Free chapter · Read without an account

1.

by Nazeefah Sabo Nashe · GASKIYAR LAMARI

★𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍✍️


★ALKALAMIN JIKAR NASHE📲

      


   *GASKIYAR LAMARI*

      (New book)


Wattpad @Nazeefah381.


Arewabooks @nazeefah.

  


*****




Page 1.



___________




A zaune a faffa’dan falon da ya k’ayatu da kayan furnitures zubin turkey Ash colour masu adon black. Tiles ‘din parlorn fari k’al sai ratsin bak’i daga gefe. Fa’dar kyau da tsaruwar falon sai wanda ya gani. Falon sai fitar da wani sihirtaccen k’amshi yake na asalin turaren wuta Halut, da sandal. Daga ganin falon kai ka san a cikin biyu dole a yi ‘d’aya ko dai ya zama na amarya ne da bata da’de da tarewa ba, ko na uwargidan da aka gina mata sabon gida ta kuma tare babu da’dewa. Tabbas an zubar da Naira wajen k’ayatuwarsa masana kuma k’wararru a fannin aiki sun yi k’ok’ari sosai wajen ganin zubi da tsaruwar falon ya tafi daidai da zamani.



Matashiyar mamallakiyar falon wato Muneeba, sun yi aure da mijinta Ammar watanni takwas da suka shige, tana zaune da tsohon cikinta a gabanta, kana ganin cikin ka san zai yi daidai da watannin bikinta wato takwas cif, duk da dai bai bayyana girma sosai ba zamantowarsa na fari.


Mijinta Ammar ma’abocin tafiye tafiye ne a yanzun ma ba ya k’asar ya tafi k’asar Jamus, dalili kenan na kawo k’anwarta da suke kusan sa’anni ta tayata zama, duk da dai Muneera ta fi Yayarta Muneebah girman jiki da tsayi da komai ma.


Tazarar su da k’anwarta a haife watanni sha ‘daya ne cif, hakan yasa idan ka gan su sai ka zata y’an biyu ne, duk da dai akwai banbancin sosai a tsakaninsu sai dai a hasashe da kamanni na zamantowarsu jini guda.


Muneeba kyakykyawa ce irin kyan da Bature yake kira Black beauty, tana da kyau sosai da dirarren jiki sai dai bata da haske bata kuma da tsayi kamar y’ar uwarta Muneerah.


Kyawun zuciya kam, anan ta yiwa Muneerah fintink’au, don koda yaushe ita a cikin takatsantsan da duniya take, tana kuma da ibada sosai da sosai Rabin lokacinta a cikin bautar ubangiji take, sosai take gujewa duniya da duk wani shagalce shagalce na cikinta. 


Ko ka’dan bata ‘dauki duniya da zafi ba, shi yasa kowa yake mata kallon kamilalliya marar wayewar rayuwa ko misk’ala zarratin.


Gefe guda kuwa Muneerah sab’anin y’ar uwarta kyakykyawar budurwa ce wacce kana ganinta ka ga kyau, ba sai ka tambayi na kusa da kai ba don shima zallar kyan zai gani da zarar ya kalleta, ba makusa ko ka’dan a jikinta ba ta da tawayar halittta tsaf halitarta ta cika hundred percent, sab’anin halaye da bata da kyawunsu ko ka’dan za’a iya ajiyeta a ten percent duk da dai akwai b’oyayyun kyawawan halayenta da suke gogayya da na y’ar uwarta a ba’dini.


Bata da son ibada ko ka’dan Farillar ma da kyar take kaita ba a maganar nafila, azimi daga na ramadan a sai na ramuwa su take iya yi idan ka cire wannan Muneerah bata jurewa ko wace irin ibada. Ta ‘dauki rayuwa da zafi sosai kamar yarda ta mayar da waya abokiyar rayuwarta duk wani social networking da Muneerah a ciki, ta yi suna fiye da tunanin mai karatu, abu d’aya ne bata yarda da shi ba, shaye-shaye da bin maza ko lesbian wannan kam bata amince da su ba, duk da idan ka ganta kai tsaye zaka iya dangnta tata da masu wannan huld’ar. Ba don komai ba sai don yanayin shigarta da ta zama ta zallar English wears matsatstsu na gaske. Idan ka ganta a irin shigar zata zaka yi daga k’asashen k’etare ta zo ba zaka tab’a yarda ta ha’da jinsi da Hausa fulani ba, duk da Ubanta Babarbarene Uwarta kuwa bafulatana ce Usul y’ar mutanen Jimeta.



Muneebah ta sauke sauk’ak’akkiyar ajiyar zuciya tana mayar da hankalinta kan y’ar uwarta da gaba ‘d’aya bata ma san me take yi ba, hankalinta yana kan waya da earpiece a kunnenta. Sosai take tausayinta da yanayin rayuwar da ta tsunduma kanta a ciki tamkar ta zo ta dawwama a duniyar ne. Bata da wani abu mai mahimmanci da ya zarce wayarta tamkar don ita ka’dai aka halicceta. A cikin kashi ‘dari na lokacinta kashi casa’in na waya ne hakan kuwa babbar asara ce ga bawa, saboda mu muke jiran lokaci ba shi yake jiran mu ba. Tabbas babbar fitina ce a cikin al’umma sharrin cikinta ya fi alfanun da yake cikinta yawa. Bature kam ya ci galaba a kan mu ta wannan fannin sai dai Allah ya shiryemu da duk zuri’a baki d’aya yasa mu mayar da wayoyinmu hanyoyin da zamu samu tsira ranar alk’iyama.


Tsakin da ta ‘dan ja ka’dan ne ya jawo hankalin Muneera wajenta ta yi saurin ‘dago kanta don sam bata son ganin y’ar uwarta a cikin damuwa ko ka’dan, tana sonta fiye da komai a rayuwarta. A hankali ta sauke narkakkun idanun ta a kanta tana fa’din “Ya aka yi Didi na, ko ciwon ne?” (Didi shine sunan da take kiran yayarta da shi)


Muneebah ta langwab’ar da kai, murya cike da sarewa ta ce “Bakomai Habibteey ina tunanin yanayin rayuwa ne kawai, musamman yarda waya ta ke ‘dauke miki hankali daga dukkan wani abu mai mahimmanci a rayuwarki.”


Muneera murmushi ta saki da har sai da beauty points d’inta na gefen hancinta suka lotsa ta ce “An zo wajen.” “Zan dameki da wa’azi ko?” Muneeba ta fa’da tana girgiza kai ka’dan. “Wa’azi ne ba kya so ko? A rayuwar nan idan kika ga mutum yana da mai gaya masa gaskiya ‘dan gata ne fa.” Cikin dariya Muneerah ta katseta tana fa’din “Ke dai Didi Akwai wa’azi, na gaya miki akwai lokacin da zan daina duka komai ma da zarar na kai 40yrs” Muneebah ta zaro ido tana cillinta da pillow “Ba na gaya miki ki daina irin wannan maganar ba sab’o kike, ko kun yi yarjejeniya da Allah zai bar ki a raye har wannan lokacin? Rayuwarki a hannunki take Habibteey? Ni Wallahi a yanzu ba ni da burin da ya shige ma na ga kin yi aure!” Muneerah ta zaro ido tana fa’din “Aure kuma Didi? Bari fa’da don Allah It’s too early ace na yi aure yanzu, yaushe ma garin ya waye, balle ma har yau ban ha’du da colour ‘din Mijin da nake so ba, duk wanda zai zo wajena sai na ga ba shi da qualities ‘din Mijin da nake mafarkin aure.” “Akwai” muneebah ta fa’da tana sakin wani murmushi da iyakacinsa lab’banta. Muneerah kuwa zaro ido ta yi tana kallonta “Bar fa’da Didi waye shi?” Muneeba ta girgiza kai “Ba wanda kike so Habibteey da ya zarce MIJINA AMMAR.” Wani irin hantsilawa Muneerah ta yi tana kallonta ga wani irin k’ugi da cikinta ya yi lokaci guda ta ji tana neman sakar mata zawo a kujera da sauri ta mik’e ta shige toilet ‘din da yake wani corridor a parlourn. Muneebah ta bita da murmushi mai nuni da zallar takaici da tashin hankalin da zuciyarta take ciki.



Muneerah ta da’de a toilet ta kasa fitowa parlourn bata son Sam su ha’du da Muneebah, abin mamakin ma a ina ta ji wannan maganar waye ya tona mata asiri? Ammar! Ta ji zuciyatta ta bata amsa da sauri ta girgiza kai tana furta “Nop! Ammar ba zai yi haka ba tunda ya san idan ya fa’da kamar kansa ta to nawa asiri da sauri ta shiga sharce zufar da take zuba daga goshinta. Da k’yar ta yi k’arfin halin fitowa parlourn ta na matsa yatsun hannunta da kyau ta kasa sakewa ta ha’da ido da Yayarta sai dai ta tamke fuskarta tana son nunawa Muneebahn ba haka bane. “Me yasa kuka b’oyewa duniya soyayyar da kuke wa junanku har kuka bari aka ‘daura mana aure da shi alhali kun san kuna son junanku?” Muneebah ta fa’da tana ‘dauke hawayen da yake son zubo mata daga idonta, da alama maganar ta da’de tana cin ta sai yau ta samu damar amayar da ita. “Don Allah Didi ki daina wannan zancen ta yaya kike tunanin zan so Mijinki ki tuna fa ciki ‘daya muke da ke uwa ‘Daya Uba d’aya ta yaya kike tunanin hakan.” Muneerah ta fa’da muryarta a raunane kamar ta saka kuka. Ita kuwa Muneeba cizan leb’enta ta yi ta ce “Hakan ba zai hana shai’dan ya kwa’daita muku son junanku ba, balle ba tun yanzu kuka fara son junanku ba, kuskurena ‘d’aya da ban fahimci hakan ba sai bayan aurena da Yaya Ammar tabbas da ba zan auresa ba zan bar miki shi ko da son sa zai zama ajali na, amma a san da na sani lokaci ya k’ure don komai ya Riga ya shiga tsakanina da shi.” Ta share hawayen idanunta “Na san ba ni ba ce a zuciyar Ammar kece a zuciyarsa ni yana so na ne don sabida kyawun halayena yayinda ke yake son ki saboda sura da kyan jikinki na kuma tabbata soyayyarki itace mafi rinjaye a zuciyarsa. Abinda yasa ban saka ya sake ni ba tilas saboda hadisin da Manzon Allah ya ce Allah yana fushi da dukka matar da ta saka Mijinta ya saketa Amma ki yi hak’uri Muneera bana son duk wani abu da zai tab’a miki zuciya balle ace daga wajena ne. Na san wata rana zaki mallaki Ammar a matsayin Miji don ina ji a jikina rayuwata tak’aitacciya ce ba zan da’de a duniya ba.” Da sauri Muneerah ta rufe mata baki tana kuka ta ce “Please Didi baba son kina zancen mutuwa. Wa ya san ranar mutuwarsa?” Muneebah ta saki murmushi kawai tana murza hannun y’ar uwarta cikin nata ta ce “Tabbas babu wanda ya san ranar mutuwarsa nima kuma ban ce miki yau ko gobe, yanzu ko anjima zan rasu ba, amma a kowane lokaci Ubangiji zai iya amsar ran bawansa ya shirya ko bai shirya ba shi yasa ake son kullu yaumin bawa ya dinga k’addarawa kansa mutuwa. Ake kuma son ya dinga tanadin lahira da tsammanin ba zai k’ara ‘dakika guda ba.”


Muneerah ta damk’i hannunta tana fa’din “Ba zaki mutu nan kusa ba Didi In sha Allah sai mun ga jikokinmu har da tattab’a kunne….” Muneeba ta saki murmushi tana fa’din “Ba na jin hakan zata faru, ban tab’a k’addarawa kaina hakan ba ni na fi so na Riga iyayena mutuwa ko bakomai zan samu adduoi daga bakunansu addu’a iyaye ga y’ay’ansu karb’abbiya ce In sha Allah, fatan da nake Ubangiji ya yafe mana kura-kurenmu…..” ta fa’da tana kawar da k’wallar idanunta kafin ta sake dank’arawa hannun Muneerah ta ce “Na fahimci kuna son juna ke da Yaya Ammar ne ranar ‘daurin aurenmu bayan an ‘daura ba ku san duk kukan da kuka yi a ‘dakinsa a cikin kunnuwana ba, duk wani sirrin zuciyarku da kuka fasa ranar na ji shi na yi kuka sosai na kuma rasa menen mafita..



★𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍✍️

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol