Free chapter · Read without an account
55
by Nabeeha Aminu · TSANANI
109/110
***
Ammar yace "ba nufi nakeyi ba, Baban ta maye ne na bugawa a jarida, yanzu haka neman ta yakeyi Ido rufe yabawa k'ungiya ita, saidai inaga tunda kazo kayi gaggawan dauk'an ta ku tafi Spain kawai, dan tanan ne kawai zaka iya tsiratar da rayuwar ta"
Saifu ba k'aramun tsurewa yayi ba dan duk iskancin sa yana tsoron mutuwa yace "anya Ammar kana sona kuwa?
Ammar yace "Saifu kaima sheda ne akan son da nake maka, bazan b'oye maka ba, lokacin da kabar mun amanan Amna ka tafi, Allah ya jarabe ni da sonta amma tunda ta sheda mun kace kana sonta na sadaukar maka da soyayyan ta dan ba abunda zaka nema a wajena ban baka ba, ka yarda da shawaran dana baka, kaje a d'aura muku aure kawai ka gudu da ita kodan soyayyan da kake Mata"
Saifuddeen yace "wayace maka son gaskiya nake Mata, kawai ina sonta ne danna more ta, amma maganan gaskiya har cikin raina bana Mata son da zamu k'are rayuwar mu tare, Ammar kaima kafi k'arfin komai a wajena kaje na bar maka ita, kuma da zuciya d'aya na bar maka bada wata manufa ba"
Ammar yace "ba za'ayi haka ba Saifu, tun lokacin daka furta kalman so akan Amna na cireta a Raina, Saifu Amna takace dakai kad'e ta dace"
Saifu yace "wallahi Ammar zan zage tushen ku, akan me zaka dage mun saina auri y'ar mayu, idan ka sake mun maganan ta zan kunce abota dakai na har abada, kaga dama halin mu ba d'aya ba, kai nitsatstse ne ni kuma d'an iska ne, kuma banyi tsammanin zan shiryu nan da shekara ishirin ba, kaga gwanda ka rabu dani kawai kaje kayi rayuwar ka"
Ammar ya danne dariyan dayazo mishi yasan Saifu yana fad'an hakane dan ya daina lik'a mishi Amna yace "shikenan tunda baka sonta ka gujeta ni bazan barta ba, duk da ba sonta nakeyi ba yanzu, zanyi k'ok'ari na aureta haka kodan ceton rayuwar ta"
Saifu yace "aiko kayi jahadi kaga kai kuna da yawa a wajen iyayen ka, ni kuma ni kad'e suka aifa, kaga ni kad'e suke gani suji dad'i sab'anin kai, sannan na rok'e ka da girman Allah karka gayyace ni bikin ku dan wallahi bazan zo bikin y'ar mayu ba"
Ammar yace "wannan ne baka isa ba, dole kazo aure na, tunda ba waje d'aya daka zauna da Baban taba yana ciki kana waje"
Saifu ganin Ammar ba kyalesa zaiyi ba yasa ya kashe wayan yace idan nabar Nigeria ai naga ta inda zanzo auran ka, bayani yama iyayen sa, suma sukace ko bayan ransu ya auri Amna basu yafe mishi ba, tun a ranan ya fara shirin barin Nigeria.
Ammar suna kashe wayan ya kwashe da dariya yace "ai dama nasan bada gaske kake sonta ba, Allah kaga zuciya ta ban fad'a mishi haka danna rabasu ba sai dan na kub'utar da rayuwar Amna daga ganin takaicin gidan miji.
Umar yana zaune a falo yana cin abinci yaga an saka photo Zainab, zunbur ya mik'e yana cewa wato ni zaki rainawa hankali ko, tabbas rayuwar ki yazo k'arshe Zainab, duba lokaci yayi yaga tara da minti hamsin na dare, komawa yayi ya zauna yana ayyana kalan wulak'ancin dazai ma iyayen ta idan yaje d'auko ta, yaso yin sammakon tafiya dan a son ransa k'arfe hud'un asuba yaso ya d'auki hanya Birnin kudu amma hakan bai yiyuba saboda kiran gaggawa daya samu daga k'ungiya, k'arfe biyar suka fara meeting kuma ba akan kowa bane illa akan shi, bayan komai ya gudana sun kurb'a jinin daya dawo musu kaman farilla, dan da wannan jinin k'ungiya take k'afa dokan ta, takance inda kashe na y'an uwan wasu suma haka zasu sha naka, Shugaba ya kalli Umar da jajayen idon sa mai firgitarwa yace "Umar soran kad'an k'ungiya ta hallaka ka, dan ka kasa cikama k'ungiya alk'awarin daka d'auka.
Umar jiki na b'ari yace "tuba nake ya Shugaban mu, dama yau nake da burin cika duk abunda na d'auki alk'awari a kansa, yanzu haka ina barin nan zanje Birnin Kudu na d'auko Zainab na kawo muku ita, sai maganan y'an biyu suma a shirye nake da damk'a muku su aduk lokacin da kuka buk'ace su"
Shugaba yace "kasan bamu karb'an yara ba tare da amincewan uwar suba, dan haka ya zamo dole ka nasarwa Matan ka sana'an da kakeyi, kuma muna buk'atan yaran bayan ka kawo mana Zainab da kwana d'aya"
Cikin girmama yace "zan zamo mai cika alk'awari ya Shugabana"
Yana dawowa gida ya shirya ya d'auki hanyan Birnin kudu, k'arfe goma sha d'aya ya isa yana shiga layin su yaga manyan motoci birjik da security, mamaki ne ya kamasa dan yasan duk layin basu da shahararran mai kud'i, kawar da tunanin yayi ya nemi wajen parking nesa da gidan su Zainab, ya futa ya k'arasa da k'afan sa, shiga gidan yayi yana kwalawa Zainab kira ba tare daya musu sallama ba, Abbah ne ya fara futowa yace "waye yake shigo mun gida batare da sallama ba?
Umar kallon banza ya watsa masa yace ba wajen ka nazo ba nazo dauk'an Mata nane, Zainab najin haka tace "innalillahi wa'inna ilaihin raju'un Amna ga ma'aifin ku yazo"
Amna najin ance ma'aifin su ta futo tace "Abba dama akwai mahaukaci a unguwar nan ne?
Kallon kallo suka tsayayi ita da Umar "wasi wasi zuciyar sa ta fara masa yasan Zainab tafi wannan girma, bai dawo daga duniyan wasi wasi daya tafi ba Zainab da Abbas suka futo a tare ya k'urawa yaron Ido, da badan girman da yafi yaron ba da sai yace shine a tsaye a wajen, Abbas yace "kana mamakin ganin kaman nin mu ko? Ka bud'e kunne ka dakyau kaji ni, sunana Abbas kuma duk da ina bak'in cikin kasancewan wanka uba a gareni amma ba yadda na iya tunda tanan Allah ya futar dani, ya nuna Amna yace wannan itace y'ar daka fara aifa ka sadaukar wa k'ungiya ita, ni kuma nine d'anka na hud'u daka sadaukar wa k'ungiya dukan mu a bakin ruwan Larro ka ajiye mu domin k'ungiyan ku na marasa tsoran Allah su kashe mu saidai Allah ya nuna maka ikon sa na idan bashi ya kashe mutum ba ba wanda ya isa ya kashe sa, Allah ya raya mu a hanun wani bawan Allah, wanda ya yarda da Allah yayi imani da Allah, muka tashi cikin tarbiyya da tsoron Allah, amma inaso ka manta daka tab'a aifan yara irin mu dan harmu mutu bazamu tab'a kiran ka da sunan uba ba Umar, nasan a jahilcin ka yau kazo dauk'an ma'aifiyar mu ne kaje ka sadaukar da ita wa k'ungiya ku, wallahi ka kuskura kazo kusa da ita na maka rantsuwa da wanda ya busa mun nunfashi saina kashe ka da hanuna Umar" ya k'arasa maganan yana nad'e hanun rigan sa.
Amna d'akin Abbah ta shiga da gudu ta d'auko gora tayo kan Umar da yayi mutuwan tsaye a wajen tsaban al'ajabi ta sauk'e masa a kafad'an sa ta d'aga zata sauk'e masa na biyu aka rik'e ta ba yadda ba'ayi ba akan a kwace goran a hanun ta amma an kasa domin ran fulani ya b'aci, ganin haka yasa Daddy yayi saurin janye Abbas a wajen dan yaga yadda yake futar da huci, Zainab ganin kowa yama Amna magana tak'i sake goran ta nufi kanta gaban ta yana faduwa ta d'aura hanun ta akan goran tana girgiza Mata kai idon ta yana zubar da hawaye, ganin hawaye a idan ma'aifiyar ta yasa ta sake goran ta fad'i sumammeyi a wajen, Umar na ganin haka ya futa da gudu najin kaman ta sauk'e masa allan kafad'a, dakyar ya iya mayar da kansa Abuja yana zuwa asibiti ya wuce direct.
D'aki aka shiga da Amna aka yayyafa Mata ruwa, tana farfad'owa ta saka kuka tace "Momma kefa yakeso ya kashe maiyasa baku barni na kashe shi ba?
Umma nasiha tayi ta Mata akan yadda da kaddara maikyau da mara kyau, da kuma ko wani jarabawan da Allah ya aiko maka dashi.
A d'akin Baffa ma hak'uri akayi taba Abbas tare da mishi nasiha mai ratsa zuciya, kafin Abbah da y'an uwan sa suka karb'a sadakin Zainab dana Aisha, iyayen Ammar ma suka bada nasu, a wajen aka yanke biki nan da sati uku.
Zainab da Aisha sun dage sai gyara Amna sukeyi saida Umma ta musu magana akan su bazasu gyara kansu bane kafin suka had'a duka sunayi tare.
Umar yana zuwa asibiti aka masa photon hanun sa akace ya goce, d'aure masa hanun akayi ya dawo gida dan yace bazai kwana a asibiti ba, harya iso gida maganan da Abbas ya masa yana ta mishi yawo a kwakwalwa, da k'arfi ya furta ya'yan Zainab suna raye, wato duk wanda ba'a yanka a gaban idon na ba suna raye, tsoro ne ya sake shigan shi dan baisan ya zaiyi da k'ungiya ba yau, gashi tunda ya d'aura Ido akan su Amna yaji wani mahaukacin sonsu ya shiga zuciyar sa, yana zuwa gida y'an biyu sukayo kansa suna masa oyoyo, janye su yayi ya haura sama, Hanifa ganin shigan sa da hanu a d'aure yasa ta bishi tana tambayan sa abunda ya faru, tayi maganan duniyan nan bai bata amsa ba, daga k'arshe ma ya rufe idonsa kaman mai bacci, futa tayi jiki a sanyaye, washe gari suna zaune a falo ya kalli Hanifa yace "Hanifa kinsan sana'an da nakeyi?
Tace "na sani kana aikin gomnati sannan kana kasuwanci, dan kaman haka na tab'aji a bakin Zainab"
Ya girgiza kai yace "bana ko daya daga cikin wanda kika lissafa mun, bani da sana'an daya wuce mafiya, duk kud'in da kike gani ina amfani dashi na jini ne dan saida na sadaukar da y'an uwana da ya'yana kafin nayi wannan azzikin, dan haka idan kinaso mu cigaba da dauwama a cikin dukiya ya zamo dole mu sadaukarwa k'ungiya da y'an biyu"
Hanifa a razane ta mik'e tana nuna Umar da yatsa, ta jawo ya'yan ta ta rungume tace "bazai tab'a yiyuwa ba, Allah ya isa tsakani na dakai Umar bazan tab'a yafe maka ba kuma yau d'in nan zanbar maka gidan ka, kafin yayi magana yaga wasu gardawan maza guda tawas sun shigo falon, ko wannen su hanu rik'e da bindiga fuskan su a rufe, daga Umar har Hanifa ba wanda bai tsorata ba, Umar yace "dan Allah karku tab'a mu, ku fad'a duk abunda kukeso zan baku shi komai yawan sa" dariya suka kwashe dashi d'aya daga cikin su yace "kaga mun maka kama da talakawa?
Umar duk da fuskan su a rufe yake yace a'a bakuyi ba, to me kukeso?
Sukace yanzu zakaga abunda muke so, y'an biyu suka jawo suka cire musu kaya a gaban sa sukama yaran fad'e ko tausayin k'arancin shekarun su basuyi ba, yaran sai ihu sukeyi suna neman agajin iyayen su, daga k'arshe suka suma, suna gamawa da yaran suka kwantar da Hanifa, dukansu takwas d'in saida suka kusance ta, idan wannan yayi ya gama sai yaba d'an uwan sa, a haka saida ko wannen su sukayi sau bibbiyu kafin suka mayar da kayan su har zasu futa suka juyo suka kalle Umar sukace bakaga komai ba, tunda gadaran ka lalata ya'yan mutane ka saurari dawowan mu na gaba" suka juya suka fuce sukabar Umar da zubar da hawaye, ji yayi kaman ya kashe kansa tsaban bak'in ciki yace "dama haka iyaye sukeji idan akayi lalata da ya'yan su, kai kaiton rayuwa ta, ruwa ya yayyafa wa y'an biyu ya d'auke su da hanu d'aya ya kaisu d'akin sirri yana kuka kafin ya dawo yaja k'afan Hanifa yana nishi itama ya kaita d'akin sirri, abu ya yayyafa musu kafin shima yasa kayan sa ya murza kyallen tsafi suka b'ullo a wajen dukan su, tsawa aka daka Masa akace ina Zainab d'in?
Yana kuka yace "Zainab tafi k'arfi na amma dan Allah kuyi hak'uri ga d'ayan Matan nawa na baku a madadin wancan d'in"
Hanifa data farfad'o tun tsawan da aka masa, tanajin abunda ya fad'a ta saka ihu tana cewa Allah ya isa tsakani na dakai Umar bazan tab'a yafe maka ba, shege azzalumi dakai da wanda kuke tsafin duka sainaga bayan ku" abunda tayi ba k'aramun b'ata ran k'ungiya yayi ba, dan haka suka d'auki y'an biyu aka cire kansu a kasa a k'ok'on tsafi, ita kuma Shugaba ya mik'a hanun sa yasa akan cikin ta ya futo da ma'aifar ta, kafin yacewa Umar ku tashi ku tafi bana buk'atan ganin ku anan, abu Umar ya watsa Mata suka bace, suna dawowa gida Hanifa tayi ta kuka tana dana sanin auran cin amanan da tayi, gashi ba y'aya ba ma'aifa, tana kuka tana ma Umar Allah ya isa, ta tattara kayan ta ta futo zata tafi, saidai tana futowa taga motocin gidan yanaci da wuta, Umar shima yana zaune a falo yaga d'akin yana ci da wuta ya futo da gudu yaga wani sabon tashi hankali anan ma, ganin ko ina yana ci da wuta a gidan yasa ya futa da gudu Hanifa ta tufa masa baya, kafin akawo a gaji gidan ya k'one k'urumus, kuma wani ikon Allah iya gidan ne ya k'one a unguwar, mutanen layin suka futo suna masa jaje Hanifa da take tsugune tana kuka tace "akan me zakuyi jaje wa mutumin daya kasance mishiriki azzalumi labarin komai ta basu, kafin kace me kowa ya watse a wajen suna ta Allah wadar da halin shi, itama zuwa tayi zata shiga gidan ta na layin y'an unguwar suka hana ta, sukace bazasu iya zama da mayu ba, futa sukayi a layin tana ta kuka, dan bata tab'a tsammanin duniya zai juya Mata haka da wuri ba, gidan iyayen ta taje tana gama fad'a musu tace "ai dama duk wanda ya shiga motan kwad'ayi dole ya sauk'a a tashan wulak'anci, kije ki k'arata saidai bazasm mu kore ki l ba amma ki sani bamai zuba miki abinci ga wajen zama idan kinga zaki iya zama" ranan Hanifa taci kuka da dana sani mara amfani a rayuwar ta.
Umar kan kwanan tasha ya koma yi ga ciwon hanu ga yinwa duk inda ya shiga mutane koran sa sukeyi, duk da basusan abunda ya aikata ba.
B'angaran su Zainab yau ya kama d'aurin aure inda dubbanin al'umma suka sheda auran su, da yamma aka d'aukan amare, Amna ta rungume Abbas da Zainab taci kuka, Abbas shima ba k'aramun kuka yayi ba dan wannan ne karo na farko dazai rabu da y'ar uwar sa" dakyar aka bashi hak'uri aka futa da amare, Zainab da Malama Aisha suka nufi Abuja, Amna kuma akayi da ita bauchi"
Dinner na gani a fad'a doctor Mansur da Abdallah suka had'a, dan haka amare na isa aka tsantsara musu kwalli aka tafi dinner, taro akayi na manyan mutane, idan kaga amare bazaka tab'a cewa sun tab'a aure ba, bayan angama dinner kowannen su ya d'auki amaryan sa suka tafi gidan su, ranan Zainab da Aisha sunsha madaran soyayyan dan har suke ganin da baya ba aure sukayi ba sai yanzu ne sukayi aure.
B'angaran...........
***
Mmn Ashfaq