Free chapter · Read without an account
Page 11
*NAAZNEEN❤🔥 <Eleven>*
EXQUISITELY BEAUTIFUL
#Mai_Dambu
'Top-Notch
Season 3
بسم الله الرحمن الرحيم
Kiran wayar ya kuma, idanunta kur akan wayar amma taki dauka. Kiran ya katse ya sake kiranta bata dauka ba, a takaice dai sai da ya mata kira talatin da biyar a na shida ya kira Mamanta. Tana ɗauka ya kwantar da kanshi ya fara bata hakuri.
"Mama ki bata hakuri, kiran gaggawa aka min, shi yasa ban samu zuwa ba. Sannan ga wurin aikina dakyar suka bani pass."
"Tun wancan sati kace zaka zo, amma baka zo ba. Yanzu kuma sai kace ba zaka zo ba, sai ka tafi Azare. Tow me zan maka?" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Ki kara bata hakuri, kakata ce bata da lafiya, ina son naga jikin ne kafin nazo. Don Allah tayi hakuri zan zo."
Haka yayi ta basu hakuri suna mishi tijara kala-kala, babu yadda ya iya ne amma tabbas yana jin babu dad'i haka suka gama rashin mutuncinsu, sannan suka kashe wayar tare da mishi zagin kare dangi da shi da zuri'arshi.
A can Azare kuwa dama maganar aurenshi da Khalwat ne haka yasa baki ɗaya hankalinsa ya rabu gida biyu, domin ya rasa yadda zai yi.
Yana shiga Azare ya nufi zaweeya, tunda ya shiga cikin gidan yake daure fuska kamar an zage shi. Don ma kada Hajja Marih ta mishi zancen Khalwat yasa shi sauka a dakin Mama Hajja,duk yadda yaso kada a yi zancen Khalwat, sai da aka dauko zancen. Cikin hucky voice dinshi me dan karen sanyi ya ce mata."Mama Hajja dole ne sai na zauna da mata biyu? Naga dai rayuwata ce, kuma iya matata ta wadace ni."
"Alhaji Malam, mace daya bata wadatar ba, muna bukatarka shi yasa muka barka da ita yarinyar da ka aura. Alhaji Malam a wannan karon kayi mana biyayya ka auri yar gida kamar yadda muka bukaci haka, kayi biyayya yau shekara bakwai muna son ganin gudan jininka kai ma!"
Cikin wani irin damuwa ya kalli Mama. Daidai lekowar Hajja Marih. "Mama Hajja idan yace baya bukatarta, ai ba laifi ba ne"
Shiru yayi domin yasan tunda ya ji Kakarshi ta faɗi haka, definitely tana jin haushinsa. Kuma yasan kawaici irin nata, ko iyayenshi ba zata yiwa magana ba, don haka ya ce. "Shi kenan Allah yasa haka shine mafi alkhairi, na amince." Dake ita Hajja Marih bata tsaya ba, tunda tayi maganar ta wuce abinta.
Addu'ar da Mama Hajja take, sai da yaji jikinshi yayi sanyi. Kafin ya kalli agogon hannunshi ya ce mata. "Zan wuce Bauchi!"
"Ba zaka kai gobe ba?"
"A'a akwai taron da za ayi a gidan, Shehi na Majalisar kolin malamai."
"Allah ya taimaka."
"Amin Ya Allah."
A hankali ya ciro kudi ya ajiye mata, sannan ya fita, zuwa dakin Hajja Marih. Yadda ta dauke kai daga gare shi, yake kara tunzura shi, amma sai ya share kamar bai ji zafi ba, ya ce mata. "Zan wuce Bauchi."
"Allah ya tsare!" Ya ajiye mata, kudi ya fita, sannan ya leka falon Hajja Kubrah, ya gaida ta, tayi mishi nasiha sosai, yayi mata godiya, ya bar falon bayan ya ajiye mata itama kudin, yana fita ya samu drivern shi da yazo tun kwana biyu da suka wuce. ya shiga motar, suka bar zaweeya.
Wayarshi ce tayi kara, cirowa yayi ya duba, Hero ya gani a rubuce.
"Assalamu alaikum, Abba!" Ya kira sunan a hankali.
"Naji zaka wuce Bauchi ko? Kayi kokarin duba Khalwat makarantarsu, sannan Mama Hajja ta kira ni ta ce min ka amince?" Lumshe idanu yayi yana jin wani irin d'aci, kafin ya ce masa. "Eh na amince."
"Allah ya maka albarka."
"Amin Ya Allah, na gode sosai Abba!" kashe wayar Abban shi yayi, zuciyarshi tana wani irin tiriri. Ba zasu gane halin da yake ciki ba shi yasa suke kokarin kwakumamishi auren wata yarinya. A rayuwarshi ya tsani abin da zai batawa Gimbin shi rai, balle yasan darajar ta.
Dake motar sabuwa ce, sosai drivern yake falfala gudu.
★★
Gidan Malam.
Tun bayan sallar asuba Malam bai koma cikin gidan ba, har zuwa karfe sha daya na rana, Almajiran da suka taya shi aiki suke bada labarin abin da ya faru. Attahiru da yake gefen Malam yayi gyaran murya, ya gayawa Malam abin da ya faru. Shiru yayi kafin ya ce masa. "Ka gayawa iyayen jibi asabar ina son ganinsu?"
"Eh Baba Malam!" Ya mike yana fadin. "Bari na shiga cikin gidan." "Tow shi kenan" dake Alhamis aka wayi garin ranar . A hankali ya dubi magidanta da suke zuwa karatun safe. Tunda suka tafi yake zaune a zauren. Abin da yasa shi zama a wurin bakin duhun da ya gani a kan Amanda yake aikin kafe shi, amma wani abin da ya bashi mamaki yadda bakin duhun yaki tafiya.
Fitowar Tahir yake gaya miishi, "Baba Malam kazo fa." Tashi yayi ya nufi cikin gidan, ai kuwa bakin duhun ya bishi har cikin gidan, kafin su isa dakin ya rigasu ta isa. Suna shiga dakin, yarinyar tayi wani irin lankwasa da yasa hannayenta suka juya suma. Yadda take juya kasussuwan jikinta zai tabbatar maka, babu dan adam da ya isa yin haka. Dariya ta fashe da shi, lokacin da ta juya kirjinta yana kallon kasa, bayanta ta juya shi sama, kamar wata dabba.
Fararen gashin kanta suka rufe mata, fuska rub tayi wani irin tafiya kamar gizo-gizo, ta shiga bin bangon dakin. Wani irin kara Chioma ta saka tare da ambatar "jesus Christ" ta zube akan gwiwarta.
"Amanda!" Ta kira sunanta da mugun ƙarfi, tana me fashewa da kuka. Kura mata idanu Malam yayi sannan ya cewa Tahir. "K shiga dakina, ka dauko min ruwan zam-zam."
"Tow!"
Zai fita Malam ya riko hannunshi, "ka tabbatar ka shiga da addu'a, domin shadanin ya wuce tunaninka."
Gyada kai yayi, sannan ya wuce, zama Malam yayi yana fara karanto ayoyin ruki'a, wani irin ihu tayi tare da fadowa daga bangon "dumm". Ta nufi wurin Uwarta da gudu."Nne take me away from then!" Sai lokacin Tahir ya shigo dakin da Zam-zam da wasu kayan rubutu, ya ajiye. "Ka dibo min gaushi."
Da sauri ya fita, ya amso gaushin ya kawo, suka shiga addu'a Malam yana tofa addu'a. Yana yi suna hayakin habbatu saudata da aka hadashi da wasu maganin, ihu ta shiga yi, tana kuka a tafi da ita, su bar gidan kawai, su bar gidan kada Maman ta ajiyeta, watsa mata ruwan Addu'a yayi, ta zube a wurin bayan ta saka wani irin ƙara da yasa gidan amsawa suma da suke dakin sai da suka toshe kunnensu. Kafin ta samu barci.
Ajiyar zuciya Malam ya sauke yana faɗin, "ya fita, amma ba dukka ba domin ya jima da ita, kuma zai yi wuya ya barta baki daya. "
"Alhamdulillahi, Jibi insha Allah kowa zai iso!"
"Allah ya kai mu"
"Amin Ya Allah!"
★★
*7:45 pm*
Ya iso Bauchi, kai tsaye gidansu Gimbi ya wuce. Ya samu tarba da bakaken magana kuwa. Amma dake yana son matarshi, sakata yayi a gaba suka bar gidan.
Zaranda hotel suka nufa, inda ya kama daki. Tunda suka shiga ta lura yana dan sussuce mata, yasa ta dauke miishi wuta da wani uban jan aji. "Ni fa na gaji da halin!" Rungumeta yayi, suka wuce ban daki. Bai kyaleta ba, sai da suka yi wanka suka fito, ya samu biyan buƙatar shi ya riko hannunta. "Kiyi hakuri, nasan ban kyauta miki ba, amma babu yadda zan iya ne, amma kiyi hakuri!"
Wani kallon banza ta miishi, sannan ta ce mishi.
"Ina aure aka ce kayi?" Hadiye yawu yayi yana kara sumbatar goshinta. "Eh my heart!"
"Ba wani heart, bayan gashi nan iyayenka zasu saka ka aure, ni dake bamu da arziki."
"Kin ga ni ba haka nake nufi ba, ki fahimce ni." Kuka ta saka mishi, a daren ba karamar rigima ya sha ba, ya mike zai shiga yayi wanka ta saka kuka ta ce mishi.
"Tun baka yi auren ba, ka fara guduna."
"Ba haka ba ne" yafada yana me rungumeta, suna hira barci ya dauke shi. Har dare ya raba, bai samu damar yin wanka ya tsarkake jikinshi ba, wurin karfe daya Uwarta tazo daukarta, anan suka zare kurwanshi. Ta kalli Uwar cikin matuƙar tsorata
"Me zaki yi da shi?"
"Babu kame miki shi za ayi, yadda ba zai miki gardama ba, sannan ba zai tab'a zarginki ba, zai rufe idanunshi akan duk abin da yake faruwa koda kuwa karya ce ke zai bawa gaskiya." Haka kuwa aka yi, suka tafi da kurwarshi, ta lashe shi tas, sannan aka yi yar tsatsuba,.suka dawo gidan. Bayan shugabansu ta bata damar ta amince da yayi auren, babu wanda ya isa ya tab'a zarginta, babu macen da ta isa zama da Saif ba tare da ta mutu ba.
Wannan abin ya mata dad'i, ba karamin gargadi aka mata ba, domin an gaya mata, ban da kishi ta hakura tayi biyayya, idan ta sake ta fara kishi zai kwace kuma zai kore domin asirinta zai tonu. Da wannan ta amince da sharuddan shugabansu. Suka dawo ta yi wanka, ta kwanta wurin asuba shima ya tashi da wani irin kaunarta, yayi wanka ya gabatar da sallar nafila, tana kallonshi sai dariya take a ranta. Bayan ya idar da sallah, yana zaune sai da garin ya waye sannan ya tawo wurinta. Ya kwanta, rungumeta yayi yana faɗin. "Tashi kiyi sallah." Kallonshi tayi ido cike da barci ta ce mishi. "Baby na amince kayi auren, tunda kaga har yau Allah bai bani haihuwa ba, gara ka yi auren ko za a dace." Ware idanu yayi yana faɗin."are you sure?" Gyada kai tayi tana shafa fuskarshi. Ba karamin dadi ya ji ba, anan ya kara turmusata kamar ba gobe, sannan suka shiga wanka, ya fito ya musu odar abinci, ana kawowa yaci ya tafi taron majalisar kolin malamai, lokacin da ya isa, anyi taron a open air theatre ne.
Taron zai dauki kwanaki uku, domin karkashin kungiyar mabanbanta akidu ne, yan darika, yan izala, da yan shi'a, mai girma gwamnan jahar Bauchi, Hamza Abdullahi rauta, ya shirya domin samun hadin kai tsakanin al'umma.
Sai la'asar aka tashi taron ranar farko, washi gari Juma'a, anan ya wuni. Koda aka tashi sallar juma'a, a babban masallacin juma'a na gwallaga suka yi sallah.
Ana tashi ya nufi makarantar su Khalwat, ya zauna har ta fito, ba laifi yar doguwa da ita, tana da kyau ga nutsuwa. Tunda ta ganshi ta dan shiga nutsuwarta. Gefen motar ta shiga, dake tana gidan Kanwar Babanta da take aure a tambari housing estate ne.
Tunda ta shiga motar yake wani cin magani, yayi ta kafa mata kashedi. "Kada ki ce zaki rena min matata, bana son rashin kunya." Magana dai marasa dad'i, yayi ta mata, kanta a sunkuye. Abin tausayi tana da wanda take so, hajja Marih tasa Babanta da Mamarta suka sallame shi. Idanunta cike da kwalla, haka suka isa gidan ya sauke ta bayan ya daura mata kudi a saman cinyarta. Muryanta na rawa ta ce masa. "Na gode!" Ta ajiye miishi kuɗinshi ta fita motar. "Ke!" Ya daka mata tsawa, "Maza dauke kafin na mare ki." Dauka tayi tana kuka, ya kuma ce mata. "Maza hadiye kukan!" Haka ta Hadiye kukan, sannan ta juya ta nufi gidan Kanwar Babanta.
Shima ya juya ya koma hotel din, Saif har ga Allah don dai Gimbi tace yayi auren ne, amma baya son abin da zai bata mata, ranar Saturday suka gama taron, ya wuce da Gimbi Lagos, ta mota domin ya rarrasheta.
★★
Tun ranar juma'a, gidan Malam Malami ake ta saukar baki, tare da dafe dafe, washi gari yaran gidan suka halarci taron, Alhaji Adamu Malami da sauran waɗanda suke kusa duk sun zo, wurin la'asar aka bude taron da addu'a. Domin a tsakar gidan ake taron, Yara da jikokin Malam suke zaune. Shiru Malam yayi kafin ya cewa Umma.
"Sa'a fito min da bakin nan, kai kuma Tahir ka je ka tawo min da bakon nan!"
"Tow, Malam." Suka fada lokaci guda, Umma ta shiga tasami su Chioma, ta ce su fito. Tana rungume da Amanda.
Ta fito daidai lokacin da Tahir ya shigo da Obinna, mikewa Alhaji Adamu yayi yana me rike kanshi.....