Free chapter · Read without an account

34

by Nazeefah Sabo Nashe · GASKIYAR LAMARI

GASKIYAR LAMARI 34.



NAZEEFAH SABO NASHE.


***.


Masu son daga farko akwai a Wattpad@Nazeefah381


Ko ku duba Arewabooks@NazeefahSaboNashe.





“Ni na kasheta kamar yarda Balkisu ta ce.”

Wani kallo Daddy ya mata cikin b’acin rai zuciyarsa kuwa kamar ta ballak’a k’irjin ta fito saboda tashin hankali. D.p.o ya saki ajiyar zuciya kafin ya ‘dan yi rubutu a wata takarda sannan ya sake d’agowa ya kalli Mommy “Maryama wannan ba amsa ba ce, kin ce ke kika kasheta Amma kamar yarda Balkisu tace, That means you are not sure.” Mommy ta saki murmushi cikin b’acin rai ta ce “To me Zan ce Yallab’ai? Kowa hasashensa yana ba shi ni na kashe Muneebah duk da ba su da k’wakwkwarar shaida, ni suke zargi duk da ba ni ka’dai ba ce abin tuhuma, abin tambaya ma me Muneebah ta min da zan kasheta?” Abba ya saki ajiyar zuciya yana kallon D.P.O “Ina ga akwai buk’atar ka ba mu ita mu tafi da ita mu zauna tunda abu ne duk na gida, dama rigimar Baba ce idan banda haka ni ba na zargin kowa da kisan Muneebah na barwa Allah ina fata kuma ta samu Aljanna In sha Allah.” D.p.o ya girgiza kai “Ba zai yiwu mu bar maganar ba ko da kuwa kai ka hak’ura tunda abin ya shigo da zargi dole ne mu tabbatar mun kwato hakkin ranta kamar yarda gwamnati ta ba mu dama, za mu yi k’ok’ari mu gano dalilin mutuwarta. Wane likita ne ya duba ta ya bada tabbacin mutuwarta?” Wata irin tsawa Abba ya ji ana masa a kansa da k’irjinsa zuciyarsa ta buga sosai a razane ya d’aga kai ya kalli D.P.0 shima D.P.O d’in shi yake kallo yana jiran k’arin bayani, tsoron da ya gani a kan fuskar Abban shi ya tabbatar masa akwai wani abu da suke b’oyewa. “Ina jin ka.” Ya fa’da yana sake kafa idanunsa a kan Abban. “Dr.Jameel Zarewa daga asibitin Zarewa clinic da yake unguwar Tarauni.” Rubutu DPO ya yi kafin ya d’ago ya kalli Abba “Zan saka a d’auko shi yanzunnan saboda akwai tambayoyin da nake son masa.” Waya ya saka ya kira yaransa ya sanar da su Asibitin Zarewa tare da ba su umarnin su taho masa da Dr.Jameel Zarewan. Yana kashe wayar ya sake musu wata tambayar da ta sake wuntsila kayan cikinsu. “Bayan Maryama ba kuma wani wanda ake zargin zai iya kasheta? Dalilin wani sab’ani da suka samu?” Tsit wajen ya yi ba mai motsi kowa da abinda yake tunani a zuciyarsa. Hakan da suka yi ya tabbatar DPO tabbas akwai wani lamari da basa son a sani. Ya saki ajiyar zuciya kawai bai kuma sake musu tambayar ba sai ma cigaba da rubutunsa da ya yi.




________________


Kuka kawai Muneerah take a motar kafin su isa gida. K’irjinta ya mata nauyi Allah take rok’o yasa ta mutu ta huta da ganin wannan rayuwar da kai tsaya ta mata suna da BAK’AR RAYUWA. Da gaske ba wani abu da zai saka ta ta sake son rayuwa bisa tarin k’alubale da ta fuskanta. Ita ake zargi da kisan y’ar uwarta kamar yarda ita da kanta take zargin kanta da kisan Muneebahn amma ta yaya? A mafarki ko kuwa a maye zata aikata kisan? Ita ka’dai ce a gidan tare da Muneebah waye zai bata guba idan ba ita ba?” Ta runtse idanunta kawai tana cigaba da kukan da ya Riga ya zame mata jiki. Bata so aka kama Mommy ba, don bata son rushewar zumuncinsu ita da Mammy don haka ya zama dole ta fito ta bayyanawa duniya ita ta yi kisan ba Mommy ba, ko ta cire musu shakku da zargin Mommy a ransu matar da ta nuna mata tsananin k’auna tun tana zanin goyo, take kuma son magaifiyarta kamar sun taso y’an biyu, gwara ita dama ta cire tsammanin da rayuwar tunda ta rasa y’ar uwa shak’ik’iyarta gwara kawai ta mutu ta huta. Mammy kuwa kasa rarrashinta ta yi don itama kukan take amma ba na zahiri ba na ba’dini wanda ya fi na zahirin ciwo da ra’da’di.




Ammar kuwa tunda ya fita daga gidan ya rasa ina zai je ya ji sanyi k’arshe sai ya b’ige da tafiya Office d’in Faruk. Tunda Faruk ya gan shi ya mik’e da sauri yana kallonsa cike da mamakin yanayin abokin nasa kamar wani mahaukaci sabon kamu. Zama Ammar ya yi yana sake cusa hannayensa cikin tarin sumar kansa da ta cukurku’de saboda rashin gyara kamar ba Ammar d’an kwalisa da aka sani ba. Faruk yana dubansa ya ce Ammar lafiya kuwa?” Bai amsa ba sai ma kwanciya da ya yi a saman carpet yana lumshe idonsa kuka yake son yi amma kukan ya k’i zuwa sai wani irin turiri da zuimciyarsa take yi sai yanzu ya san ashe Kuka ma Rahma ne. 


Faruk barin abinda yake yayi ya taso ya zo kusa da shi ya zauna. “Ammar tashi mu yi magana me ya faru?” Cikin dakusashshiyar murya Ammar ya ce “Komai ma ya faru Faruk, Mommy tana station an kamata, ana zarginta da kisan Muneebah.” Faruk ya zaro ido yana kallon Ammar kafin ya ce “What! Kai kuma me ka yi a kai?” “Me Zan Yi Faruk? Ban san me Zan Yi ba? Ba ni da k’arfin gwiwa gaba d’aya na sare dana sani nake mara adadi a zuciyata, sharrin shai’dan yana neman ya jawo mana rushewar dangin da aka gina cikin soyayya da k’aunar Juna.” Faruk ya lumshe ido wata zuciyar na son tausaya masa, wata kuma na nuna masa dama ce ya samu amma ta yaya? Ta yaya zai shaidawa duniya Ammar ma abin zargi ne akan kisan Matarsa?






__________________



Samun sak’on kiran DPO ya wuntsila cikin Dr.Jameel tsoro ya mamaye farar fuskarsa da tausayin Abba da ya Riga ya masa alk’awarin rufe wancan gungumemen sirrin? Tambayar da yakewa kansa bayan Abba da Mammy waye ya san Muneebah ba mutuwar Allah da Annabi ta yi ba? Da har maganar ta kai wajen hukuma? Tashin hankali wanda ba a saka masa rana ya zama dole gareshi kenan ya fito ya sanar da hukuma zahirin gaskiya ya gaya musu k’akkarfar guba ce ta kashe Muneebah irin gubar da ko mutum shak’arta ya yi sai ya ji a jikin sa balle ta kai tajallin da ya sha. Ya yarfe gumin da yake fuskarsa kafin ya goge glass d’in idanunsa ya sake mayar da shi ya mik’e don amsa gayyatar da DPO ya masa da sakamakon gwajin Yoghurt d’in da Muneebah ta sha a daren ranar da zata mutu, yana ayyana yau dai dole GAKSIYA ZATA YI HALINTA. Abba ka gafarce ni.



Tunda ya shiga Office d’in ya yi arba da su Abban ya sake samun kansa cikin tashin hankali da tsoron kada a tabbatar da kisan a kan Muneerah don wata irin k’auna yake mata ba tun yanzu ba, sai dai ya kasa bayyana mata don ya san da zarar ya bayyana ko bata so sai Abba ya aura mata shi. DPO ya d’ago yana kallon Doctor kafin ya mik’a masa hannu suka gaisa cikin mutunci, Doctorn ya sake mayar da akalar gaisuwarsa wajen Su Abba suma suka amsa jikinsu a sanyaye. Cikin dakiya da nuna kwarewar aiki DPO yace “An sanar da ni kai ne likitan da ya tabbatar da mutuwar Muneebah a wannan ranar, ko zaka iya gaya mana menene silar mutuwarta?” Doctor ya ja ajiyar zuciya yana jin sautin bugun k’irjinsa yana k’aruwa. DPO ya sake nazarinsa kafin ya ce “Ina sauraranka.” Murya a sanyaye cikin k’arfin hali ya ce “Poison ta sha a abincin da ta ci na k’arshe a saman gadonta.” DPO ya yi rubutu kafin ya ‘dago ya kalli likita da su Abba “Me yasa tun lokacin mutuwar baku sanar da hukuma ba ku ka yi k’ok’arin b’oye hakan?” Abba ya ‘dago yana kallonsa da yanayin kallonsa na rashin nutsuwa tun bayan mutuwar yake tsoron zuwan ranar duk da k’ok’arin da Balkisa ta yi na a bayyanawa hukuma kisan Muneebahn Abban ya hana don yana tsoron laifin ya fa’da kan y’a guda da ta rage masa. Har sab’ani suka samu da Balkisan a daren da aka yi bakwai taje masa da zancen da ya girgiza tunaninsa ta yarda ta nuna masa lallai tana so a kai Muneerah wajen police don su tuhumeta? Wani kallo ya zuba mata cikin b’acin rai ya ce “Amma dai ba ki da hankali ko Bilkisu? Ita y’ar ta mu guda da ta rage ki ke son mu rasa ta?” Kuka ta saka masa sosai tana fa’din “Ni dai in dai za ka bi ta tawa gwara mu rasa ta d’in akan ta zauna da laifin kisan kan da zai d’aid’aita rayuwarta don hak’kin rai ba abin wasa ba ne.” Cikin b’acin rai da hargagin fa’da ya ce “To idan kina son ki ga b’acin raina Bilkisu ki kai zancen nan wajen hukuma ko kuma ki fidda shi wani ya ji, ke nake ji ke nake tausayi saboda ke ce ba mahaifa a jikinki ni ko a yanzu na yi wani auren ina tabbatar miki zan samu haihuwa.” Ta fashe masa da kuka tana fa’dawa jikinsa shi d’in ma hawayen yake zuciyarsa na sake masa k’una. Ya saki ajiyar zuciya yana ‘dagowa da sauri jin maganar DPO “Ku gaya min wa ku ke zargi bayan Maryama a kisan Muneebah.” “Muneerah!” Abba ya fa’da a hankali cikin wata murya da ta nemi tokare masa a mak’ogaro saboda rashin k’arfinta. Da sauri Daddy ya ‘dago ya zubawa Abban ido cikin b’acin rai ya ce “Ya haka Ahmad wani irin zancen banza ne wannan? Ba mu gama solving wani case d’in ba zaka kawo mana wani?” Abbu ya ha’diye yawu mai d’aci da ya gauraye bakinsa murya a raunane ya ce “Dole na fa’da masa Yaya, saboda ko ban fa’da masa ba nan gaba idan aka tsaurara bincike za su iya ganewa da kan su don haka fa’dar shine masalaha.” Ya fa’da yana sadda kansa k’asa yana jin sarewa gwiwa da gab’ban jikinsa gaba ‘daya, shi da kansa ya san a lokacin da za’a auna jininsa za’a ga ya yi mummunan hawa. Daddy ma tashin hankalinsa ya fi da ninkuwa zuciyarsa ta shiga cikin wani irin k’unci, haushin Abba da yarda ya yi azarb’ab’in magana ya b’ata masa rai sosai. Dpo kuwa nazarinsu yake yi sosai kafin shima cikin wani yanayi ya ce “Wacece Muneerahn?” Abba ya ‘dago yana k’ok’arin kawar da k’wallar da take masa barazana ya ce “K’anwarta ce duka y’ay’anane su ka’dai na mallaka a duniya k’addara soyayyar Mutum d’aya ta afka musu.” Nan ya fara bawa DPO labari In briefly. Sanda DPO ya gama jin labarin sakin ajiyar zuciya shima ya yi abin ya girgiza tunaninsa ya kuma tausayawa Abban k’warai da gaske kafin ya d’ago yana share zufar goshinsa ya ce “Ba Muneerah ka’dai ba, Ammar ma abin zargi ne! Tunda ya bayyana soyayyarsa ga Muneerahn shima ku ne baku musu masalaha ba dukkansu kuka bi umarnin zuciyarku ku ka k’i mallaka musu junansu komai ya faru kune kuka jawo, zan saka a taho da Ammar da Muneerah gaba ‘d’aya saboda suna k’ark’ashin mutanen da ake zargi.”


Shiru su Abba suka yi ba wanda zai ce hankalinsa a kwance yake, kowa tsoro da firgici ya danne zuk’atansu. Suna gani DPO ya aika a taho masa da Ammar da Muneerah.



Sanda Labari ya riski Mammy na zuwan y’an sanda gidan da umarnin taho da Muneerah da aka basu, zuciyarta ba k’aramin bugawa ta yi ba, ta dinga jin jiri har sai da ta dafa bango, ga duhu da idanunta suke gani. Kafin ta yi aune Muneerah da ta ji komai ta fito sanye da hijabinta har k’asa zuciyatta zuwa lokacin ta bushe gwara kawai ta je ta amsa laifin ta. Da sauri Mammy ta ja hannunta “Tsaya Muneerah ba inda za ki je na tabbata ba ke kika kasheta ba ba ta yarda za’a yi ki kashe y’ar uwarki saboda soyayyar d’a namiji.” Muneerah ta juyo idanunta Jawur kamar gauta ta ce “Ki yi hak’uri Mammy zan je na amsa laifina kowa ma ya huta.” Ta mik’awa y’an sandan hannunta Suka saka mata Handcuffed suka yi waje da ita. Da sauri Mammy ta bi su tana ihu, ta k’walawa Driver kira “Mu je duk inda suka je za su tafi min da Muneerah alhali bata da laifi na shiga uku Baba driver shikkenan itama Muneerah zan rasata kamar yarda na rasa y’ar uwarta.” Tausayinta sosai ya kama Baba Driver ya kuma bi umarni ta da sauri suka bi bayan motar shiga ba biya fita da Allah ya isa.



Ammar kuwa sanda sak’on ya sameshi bai wani nuna damuwa ya bi bayansu bayan shima sun saka mata handcuffs d’in suka tafi da shi. 




D’aya bayan d’aya DPO ya dinga kallonsu tausayin ahalin na neman rinjayar zuciyarsa sai dai ya san ba wata mafita dole sai an yi bincike an gano makashin. Ammar kansa na k’asa ita kuwa Muneerah kukan ma ya k’i zuwa sai na zuci da take. DPO ya kalli Muneerah ya ce ta kan ki zan fara ance sanda kina gidan ta mutu, kamar yarda labari ya bayyana kuma kuna son juna ke da Mijin Yayar taki hakane?” Muneerah ta d’aga kai tana jin takaicin wannan kalmar ta suna son juna a yanzu duk duniya ba wanda takewa kallon mak’iyi sama da Ammar, ta kuma yi dana sanin son sa da ta yi a lokutan baya yanzu ne ta tabbatar bai cancanta ta so shi ba. “Ke kika bata guba kenan ta sha ta mutu saboda ki mallaki Mijinta, ki samu damar aurensa?” Runtse ido Muneerah ta yi kafin cikin wani yanayi ta d’aga kanta ta ce “Ni ce.” Da sauri Ammar ya ‘dago yana kallonta da duk mutanen d’akin ganin yarda ta amsa kai tsaye. Ammar ya saki ajiyar zuciya mai bayyana hucin numfashi murya a shak’e ya ce “K’arya take DPO ni ya kamata a tuhuma da kisan ba ita ba, kuma zan amsa laifi na tun kafin ku tambayeni………….




Jikar Nashe.✍🏽😊

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol