Free chapter · Read without an account
Chapter 3
*Makauniyar Shari'a*
_Sai a Lahira_
*NA*
_*IKILIMA ADAM*_
_( kyauta daga Allah)_
*Littafin nan , na kuɗi ne da zaran free page ya kare zaki daina ganin sa.hanzarta kibiya naki kada ayi babu ke.*
*Dari biyar kacal*
*3115484026 Ikilima Adam firts bank*
*Tura shaidar biya akan wannan lambar* *( ***) ko kuma kati kuna iya turawa ta wannan number.*
*Siyen Nagari maida kudi Gida*
_*Jarumai writ association marubuta masu aiki da jarumta wajen Fadakar da Al'umma.*_📚📚
SHAFI NA UKU
Nan da nan ya kama hannunsu , suka boye bayan wani kantin, wani bawan Allah da besan suna wajen ba , cikin tsananin tsoro suke kallon yanda suke tafiya irin na iska , daya daga cikin sai fadi yake , " ai sai mun mata fyade kana mu binne ta , shegu tarkacen Fir'auna ". yakai karshen zancen yayin da suke doshi hanyar jejin.
Ganin tafiyar su ne yasa suka fito daga buyar ta su , cikin azzama da sauri suka karaso bakin titi , banda bugawar zuciya babu abinda kake ji , Fat ! fat ! fat ! tafiya me dan nisa su kayi kafin suka samu motar daya debo fasinja, hannu suka fara yiwa motar alamun yatsa . Motar fakawa yayi daga gefe daya , Drever dake kallon su , ta cikin motar , cikin daga murya yace , " ina zakuje ne ?." ya yi magana me nuni ahanzarce yake . Cikin rawar murya Salim yace " malam motar ina ce ?".
" Abuja zamu je ". Direba ya bashi amsa a dakile.
" su ma cen suka nufa." ya yi magana yana me zaro dubu biyar daga Aljihun wandonsa , mikawa dreba yayi tare da fada wa drever basu da kaya . Babu bata lokaci suka shige motar , bakinsu na rawa suna shirin yi wa Salim godiya , drever yaja motar cikin hanzarinsa.
Salim kuwa durkushewa ya yi awajen yana kuka mai tsuma zuciya , domin Allah kadai yasan irin kaunar da yake wa Amatullah yau yana ji yana gani ya rasata a kauyen . Ganin kukan ba mafita bane yasa kama hanyar Gidansu , tafiya yake duk babu kuzari ajikinsa.
Amatullah cikin motar , sauran fasinjojin sai rufe hancin su , suke sakamakon cika su da wari da sukayi . Cikin fada wani yace , " bayin Allah , ya zaku shigo mota kuna doyi , haba ai wannan cutarwa ce ."
Amatullah da Papy kasa magana sukayi sai kif kif da idanu suke domin su kansu sun san suna wari , to amma ya zasuyi da ƙaddararsu tun da akauyen ba kullum suke samun dibar ruwa ba.
Bangaren Matasan
Su na isa suka ga babu su , babu alamunsu , sai kayayyakin su dake wurin , ganin hakan yasa suka fara dube-duben ko sun dan fita ne su dawo , sun fi minti talatin suna jiran tsammani , daya da ga cikinsu ne ya yi karfin halin fadin , " anya ba'a samu munafukin da yazo ya sanar mu su ba kuwa?." ya yi magana cikin kaduwa.
Babu abinda ka ke ji a jejin sai tashin hayaniyar su , suna fadin " wallahi koma waye ya fada musu ze fuskanshi hukunci". cike da takaici suka baro jejin suna tafiya suna yarfa hannu , alamun tarin damuwa.
Aguje cikin azzama suka karasa Gida inda suka sanar da rashin nasarar su , mamaki ne yakamasu , jin wai ba'a gansu ba. Kannen Salim su kace ," Baba ina Salim yaje tun dazu da sai yanzu ya dawo, wallahi muna da yakinin shine ya fitar dasu ". Su kayi magana cikin confidence.
Nan da nan hantar cikin Salim ya kada idanunsa su ka juya daga fari zuwa ja , cikin tsoro da rawar murya da in'ina da ya zo masa lokaci daya yace , wan ....nan....wa..ni....i..ri...ma....ga..na..ce , Au...wal.". ya karashe maganar cikin kaduwar harshe.
Auwal yace, " wallahi kai ne ai rannan da kofinta ya fadi , kowa yaki daukar mata kaine ka dauka ka bata , kuma kana yawan zuwa kai musu abinci , daga magana fa nan da nan ka rude, kasan mara gaskiya ko a ruwa gumi yake ". ya karashe zancen yana tabe baki. Ran Iyayen nasu ya yi matukar ɓaci , cikin takaici Baban Salim ya hau dukansa duk inda ya samu ajikinsa, ganin be gamsu ba , yace wa'yannan matasan da su tara masa gajiya. Cikin kuka ceton rai , Salim yace, " bani bane bansan wanda yafitar dasu , Auwal karya yake min , don Allah ku fahimceni". ya karashe magana murya a rude. Baban Salim cikin takaici da haushinsa yace, " wallahi in baka fadi inda suke ba a jejin nan zakasha na jaki ".yayi furucin iya gaskiyarsa. Banda hawaye babu abinda ke kwaranya daga idanun Salim , kin magana ya yi hakan yasa Mahaifinsa ya bada umarnin a masa duka. Sosai suke bugunsa , muryarsa kasantuwa dare ne saida ya karade gidaje mafi kusa dasu. Saida mahaifiyarsa tasa baki ganin yanda hancin Salim ke fitar da jini , tsorata tayi , arude ta kama d'anta ta yi cikin gidan dashi tana tafka salati wanda yasa gabakidaya kowa dake wajen rikicewa harda masu bugun nasa.
ABUJA CITY
Ridwan sai karfe goma ya dawo Gida tun fitarsa , Sallah , ya na karasowa yaga dukan kannensa a falon banda Mamyn a cikinsu. Gaisuwar da suke masa ya samu damar amsawa fuska asake , kana yakai dubansa akan Faisal dake kallon tv , cikin zazzakar muryansa ya ce, " ina Mamy ta ke ?." ya yi furucin cikin kosawa da jiran amsa. Cikin sakin fuska da murmushi Faisal ya ce, "ai tun da ta je sallah isha'i bata dawo ba ". ya karashen zancen ya na mai kokarin bin hanyar dakin Mamy domin dubota. " Dakata ." ya ji muryan Ridwan ya doki dodon kunnensa. Cak ya tsaya tare da waigowa , fuska a sake yana kallon yanda yake juya labbansa.
" Ba sai ka je ba kyaleta , za mu hade da safe in sha Allah." ya kai karshen zancen tare da hawa kan matakalan step cikin nutsuwa da haibarsa.
Anisa da Rukayya cikin sanyin murya suka ce , " yaya Faisal Please dawo ka ci gaba da kallonka, domin yaya Rid lamarinsa sai du'a i ." Samun kansa ya yi da bin maganganunsa , mamaki fal acikin ransa , cikin damuwa ya ce " bansan me yasa ya'ya Rid kwata kwata babu walwala arayuwar sa ba." Anisa kwabe baki ta yi tana kallonsa cikin gajiyawa da zancen yayansu ta ce , " ba mamaki shi haka Allah ya halicce shi kawai dai , shi bame son hayaniya bane ". Rukayya dake jinsu cikin yar dariya ta ce ," ku kyale yayan mu ya huta haba kunsan yawancin yayye maza basa son kannensu su rainasu". ta kai karshen zancen tare da maida hankalinta akan kallon TV. Faisal da Rukayya sosai suka shiga juya kalamanta suna murmushi.
_________
Bangaren Amatullah da Papy sai karfe sha_biyun dare kusan karfe daya , motar ta faka a Garin Abuja direct tasha a ka saukesu .kasantuwa Dare ne yasa ba duka suka samu damar tafiya gidaba . Amatullah bayan sun biya kudi , wajen Masallaci dake cikin tashar suka samu wuri suka zauna itada Papy ga mamakinta , ganin Papy tayi ya dauko rawani yana daure kansa , ya kuma zagaye fuskarsa dashi baka iya ganin komai sai kwayar idanunsa , ma'ana shigar buzaye yayi. Amatullah ganin tsohon dare ne , hakan ya sa bata samu damar ce masa ya ajiye rawanin ya huta mana.
Kiran Sallah farko na Asuba akan kunnensu, cikin rarraba idanu Amatullah ke fadin " Papy banda suturar kirki a jikina ga shi muna cikin babban gari , kuma har gyalena na barshi acen kauyen ya zanyi." ta karasa maganar cikin damuwa . Ganin ana kokarin ta da sallah ya sa be tsaya bata amsa ba , kai tsaye alwala ya dauro , cikin hanzarinsa ya yi cikin masallaci. Ana idar da sallah ya fito , cikin rashin kuzari da rashin sabo da inda su ka zo . Hango Amatullah ta zabga tagumi ya yi ba karamin shock ya shiga ba nan da nan idanunsa su ka cika da kwalla , murya a disashe ya ce , " Amatullah !! kina bani tausayi, Amatullah!! Bansan yan da zan miki bayani ba , Amatullah !! Amatullah." ya karashe kalamansa cikin kuka mai gunji. Barci barawo ya yi awon gaba da ita , bare tasan halin da ya ke ciki. Be tashe ta ba illah kai tsaye wajen wani mai shago ya nufi ganin shine farkon wanda ya fara bude shagonsa da sanyin safiya , cikin muryansa da sam bayason a tantance ya shake murya cikin kasa _kasa da murya ya ke tambayar inda ze samu doguwar riga da hijab , mutumin kwatance ya masa , tare da tabbatar masa sai karfe wajen tara na safiya suke bude kantinsu .
Kauyen Daguzau
Iyayen Salim cikin tsananin damuwa suka fara shawarar , kai Salim Asibitin Murtala dake cikin jahar Kano , kasantuwa yanda ko kwakwarar motsi baya yi , Mahaifiyarsa cikin rudani ta ke fadin " gaskiya baku kyauta min ba , akan zarginku na banza! da wofi kuna neman kashemin D'ana ".
Babu wanda ya tanka mata ganin yanda duk ta rude ta fita hayyacinta. Burinsu be wuce ganin ankaisa asibiti kai tsaye ba. Baban Salim cikin ban hakuri yake rarrashinta dan yasan sun tafka kuskure mai girma.
Kwanaki suna shudewa inda yau sati daya Amatullah da Papy suka yi a Garin Abuja a unguwar Ghetto , dan karamin bukka suka kama haya , tare da siyen duk abubuwan bukatunsu, ciki harda botiki da tsontson wanka da brush da makilin harda sabulun wanka , sabuwar butar da suka mallaka bakaramin sanya Amatullah jin dadi ya yi ba , haka ma yanzu da take ganin tana da sutura har kala biyu , haka ma hijab da takalmi, tukunyar tuwo dana miya da plate da cokula har da kofi da botiki wanka dana shan ruwa , ba karamin sanyata a nishadi yayi dan wannan shine karo na farko a rayuwarta data ga sun mallaki sabbin abu na kansu. Cike da jin dadi ta dauki sabuwa katifar soso wanda ta shimfidawa zanin gadon gwanjo . daga katifar ta yi hade share dakin , ta gyara shi tass kana ta dawo ta zauna tana kallon yanda Papy ya zabga Uban tagumi kamar bashi ba. Har ta bude baki za tayi magana sai taga ya lumshe idanunsa kamar me shirin yin barci , kokarin kai hannunta take domin kwantar dashi , cak ta ji muryansa cikin sanyi da nutsuwa yana fadin" Ba fa barci nake ba ". daga haka be sake furta komi ba , yaja bakinsa ya yi shiru .
Kallon kallo take masa tana son ta fahimci wani abu tattare dashi to amma mene ne? Wannan abun tasan babu wanda ze bata amsa sai shi da kansa. kokarin yin magana take , ya yi hanzarin fadin" Amatullah dauko min Rediyo dina in kunna domin debe kewa ". ya yi furucin cikin yanayin damuwa. Babu musu ta mika masa kana ta kasa kunne jin yana chanza tasha har yazo kan tashar Dala FM na Kano kasa kunne ta yi domin ita kanta tana son sauraren rediyo musamman in ansanya shirin Farar Saka . Jin labaran Duniya ake yi yasa ta danyi karamin tsaki. Papy kuwa sosai ya razana jin Muryan Hajiya Rabi mai Iko , nan da nan ya dimauce ya nemi nutsuwarsa ya rasa , Amatullah sosai take hankalce dashi , kasa kunne tayi domin jin abinda ake fade a rediyo.
Ga abinda ake fade daga cikin rediyo kamar haka .
Hajiya Rabi ....................
Karku Manta Makauniyar Shari'a kuke biya kudai ku biyoni inda zaku nishadantu fadakarwa .
Domin son magana dani
***
Taku har kullum ( Kyauta daga Allah)
Share and comment pls