Free chapter · Read without an account

Page 4

by Ramlat Abdulrahman Manga · NAZNEEN.....

*NAAZNEEN❤‍🔥 <4>*

   EXQUISITELY BEAUTIFUL 

#Mai_Dambu

Top-Notch

Season 3

بسم الله الرحمن الرحيم

Zagaye wutar suke, suna ihu da waka wasun su,suna kukan halittun da suka koma. Kid'an da ake musu ne ya tsaya cak, kafin kuma suka koma suffarsu ta asalin, wani katon tire aka kawo musu aka ajiye a gabansu, cikin siddabaru wata karamar tukunya ta bayyana, a hankali aka dora akan wutar. Suna zaune sunyi jigum-jigun. Kafin kuma suka ware idanu akan tukunyar, yawunsu sai dalala yake yana kara sauka, saboda murnan zasu ci abin da yake tunkuyar.


   A hankali dabban nan ya isa gaban Gimbi. Yayi wani irin tsalle ya dirka akan kirjinta, "ahhhhhhh!" Taja nishi sannan ta bude idanunta. Taga dabban ya juya yana taku ɗai-ɗai, cikin izza. Ya isa bakin wurin zamanshi ya zauna, tashi tayi ta zauna tana kallon yadda kowa yake kallonta, ita ba mamaki yau irin mafarkin da tayi kenan, zuciyarta cike da tsoro ta d'ago kai zata yi magana, ta ga an juye abin da yake cikin tukunyar nan, sun hada da kai da kafar dan mutum, kayan cikin dan adam, gudan jariri, a cikin mahaifarshi. Sai mace da ciki. Bata san lokacin da ta sake komawa wani sumar ba. Domin ta masifar razana, haka ya kuma daka tsalle akanta, ta bude idanunta. Sannan ya ce mata , "kin zata zaki samu nasarar rayuwa ne da tsoro? Ko ance miki shiga wancan kasungurmin dajin da kika yi wani abin mamaki ne? Can ba zai tab'a miki aiki dawamamme ba, nan kuwa zamu miki aiki dawamamme. Ki ajiye a ranki, babu gaggawa babu shakkar wani zai lalata miki shiri, da kanki zaki sarrafa shi yadda kike so ba tare da wani ya saka wasu sun miki ba. Maza ga D'a a cikin mahaifarshi ki dauka, ki cinye kada ki rage min ko kashi ne ki cinye. "


     Duk yadda take son yin musu, ta kasa domin tsintar kanta tayi da rarrafawa har gaban tiren ta saka hannu tana ci, bibiyu har bata san yadda akayi take durawa ba. Sai da ta gama cinyewa tass, har ta riga kowa komawa gefe, domin jin wani irin abu yana bin jikinta, juyi take a wurin har sai da ta rikide zuwa farar mage, ta d'ago kai tana gurnani. Murmushi Mamanta tayi tana me rikidewa magen, amma bakakiririn.

  Doro suka yiwa juna, kafin suka fara sunsuna juna. Sannan suka koma mutanensu, da matukar gajiya Gimbi ta zube jikin Mamanta. "Shugaba aiki yayi kyau, ya batun mijinta?"

   "Babu wanda iya isa kama mata shi, sai ita. Domin kuwa mutum ne me rikon addini yana da yawan ibada. Ita tasan lokacin da zata kama shi, ai mace ce ita idan ta sake ya kubuce mata ba zata tab'a nasara ba."

   "Shugaba taya zata samu mace me cikin?" Kura mata ido yayi kafin ya ce mata. "Me kika gaya mata kafin kizo da ita? Haka zata bi, mu mayyu muna da tarbiyya da iya mu'amala da kowa. Sannan ki gaya mata, ba kowani kurwa zata kawo min ba, ga tukunyarta can, zan tura mata gidanta. Sannan wanan karamin madubin ta ajiye tunda ta daurawa ranta son yawo."


   "An gama!" Basu watse ba, sai da suka ji garin yayi wani irin sanyi, sannan masu d'ana tarko, masu mika bukatarsu suna mikawa, kafin suka watse. Maman Gimbi kuwa, ɗaukar yarta tayi suka nufi takalminsu, suka bar dajin a guje. Tunda bukata ta biya me kuma rage mata.

★★

Jajja.

A bisa al'adar Malam, kafin ya kwanta sai yayi karatu kafin ya kwanta. Kuma koda kuwa barci ne ba zai tab'a yi ba, sai yayi wannan karatun. Yau girkin Hajiya Lami ce. Tunda ta ga yana karatu ta wuce dakinshi ta kwanta. Tunda goshin asuba zata koma daki. Yana cikin karatun barci me karfi ya fara fisgarshi. A wurin ya kwanta, barci me nauyi yayi gaba da shi.


  Midnight.

  A kofar gida yake zaune, yana tsakiyar almajirai ana karatu, ya hango wata mace hannunta rike da yarinya, kallon yarinyar yake sosai amma duhu ya hana shi ganin fuskarta, balle na matar. Abin da ya iya fahimta kawai shi ne kan yarinyar inuwowi biyu baki da fari, har bakar inuwar tana son rinjayar farar inuwar, yadda matar take tafiya ba haka yarinyar take tafiya ba, kamar bata taka kasa, asalin tafiyar a iska take yi, a raunane yake kallonsu har suka iso kofar gidan. Matar ta mika mishi yarinyar tana kuka. Sautin kukan yarinyar da takeyi yaƙe jin shi har tsakiyar kanshi, ambaton sunan Allah yayi, wanda yayi sanadin bude idanunshi. Yana kallon inda yake kwance, dafe goshinsa yayi sannan ya mike, jikinshi a mace. Ya nufi dakinshi, ya sami Hajiya Lami tana barci don haka ban daki ya shiga yayi alola sannan ya fito ya gabatar da sallar nafilla tun tashinsa.


  Bai yarda ya tashi ba, sai da ya kuma hada da salatul istahara, sannan ya nufi masallaci. Da yakinin Allah yana sane da kome. Kuma shi zai kawo mishi dauki. Bai da tsimi bai da dabara. Anan yayi sallah asuba har gari ya waye, suka fito aka fara karatu. Karfe bakwai da wani abu aka tashi saboda masu zuwa boko. Sannan ya shiga cikin gidan ya kwanta kafin tara yayi walaha, ya nufi fada.

    Yana shiga cikin gidan, ya bi kowani daki yana gaishesu. Dakin Innayo ya fara shiga, sannan ya fita ya nufi dakin Goma, bayan sun gaisa ta ce mishi. "malam ina son zuwa jahun na duba yar Kanwata, dazu Jamila take gaya min tana asibiti batajin dad'i." "Allah ya bata lafiya, sai kin dawo."

  "Amin!" Ya juya zai fita, ta ce mishi "Malam ban gaya maka ba." Juyawa yayi yana faɗin. "Ina jinki!"

"Wai dama Hadiza ce tace, na roka mata Baba karami ya tura mata wani abu, zata biya kuɗin makarantar yaranta ne?" Shiru yayi yana kallonta, kafin ya ce mata.

"Amma goma baki da tausayi, yaron nan yayi iya bakin ƙoƙarinshi wancan lokacin ya bata kudi ta kara jari, karewa a shagon shi take amsar kaya tana sayarwa, ta cinye kudin kuma ta koma ya bata, ai ya dace ki mata fada, ta adana na hannaunta gara ita aiki take, shi kuma kasuwanci ne da taimakon Yan uwanshi maza, ai Yaran suna da ubansu idan ba zai iya ba ya sakota zan rike ta da ita da yaranta. Ai ba gajiya nayi da riƙesu ba."


   "Ka dai yi hakuri, a mishi magana ya taimaka domin nayi mishi magana ya ce zai duba, ban san wani irin dubawa zai yi ba." Ta faɗa tana saukar da kai, Ita fa Goma tana da saukin kai da iya biyayya matsalarta daya munafunci, wanda kowa yasan da haka, amma kuma dake mace ce da take iya kyautatawa yasa ake mata uzuri da halinta amma tabbas babu wanda bai gaji da ita ba, sannan tana da wani irin hali duk munafuncinta bata kaunar ka san halin da take ciki, balle kuma akan Yaranta tana da son taji na wani, amma ita ko ka kai kaska naci baka tab'a sanin halin da take ciki. A bisa tsarin Alhaji Adamu ko Abdullahi ya dace ta samu da zancen ko ta ce Malam ya musu magana amma kada wani yasan halin da take ciki yasa tayi gum su yi kominsu ita da Yaranta.

   Sannan ta gefe guda, Jamilah tana karawa borno masu, domin itama ba ƙaramar makira ba ce. Don ma Allah ya taimaka Umma da Hajiya Lami, basu da sauki tass suke mata a gaban uban ko uwarsu.

    Wannan yasa gidan ake zaune da karamin zaman lafiya, Bayan malam ya bar dakin Goma, Jamilah tana kallonshi. Ya shiga dakin Umma yana faɗin. "Sa'adatu!" Dake Umma mace ce me yawan jiki, wanda hakan ya haifar mata da ciwon kafa. Ta fito daga uwar dakinta, tana me zama a kujeran falonta. "Barka da asuba, Malam" "yawwa barka dai." Ya kalleta yana faɗin. "Kunyi waya da Alhaji kuwa?" "Mun yi dashi, yanzu ma haka ina niman Fatu ce. Ya ce min Attahiru zaizo bautar ƙasa watan nan, ina son naji kan zancen ne domin Manu yaki tsayawa muyi magana da shi."

Murmushin jin dadi yayi yana faɗin. "Taya zai yarda ku ji zancen a bakinshi yana uba guda? Kawai abin da ya kawo ni, shi ne a je a gyara wancan dakunan samarin tunda duk basu nan,. A saka mishi duk abinda yake bukata."

   Kallonshi tayi tana faɗin. 

"Malam ni kuwa ina son." Sai tayi shiru, sannan ta ce mishi. "Jiya nayi mafarkin zamu yi baƙi." Kura mata idanu yayi sannan ya gyara zamanshi. "Nima haka, sai dai ban san daga inda zasu zo ba."

   Wayar hannunta ce tayi kara, ta kalla sannan ta ce mishi. "Yawwa ga fatun nan ma!" Mikewa yayi ya fita zuwa dakin Hajiya Lami. Yana shiga ta ajiye miishi abin karyawar shi tana faɗin. "Malam yau ba zaka fada bane?"

 "Zan je." Ya faɗa yana cigaba da karyawa. Har ya gama tana zaune, ya ce mata. "Jiya mun fara magana kafin na dawo kinyi barci, shi yasa ban tashe ki ba." Gyara zama tayi, tare da tattara nutsuwarta ta zuba a kansa ta ce mishi. "Eh dama akan maganar, Kungiyarmu ta fowan ne nace na maka magana a kai, zasu shiga garuruwan azare, itas gadau, shira, gamawa, odubo, bulkacuwa." Kura mata idanu yayi ya ce mata. "a cikin kwana nawa?" Shiru tayi kafin ta ce mishi. "sati daya!" Shiru yayi, kafin ya ce mata. "Kina son zuwa ne?" Girgiza kai tayi tana faɗin. "Da suka zabe ni, sai da na gaya musu cewa, bani da tabbas a zuwa na kawai su zabi wasu."

"Allah ya dawo daku lafiya, ya tsare kunsa sharrin ƙarfe." 

"Ka amince kenan?" Murmushi ya mata yana cewa. "Ai dole na" "a'a babu dole Malam, idan baka son zuwana, ai dama ban daurawa kaina ba."

Dariya yayi irin na manyan, suka tab'a hira kafin ta tafi dakinshi ta haɗa masa ruwan wanka.

★★

Gidansu Gimbi.

Har gari ya waye, Gimbi tana can dakinta kamar gawa, Uwarta kuwa tana sane da ita, ta cigaba da aikinta tare da hada kunun zak'inta, wanda ya ji had'in maita da siddabaru. 

 Gimbiya Baby Yusuf Bogoro.

 Iyayenta sayawa ne, daga Bogoro local government. Gimbiya tana da yayu maza biyu mace daya, waɗanda suke uba daya.

 Kabiru, Falalu, Saratu, sai ita Gimbi amma sauran ukun Uwarsu daban, domin Malam Yusuf ya muslunta da jimawa duk da kowa yasan yadda sayawa suke da mugun taurin kai da kafiya, haka yasa basu cika dogon sha'ani da kowa ba, sai kabilarsu da tsirarun hausawa ko fulani.


    Mahaifiyarsu Kabiru rasuwa tayi, wanda kafin rasuwarta taji labarin mijinta yana niman budurwa, wanda bata so ba amma sanin mijinta ba zai tab'a rabuwa da ita ba, yasa ta kwantar da hankalinta, wata shekarar da akayi kirsimeti, aka kawo musu abinci daga bayan gida su, sannan dan aiken yake gaya mata cewa, budurwan mijinta ne, yasa taji haushi ta ce maza ya maida mata abincin, ba za a karba ba. Ai kuwa sai ga Wasube wato maman Gimbi, suka tawo da kawarta balla, suka tawo akayi ta faɗa kaca-kaca, cikin fushi ta dauki murfin tukunya ta buga mata a goshi. "Kina buga min murfin tukunya!" "An buga miki, me zaki yi?" "Babu" daga haka ta fita, bayan anyi rabo da kyar, ita Wasube a tunaninta Malam Yusuf zai ɗauki mataki ne a kan matarshi, sai ta ga ma ya daina kulata. Haka ya fusata ta har ta kai da ta kama kurwan Mamansu Kabiru , bata mata kamun wasa ba, domin tana kamata ta murde wuyarta, ta kashe. Anyi haka da sati daya ranar new year, tace ga garinku. Ko sati Uku ba tayi da rasuwa ba, sai maganar aurenshi da Wasube. 


  Abin ya mugun bawa Yaranshi haushi, wanda ya kai suka bar gidan suka koma wurin kakansu da yake Kafin tafawa. Ita kuma Wasube rabo ya kawota domin ana auren sai cikin gimbiya Baby. suke kiranta da Gimbi. Duk inda ake niman namiji Malam Yusuf ya kai, domin yana aiki da IDC. Duk da shi karamin Ma'aikici ne, amma yana iya kokarin shi, saboda ko su Kabiru ma yana musu aike.....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol