Free chapter · Read without an account
3
by Nana Disoo · RUDIN ZUCIYA
RUDIN ZUCIYA
NA NANA DISO
PAGE 3
Mashin ne ya bugeni tasak'a kuka sannan takasa karasawa ko'ina. Baffa ne yakamo hannunta har kan tabarma ya zaunar da'ita inda inna kuwa har hawaye ya wanke mata fuskarta nan tashiga dafa ruwan zafi sannan ta mammatsawa surayya kafarta. Yadda iyayen nata keyi da'ita ne yakara samata tausayin su, wata zuciyar tana raya mata da bata kyauta ba wata kuma tana gayamata wannan shine 'yancinki da farin cik'in iyayenki, muryar malam ce ta katse mata tunanin ta "Daga yanzu ni zan dinga kaiki makaranta ina zuwa ina daukarki, surayya kece babba amma kuma kina wasa d rayuwark'i." Murmushi tayi mai hade da hawaye ita kadai tasan me zuciyarta take ciki, Tabbas zuciyarta ta Rud'ita, Dago kanta tayi tace " malam baka yarda da kaddara baniba? Allah zai iya jarabtata aduk lok'acin da yaso nidai kawai addu'arku nake bukata" Sosai jikin malam yayi sanyi yana mai Alfahari da diyarsa. Inna kuwa da zance ke cinta tace " Ni malam ban baka labarin larai ba jiya kai larai ko me ta aikata yaranta duk karuwai ne jiya ina ganin diyarta wani alhaji ya sauketa kai Allah wadai da irin iyaye irin su larai ba..." Ran malam yagama baci duk kyan halin matarsa amma anan ne batada kyan hali cikin fada da masifa yace " Innar kausar wai ke bazaki iya bakinki bani ba koda yaushe cikin tsinewa yaran wasu bakya tunanin Allah kema ya jarrabeki? Ko ke kike bawa yaranki tarbiya bakisan daga Allah baniba?" " Ji malam da wata magana danAllah wanene baisan tarbiyar yarana ba bama surayya kaf unguwar nan babu wanda yakaita nutsuwa kadaina hadamin yara da karuwai nadai gayamaka". Surayya dake kallon mahaifiyar tata cike da damuwa tabbas itama tazama karuwa kuma tanada tabbacin bakomai yajawo hakan ba sai gazawarsu a bukatunsu da kuma irin zagin 'yayan wasu a innarsu keyi ako da yaushe.
************
Bakin Ahmad yakasa rufuwa dadi kamar me yau zai tabi gari har London domin karatu kai wannan bawan Allah Alhaji yana taimako haka ya shirya komai sannan ya fito iyayensa suna zaune suna jiransa ya fito. Umar ne ke rike da jakar kayan nasa idonsa yayi jajir sai yake ganin kamar shikenan sun rabu da Ahmad, malam ne yace " Umaru menene haka sai kace yaro? Wannan kukan naka namenene?" Mama da daman ita Bason tafiyar take ba tace "kabarshi yayi k'ukansa danAllah". Ahmad kuwa yafito ya rungume dan uwansa yana kuka yana masa addu'a, " Ahmad please make us proud danAllah kayi karatu Ahmad danAllah kada ka canza nafi kowa sanin k'a inaso ka samu murmushi alok'acin da kagama karatunka inaso ka faranta ranmu alok'acin da mukaga kwalin k'a" " Yaya inshaaAllah bazan baku kunya ba Amma yaya kadaina kuka Addu'a zakayimin yaya k'aji kaima ubangiji ya haskaka rayuwarka kamar yadda tasanadin ka tawa zata haskaka" " Nidai fatana kayi karatu." Haka Baba yashiga yiwa Ahmadu fada sosai akan abokai da kuma shashanci. Mama dai batace komai ba sai da Ahmad ya riko hannunta " Haba Mamata karkiyi fushi dani bazanji dadin karatun ba danAllah wannan abun ki dauka haka Allah ya k'addara kiyimin addu'a kinji." Murmushi tayi saboda Tina irin fadan da malam yayi mata akan zata haifar da rabuwar kansu indai har tana nuna Ahmad bai cancanta ba, Dagowa tayi hawaye yana wanke mata fuska tace " Nayafemaka Ahmadu Allah yayi muku albarka ya kuma bada abunda akaje nema, InshaaAllahu sai kayi face kazama wani aduniya ina rokon Allah yatsaremin kai daga fitinar matan duniyar nan" Ameen duk sukace sannan aka tafi da Ahmad har airport.
Duk yadda Umar yaso ya danne damuwarsa Amma sai da yayi kuka sai da yayi hawaye tabbas komai rabo ne shima inshaaAllah zai dage yayi karatu a nan jami'ar tasu ta zaria tunda Allah ya taimakeshi Alhaji yace zai samarmasa gurbin karatu, Tashi yayi ya kau da tinaninsa sannan yafita zuwa islamiyyar da yake koyarwa.
**********
Larai nace ba me zai hana kiyiwa yaronki aure ki huta da wannan bakin fentin da suke shafa mik'i, larai tunda ba yau tasaba da halin innar kausar ba sai tayi dariya k'awai, daya daga cikin yaranta ce tafito aguje tana kwara amai, " ohh ni 'yasu har kin dakko ciki? Cewar inna dake saurin barin gidan taje ta yada makotaa, haka kuwa akayi sai da tashiga gida bakwai tagaya musu sannan ta koma gida inna ta tarar yaranta sun gama shiri. " Ke surayya wallahi wallahi idan naganki da yaran larai ..ko dayake ai ke ba irinsu bace bama nama baki izini kyadinga yimusu wa'azi yanzu gashi har karamar ta dakko ciki, " Kausar dai da batason halin mahaifiyar tata gaba tayi ta kyalesu anan inda Surayya jikinta yayi sanyi sosai.
Tunda taje aji ta tarar Bintu batazo ba sai kawarta wata Hindu, hakan yayiwa Hindu dadi sosai inda ta zauna sit daya da Surayya tana ta kamo hannunta, " Inaso muyi kawance Surayya inada manyan masu kudi a hannu na zasu baki gida da mota Amma kafin nan sai kin biyamin bukatata tukunna" " Wacce bukatar?" " Inaso muje mukwana tare agidanmu". " Ke bakida iyaye ne cewar Surayya tana k'allonta da mamaki" Murmushi yarinyar tayi tace " kenan kinada matsala da iyayenki?" Surayya ce tace " mata kwarai da gaske kuwa" Hindatu ce tayi dariya tace " Bakida case a yau dinnan za'arufe musu baki, kici karank'i babu babbaka." Murmushi Surayya tayi tana bin bayan hindatu har suka bar cikin class dinsu directly principle offices suk'aje yana ganin hindatu da Surayya yayi saurin washe baki dan ya dade yana maitar yarinyar daman ashe itama 'yar hannu ce.
Mutumina zamu ware akwai lok'acin ka da daddare fa cewar hindatu. " Kice ansamu sabuwar leda? Yaushe za'a bani in dandana?? ". Sai ka zazzage mana account dinta kaga oga banda time zamu huce test dinmu ka tabbatar munci wannan shine maganar hindatu ta k'arshe rike da hannun Surayya. Suna fita taga Hindatu tashi wata 'yar karamar mota abun ma har ya bata tsoro sai da hindatu tace mata tashige su tafi sannan ta bude motar tashiga. " Kinaso kice min wannan motar takice?" Cewar surayya. Hindatu dake k'okarin juya mota tace " ke zaki iya fina samun arziki Surayya ke dai kibani hadin kai" " Hadin kai ai dole na baki tunda abunda bake nema kenan kuma gashi zansamu sai nazama numba ta daya a bariki sai nazama shahararriyar mai arzuki, wannan shine babban furucinta acikin zuciyarta. Basu tsaya ko'ina ba sai daidai wani dan lungu suna shiga suka tarar da mutum azaune da kasa agabansa, Hindatu ce tace " malam bakawo kawata inaso abata na sa'a, sannan ka rufe bakin iyayenta." Gyara zama yayi yace " Aikinku dubu ashirin." " Bakada case" Shine furucin Hindatu. " ke ya sunanki da iyayenki? " " Sunana Surayya babana kuma yakubu babata kuma asmau." Ga wannan layar ko yaushe tazamana a kanki sannan wannan ruwan ki tabbatar ki zuba inda suke bacci bazasu taba jayayya dake ba sannan bazasu taba cewa komai akan duk abunda zaki aikata " Godiya sukayi masa sannan suka bar gurin directly gidansu Hindatu sukaje awaje suka tarar da baban Hindatu Amma babu abunda yace mata haka suka huceshi Suna shiga daki hindatu tafara jan ra'ayin Surayya har sai data biye mata suka aikata ta'asa duk da rashin dadi da zuciyar Surayya take mata Amma hakan baisa taji nadamar Abunda take aikatawa ba, Sunayin wanka Hindatu ta dauketa ta kaita har kofar gidansu tace gobe ta fito da wuri akwai alhajin dazata hadata dashi, to tace sannan ta karbi kudin da Hindatu tabata Dubu Dari tashiga gida.
Abun mamaki har tayi sallama inna batace mata k'omai ba, hakan yasa tayi shirin islamiyya tafito tana fadin inna nature makaranta. " Allah yakiyaye, kitsaya gidan mairo kisiyo mana kuka idan kuntaso" To inna shine lafazinta sannan ta fita tana zuwa ta tarar da ya ustaz k'allon tuhuma yayi mata sannan yace ta biyoshi office dinsa tana shiga ya rufeta da fada " Haba Surayya yaya zaki dinga wasa da karatu kaf makarantar nan kinsan kece Amira haba Surayya." " Nazo naja maka kunne ne daman rayuwata ba rayuwarka ba billahilazi kakara samun babana akan masa maganar bana zuwa sai nace fyade kak...
More comments....