Free chapter · Read without an account

11

by Khadeeja Candy · HURRIYA

☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆

          


 𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲


Hello Habibaties 😍🥰

Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy 


https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy



𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣1️⃣


Hanya Hurriya ta hadu da Hamad ya zo zai kirata domin ita Hajiya Binta ta fara tambaya daga isowarta gidan. 


“Me ya same ki? Hajiya na kiranki tana bangaren Appa”


Ya tambaya kamar irin hankalinsa be tashi ba dan ya ga hawayenta.


“Momy ce ta yi baki shi ne namijin ya mare ni”


“Me kika masa?”


“Ban masa komai ba, kawai saboda na je fitowa da sauri shi kuma zai shiga na buge shi, shi kuma ya mare ni gilashina har ya fashe, da jikinki kamar itace mugu kawai”


Ta farasa tana kuka ita ma kanta ciwo yake an karon da suka yi, balle kuma shi da bata san yadda ya ji ba. 


“Ina yake?”


“Yana bangaren Momy”


Ta bashi amsa ta bar shi a gurin tsaye yana kallon apartment din Momy kamar mai tunani tafiya, ita dai ta yi gaba abinta, har Namra ma ta zo ta wuce Hamad na tsaye a gurin yana kallon part din. Hurriya na shiga bangaren Mahaifinta ta rungume Hajiya ta fashe da kuka. Hajiya Binta da tsayi ke neman gagararta sakamakon rikon da Hurriya ta yi mata kalli Alhaji Haruna. 


“Kalli abun da ka yi”


Appa ya sauke kansa kasa ba tare da ya ce komai ba. 


“Allah ya kyauta”


Hajiya Binta ta fada sannan ta taka a haka ta isa gurin kujera ta zauna Hurriya na rike da ita, har jikokinta da matar ďanta Momy suka shigo suka gaisheta, suka fita Hurriya bata dago daga jikinta domin ji take kamar Amman ce ta rumgume, wani gatan ma da kakanin suke mata Hajiya Binta da Gwaggo Amma bata mata irinshi. 


“Kullum idan na zo gidan nan bangaren Iyami nake sauka, amman yau ka raba wannan a dole na sauka a nan, mace mai hankali da girmamawa, wannan matar ta san kimata, har abada ba zaka taba samu mace mai irin tarbiyarta ba tsoho”


Appa ya sauke ajiyar zuciya domin ya san gaskiya Hajiyarsa take fada, iri irin Iyami masu son iyayen miji da girmamasu kadan ne a duniya ba su da yawa. 


“Hajiya ga abinci ki bari na zuba miki”


“Aa Hurriya zata zuba sai mu ci tare ai kasan da ita na saba cin abinci idan na zo”


Appa yayi murmushi. 


“Hurriya dago haka Hajiya ta ci abinci mana”


Hurriya ta dago ta bude kulolin ta dauki plate ta fara zubawa. Sai a lokacin Appa ya lura da fashewar da gilashinta yayi. 


“Me ya sami gilashinki Hurriya?”


“Faduwa na yi”


Ta yi karya kai tsaye. Hajiya ta kalli Hurriya sannan ta kalli Appa ta ce


“Kana da dai jin abun da Hamad ya fada min a mota, idan ba zaka dauki mataki ba ni zan zo da kaina na dauke yaran nan na maida su gidana, domin ba zan bari a rika wulakanta kamar wasu bare ba”


Appa ya shiga mata rantsuwa domin kare kansa. 


“Wallahi Hajiya, ban san da duk wannan ba, ai kin san idan na sani ba zan bari ba, ni kaina sai a yanzu nake ji a gurin Hamad din, kuma In Shaa Allahu zan dauki mataki, Hurriya me yasa baki fada min abubuwan da suke faruwa ba?”


Hurriya ta kalli Appanta ta sauke kai ta cigaba da zuba abinci, daman ta sani ko da Hamad be yi ikirari ba zai iya fada balle ma har yayi. 


“Wallahi ban sani ba, amman zan dauki mataki yanzu da yardar Allah”


“Na dai fada maka, dan ba zaka saki uwarsu ba, kuma ka barsu ana musguna musu kamar wasu ba yi, har dokoki ake saka musu a gida, kuma duk tarin masu aikin gidan nan ace Hurriya sai ta share dakinta da na Hamad su sauran yaran ai ba haka take musu ba, shiyasa tun a lokacin da na ji ka saki Iyami na kira Nafisa da Kaltume na ja musu kunne akan yaran nan ashe na yi a banza, da Iyami ce ko ba zata jefar da magana ta ba”


“Za a gyara Hajiya, amman dan Allah ki aje maganar daukarsu ko maida su gurinki, tun da Iyami ta bar gudan nan yaran nan kawai nake gani ina jin sanyi, idan kika dauke su karin wata damuwar ne a gareni”


Hamad ne ya shigo falon rike da karamar wuka a hannu ya zauna kusa da Hajiya Binta ya aje wukar gefe. 


“Me ya hadaka da wuka Hamad?”


“Apple na yanka”


Ya amsa tare da daukar spoon ya saka a abinci da Hurriya ta zuba. 


“Hamad abinci Hajiya ne fa kana ganin na saka nama da yawa shi ne kuma zaka saka spoon”


A take ya daka mata tsawa. 


“Toh ina ruwanki da ni, ba zaki daina shiga min hanci ba ko? Hajiyar ta ki ce ke kadai”


Hurriya ta kalli Hajiya tana turo baki alamar ta fusata. 


“Hajiya kin gani ko?”


“Kyale shi zuba mana wani”


Hamad yayi kwafa, Hurriya ma ta yi kwafa daman tana da haushin marin da aka yi mata zuginsa be gama wucewa a kuncinta ba. Ai a take Hamad ya daga hannu zai kai mata duka Appa yayi saurin rikewa. 


“Kai Kai Kai Kul daga magana sai ka ce zaka duketa, ita ce yayarka fa, ba zan daukar maka wannan ba Hamad, haka Iyami ke ta fama da kai kai baka san ka ragawa kowa ba?”


“Amman Appa ai ita ta fara”


“Yi mata hakuri kyaleta ai yar'uwarka ce baka da kamar ta, kyaleta”


Ba dan kakarsa Hajiya Binta ta saka baki ba zai bar Hurriya ta zauna lafiya ba, hakan kuma be hana shi sake yin kwafa ba sannan ya fara cin abinci. 


“Ni wannan zuciya ta Hamad ban san gun da daukota ba, fushinsa har tsoro yake ba ni”


Appa ya fada yana shafa kan dansa, Hajiya ta ce. 


“Zai daina kurciya ce, da zarar ya girma ya mallaki hankalin kansa zai daina, wani lokacin yara idan suna jin tashin balaga haka suke jin kamar daidai suke da kowa, ka bar shi ya cike 20 ko 18 fushin nan duk zai hauka”


“Allah yasa, ya shirya mana”


Hajiya ta amsa da Ameen. Sai da suka gama cin abinci sannan Hajiya ta tashi tare da jikokinta Hamad da Hurriya Appa na gafenta suka fito daga bangaren na Appa zuwa bangaren Hajiya Kaltume domin yi mata jaja da kuma barka da kubuta. Ko da suka shigo falon na Hajiya Kaltume yana cike da yayanta da kuma yayan yan'uwanta da ma ita kanta sai hira ake har da Namra. Kamar ta Allah haka Hajiya Kaltume ta washe baki tana maraba da zuwan Hajiya Binta. 


“Sannu da zuwa Hajiya, ai da ma baki zo ba, ga kafafuwa suna ciwo ni kaina idan na warware ai sai na zo na gaishe ki, kuma ai kin kira waya haka ma ya wadatar”


“Aa kara dai na zo, fatar na same ku lafiya”


“Lafiya Kalau Alhamdulillah, ya ciwon kafafuwan yayi sauki?”


“Alhamdulillah”


Sama sama dai suka yi ta gaisawa Appa na zaune kusa da Hajiyarsa daga kasa, Hajiya Kaltume kuma na daga kan kujera ita da duka yaranta, Hurriya da Hamad ne kadai a kasa domin haka Amma ta koya musu idan babba yana kan gado ko kujera to su kuma su zauna a kasa, kar su zauna tare da shi ko kuma a yadda yake zaune. Da hira ta yi hira ne Hajiya Kaltume ta dauko zancen wahalar da suka sha a dajin tana fadar yadda aka rika mistreated dinsu kamar wasu dabbobi. 


“Shiyasa ake son a samu soji masu kishin kasa da za su iya yakarsu idan ba haka ba, kasar nan da wahala ta gyaru domin Shugabannin ma sun zama sai a hankali”


Cewar Yasir. Cikin murmushi Hajiya Binta ta kalli Hamad ta ce. 


“Da yardar Allah Hamad soja zai yi, wannan fushi da zuciyar ta soja ce”


Hamad ya girgiza kai. 


“Aa ba soja nake so ba?”


Namra ta ce. 


“To me kake so? Wannan zuciyar taka Hamad ai soja ya dace da kai”


“Aa ni Likitan idanu nake son zama, idan na kware zan yi ma Hurriya aiki ta, ita ma ta rika gani kamar kowa”


Tsit katon falon na Hajiya Kaltume yayi domin babu wanda ya za ci abun da zai fito daga bakin Hamad kenan. Hurriya ta yi murmushi tana masa kallo irin na so da kaunar dan'uwa, ita kanta ba yi zaton Hamad yana sonta kuma ya kula da damuwarta har haka ba. 


“Come here my friend”


Yasir ya mika masa hannu, sai ya taso ya iso gurin Yasir din Yasir ya rumgume yana buga bayansa. 


“Yayi kyau babban mutum”



Cikin jindadi da alfahari Appa ya kalli Hamad ya ce. 


“Da yardar Allah da yardar Allah, Hamad ba zaka yi karatu a kasar nan ba, waje zan kai ka ka sha ilmin akan idanuwa har ka gaji, da ikon Allah wannan kudirin naka sai ya cika ko da bana raye”


Hajiya Kaltume da ta rasa abun da zata yi ta kalli Appa da murmushin dole.


“Za a karya dokar fitar da yara waje karatu kenan Alhaji akan Hamad?”


“In Shaa Allah, ba shi kadai ba Hurriya ma ba zata yi karatu a kasar nan ba, yadda take da kokarin nan waje ya kamata ta yi karatu, kuma ko ba ni ba Principal dinsu ya fada min suna sa ran da zarar ta gama secondary school zata samu scholarship mai kyau a manya kasasshe saboda kokarinta da yadda take cin gasa ta bangaren lissafi”


“Maa Sha Allahu, Allah ya nuna mana yara masu albarka Allahu akbar Allah dai yayi albar....ya bar zumunci”


Sai ta kasa karasa da Allah yayi albarka ta canja zuwa Allah ya bar zumunci, domin ta san hausawa sun ce addu'ar makiyi karɓaɓɓiya ce, ita ko ba zata so su yi albarka ba. Gashi abun da Appa ya fada cewar yaran Iyami za su karatu a waje ya daki zuciyarta mugun daka irin dakan da ace mashi ne, babu abun da zai hana ya bullo ta bayanta, yanayinta ma gaba daya sai ya sauya hankalinta yayi mugun tashi, ba dan ta yaki zuciyarta ba wata kila ma da ta rasa sukuninta har kowa ya gane halin da take ciki. 


“Allah sarki dan'uwa mai kaunar yar'uwarsa, duk da fadan nan da kuke da rashin jituwa wannan soyayyar da kaunar tana nan a zuciyarsa, Allah ya kara hada kanku, ya shirya mana”


Kowa ya amsa addu'ar da Hajiya Binta ta yi da Ameen ban da Hajiya Kaltume da gume ma ya karye mata kamar wadda aka kwancewa zane a kasuwa. Daga bangaren Hajiya Kaltume Hajiya Binta ta fito ta shiga bangaren Momy suka gaisa sannan ta fito tana jin kewar Iyami. Sai addu'a take ma Appa idan dawowar Iyami alheri ce Allah ya daidaita tsakaninsu, ya kasa amsawa da ameen bayan kuma abun da yake nema kenan a zuciyarsa. Mota daya suka shiga Hurriya bayan ta dauko mayafinta, ita da Hajiya suka zauna a back seat, Appa da Hamad kuma suka shiga gaba, Appa yana jan motar suka fi daga gidan. 


After mintuna goma da tafiyar Hajiya Binta, Momy ta fito tare da bakuwarta da kuma ɗanta da be ci komai ba a cikin abubuwan da Momy ta saka a shirya musu, Miwan na bayansu tare da dan'uwansa Musib sun yi ma bakuwar Momy da ďanta rakiya ban da Namra da har yanzu tana can bangaren Hajiya Kaltume. 


“Captain ai yana yawan zuwa nan, duk lokacin da zai zo garin na ba ya tafiya sai ya shigo, ina jindadin haka Wallahi”


Hajiya Turai ta yi murmushi. 


“Ai danki idan yana son mutum to ya huta, Allah ya hada jininku”


“Sosai kam, Allah dai ya nuna mana lokacin auren nan mu rakwashe”


Cewar Momy, Mutumen da aka ta maganar akansa be ce uffan ba ya fara sauko Entrance din hannu dafe a kirjinsa yana murza a hankali domin ba karamin zafi ya ji ba a lokacin da suka yi karo da Hurriya, taku daya biyu uku hudu yayi kamin ya ja ya tsaya yana kallon yadda tsaddadiyar motarsa ta yi ta kasa gaba daya, saboda tayun motar da aka succe duka hudu. Ya juyo ya kallesu.


“Waya taba motar nan?”


 “Wace motar?”


Kusan a tare suka kalli motar Musib yayi sauri sauka ya karasa gurin motar da mamaki. 


“Lafiya kalau kuka zo da ita?”


“Idan bata da lafiya zamu zo da ita ne? What kind of stupid question is this!”


“Subhanallahi, garin ya haka ta faru!”


Cewar Momy tana saukowa ta nufi gurin motar. Miwan ya ce


“Gaskiya wannan succe tayun aka yi”


“To waya aikata haka? Wannan dai rainin wayo ne da neman mutum yayi magana ace ya cika masifa”


Ya fada da karfi wani karin bacin dai na tunkarosa, cikin bakinciki ya sauka ta isa gurin motar. Momy ta kai hannu ta dafa karjikinsa. 


“Kwantar da hankalinka Captain, a cikin yaran nan dai wani ba zai yi gigin yi maka haka ba, akwai dai matsalar da aka samu”


Momy na rufe Hajiya Turai ta miko masa hannu kamar wani karamin yaro dan yaye. 


“Captain shigo ka zauna, sai mu shiga wata motar”


Ya sauke ajiyar zuciya tare da jan dagon numfashi ya fi sau goma, sannan ya shuri motar da kafarsa da karfi. 


“Duk wanda yayi min haka da gangan yayi, saboda a bata min rai”


“Toh waye zai maka haka Captain? Dan Allah karka bata ranka, na gano, yanzu haka ba zai wuce bakar matar can ba Kaltume, domin na dade da lura da yar bakinciki ce ta karshe”


Momy tana maganar tana jin kamar ta yi tsalle taje ta shake wuyan Hajiya Kaltume. 


“Oh kekam baki zaune cikin mutane kwarai Hajiya Nafisa, rayuwa a gidanku tana da wahala”


Momy ta amsawa Hajiya Turai tana kwafa. 


“Barta na san yadda zan yi maganinta, da ni take zancen, Captain yi hakuri shigo ka huta sai ka dauki motata ku tafi da ita, idan an gyara wannan Musib zai kai maka ita gida”


Jameel ya juyo ya nufo hanyar falon, sai duk suka dugunzuma suka biyo bayansa, ban da Hajiya Turai da bata matsa daga inda take tsaye ba tun bayan da suka fito daga falon. Cikin natsuwa da kamala ya shiga falon, sai ka rantse ba shi ne ya gama bacin rai a waje ba, zaunawa yayi ya hade hannayensa ya sadda kai kasa ya rufe ido yana motsa bakinsa a hankali, kokari yake na ganin be bar bacin ransa ya ninku a zuciyarsa ba...

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.