Free chapter · Read without an account

35

by Nabeeha Aminu · TSANANI

69/70





***





"Amna zuciya ta takamu da sonki tun ranan dana fara jin muryan ki, ta kwad'etu da son mallakan ki tun kafin tasan waye ke, ban damu dake waye ba kuma ban damu da abunda kika aikata ba burina kawai naga kin dawo Mata agareni, wallahi Amna ina sonki sona gaskiya da amana dan Allah ko baki sona ki yarda ki aure ni nasan zan iya zama dake a haka, a kowa ne dare idan nazo wajen ki nakan koma gida ina kuka saboda nasan bazan sake ganin ki ba har sai gobe idan na dawo, bazan sake jin muryan kiba harsai na sake zuwa gare ki, ina son ki zamo mallakina a cikin mafarkina da kuma a zahiri, ki zamanto cikin hirata da sauran dukka zantukan bakina, faruwar hakan zai inganta farin cikin zuciya ta"


Durk'usawa tayi a wajen ta saki kuka maicin rai tace "kaito na kaiton rayuwa ta kaiton kasance ta a raye kaiton ganin wannan ranan danayi a rayuwa ta, ina ma na mutu kafin wannan ranan, Hamma Ammar maiyasa ka fara furta mun wannan kalman mai tsada da muhinmanci a rayuwata, naso harna mutu karna gamu da wanda zaice yana sona, nasan faruwan hakan zai iyasa nagama rayuwa ta cikin k'unci da takaici, Hamma Ammar niba kowa bane face shegiya wanda aka aifeta ta hanyan Zina, kuma bana bak'in cikin kasancewa ta hakan domin tanan Allah ya tsara zuwa ta duniyan, sannan niba y'ar kowa bace ma'aifina ba kowa bane face baffulatanin riga mai kiwon shanu, amma ina alfaharin kasancewar sa uba a gareni, meyasa kana cikekken d'a wanda aka aifesa ta hanyan raya sunan Annabi s.a.w, sannan kai mai arziki ne iyayen ka masu arziki duk wani wanda ya futo daga tsatsan ku masu arziki ne sannan ba d'an shege a zuri'an ku, nasan iyayen ka bazasu tab'a amince da auran mu ba saboda ni ba kowa bane ma'aifina ba komai bane maiyasa zaka had'a kanka dani, kuma bani da kowa a duniyan nan daya wuce Allah na"


Murmushi yayi yace "ki zamo na kowa koda kowa bazai zamo naki ba, yiwa kowa fatan alheri koda akwai masu yimiki fatan sharri, saka dukkanin musulmi acikin addu'an ki koda babu mai sakaki acikin addu'ar sa, nufi kowa da alheri koda akwai masu nufar ki da sharri, kyautata tsakanin ki da Allah kada ki damu da abinda mutane suke cewa akanki, Allah zai kyautata rayuwar mu, a koda yaushe anaso mutum yana kwatanta kansa da abu mai kyau kuma yana hango wa kansa alkairi ba sharri ba, iyaye na ba haka suke ba, duk abunda nakeso indai abun bai sab'a wa shari'a ba zasuyi fari ciki dashi kuma zasu so sa, indai kin karb'a soyayyan Ammar nasan Allah zai saka mana albarka a cikin rayuwar mu, bazan takura kiba amma zan rok'i alfarman dan Allah karkice baki sona"


Sunkuyar da kanta k'asa tayi tace "bani da abunda zance maka yanzu dan tun muna yara d'ayan mu baya gudanar da abu ba tare da shawaran d'an uwan sa ba, danje nayi shawara da Abbas idan yace yana sonka nima na amince idan kuma yace baya s....kasa k'arasa tayi saboda ganin yadda ya kafeta da idonsa da yayi jajazur kaman jan gauta lokaci guda tace kayi hak'uri Hamma Ammar ba haka nakeso nace, ba kuma ban fad'a ba fa"


Ganin yadda ta rud'e a lokaci guda yasa ya kwakwulo murmushi tare da kwaikwayon yadda tayi magana yace "kiyi hak'uri Adda Amna nima ba komai nace ba kawai na tsaya naji abunda zakice ne sai kuma naga kinyi shuru, amma nasan zan iya mutuwa idan kikace baki sona, kiji tausayin marayan Allah"


Ido ta zaro waje tace "kaima Baffan ka ya rasu"


Kai ya girgiza Mata yace "bai mutu ba, amma soyayyan ki yana so ya dawo dani maraya"


Murmushi sukayi a tare kafin ya tashi yace "gaskiya bazan iya mayar dake ba hijabi ba, dan nafi Saifuddeen kishin ki, danni ina kishin kine a matsayin uwar y'aya na shi kuma yana kishin kine a matsayin.....furzar da iska mai zafi yayi daga bakin sa yace ki jirani naje kasuwa na siyo miki hijabi saimu koma gida" kai kawai ta d'aga masa ya juya zai futa tayi saurin cewa "Hamma Ammar baka cire mun ba, kuma ruwan ya k'are harya fara k'arar mun da jinin jikina" kallon hanun ta yayi yaga yadda jinin yake bin roban ruwan, ya dawo da baya ya cire Mata yana kallon jinin ya lakato a hanun sa yakai bakin sa ya lasa yace "komai naki maikyau ne ga jinin ki jajazur Allah yasa ya'yan da zaki aifamu su ibo komai naki" rufe fuskan ta tayi da tafin hanun ta domin zuwa yanzu maganan sa ya fara bata kunya" yadda tayi ba k'aramun burge sa tayi ba, ya futa yana murmushi rufeta yayi ta baya, yana zuwa kasuwa ya siyo Mata k'aton hijabi da takalmi, ya kawo Mata ta saka kafin ya rubuta magungunan da zai siya Mata suka futa, suna futowa idon mutane yayi chaaa a kansu masu kishin ganin su tare nayi, wanda suka birge su kuma sai sambarka suke musu, ba abunda yafi d'aga masa hankali kaman ganin yadda maza suke kallon ta, ji yayi kaman yace ta koma zaije ya d'auko Mata nikaf tasa, amma ba halin yin hakan, jan hanun ta yayi suka k'arasa wajen motan yayi saurin bud'e Mata ta shiga, suna zuwa pharmacy sai yaga kallon nan ma har yafi na asibitin, d'agawa mai maganin hankali yayi ya basa da wuri suka bar wajen yana ma wanda suka kalleta Allah ya isa a zuciyar sa, suna isa gida ta hango Abbas a tsugune a k'ofan gidan ya had'a kai da gwuiwa yana kuka, da sauri ta bud'e motan taje ta rik'esa tace "lafiya Abbas? Yana jin muryan ta ya d'ago kansa da sauri ya rungume ta yana kuka yace "ina kika shiga Adda Amna, naje ko ina ban sameki ba, na shiga mak'ota sunce mun basu sanki bama ballan tana su ganki, saidai d'azu sunga an futa da wata balarabiyan yarinya daga gidan mu, hankali na ba k'aramun tashi yayi ba" ya k'arasa maganan cikin kuka mai sauti.


Rungume sa tayi idonta yana zubar da hawaye ta bud'e baki zatayi magana Ammar yace yanzu so kike ki shedawa mutanen unguwar kamannin kin kome? Ganin bada wasa yayi maganan ba yasa suka shige ciki da sauri, suna shiga tace "kayi hak'uri Abbas tun jiya cikina yake ciwo dan ko school banje ba, da Hamma Ammar baizo ba inaga da yanzu na mutu, Allah ne ya ceceni dana kirasa yazo ya kaini asibiti ya dubani kafin naji sauk'i, amma ka yafemun d'aga maka hankali da nayi"


Zare ido yayi yace "shiyasa tunda naje makaranta na kasa fahintan komai ashe baki da lafiya ne! Adda Amna ai idan kika mutu nima mutuwa zanyi, dan ko lokaci na baiyi ba saina sha maganin mutuwa na mutu domin rayuwa ta zata dawo mara amfani, yanzu zauna na dafa miki abinci kici kisha magani, ciwo baimum adalci ba ai dani yafi kamata ya kama bake ba"


Ammar kallon su yakeyi da burgewa abunda ya bashi mamaki ganin Abbas da iya gaskiyan sa yake magana dan har yanzu hawaye bai d'auke a fuskan sa, aiki yakeyi yana kuka kaman wanda har yanzu tana cikin halin ciwon, kallon sa yayi yace "Abbas zonan?


Barin abunda yekeyi yayi yazo ya tsuguna a gaban sa yace "kukan me kakeyi?


Kaman wanda yace ya k'ara sautin kukan sa cikin kuka yace "Hamma Ammar kalli yadda fuskan Adda Amna yayi fiyau duk ta rame a ciwon lokaci guda, halamun ta wahalan sosai a ciwon da tayi"


Ware Ido Ammar yayi yana kallon ta yace "dama tafi haka k'iba ne?


Kaiya d'aga masa kafin ya d'auko wayan ta ya nuna masa hotunan da sukayi, Ammar mantawa yayi da ganin k'iba akace yayi ya zarce da ganin hotunan ta yana casbihi wa ubangiji a zuciyar sa muryan Abbas yaji yana cewa kaga yadda ta rame dan Allah Hamma Ammar ka rubuta Mata maganin da zata warke dan bana son ciwon ya sake tashi Mata"


Murmushi Ammar yayi yace "ka kwantar da hankali ka ciwon da ba'a ganesa ba shine yake d'aga hankali amma ita nasan abunda yake damun ta har mun siyo magani tana fara sha zata warke cikin ikon Allah" godiya ya masa kafin ya tashi ya cigaba da aikin sa, Ammar Ido ya zuba Mata ganin tunda suka fara magana batace komai ba sai sunkuyar da kanta da tayi tana wasa da yatsun hanun ta ganin ta takura da yawa ya tashi yace "zan koma aiki idan Saifu ya kiraki a waya karki fad'a masa yadda mukayi dan inaso na bashi mamaki na nuna masa na iya raino fiye dashi" ta d'aga masa kai tare da mishi godiya yana futa a zuciyar ta tace "kaika damu dashi dan yanzu bai isa ya hanani abunda nakeso ba"



Zainab jiki yayi sauk'i dan har an sallame ta yau zata koma gida, saidai rashin zuwan Umar yana bata mamaki, da zasu tafi gida likatan yayita Mata nasiha sosai akan ta kula da kanta kafin ya bata number sa akan idan taji wani canji a jikin ta ta sanar dashi, godiya ta masa sosai suka futo driver ya jasu zuwa gida, suna shiga taga motocin gidan duka suna nan hakan ya tabbatar Mata da Umar yana gari kawai baiyi niyan zuwa duba ta bane, suna shiga falon ta taga komai a gyare kaman yadda ta zata, batayi fushi ba ta kira munbar Umar d'in yana d'agawa yace "........






***






Mmn Ashfaq


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol