Free chapter · Read without an account

Chapter 2

by Azizat Hamza · Mutum Mugu Ne

*MUTUM.....Mugu ne*


                     02


         ©AzizatHamza2019      


                    *LAGOS*

Cikin office d'in babba ne sosai, da alama mamallakin office d'in yanada girma sosai.

Tag d'in dake kan office table d'in an rubuta *CEO Madam Bridget N Aliyu* ajiki. Tun daga takalmin k'afarta zuwa gwagwgwaro dake kanta kasan babbar mace ce balle kuma d'an kunnen da sark'an gold da tasa. Matar ta nitsu sosai wajen yiwa wasu mutane biyu sanye cikin bak'in suit bayani, sun kai minti goma kafin daga k'arshe suka tashi.

Mik'a musu hannu tayi suka gaisa kafin suka bar office d'in. Wani dariyar mugunta tayi kafin ta ce 'Nafi k'arfin ka Dr Sajid, na riga na winning case d'in nan angama, kuma bayan mun gama da court, sai na dealing da kai gaba ba za ka sake shigo min gonata ba' ta had'e rai sannan ta zauna ta cigaba da latsa computer....


*

Tun da ta idar da sallar asuba ta shafa fresh aloe vera gel a fiskarta, da shi tayi duk wani aiki da zata yi kafin tazo tayi wanka. Bayan ta fito daga wanka ta d'auki man da take shafawa wadda ita ta had'a da kanta, pure coconut oil ne da olive oil sai sesame seed oil. Ta shafe jikinta dashi gaba d'aya. bata yi wani kwalliya ba, powder kawai ta shafa sai kwalli data sa, uniform d'inta dake shimfid'e akan gado ta ɗauko ta saka. Riga ce fara da wando maroon color sai k'aramar farin hijab, saboda yadda mutane ke sa mata ido a hotel d'in yasa ta maida riganta dogo iya gwiwa, ita kanta tasan Allah ya bata shape mai kyau, tun tana JSS 3 mutane ke sa ido akan hips d'inta.

Bata saka hijab d'in ba sai farar hula data saka a kanta daya sha k'ananun kitson shukun igbira.

Kai tsaye dining ta isa taga Uncle yana karanta jarida, har k'asa ta tsugunna tace "e' karo Daddy" duk da kasancewarsa yayan mamanta amma Daddy take kiran shi saboda haka yaranshi ke kiran shi.

" Karo my dear, bawo ni?"

"Adupe Sir" ta amsa masa.

Waje ta samu ta zauna a kujerar da ta saba zama ta bud'e tsohuwar Tecno Y2 d'inta taga ko Stark VPN sun bata data, amma basu bata ba. Baifi minti biyar ba, Mommy, Timothy da Ronke suka iso dining d'in. Zama suka yi aka fara addu'a itakam tuni tayi Bismillah ta fara cin abinci. By the time suka gama "Our father, we thank you for this wonderful meal, father in heaven bless this food for us......" Ta riga ta kusa kammala k'osanta, tana gama cin nata abinci tayi godiya wa Ubangiji a zuciyarta ta tashi ta d'au kwanon tayi kitchen dashi, a take ta wanke su a sink ta koma d'aki, ta sake gyara fiskarta sannan ta saka lip gloss kad'an a lips d'inta, bakinta ba k'arami bane, koda yake ance yarabawa nada manyan lips haka dai taji ana cewa, sai dai lips d'inta yana da kyau dan sama da k'asa bak'i ne, tsakiyan kuma kaman irin light peach haka, ta saka hijab d'inta kafin ta d'auko ID card nata ta sak'ala ajikin riganta, *Naziha F AbdulSamad* aka rubuta ajiki.

Daddy ya k'olo sunanta "*Funmilayo* so t'i se tan?" da yake sunanta na yare kenan kuma anan sun fi kiranta dashi. Da sauri ta ce "mo t'in bo Sir" ta fito da sauri tace da mommy dake goge kan dinning

"O` dabo mommy" mommy ta amsa da "O`dabo Funmi".

Tuni Daddy na cikin mota shi da Tim. Tana shiga suka kama hanyar hotel d'in da suke aiki, Daddy shine manager na hotel d'in. Idan Tim (Timothy) ya zo hutu yana yin part time aiki a wajen, Naziha ma tunda ta gudo daga Kano gidan yayanta shekara guda kenan, anan take aiki. Kuɗin makaranta take tarawa, Daddy ko naira baya k'ar'ba a albashinta, cewa yayi ta dinga tarawa idan Allah yasa taci Jamb ta samu school kud'in zasu rage mata wasu abin.

suna Isa hotel d'in suka fito kowa yasan wajensa dan haka tayi wa Daddy sallama zata wuce Tim ya maki bayanta kad'an yace "goodbye my hipsy" amma a hankali ya fad'a, ita kuwa ta k'walla k'ara "Daddy" yasan sun saba da fad'a tsakaninsu shiyasa ya daka masa tsawa "Adeleke!" Sunan Tim na yare kenan. Da sauri yace "sorry Daddy" ita kuwa ta fara masa dariya k'asa-k'asa tareda gwalo ta wuce abinta.

Hotel d'in ba wani babba bane sosai, dalilin dayasa ake samun customers sosai a wajen saboda yawanci mutanen da ke tsoron kada a gansu a hotel suke gujewa zuwa manya-manyan hotels, irin ƙananan hotels da ba su yi suna ba su ke zuwa saboda baza ayi tunanin suna wajen ba.

Tana zaune ta samu stark VPN sun bata data dan haka ta shiga Facebook tana d'an duba labarai, Tana cikin scrolling facebook feed kawai taci karo da wani post da aka saka hoton wani matashi da ya tafi da imaninta lokaci guda. He's damn handsome. Kyakykyawa ne sosai gashi yadda yayi murmushi a hoton ya k'ara fito da kyawunsa, abinda aka rubuta a saman hoton ta karanta

*Happy Birthday Dr Sajid Usman Abdallah* "wow such a beautiful name" ta fad'i a zuciyarta ta bud'e post d'in taga wai 45th birthday d'inshi ne, "Kai wannan k'arya ne, see how young he looks a ce wai 45yrs.....Koda yake zai yiwu tunda gashi su SRK, Salman Khan duk 53yrs amma ba za ka ce sun kai haka ba" ta fara bud'e sauran pics d'in tana saving ɗinsu.

Wani pic ta gani tareda iyalinshi matarsa da yaransa uku "kai! Such a perfect family" sai kuma ta girgiza kai tace "ehm yanzu babu perfect family a doron k'asa kowa yana fama da tashi matsalar. Kai amma this guy is handsome, ga matarshi ma mai kyau, Wasu kan dai Allah ya basu duniya. Kyau, k'udi, suna"

Ta shiga opera ta browsing sunan shi ai kuwa nan google search engine ya nuna mata abinda take buk'ata, bata san meyasa ba kawai ta samu curiosity na sanin rayuwarshi.

Ta fara karanta tarihinsa a bisa yadda Wikipedia ta rubuto, tun daga inda ya fito inda yayi karatu, k'asashen da ya yi aiki, duk ta karanta. Ba abinda ya k'ara birgeta sai wani guri da aka ce k'asar America ta karramashi sati biyu da suka wuce a matsayin one of the best Neurosurgeon in the world. "To ma who is a neurosurgeon, wani irin Likita ne haka?" ta tambayi kanta.

Bisi ce ta k'wala sunanta "Funmi zoki k'ar'bi order na room 13" da sauri ta mayar da wayarta cikin jaka ta tafi k'ar'bo order d'in....

            *ABUJA

Kwanciya yayi akan gado yana jinjina rayuwar Zaytunah kwata-kwata a rayuwarta tafi damuwa da abinda mutane za su ce fiye da abinda zai faranta masa rai. Countless times sun sha samun matsala akan irin haka amma bata damu ba, shiyasa ma wasu abin yake d'aga mata k'afa baya complain akai. Watarana data posting wani picture a Instagram da Twitter page d'inta kamar yayi kuka saboda shigar da tayi ba shiga ne da ya kamata wasu su gani ba amma haka yayita gani dubunnan comments wadda kusan duka maza ne.

wai da ya mata magana sai tace idan ba ta updating pictures d'inta, followers ɗinta ba za su ji dad'i ba, ranar tsabar takaici kasa ce mata komai yayi...

Zaytunah na saukowa tace ayi hak'uri Sajid baya jin dad'i ya sha magani zai kwanta, ganin mai taron ba fitowa zai kuma yi ba yasa aka fara watsewa a hankali-a hankali.

Duk da ranta ya 'baci amma haka ta daure bata nuna a fiskanta ba saboda kar mutane su gane akwai matsala. Masu gifts sun ajiye sunyi tafiyarsu wad'anda basu zo da komai bama sun tafi. Kusan minti Arba'in kowa ya tafi amma banda Sady ta k'i tafiya. Suna zaune a kujera suna cin cake, Sady tace "Babez kamar da kika sauk'o naga ranki a 'bace, ko kun samu matsala da Sajid ne?" Zaytunah tace "ai barshi kawai, ni na rasa gane masa, wai meyasa ya tsaneki ne daga ya ganki sai mood d'inshi ya chanja, kin ta'ba masa wani laifi ne?"

Sady ta ce "oh come on Zaytunah, mi zai had'a ni da Sajid, kawai dai kin san anata yad'a gulmammaki akaina wai nak'i zaman aure, wasu suna cewa na bar gidan mijina saboda zan dinga karuwanci and all those lies they are spreading about me, kin sani ai, k'ila shiyasa shima ya d'auka gaskiya ne baya son mu'amala ta da ke"

"Amma indai dan wannan ne Sajid bai miki adalci ba, ai mutuwar aurenki ba laifinki bane ai"

Sady ta ce "nayi aure sau uku duk ban samu kwanciyar hankali ba, ba sai na hak'ura ba, at 38yrs wani aure zan kuma yi, na gaji kin san men are dogs"

"No no no" inji Zaytunah "hell no Sady, kice wasu mazan amma banda My Sajid, he's too perfect for me, thou wani lokaci bana ganewa zuciyarsa amma I love him like that, ke dai kawai ba ki yi sa'a ba amma ni nawa mijin is the best husband anybody could ever had, kyau, ilimi, kud'i da dukiya, and when it comes to that thing......" Hehe tayi dariya "my Sajid is the king, duk jarabar ki saidai ki barshi amma sai ya wujijjigaki ya kai ki 360° and will still do more"

(Hattara mata, mu ji tsoron Allah mu daina bayyana sirrin gidanmu wa k'awaye ko 'yan uwa, musamman abin daya shafi sirri tsakanin miji da mata, haramun ne, Mala'iku na tsinewa me hakan, kuma yin haka na buɗe ƙofar fitina).

Ta ci gaba " Kinga kujeran nan da muke zaune, wow! we did it here ya fi sau biyar, infact asali dama My Sajid likes it on the couch, like when we where in Germany we did it on the dining table, in the kitchen, in his study room ....kai ba mu da specific place ma " Sady ta baza ido tana kallonta cike da sha'awan Sajid, inama ita ce mallakin Sajid, ta tuna sau d'aya a rayuwarta da ta same shi irin dad'in da ta ji. "Kuma Zaytunah, ya kuke yi da yaran? ba kwa tsoron su shigo su same ku a falo ko kuma mai aikinku ta lek'o ta ganku" 

Zaytunah ta sake baza baki tana bata labari "kin san dai suna zuwa Islamiyya da yamma, wancan Babar kuma akwai sanda ta tafi k'auyensu, so muka sha sha'aninmu. Kin san Allah Sadiya idan da Sajid kika aura tun farko da ba za ki ta'ba iya rabuwa da shi ba, shi yasa nima I can't live without him".

Sady tace "you are lucky my friend" .......

Sady ta fi awa tana jiran ko Sajid zai sauko ta ganshi taji dad'i amma bai sauko ba.

shi kam tuni yayi bacci. ganin ba fitowa zaiyiba gashi duk Zaytunah ta tayar mata da sha'awa yasa ta mata sallama ta tafi dan ta nemi wanda zai biya mata buk'atanta.....

           *KADUNA*

Suna zuwa ma'aikatar tasu ta fito daga motan, wani security ya k'ar'ba jakarta suka shiga ciki .

Fitowa yayi daga motar ya nufi wajen wata bishiya mai inuwa ya zauna, ya fito da wayarsa ya bud'e hoton iyalinshi dake kan screen d'in tuni hawaye ya cika idonsa, ya daure ya shafa fiskar matarsa yace a zuciyarsa " nayi nadama mai yawa Aisha, kin sha cewa hankalinki bai kwanta da aikin da na ke yi ba, nace miki k'asata nake yiwa hidima ashe duniya babu gaskiya yanzu, mugayen mutane sun yi yawa a doron k'asa, bayan abinda aka muku nak'ara yarda cewa *"mutum mugu ne"* wayarsa ce tayi k'ara ya duba sunan Agent SY. Ya amsa kiran " Hello SY ya aka yi ne?"

Daga d'aya 'bangaren SY ya amsa "Oga kana lafiya, ya ayyuka?"

"Ba wani kana so ka tambayi information ne kawai, to kasani ban samu komai ba for now, yarinyar tasa ma shegen ji da kai, d'azu wallahi saura kad'an na maketa"

"Yi hak'uri Oga, nasan kafi k'arfinta but I really need information, kasan akwai case akan Babanta and ina buk'atan a bani nayi handling ban san me yasa ba inata wasu irin mafarkai akan garin kaduna, kuma kasan I used to follow my instinct"

Murmushi ya yi yace "Agent Shabbir kenan ka dai yi a hankali yanzu mutane irinku masu gaskiya su ake hallakawa, kaga inda son bin gaskiya ya jawo mini"

"Hakane Oga amma Allah zai taimaka mana, and thank you for the help"

"Ba komai SY zanyi k'ok'ari na nemi information kafin Aaliyah ta yi hutu"

.......Kusan k'arfe d'aya na rana ya nemi masallaci akace ba masallaci a ma'aikatar abin ya bashi mamaki kawai ya fita ya gangara k'asa yaje wani masallaci yayi sallar Azahar.

Tana fitowa kai tsaye wajen mota ta nufa sai dai wayam ba driver, gashi dama yunwa ta ke ji saboda ko breakfast ba ta yi ba, wani dogon tsaki ta ja tace "lallai wannan driver ya cika tantiri, Ina kuma yaje" wani security ta kira ta tambayeshi ko ya ga inda driver d'inta yaje, yace mata ya je Sallah.

"Kutmelesi.....dan iskanci bai gama aiki ba zai tafi sallah"

"Hajiya gashi nan ma tahowa" inji security d'in.

K'ura masa ido tayi tana kallonsa tun daga sama har k'asa, bak'i ne ba sosai ba, yana da saje da gashin baki amma ba mai yawa ba, yana da tsayi ga fad'i da ka ganshi kasan k'ak'k'arfa ne, zubin sojoji, yana da kyau Masha Allah ga kwarjini, yana sanye da goggles bak'i saboda ana rana, shadda light blue yasaka d'inki half jumper, babu hula akansa. Har ya k'araso bata dena kallonsa ba, yana zuwa ya mata sallama zai bud'e mota, nan hankalinta ya dawo jikinta tace "Kai d'an renin hankali da izinin wa ka fita sallah?"

Tsayawa yayi bai juyo ba yace "bana buk'atan Izinin kowa wajen bautawa mahallicina"

"What! wato ma kai ustaz ko, zaka nuna kafi kowa son yin sallah" Bai kula ta ba ya shige cikin mota. Cike da takaici ta shiga cikin motan itama tace "Kai kaini nearest eatery na ci abinci" kamar da mota take magana dan ko motsawa bai yi ba, "Kai ba ka jina ne? Nace ka kaini naci abinci" still shiru sai ma wayarsa da taga ya fara dannawa, a harzuk'e tace "Kai Ustaz you are fired tunda ba za ka....." Bata k'arasa ba taga ya fita a motar, hankalinta ya tashi gashi tana jin yunwa gashi bata tuk'a mota saboda matsalar da take dashi, gashi kafin ta koma cikin ma'aikatar ta nemo me driving d'inta wani 'bata lokaci ne, kawai ta kira mom d'inta. Cike da shagwa'ba tace " mom driver da kika kawomin yana da ta'bin hankali yak'i ya kaini naci abinci,"

Mom tace "Kar ki damu barin kira shi na ji".

Minti biyu sai ga shi ya dawo ya shiga cikin motar, ya juyo ya kalleta yace" kinci sa'a Hajiya tace min baki san sunana ba, amma daga yau kika sake kira na da 'KAI' zan bar miki aikinki"

"To miye sunanka? Ta tambaya a tsorace

"*Alyasa'a*" ya ce mata

"Miye kuma Aleyi..."

"Kar ki nemi 'bata min suna dan suna ne me daraja, sunan Annabi ne, idan baza ki iya kiran sunanba, kice Ali yafi sauk'i haka wasu ke ce min"

Ta yatsina fuska "what a funny name wai Alyisa..."

"Ke!" Ya daka mata tsawa ya cire goggles d'insa ya juyo ya kalleta da kyau ya ce "dan baki da hankali sunan Annabi ne, funny name, sunan da Allah ya kira a Qur'ani shine funny name" gaba d'aya ganin idonsa yasa ta tsorata matuk'a kamar ta sake fitsari, cikin in'ina tace "na tuba, wallahi na tuba, ban ta'ba jin sunan bane"

"And so what, dan baki ta'ba jiba sai akace ki mai da shi abin dariya, saboda bakisan darajar Annabi ba" ganin yak'i ya d'auke idonsa akanta gashi yadda yake magana kamar zai daketa yasa tace "Astaghfirullah Allah ka yafeni"

Ya juya ya tada motar tareda cewa "koda yake ke kika sani"

Sunyi nisa da tafiya kafin ta iya sauke numfashi mai kyau cikin zuciyarta tana cewa 'gaskiya dole mom, ta koreka bazan iya aiki da Ustaz ba'

Ganin zasu wuce wani restaurant bai tsaya ba yasa tace"Al... Dan Allah na kiraka da AY zaifi min sauk'i"

Ba tareda ya kalleta ba yace "ba matsala" ta had'iyi yawun wahala ta daure tace "AY ka tsaya anan zan shiga restaurant d'in nan" ita bama abinci ne ya dameta yanzu ba, tsabar tsoratar da ita da yayi yasa ta ke jin wani masifaffen fitsari. Tana fita kai tsaye toilet d'in restaurant d'in ta wuce data fito kuwa ruwa kawai ta siya ta fito saboda yasa ta loosing appetite, kai tsaye gida tace ya kaita. Tana Allah-Allah su isa gida ta gayawa mom a koreshi..........

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol