Free chapter · Read without an account

10

by Nana Disoo · LATYFAH IMAM

10


LATYFAH IMAM


Na nana diso


Mayan yaran gidan suka taimaka aka shigar da'ita inda kawu bala yace asanar da maƙota da aboƙanan arzuki cewar za'ayi jana'izar Abdulkarim mai lema karfe 2 Narana bayan sallar azahar, haka kuwa akayi duk wasu aboƙanan arzuki sai da aka sanar dasu ta inda ta tabbata cewa Abdulkarim yarasu! Kukan da ƴan gidan sukeyi yasaka gidan kara rikicewa haka ƴan uwan mahaifin amiey suka tawo daga kauye domin halattar jana'izar.


Yanzu kagani kai bawa amma anjima da gobe ba taƙa bace ba, yau abdul dake ji da ƙansa taƙama da isa da wadata ga kyau uwa uba ga asali mai kyau, shine kwance cikin farinyadi aciƙin makara ana masa sallah, daga nan kuma a daukeshi zuwa gidan gaskiya! Allah muntuba wanda baiyi darasi acikin rayuwarsa to tabbas babu abunda zaiyi. Gunjin kukan Aliyu kadai da laila zai tabbatar maka da gidan babu lafiya ammy kuwa kokari kawai takeyi dan kaɗan ya rage ta dora hannu ta kurma ihu. " DanAllah kubarni nima na kasheta kubarni danAllah ammy take faɗa ana bata baƙi tare da hakuri." " Ammyn laila addu'a zakiyi masa ba ihu ba danAllah." " Mumy ƙinsan zafin danakeji kuwa? Ƙinsan radadin danakeji? Ƙinsan zafin mutuwa? A'a bakisani ba? Shiyasa kike hanani kuka shiyasa kuke bani haƙuri." " Hakuri bazan daina baki ba amma kisani dani dake da duk jiranku takeyi daj duk abunmu watarana sai mun tafi gidanmu na gaskiya naga numbar Dadynsu tana shiga zan samu mu zanta Allah ya gafarta masa.


***


Haka kasarmu ta lallace iyami babu wani wanda zai dubeka idan kana talaka idan kanason amutuntaka to kanada kudi ne kokuma ka bada kudi, shi talaka bashida alfarma kenan?.. hawayen fusƙarta ta goge, bakaramin rama tayi ba dan bacci ma har yanzu ɓarawo ne yake saceta, kullum kwana taƙeyi ta tashi da halin da ĵiƙarta taƙe ciki. Kallon malam idi tayi tace " Ai mai alfarma shine mai kudi a hannunsa idan bakada su kana tsaye zaka rasa abunda kazo nema! Yaya andace kuwa?." " Tabbas nagani Iyami wannan aikin namu yana buƙatar jajircewa da kuma hakuri wannan kukan naki bazai kaimu ko'ina ba addu'a dai itace mafita." " Malam idi wayasan halin da yarinyar nan take ciki sai Allah rayuwar kurku masiface malam idi idan bakayiba ko kaje ka gani bazakasan kana ciƙin ni'imar Allah ba." " Tabbas tabbas haƙane, yanzu dai kusan lauyoyi goma nasamu amma wallahi iyami babu wanda ya saurareni guda dayane yasaurari ne sunanshi Barrister zakariya shima yace kudin farko abunda zamu bashi shine dubu dari uku da sha biyar shine zai sauraremu amma sauran ma babu mai kallona idan sukaji alfarma nazo nema shine ma ya zaunar dani yacemin shariah da masu kudi sai da kudi idan bahaka ba babu mai sauraronmu." " Innalillahi wa'inna illahir raji'un nashiga uku dubu dari uku ina naganta kaga nan dubu 30 ne shima ranar datazo tabani da naƙi yarda na karba wallahi sai daga baya kuma danaga ta nace na ƙarba, amma babu komai sai nafara sana'ar kosai ko? Ko Allah zai sa muhaɗa wani abun mudinga biyansa a hankali." " Tabbas haƙanma shawarace nima gurina akwai dubu goma zanga yadda hali zaiyi kamin ƙarshen wata, gobe idan Allah yakaimu sai ki shirya da sassafe muje kiganta daman nace miki akwai abokina dake aiki agurin." " kai Allah yasaka maka da Aljannah nagode nagode tafashe da kuka."


****

Dady tunda na ƙunna wayar kawu bala ke kira. Sanin bakaso a daga maka waya yasa ban dauƙa ba. Hamid din yaƙalla kamin yaƙarbi wayar daga hannunsa yanayin sallah tare da karawa akunnansa." Bala dady yafaɗa yana gyara zaman akan kujerar." " Naam Alhaji barka da yamma inata kiran wayar shiru nan ma iyali sunce basu samunku dafatan kuna lafiya?" Yanayin muryarsa kawai yasa dady ya fahimci babu lafiya. " Uzurine yarikemu lafiya dai bala?" " Wallahi munyi babban rashi alhaji Allah yayiwa Abdulkarim rasuwa, yanzuma bamu daɗe da dawowa daga maƙabarta ba." Hawayen dayake kokarin dannewa ne ya wanƙe fuskarsa yana faɗin " Allahu Akbar abdul kuma lokaci yayi bashida lafiya ne mahaifin yafada cike da damuwa da takusa sakashi zamowa daga ƙan kujera. " " Wallahi nidai naji ana kasheshi akayi kasan iyalan naka basu sakani akomai ance ansace gawar tasa sai yau aka bayynata to nima yau ita mumyn umaru take gayamin." " Allah dai ya gafarta masa zai iya yihuwa gurin yawon banzan nashi wata ta illatashi ko abokanan da nadaɗe ina rabashi dashi, ita matar tasa fa?" " wallahi banji komai dangane da matarsa ba Alhaji abunda nasani dai ita faɗimar tana cikin damuwa sosai." "Allah yayi masa rahama yafaɗa yana kashe wayar."


Hamid daƙe sauraron komai da mahaifin nasa ke faɗi yasa hanƙalinsa yatashi " kenan dady ma yasan abdul yana neman mata? Innalillahi wa'inna illahir raji'un yafaɗa a fili Allah yayi masa rahama." Sautin kukan dadyne kadai ke tashi adaƙin " inama kazama mutumin ƙirki kamin ka koma ga mahaliccinka? Inama ace kana girmana iyaye, inama ace ka kyautatawa matarka yafɗa yana kuka mai cike da taɓa zuciya! Allah ya sassauta maka Abdulkarim yayi maka rahama." Ameen yaaAllah hamid yafada shima yana goge hawayen fusƙarshi. Dady ne yajiyo yace " Abdulhamid danAllah in nemi alfarma agurin mahaifin nasa yafaɗa yana kuka?." Dady babu alfarma tsakaninmu sai dai umarni komenene kakeso zanyi maka." " DanAllah ka auri LATYFAH ƳAR GIDAN IMAM. Dasauri ya jiyo yana kallon mahaifin nasa dake kuka. " A hannuna mahaifinta yarasu yana faɗin ga amanarsa ga amanarsa bataji dadinsa ba inzame mata uba ga amanarta, danAllah kataimaka min gurin cika amanar nan ka aureta idan munkoma nan da shekara daya, inaso kazame mata uba, yaya ,miji kuma abun alfahari, inaso kasota kamar yadda kake kokari gurin nunamin so." Sosai ƙan hameed ya Sara haƙan yasa ya durkusa kusa da mahaifinsa yace " Indai har hakan shine abunda kakeso gareni na amince zan aureta." Sai kuma mahaifin nasa yatsayar da kukansa idan dai har zaka aureta dan ka wulakanta ta kamar yadda Abdulkarim yayi to ina roƙonka da girman Allah ka gayamin bakason." " Bazan taba zama daga ciƙin asararru masu kushe halittar Allah ko kuma wulaknta mata ba, ko banasonta zan tursasa zuciyata dady nayi maka alkawari." " ubangiji yayi maka albarka yarabaka da duniya da mutanen ciƙinta lafiya hameed.


*****


Juyi ƙawai yakeyi a offices dinsa mutuwar bakarmin daƙar masa kansa tayi ba, innalilahi ya ambata yana tuna zancen daya daga ciƙin ma'aikatan da sukace masa latyfah imam tana prison, mikewa yayi yana kiran daya daga cikin ma'aikatan akan suyi hanzarin kawo masa report din da zai duba. Sallama akayi sannan aka shigo. Nawal ce ta ƙalli sir tahir tace " Sir ya hakuri? " " Da godiya." Yafaɗa yana duba taƙardun dake hannunsa. Ashe wai matarsa ce latyfah imam ni wallahi bansaniba kuma naji ance itace tayi ƙisan amma ahaka kamar bazata aikata ba sir." Dagowa yayi da idanuwansa da suka rikice yace " bawai bani ba, latyfah imam bazata taba aikatawa ba can dai shiyasan mai yakashe shi kawai anyi amfani da kuɗi ne an zalunci baiwar Allah dake hakuri da ɗansu." " Gaskiya kam muma munyi tunanin nan, Allah yasaka mata cewar nawal." " ameen nawal danAllah kusata a addu'a dan inda take ciki aprison din karshen horo ne kuma daurin rai da rai yafaɗa yana goge hawayen da suka zubo masa." " munata Addu'a tafaɗa tana ƙarbar taƙardar da ya miko mata tafita tana saƙin wasu tagwayen dariya."


__


Farhan " Mom dagaske nake fa wallahi." " To saboda Allah farhan sai nace maka ga abunda yakamata? Kadai mayar da gawar nan dai ko?" " mom me isa zanmiki karya na mayar tun sanda kikayi mun nagana to saboda Allah mom dan zauna in rayu da gawa ne?" " To yanzu kana ina." " nayi tafiya ne basai ƙinji ba." " To Allah yatsare yakareka yashiryamin kai." Murmushi yayi ya amsa ya kashe wayar. Shegen yaro mai kama da taliya uwar taka ma.sai kayi mata karya kudai yaron yanzu bakuda tarbiya." Kallonta yayi yace " ai sai kibani tarbiyar ke kuma ni ba taliya baniba." " Fitsararre haka daman nasan zakace." " Wallahi kidaina jifana da muna nan kalaman nan nagayamiki fa. Shiru tayi bataƙara cewa dashi komai ba."


*****


GIDAN YARI


Ladabtarwa iya ladaftarwa horo, iya horo bayanin horon da muke samu bazai taɓa faɗuwa ba, Ashe akwai lokacin da zan rame? Ashe akwai lokacin da azaba zata sanyani rama? Tabbas ko wata banciƙa ba acikin wannan gida mai ciƙe da ladaftarwa na zabge na waɗa, ƙallon ƙaina nayi daga sama har ƙasa inama ace zan samu sabulun wanka yau da na cire kazantar dake jiƙina, Nonuwana tsami sukeyi saboda kazanta ko yaya na gifta iskar rigata tatashi sai akaji yadda yanyin jikina ke bada wari, ganin anzage wata yarinya da banajin tayi sati biyu da zuwa yasani ƙarasawa gurinta, Ashe wai maggi ne da'ita nan naga ana mata ladabi tsoho da yara domin samun Maggi nan kowannen mu yashiga yimata kirari ana kiranta da sarauniyar wannan satin tunda taasamu maggi, nan tace mana muyi layi, dukanmu mukayi layi karkaso kaga maggin da ta bamu. Maggi ne guda daya sai tabawa mutum 10 tace su raba, ahala akasamu wata kazamar leda kowa ya nannade nasa ajiƙinsa, gudun ƙarbar abinci muka shigayi sosai nan nadinga turerenuwa har sai da nasamu naƙarbi abincina na ciro maggin nan tazuba inajin yau taƙe sallah agurina, domin wani baƙin tuwo ne da ruwan tattasai aka kawo mana, maganar dadi ko ɗandano babu kwata kwata, babu zaben abinci dole ne kaci kokuma ka kwana da yunwa kuma maganar koshi bama ayi kwatakwata abun yayi munin da duk yadda zan lissafa baza'a fahimta ba sai dai kawai mukira abincin da kasumu ci ƙada mu mutu shine sunan abincin amma haka acikinmu murna fa mukeyi saboda tuwon zai ɗan riƙeka na wani lok'acin duk halin da kake ciki agidanka na babu nama kokuma bakason abinci idan kaga abunda mukeci zakayi godiya da Allah kakuma godewa mai ciyar daƙai domin kana ciƙin ni'ima bakarama ba. Bamu gama cin abinci ba naga matan dake bangaren mu suna gudu Ashe hajiya ladi ce tabiyosu aƙan zasu shiga wanke bandaƙuna dakuma kaya, abincin da ban karasaba nim nahau kudu abun tausayi ƙyara kamar akuyoyi duƙa kamar jakuna, yau abunda nagani ina wanke bandaƙi yadaga min hankali dan jini ne tako'ina wato samun tsumman da zakayi kunzugun jini dashi wata ni'imar ce bakadan ba, ballantana masu saka pad sai dai suyi sujjada su godewa Allah dan wasu gasu anan basuda cikkaken wandon sakawa ma. Daruwa na wanke da wani omo ɗan kadan sai nayi dabarar yin alwalah kamin kace me yamma nayi aka shiga ƙadamu mukoma daƙi mukwanta, kara kallon daƙin nayi masu gata zaka gansu da zani akasa kai kam da bakada mai zuwar maka ƙan sumitin zaka zauna kuma ka kwanta, zamane na kunci da takura dan babu cikakken gurin da zakace zakayi juyi acikin dakin, gashi bawai hira akeyi ba a'a zamani na ƙunci da baƙin ciki, acikin kowanne dakuna akwai ƴan sanda da alkalai saboda masu rigima da rikici da tsageru, kadafa kuce wai wasu ƴan sanda masu muƙami a'a basu baniba irin masu laifin da suka dade acikin gidan yarin sune ake naɗawa, tunda nasamu guri daya na zauna naji lokacin sallah nayi nan kuma naji ciƙina yakwashe kamar babu komai aciki watace aciƙinmu tayi tsaki, kai ranar naga masifa da bala'i da bantaba gani ba kusan sai da suka goga baƙinta akasa sai dayayi jini horo mai girma akayi mata sannan akace zata ladaftu gobe. Nidai tsif nayi ina hawaye da tunawa da iyami nasan tanacan tana cikin damuwa. "Ke" naji an ambata nasan dani ake siyasa nayi saurin juyowa jikina narawa. " Ƙukan ubanki kikeyi shegiya kinadamun mu da kuka fa ubanki yasaki laifin wallahi idan kika damemu zamu ladaftar dake." bance musu komai ba. Sai ihun wata da mukaji wai zata gudu ne aka kamota acikin daren nan ana mata bulala sautin kukanta kaɗai ke tashi....


******


KURAJEN GABA ANA SAMUNSU NE TA HANYAR SAKA MATSETSEN WANDO KOKUMA ASKE GASHIN GABANKI BATARE DA KINSHAFA MAI BA BAYAN ASKIN KOKUMA WAFA LARURA TA DABAN, KAMAR ZAMA DA JIKAKKEN WANDO AMFANI DA WANDO MAI DATTI.



Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol