman mata tamkar hauka, sunyi faɗa sunyi nasiha sun razanar duk a banza, dan haka suka zubawa Junaid Dikko ido sai dai a duk safiyar Allah suna yiwa yaron nasu addu'ar shirya, da ga uwar har uban sun buɗe massalatai da islamiyya masu sunan (Junaid Ali Dikko ) suna nemar masa sassauci a wurin Allah, baya ga halin neman matan banza Junaid bayada wani hali wanda ba'a so kuma shi ɗin mutune na Jama'a haka abun hannunsa baya rufe masa ido. Kallo ɗaya zakayi masa kasan Mamma ta haifesa komai nata ne har kalar fatar watau baki, da wasu irin idanu Masha Allah wanda mafiyawancin idanunsa suke jan hankalin wasu matan, tsayawa zuba maku bayanin kyan Junaid Dikko zai ci mu lokaci ba'a gama ba yana da kyau sosai, ko kaɗan baya kama da Aliyu Dikko kasancewar Ali Dikko bafullatani ne kuma ɗan tsurut kun san jikin Fulani yadda yake saɓanin Junaid ɗin dake dogo kakkarfan namiji.
Cigaban labari..
#ASMY B ALIYU
#BA(secret relationship)
#Love, Romance and Destiny
#Junaid Dikko