Free chapter · Read without an account
ZAZZAFAR KAUNA 151&160
*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*
*BOOK THREE*
_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_
_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_
_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! ***_
***
*151-160*
Tura office din Moha yayi yana shiga da sallama a bakin shi, d'agowa yayi yana ansa sallamar sai kuma ya ajiye pen din hannun shi yana kallon Moha,bayan Moha ya samu waje ya zauna suka fara gaisawa sai da suka gama gaisawa sannan Moha ya fara cewa..."Munyi magana da wannan yarinyar fa Najeeb." Murmushi Dr yayi yana cewa.."Gud ya kuka yi da ita.?" Gyara zama sosai Moha yayi yana kallon shi ya cigaba da cewa.
"Komai ya tafi normal yanda ya dace na kuma tsara sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba."
"Wani hanzarin kenan.?"
"Maganar waya ba da ita zaka dunga pretending din waya ba bcox kar da a shiga hak'in yarinyar kamar yanda kace tun farko shiyasa nayi tunani bayan na koma gida sai na yanke wani plan din."
Kallon karin bayani yayi mashi,kuma Moha ya gaya mashi duk yanda sukayi da Baby ba abunda ya manta bai gaya mashi ba, cigaba da cewa yayi..."kasan dawa yanzun Kai zaka dunga pretending din.?" Girgiza mashi Kai kawai Najeeb yayi yana murmushi,shi abun dariya ma yake bashi kuma Moha tausayi yake bashi kamar yanda yake tausayin kan shi,yasan wacece Zulaihat kuma yasan taurin kanta da yar'banzar zuciyarta kamar ta kafiran farko.
Shi yasan sam yarinyar ba son shi take ba kamar yanda ta ambata ,daga zuciya har baki haka maganar take bata son shi ta fito kuma yaga tsintsar gaskiyarta a cikin kwayar idonta..tabbas yana fatan sun sansanta sunyi rayuwa irin ta kowa sun nuna ma junansu so su taitala junansu su tairairayin juna su nuna ma juna zazzafar kauna...amman taya?yaji ya kuma yarda yana da laifi tun farko shine bai jata a jiki ba bai nuna mata taitali ba balle kuma so da kauna,ya dauka to yana son ta ba shi chain yana son ta bashi dama ta karshe ya nuna mata irin son da yake mata.
Yana son ta bashi Koda wata d'aya ne tal ya nuna mata matsayinta da girman da take da shi a zuciyarshi,yana son ta bashi dama ya bude mata zuciyarshi taga gidan da ta gina a cikin zuciyarshi ba tare da ita ta sani ba,shima kasan shi bai sani na bai fargaba sai dai kawai yaji ginine wanda ba zai tab'a iya rushewa ba.
Tabbas yasan zata kaunace shi zata so shi zata riritashi,amman idan ta daure ta bashi chain na wata d'aya wata d'ayan ma yayi yawa shi sati d'aya ma is okay,amman idan zata daina yi mashi tsiwa da rashin kunya sune bai jin zai iya dauka a matsayin shi na mijinta ta dunga kallon idon shi ba kunya ba tsoro ta gaya mashi magana.
Abunda kuma ba zai dauka ba idan har tace zata cigaba da wannan bed behevoir din nata ba zasu tab'a shiryawa ba,ba zasu tab'a zama inuwa d'aya da ita ba,zaman su ba zai tab'a daurewa ba kuma ba dan bai sonta ba ,a'a dan rashin kunyar ne kawai zai rabasu shi dai ba zama zaiyi yai ta bugunta ba,balle ma da iliminta da hankalinta ba zata tsaya ta saki jiki ya kama wani bugunta kamar wata jakka..tabbas yasan ba zata yarda ba maganin ayi karda a fara. numfashi yayi yana ce ma Moha.
"Da wa zan dunga yin wayar."?
Dan shuru Moha yayi sai kuma yayi murmushi yana cewa.."Da Seemarh." Kallon baka da hankali Najeeb yayi ma Moha sai kuma can yayi tsaki yana girgiza kai yana mamakin yanda komai za'ayi da Moha ba'a gamawa sai ya kawo shirme da hauka kamar wani yaro,shi gashi dai kamar ya fara hankali amman idan yayi wani abun sai kaji kamar ka tashi kamashi Kai ta Mari ko kaji saukin takaicin da ya kunzuga maka,tsaki yayi a karo na ba adadi yana hararar Moha yace.
"Kaji matsalarka ko?kaji shirmenka ko?Kai yanzun a tsakaninka ga Allah Moha ka rasa wa zaka sako a cikin shirmenka sai Seemarh? Seemarh fa Moha?kana nufin da girma na zan dunga yage baki Ina gayama kanwata kalaman soyayya kanwata din ma wai Seemarh,yarinyar da take ganin girma na da mutuncina tabbas yau na ida yarda hankalinka ragaigeni ni wallahi Zubaida tausayi ma take bani da take zama da kai kana da wannan halin Kai dai ga ka nan hankali hankali hauka hauka to sake wata ko kuma a bar plan din baki d'aya kawai."
Dan shuru Moha yayi yana kallon shi sai kuma ya b'ata fuska yana cewa.."ni din ne mahauka ci ko.?" D'aga Kai yayi yana cewa.."kusan mahaukaci mana Moha,inba hauka ba taya zaka ce nayi soyayyar karya da Seemarh bari fa kaji Seemarh matar aure ce kuma ni nan akwai aure tsakani na da Seemarh tun da ba ciki d'aya muka kwanta ba understand me Moha."
D'aga kafad'a Moha yayi yana cewa.." ka kawo uzurinka amman har na samu wani mafitar kuma Allah yasa shima yayi maka karda ka sake zagina dan kawai kaga na damu da damuwarka ai dole kayi man duk abunda ka gadama ai." Murmushi Najeeb yayi yana cewa."sorry nawa ba zan sake ba ai nima ai na damu da damuwarka idan baka damu da damuwata ba wa zai damu da ita tun da wanda zan ma gaya ma damuwar bata bukata ta a rayuwarta Kuma dai kasan su Ammie su ba cika maida Kai sukayi da wani concentrate akan damuwar mutun ba idan ba babba bace."
"Yeah! Haka ne kuma ni cewa nayi mai zai hana mu dunga yin wayar a matsayin saurayi da budurwa idan kuna tare muna message ya kaga wasan zai kasance." Kure Moha da Ido Najeeb kawai yayi yana tunanin anya Moha ba kwayoyi ya fara sha ba?Kodai wannan sanyin da ake ya fara rudashi daman yasan shi bai son sanyi ko kadan,kallonshi yake sosai yana son gano Ina matsalar take ya ke ta soki burutsu sai kace wani wawa.
Ai ko wawa ma baya haukan da Moha yake yi a yau din nan,taya zasu wani kama wayar soyayya bayan shi bai da muryar mace?shi da yake da murya irin ta ingarman mazajen nan a haka zai kama waya da shi yarinyar ta koma yi mashi kallon banza yana soyayya da mace mai murya maza babu langwasa murya balle kuma azo ga yar'shagwabar nan da ake ta soyayya sai kawai yayi tsaki yana cewa.
"Heyy Mr Man I beg please get out of my office."
Dariya Moha ya fashe da ita yana k'ara gyara zaman shi sai dariyar shi yake, daman yasan da wuya ya karbi wannan shawarar amman kuma dolen shi yayi accepting dinta , Dan ita ce last chain din su a wannan plan din nasu,haushin yanda yake mashi dariya yaji wato haukan dai ne yake da gaske kuma ya rasa a Ina zaizo yayi shirmenshi sai a office din shi yazo ya hanashi aikin da ya dace yayi, yana ta yi mashi wawanci tsaki yayi yana cewa.
"Dan Allah Moha ka tashi ka barman office kaje office dinka ka kira matarka tazo kayi mata haukanka ko kuma ka kwasheta kuje gida sai kayi haukan nasan ita zata iya dauka,ko kuma nace ta saba da wanann wawancin naka ni dai kam ba saba ba balle kace."
Tsagaitawa da dariyar shi Moha yayi yana cewa.
"Ai Najeeb a wajenka na koyi hauka da wawancin my friend c'mon tsaya kaji yanda abun zai kasance sai ya ma fi show akan wata Seemarh dan sai yanzun naga tsab zata iya yi mana hauka da shirme tunda kasan ta da wasa ,sai ana maganar gaske ta maida ta wasa da dai Meelat ce kuma daman nasan ba zaka yarda a saka Meelat a maganar ba shiyasa ma ban kawo ta ba."
Dan shuru yayi yana hutawa saboda da dariyar da yayi sai kuma ya dauko ruwa mai saukin sanyi a freeze ya sha yana zama ya kalli Najeeb ya fara cewa.."haba Najeeb sai kace ba wani dan Boko ba haba Dr ne fa kai?Dr fa Najeeb amman ace baka san komai na technology ba?abun kunya ne wallahi wasu ma suji halin da ake ciki kamar ka dai baka san ana chanza voice ba a waya haba mana just voice dina zan chanza ba Ina da waya Smart phone ba.?"
D'aga ma shi Kai kawai Najeeb yayi yana kallon shi yana son yaji karshen wannan game din dan shi mamaki Moha yake ba shi sosai,Ina yasan ana chanza murya a waya? tambayar da yake ma kan shi kenan,Dan shi yasan kullun dai suna tare basu rabuwa ada harda bacci a room d'aya suke yi da suna kano amman duk bai san ana chanza voice ba sai yau to shi wa ya koya mashi ana wani change of voice a waya,cigaba da cewa Moha yayi.
"To yanzun nan zan tafi na sawo sabon layi nayi mashi register zan kiraka sai kayi man saving da Baby or hayateey Kai kawai ka saman man kalbi ka bani da heart din soyayya zan dunga kiranka muna waya zaka sha mamaki wallahi guy sai kazo kana man godiya daga baya I swear."
Dariya Najeeb yayi sai da yayi mai isarshi,tun da ya fara dariyar Moha yake kallon shi yana mamaki yana mamakin yanda yau yaga Najeeb yana dariya har da rike ciki dan mugunta,wato ya hango irin muguntar da suka shirya ma yarinyar mutane shiyasa yake wani wage baki yana dariya, haka kawai ai ba zai yi dariya ba sai dai yayi murmushin banza da wofi komai zakayi sai kowa yayi dariya a waje banda Najeeb sai dai ya murmusa kawai...amman ba dai yayi maka dariya ba, murmushin ma ba ko da yaushe yake yin shi ba zaka iya yin abunda kowa zai yi dariya shima ko murmushin ba zai yi ba, weaving Najeeb yayi mashi yana cewa.
"Wanann kallon fa?ko naci ban biya ba.?"
Tsaki Moha yayi yana girgiza kai sai kuma yace..."wallahi Najeeb baka yi ba sai an chanzo ka gaskiya Najeeb." Harararshi Najeeb yayi yana cewa.."ai Kai kayi ko.?" D'aga Kai yayi yana tashi tsaye yace.",yeah sosai ma." Dariya Najeeb kawai yayi yana cigaba da aikin da yake shi kuma Moha ya fito dan zuwa ya sawo sim kuma ya tafi gida ya dan huta kafin lokacin tashin Darling din shi yayi yaje ya dauko kayan shi.
★★
Koda suka koma cikin class wajenta suka nufa suka zauna suna dan labari ita dai Zulaihat da uhm kawai take bin su dan bata son wata magana...kuma ita bata son wata magana mai tsawo tana had'a ta da Baby dan haka kawai take jin haushinta ganinta bata son yi dan kawai bata da yanda zata yi ne.
Bayan second lecturer din su na yau ya shigo ya fita Baby ta kalli Zubaida tana cewa.."Sister bari naje office din Habibi Kinga yace idan muka gama wannan lecture din nazo zamuyi maganar da nace kafin muyi 2-4 din nan fa."
Dan kallonta Zubaida tayi tana cewa.."Sis Baby yaushe kika samu damar shiga office din Dr har kuka yi magana duk zafin shi ba ko jin tsoro.?"
Murmushi Baby tayi tana kama baki sai kuma tace.."abunda kake so fa Sister kuma kake kauna kake mararin kasancewa da shi har *DA'IMAN ABADAN* kake fatan kuyi soyayya a kal'kashin inuwa d'aya kununa ma juna *ZAZZAFAR KAUNA* shine zan ji tsoron shi har na kasa gaya mashi sirrin da ke raina.?"
Dan shuru Baby tayi sai kuma ta cigaba da cewa..."mutun har mutun kamar Dr Najeeb ai ba zaka yi wasa da shi ba, idan Allah ya baka shi rike shi zakayi kam ka samu ka mamaye zuciyarshi ka samu ka saka mashi kaunarka yaji idan har babu ke sai dai ya mutu,yaji ba zai iya rayuwa da kowace 'ya mace ba sai ke,ki samu ya mamaye komai ki baibaye komai kiyi kaka gida da zuciyarshi ki anshe makullin zuciyarshi taya na samu wannan damar zan yi wasa da ita?ai samun namiji kamar shi ai babban aiki ne dan haka bari kiga tun da har yace nazo ai zuwa zanyi ba zan yi wasa ba."
Tunda ta fara maganar Zulaihat take bin ta da wani irin kallo,ji take kamar ma da ita Baby take dan yanda take maganar sai kace tasan akwai alaqa tsakaninta da Najeeb, wani irin kunci da rad'adi ya tokare mata zuciya da taji tama je wajen shi har sunyi magana and yama ce ta dawo su ida maganar kenan saboda karda tayi missing din lecture shiyasa yayi excuse din ta?wato yasan zai hadu da Baby su yi soyayya shiyasa yau yaci uban wanka ya wani sha gayu kamar wani ba indiye.
Shiyasa taga yana ta rawar kafa yana wani rawar Kai ashe duk akan haduwa da Baby ne,tabbas ruwa baya tsami banza shiyasa jiya bai shigo gida ba sai wajen 9:30 yana can suna wayar soyayya kenan,shiyasa yanzun ya daina nuna ya damu da ita balle ya nuna yasan da zaman ta a gidan shi,ai dole tin da ya samu wanda yake so daman ita ba sonta yake ba shiyasa har yace zai sake ta nan da yan watanin masu zuwa..maganar Baby ce ta dawo da ita daga duniyar da ta lula Baby tana cewa.
"Sister Zulaihat na tafi bari naje karda na b'ata ma Masoyina lokaci Habibi daman yace man bai son b'ata lokaci da kuma rashin kunya da tsawa a wajen mace,yana iya rabuwa da kowa mace ce idan har zata dunga yi mashi rashin kunya da kuma tsawa dan bai dauka." Tafiyarta tayi tana dariyar mugunta dan tana hange kishin da yake yawo a saman fuskar Zulaihat har da hawayen da suke kwance a saman idonta.
Maida kanta gefe tayi tana goge hawayen da suka zubo mata tana sauke ajiyar zuciya,sai kuma ta girgiza kai tana hangen duniya juyi juyi yau itace take fama da ciwon son wanda bai sonta,tabbas ta yarda da tana son Najeeb tun randa ta nemi ya saketa ya kuma ce zai saketa bata sake samun natsuwa ba a zuciyarta babbar damuwarta yanzun Baby ce taya ta samu fuska a wajen Najeeb har yake gaya mata role din shi haka? tabbas da gaske take baya son rashin kunya da tsiwa itama sheda ce tun da har ya gaya mata.
Abun da yaja mata kenan har ya daina sonta idan ma da gaske yake yana sonta kamar yanda ya gaya mata..."zan iya rabu dake Koda kuwa sonki da kaunarki zasu zamo ajilina Zulaihat dan ba zan iya daukar wannan rashin kunyar taki ba da rainin wayau tun dai a matsayina na mijinki zaki iya yi man tsaki da tsawa babu ko tsoro ni a gidan mu ba'a koyaman yi ma na gaba dani tsaki ba." Kalaman shi na karshe da ita kenan dashi da yayi mata lokacin da tayi mashi tsaki da tsawa,tabbas ta anshi laifinta ta kuma yarda tayi kuskuren da tayi mashi tsaki a matsayin shi na mijinta,duk lalacewarshi ai mijinta ne tun da har ya bada sadakinta.
Da fata Zubaida tayi tana cewa.."Sis kina jin abunda naji kuwa a wajen Baby.?" Kallon Zubaida tayi daga sama har k'asa sai kuma tayi murmushi tana cewa.."to Ina ruwana da hadimarta?kin ma bani mamaki da har kike man wanann maganar,bayan kuma maganar bata shafeni ba kuma ai ke kikayi mata hanya har ta samu abunda take so,ba wani abu mamaki bane dan dan'uwanka ya nuna bare ya fika a wajen shi Thank God ba a kaina aka fara ba ai."
Zaro Ido waje Zubaida tayi tana kallonta sai kuma tayi murmushi da ta tuna daman Moha yace sai tayi hakuri ta daure ta kauda kai da duk abunda Zulaihat zata ce mata akan wannan plan din,sai ta cize ta nuna bata san tana yin duk fushin da zata nuna tana yi da ita , numfashi ta furzar tana cewa..."nayi mamakin jin wanann maganar a bakin ki Sis,amman ba komai tun da haka kika dauka ba zan hanaki ba sai dai ki sani ban san komai ba,asali ma tare dakai ta gaya mana abunda ke ranta akan Dr and kuma ba waya muke da ita ba,bamu haduwa sai a school kuma tare dake dai muke zaune,wallahi ban san sanda taje har suka kulle ba amman idan kin yarda."
Wani kallo tayi mata tana cewa.." wai sai mai idan sun kulle?nifa ba damuwa ta bace idan sun tashi sun Isa su masoyane gobe ya kawota gidan shi a matsayin mata ni banda damuwa da wannan Ina fatan kin gane and daga yau karda ki sake yi man wata magana da ta danganci Najeeb da Baby bani bukata dan ba wannan shirmen bane a gabana please take note."
"Shikenan Sis Allah ya baki hakuri kuma ki yafe man idan ma nayi maki laifi ni ban sani ba and maganar Baby na daina yi maki ita amman ba zan daina yi maki maganar Najeeb ba ko baki son komai ya wuce ya zama kamar bai faru ba?shin baki shi'awar kuyi rayuwa irin ta masoya har *DA'IMAN ABADAN*? Sis lokaci yayi da zaki gane gaskiya gaskiya ce , lokaci yayi da zaki sauke girman Kai ki rungumi mijinki hannu biyu ki taitalashi ki nuna mashi so ki nuna mashi *ZAZZAFAR KAUNA* lokaci yayi da zakiyi yaki da zuciyarki ki Kori duk wani sheda da yake maki wasa da hankali yana nuna maki wai ba sonki Dr Najeeb yake ba."
Sauke ajiyar zuciya Zubaida tayi tana cigaba da cewa.."haba mana Sis ya kamata ace yanzun ace kin zauna kiyi tunani kin gano irin son da mijinki yake maki,kiyi tunani mana baya sonki har zai aureki?inace da bai sonki wallahi ba zai tab'a aurenki ba and bama zai dauki duk abunda kike mashi ba,wallahi son da yake maki ya wuce wasa ya kuma wuce a kwatantashi wallahi kin san tun ganin farko da yayi maki a duniya ya kamu da kaunarki kuwa Sis.?"
Ita dai Zulaihat kallonta kawai take tana auna duk maganar da take mata,dan yanzun ta yarda tana bukatar wanda zai nuna mata hanya tana bukatar wanda zai haska mata hanya ta gano irin kaunar da yake mata,tana bukatar itama a nuna mata so da kauna kamar yanda ko wace mace take samu a wajen mijinta.
Tabbas hakane da ace bai sonta ba zai aureta tabbas hakane kuma yasha gaya mata irin son da yake mata a zamanta gidan shi,maiyasa ta kasa fahimtar son da yake mata?maiyasa kwakwalwarta ta toshe ta kasa gane irin *ZAZZAFAR KAUNAR* da mijinta yake mata?maiyasa bata gane tarin son da yake mata ba sai da ta makara?sai da komai ya ceb'e mata har yana kokarin bama watanta makulin zuciyarshi bayan ita ta dace da ya ba wannan makullin taya zata wargaza komai?taya zata yakice Baby a cikin rayuwarshi?
Taya zata hana faruwar abunda yake kokarin faruwa bata da saurin current komai ya tsaya mata cak ya tun kushe mata,tabbas akwai aiki babba a gabanta dan ba zata tab'a barin Baby ta shigo gidanta ba a matsayin kishiya ba, kishiya fa?Taya ma zata iya kishi da wanda ta nuna tana sonta tun haduwar farko?bama zata tab'a barin hakan ta faru ba..(hmmm! Namu Ido yan team Najeeb 🤣 mudai ai mun gama da babinta ahtoh ,ta Baby muke Yar soyayya 🤓).
Dafata Zubaida tayi tana kallon yanda hawaye suke zuba daga cikin idon Zulaihat,goge mata hawayen ya dunga yi tana cewa.."haba Sis ba kuka zakayi ba,yanzun ba kuka bane a gabanki tashi zakiyi kiyi yaki kwato mijinki daga hannun Baby tashi zakiyi ki hana faruwar wannan soyayyar da suke kokarin kullawa and kuma ki daina wanann hawayen karda hankalin mutane ya dawo wajen mu."
Shuru tayi tana share hawayenta tace.." Taya zan iya maido da hankalin shi wajena Sis?Taya zan iya wannan babban aikin?mutumin da ko kallona yanzun bai yi balle yayi man magana ko sallama ta baya ansawa kuma bai zama a inda nike ya zanyi da rayuwata? Damai zanji da I don't care attitude da yake nuna man? ko kuma da soyayyar da yake shirin fara yi da Baby Sis? seriously ban son ko kallona Baby tana yi taya zan gaya mata ta daina yi man magana tayi hidimarta nima nayi tawa."
Girgiza kai Zubaida tayi tana cewa.."Ai daurewa zakiyi ki cire wannan kishin naki ki dunga nuna mata kina supporting din ta akan soyayyar tana nan zaki dunga jin ya yanayin alaqar tasu take Kinga ba zaki sha wahalar kawo karshen alaqar su ba and ki chanza ki chanza daga yau ba sai gobe ba,ba kunya da kin sauko kin nuna mashi komai ya wuce ba wani abu bane zaki Kara martaba a idon shi ki kara mashi sonki a zuciyarshi balle ke da yake so ma. rashin kulawar da kike mashi da gaya mashi maganar da kike yanda kika gadama yasa fa ya fara kula wata Baby, amman yana dake Mai zaiyi wata Baby wallahi da yana samun kulawa a wajenki wallahi kallo Baby ba zata ishe shi ba."
Cigaba da cewa Zubaida tayi.."kin fa San waye Dr Najeeb sarkin yan disgi... har ya gama zaman BUK bai dauki nonsense ba balle nan yanmata nawa suke son shi a BUK wani irin abu ne bai masu idan suka kawo mashi kan su ba wulakancin da bai masu fa Sis,manya mata ma yan duniya sun buka sun kasa balle Baby cikin minti nawa zakiyi solving din case din nan ki cigaba da kula da mijinki Sis."
"Hakane Sis kuma na fahimceki in shaa Allah daga yau zani chanza ,chanzawa ta har abada dan nima yanzun na daura d'amarar kula da mijina zan kula da kayana na nuna mashi *ZAZZAFAR KAUNA* na rayu da shi har *DA'IMAN ABADAN* Dan haka na shirya Karawa da duk wata banza da zatayi gigin shigowa gonar da ba tata ba Sis."
Murmushin nasara Zubaida tayi tana cewa.."Ahtoh kinyi ma kanki fad'a idan kuma kika tsaya girman Kai kina ji kina gani zaki zama banza a gidan shi ko kuma kina ji kina gani a fiddaki a gidanki dan haka ki kama mijinki ki kula da mijinki karda kiyi wasa da damarki Sis." D'aga Kai kawai tayi tana hasashen yanda zata maido da hankalin shi kanta,tana hasashen yanda zata mantar da shi duk wata soyayya 'ya mace ta maina mashi tata soyyyar ta mallake mashi zuciya ta mamaye duk wani Sako da Loko a zuciyarshi.
*Hhhhhh warrrr! Ya kuke tunanin wasan zai fara Zulaihat tana Shirin yada makaman yaki ta rungume mijinta....ooooo ni Jameey ba ko kunya ga Zulaihat wai kayana🤔,kuji fa wai Najeeb har ya samu matsayin da ake kiranshi kayana ahtoh ba ruwana nidai🌚*
*Akwai Data available masoya akwai ko wane network kuma cikin rahusa 270 1GB ko wane network,banda 9Mobile shi 300 1GB*
*Zaki biya kudin data idan kina bukata ta wannan account din *** Jamila Bello Abubakar Opay bank,*** for call or whatsapp*
Share✓