Free chapter · Read without an account
Chapter 14 to 15
[10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: _*Makauniyar Shari'a*_
_Sai a lahira_
NA
*IKILIMA ADAM*
*(Kyauta daga Allah)*
*Kai ka Jawa kanka*
*Kanwata*
*Rai daya jan zaki*
*Rudani*
*RAYUWAR Ma'aurata*
*Kaicona*
Duk wanda kuke so sai ku tuntubeni akan wannan lambar
***
Akwai rangwame sosai ga me buƙatar dukansu.
Karku manta Makauniyar Shari'a littafin kudi ne free page ya kusa karewa.
SHAFI NA HUDU
Wannan Yar kauyen Daguzau ce ? me ya kawo hoton ta a nan " yake tambayar kansa cikin zallan mamaki , hannunsa na zoomin din hoton , nan da nan ya fara tariyo abinda ya faru a kauyen da kuma irin takaicin da ya daya kwasa akanta , cikin kadawar tunani yake kokarin nazari akan lamarin anya kuwa ita ce ? rasa me bashi amsa yasa shi kara nusawa cikin tunanin son gano gaskiya , sai hamma yake. ciki kasala yake toshe bakinsa hade da fara lumshe idanunsa , idanunsa na cigaba da tariyo masa hoton cikin computer a kasalance ya yarufe laptop din , ba tare da ya kashe komi ba. Wannan karan kwanciya ya yi ba tare da ya yi adu'oi da ya saba na kwanciya barci ba . Yadauki awa biyu yana barci inda sosai barcin yau ya masa ma mugun kamu . Ahankali daga waje ake turo kofar dakinsa, sanin da aka masa baya kulle kofarsa sai weekend , suna tura kofar sannu ahankali cikin sanda_sanda suka fara leko kai , ganinsa yana kwance ya baje yana barci , alamun ya yi nisa sosai dan ko kwanciyar kirki beyi ba a bakin gado ya kwanta.
Mamy da Madina kallon juna su kayi suna rarraba idanu akan dakinsa da sam babu takarce , computer dake gabansa suke kallo , cikin kasa kasa da murya Madina ta ce " Saratu ko zaki iya fita dakin dan Malam yace ke Mahaifiyarsa bazaki iya aikin ba dole sai an samo wani , da muje waje samun wani gwamma na yi miki mun rufawa juna asiri". Tayi magana cikin kasa da murya . Mamy jin hakan ba tayi musu ba ta fice tare da jan kofar ahankali ta fita cikin sanda . Ita kuwa Madina tana ganin fitar Mamy ta karaso tsakiyar dakin , gab da shi ta karaso tana karewa kyakyawar fuskarsa mai haske da sheki kallo , sajen fuskarsa yanda suka kwanta lub lub take bi da kallo , bata san sanda ta furta " Ma sha Allah" , Kasar zuciyarta . Kallon yanda yake barci bil hakki take tana kwabe baki , cikin karfin hali da kokari irin nata , ta zauna kan gadon nasa ahankali , hannayenta masu kaushi ta sanya ahankali tana shafa fuskarsa , shi kuwa Ridwan acikin barcin ya dan kara motsawa hakan yasa ta yi hanzarin cire hannunta , durkushewa tayi da kanta tana kokarin sumbatarsa a baki , kamar yana sane sai ya kifa a gadon. Ahanzarce ta dago tana kallon ikon Allah cike da fargaba , mutum sai kace mai ido hudu , ganin yanda yake a kife hannayensa duk ya sake su bakin gado , cike da kokari da rashin tsoro ta kamo hannunsa daya tana shafawa ahankali , wani bakon yanayi ta ji yana fisgarta ji take tsigar jikinta na ta shi , nan take ta ji yarrrrrrrrr a ilahirin jikinta, abinda zata iya rantsewa duk auren da tayi a baya bata taɓa jin hakan ba , jikinta na tsuma kamar mazari yasa ta yi hanzarin sakin hannunsa wanda ya janyo hannun buguwa da bakin gadon . Daga cikin barcin ya ji zafin buguwa , hakan yasa ya yamutsa fuskarsa , tare da fara yunkurin juyowa , Madina na ganin réaction dinsa son tashi.
Ahanzarce cikin azzama ta labe bayan labule cikin tsananin tsoro da fargaba .
Shi kuwa zaune ya yi bakin gado yana kallon hannun nasa da ya buge din , cikin jin inda ya bigen na masa zafi , ya rike dai dai inda ke masa ciwo yana matsawa ahankali tare da ciza labbansa , tsaki yake ta jerowa ta yanda akayi ya kwanta ba Alwala da adu'oi , tashi ya yi yana mika tare da kai dubansa kofar dakinsa cikin idanunsa mai dauke da tarin barci , dauke ganinsa daga nan ya yi ya dawo dashi kan labulen dakinsa da yake gani dishi dishi tare da tsurawa wajen idanu sosai ba kiftawa , rike da kungunsa ya ke bin wurin da kallo sosai , kana ya kai dubansa akan kasan labulen. Har ya fara yunkurin tashi domin zuwa wurin , Madina na ganin ya tashi kamar ze nufo inda take banda innalilahi babu abinda take maimaitawa wani uban zufa ne ya karyo mata lokaci daya .
Ganin ya canza akalarsa zuwa banɗaki , yasa ta fara sauke nauyayyen ajiyar zuciya. Tana jin sanyi na ratsata ganin ya shige banɗaki.
ganin ya shiga , kwararan ajiyar zuciya ta ringa sauke wa akai akai , kana cikin sauri da hankali ta bude kofar ta fita tana haki , koda ta karaso wajen Mamy zuru zuru da idanu take bin Mamy da kallo cikin boye tsoronta hade da zama kan kujera ta ce " wallahi Saratu Danki Ridwan Aljanunsa suna da karfi sosai, amma a karshe dai sunce sai kin taimaka min wajen gudanar da aikina ". Ta karasa zancen baki na rawa.
Mamy da zallan mamaki take kallonta , cikin hanzari ta ce " wani Irin taimako zan baki, fadi kawai kinsa baze gagara ba".
" Inason mu sanyawa Ridwan maganin da ze sanya ya fita hayyacinsa na tsawon awa biyu ko uku , amma acikin abincinsa". Ta karasa zancen cikin bukatuwa.
Mamy cike da faduwar gaba ta ce " ai Ridwan kwata kwata tunda yayi wayau baya cin abincin Gidan nan , kuma ko da yana ci taya zan amince a sumar min da yaro har tsawon wannan lokutan , kinsan bazan yarda ba gaskiya , Malamin naki besan aiki ba ". Cewar mamy cikin takaici.
Madina kuwa ranta ya soma baci , cikin fushi ta dau jakarta dake kan Centre table tana fadin " ai ke ce kika ce bakya son ya yi aure yanzu kuma ɗan ana neman hanyar da baze taba sha'awar yi ba kinzo kina fadamin maganganu , wannan ba komai kike min ba illah gorin haihuwa , ai na dauka Ridwan ni ma dana ne zamu iya cika burinki ashe kallon muguwa kike min , bayan ke ce kika bukaci hakan ". Ta kai karshen zancen tare da kama hanyar fita daga kayataccen falon , ahanzarce Mamy ta bita cikin damuwa ta fara bata hakuri , tare da tabbatar mata Ridwan baya cin abincin Gidan , da wannan bayanan ne 🔥ta sauko tare da cin alwashin kullum zata ringa zuwa sanya masa magani na kwana bakwai daga nan shi ke nan babu shi babu Aure sai dai a lahira. Mamy taji dadin hakan daga gare ta inda suka dawo falon tare da ci gaba da tattaunawa.
Cotonou
Ranar Alhamis
Yasmin tsaf ta gama harhada kayayyakinsu domin zama acikin shirin ko ta kwana , Fauziyya da Safiyya da Firdaus ko wannen su ya zabga uban tagumi , cikin karfin hali Fauziyya ta fesar da numfashi cike da bakin ciki ta ce" ai yaran Alkali sune suke kawo sammaci daga kotu ya akayi Dsp ne ya kawo bayan ba huruminsa bane ?". Tayi tambaya cikin tsananin bacin rai.
" Ai abu in akace babu Allah aciki ko meye ai zaka gani , sun wakilci yaron Alkalin ne dan su zo su ganewa idanunsu ya muke ciki ". Cewar Safiyya tana hura .
" Ni fa tunda abun yakai ga haka wallahi banki inci Uban Alhaji Isah ba , haba ! ga abun magana ace ba zamuyi ba , kuma wallahi ko da bashi ne sai mun harhada mun dauki lauya mu ma ". Cewar Firdaus cikin fada.
Fauziyya ta amshi zancen da fadin " ai dole mu dau lauya , in ba haka ba cutar zata yi yawa kusan shekara goma be tare da Mamy shi be sake ta kuma yana kiran mu shegu ze fada mana ta inda aka same mu ". tayi magana cikin fusata .
Duk hirar da suke Mamy da Kakarsu Mariya suna jin su babu wanda ya tanka musu domin , su kansu kukan zuci suke daga zaunen.
Yasmin da yanzu taga zata iya tofa bakinta cikin maganar cikin muryan kuka ta ce " wallahi ankara kawo mana wani takardan sammaci daga yaron Alkali cewar sa ranar monday za'a fara zaman kotu ". Ta kai karshen zancen a raunace.
Gabakidaya zazzare idanu suka yi har da kaka Mariya , cikin kuka kaka Mariya ta ce " Ni na dauki cikin Isah har tsawon wata tara da kwana tara , na shayar dashi , na ci kashin sa da fitsarinsa , in har ina hakkin akansa ya zama dole na masa baki ". Juya kwayar idanunta tayi zuwa sama alamun za tayi mummunar furuci akansa. Taci gaba da fadin " Isah kamar yanda kasani kuka kasa iyalinka da yayayenka kuka ya Allah ya .......". Cikin sauri Mamy tasa tafin hannunta ta rufe mata baki , cikin kuka take girgiza kai baki na rawa ta ce" karki tsine masa wallahi ze kara lalacewa , wallahi inason Isah , kuma nasan kinfini sonsa , sai de ni dake mun tsani halayayyensa , Isah mutum ne da nasani mai tausayi da jinkai , nayi imani inhar Isah na ne wallahi ko da yaran nan nazo Gidan nan ze rike min su , amma shedan ya masa kidan ganga baya ji baya gani". ta karshen cikin kuka .
Kaka Mariya kuka take harda shidewa , murya na rawa ta ce " A'isha ki barshi ya kara lalacewa kuma ni Mariya na ce Isah sai kagani". Takai karshen zancen a raunace tana jin komi zata iya masa.
dan kullum da bakin ciki suke kwana suke tashi.
Shigowar me Gadi da waya ne da sallama a bakinsa yasa sunyi shiru , tare da basa amsa cikin kasa da murya , tashi Yasmin tayi dan amsar waya daga hannunsa , dan tasan be wuce Umar ne ke kira , tana karba cikin hanzari ta bawa Mamy wayar tare da gayamata me kiran nata.
Murya a raunace Mamy ta fashe da kuka yayin da takai wayar saitin kunnenta domin bawa Umar labarin halin da ake ciki domin yanzu tafi buƙatar ganin ya dawo gida.
Cen Ɓangaren Basma.
Zaune take bakin gadonta Alhaji Isah na gefen ta yana harhada wasu takardun aikinsa , cikin fara da sakin fuska ya ce " Basma ga wannan takardan na baki mallakar gidana dake unguwar *Gbegamey* dan nasan yanda kike son gidan nan ". Ya yi furuci cike da begenta.
Cike da tsananin jin dadi ta ce " tu es sûr ? ma'ana ka tabbatar , ya bata amsa da " oui ma chérie". Ma'ana kwarai kuwa masoyiyata .cikin jin dadi ta kai masa kiss a goshi , sannan cikin iya bariki ta ce " kai de dan Albarka ne wallahi ga shi Allah na fiddaka tsakiyan makiya , kuma ranar monday hummm A'isha zata gane illah cin amanar miji". Takai karshen zancen cikin yatsine fuska.
Kallonta yake kamar me nazarinta , sannan ya yi dan jim kamar yana son fadin wani abu ko tuno da wani abu da yake ta mancewa tsawon rayuwarsa , hakanan ya ji be ji dadin furucinta ba , a fili kuma ya ce " Hummm kedai Allah yakaimu kowa ma ya huta. Dan ni da A'isha kotu ce zata raba.
Cikin yauki ta kara narkewa jikinsa har takardunsa suka fadi kasa reras , idanunta masu wutar fitina ta sauke cikin nasa suna kallon juna , murya cike da shagwaba ta ce " wai yaushe zaka saki A'isha ne , naga babu Aure tsakanin nagari da mugu da". Tayi furucin tana cunno baki gaba.
Bakin nata yake bi da kallo , nan da nan yaji kalmar sakin ta soke shi har kasar zuciyarsa , ta maza ya yi tare da fadin " Basma bana son firan A'ishah pls maganar saki a barta sai nan gaba , zan mata har saki uku". Ya karashe zancen yana juyayin kalamanta.
Ita kuwa ranta babu dadi amma kuma ta dau alwashin nan gaba shine ze zo mata da maganar ya saki A'isha ta karashe tunaninta tana yar dariya.
Gwarinfa
Kashe gari Ranar Juma'a.
Da sanyi safiya Amatullah ta fito daga dakinta , tana sanye cikin sabuwar dinkinta doguwar riga atamfa da ya zauna mata daram ajikinta har shap dinta da hip dinta duk suka bayyana , sosai dinkin ya mata kyau wanda ya kara maida babban yarinya , Hasina ta dinka mata bisa ga umarnin karfin Iko . Cikin gidan har teloli gare su da kasuwa masu siyar da kayan miya, su atamfa leshi , harda gareji akwai cikin gidan , sauran kuwa ba'a cewa komi.
Yau ne karo na farko da Amatullah ta sanya kafafunta a farfajiyar Gidan , cikin zallan mamaki take kallon yanda gidan yake ci kamar kasuwa , kuma sam babu hayaniya kowa harkan gabansa yake , sautin zazzakar murya anan karatun Alkur'ani mai girma , ta ji daga dayan bangare na Gidan , hakan ya sanya ta fara bin inda take jiyo karatun ahankali tana tafiya bakinta na dan motsawa kamar duk abinda yake karantowa ita ma tana maimaita shi abakinta. Sai da ta iso gab da madaidacin massalaci me kyaun haduwa da tsaruwa cikin zallan mamaki ta ce " massalaci acikin gida ? ganin babu me bata amsa yasa ta yin shiru , barin wannan tunanin tayi ta fara ci gaba da tafiya , har ta iso inda karantun ke tashi , jin muryan dalibai yan amshi na tashi , kusantowarta wurin yana dai-dai da tsananta bugawar zuciyarta , ahankali ta matso kofar massalacin tare da da lekawa domin ganin abinda ake . Zararan idanunn ta ware akan fari kyakkyawan dattijo da ya tankwashe kafafunsa yana sanye cikin farar jallabiya fuskarsa dauke da gilashi , cikin kaduwa da al'ajab take masa kallon kamar ta taɓa ganin fuskar sa , muryan dalibai ne daga ciki ya katse mata tunani tana jin daga ciki wata daliba tana fadin " Malam ya hukuncin wanda ya labe yana gulma bayan ba'a san da zamansa a wurin ba , ina nufin yana son yaji kwaf". ta yi tambaya yanda kasan sako ta aikawa Amatullah.
Amatullah zazzare idanu tayi tana nazarin wannan tambayar anya be da hadi da ita kuwa ? , wata zuciyar ta raya mata ai karatunsu suke basu san da zamanki ba , fesar da numfashi ta yi tare da yunkurin komawa cikin gidan , muryan Malam ne ya dakatar da ita , jin yana fadin " gulma ba shi da kyau da yawan gulmace gulmace ake koyon munafunci , sannan akwai gulma mai fa'ida irin mutum yazo wuce wa yaga ana karatu sai ya tsaya dan ya saurara domin ya amfana , na shi akwai lada kam awajen Ubangiji ' wallahu Ahlam". Ya bada amsa yana mai cigaba da karatunsa.
Sanyayar ajiyar zuciya Amatullah ta sauke jin amsar da ya bayar.
Tana ganin ana kokarin tashi ne yasa ta fara yunkurin barin wurin har ta karya kwana zata fice , taji sautin muryan Malam daga sama yana fadin " dakata ". Ya yi furucin yana mai kusanto inda take cikin kasaita da kamalarsa , innalilahi wa'inna ilairajun ". Ya shiga maimaita da bakinsa , kana cikin rawar murya ya ce.......
Makauniyar Shari'a taku ce
Comment and share
[10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: _Makauniyar Shari'a_
_Sai a Lahira_
Na
*IKILIMA ADAM*
_(Kyauta daga Allah)_
*** whsap
SHAFI NA SHA BIYAR
Kana cikin rawar murya ya ce dakata Baiwar Allah ". Furucinsa ya yi dai-dai da tsayuwarta. Karasowa gab da ita ya yi yana kokarin ganin ta juyo dan babu abinda yake bukata sama da yaga fuskarta.
Ita kuwa daga tsayen take ji wani irin faduwar gaba mai karfi , a hankali ta juyo domin ganin wanda ya tsayar da ita , kwalalo idanu tayi ganin Malam ne wanda ta gani yana koyar da karatu , cikin rudewa take kallon kyakkyawan dattijon fari sol wanda yake nuni da a kuruciyarsa ya yi tashen kyau , bangare daya na zuciyarta tana hasaso mata kamanninsa kamar ta taɓa ganinsa ko a hoto ko kuma a mafarkinta.
Malam ganin ta tsura masa idanu ta shiga duniyar tunani ne yasa shi katsee mata hanzari ta hanyar fadin.
" Yan mata ya sunanki? Kuma tun yaushe kike Gidan nan , meyasa kika labe kina jin karatu bayan kinada damar shigowa daga ciki ". Ya kai karshen zancen yana jin zuciyarsa na tsinkewa abun da yake son tabbatarwa ya gani da idanunsa , hawaye ne suka samun daman cika a idanunsa , cikin hanzari ya sa tissu ya dan goge hawayen ba tare da ya bari Amatullah ta fahimci halin da yake ciki ba.
Rau rau da idanu take kallon sa rasa amsar da zata basa yasa ta fadin " Ayi hakuri Malam daga yanzu zan fara zuwa karatu dan banyi nisa sosai ba ". Ta karshe zancen cikin cool voice dinta.
Shi kuwa sosai ya shagala da kallonta cikin boye abinda ke kasar zuciyarsa ya ce " baki fadamin sunanki ba".
" Suna na Amatullah amma ainahin sunana Faridat , yan kauye na kirana da yar wahala". Ta karashe zancen cikin tsantsar kuruciya.
" Innalilahi wa'inna ilairajun ". Malam ya shiga maimaitawa ba kakkautawa hakan yasa Amatullah , dan tsoracewa har ta fara tunanin ko duka ze mata ne , ahanzarce tabar wurin ta shige sashin su , ta bar shi anan tsaye.
Shi kuwa yana ganin ta fice ya lallaba ya samu wuri daga nan gefe dakali ya zauna babu abinda kwanyar kansa ke juyawa sai kalaman Amatullah .
Amatullah tana karasawa daga cikin falon , cikin rudewa taga Ƙarfin Iko zaune akan kujerar falo ya daura kafafunsa daya kan daya yana kallon tashar *Tauraruwa* in da ake sanarwa da neman agaji akan wani yaron kauyen wanda rai yake hannun Allah , sakamakon bugawar da yan daba suka masa . Amatullah cikin sanda sanda ta karaso falon murya na ta rintsina gabansa.
Ina wuni! Abba ". Tayi furucin idanunta na kan TV da yake kallo ba tare da ta jira amsar sa ta tashi tsaye cikin kidima take kallon Salim a cikin TV shida iyayensa yanda suke kuka suna neman taimako Naira miliyan Biyar domin fitar da salim kasar waje . Cikin gigicewa da fitar hayyaci ta ce " innalilahi wa'inna ilairajun Salim dinannnn". Yanda tayi furucinne yasa karfin iko dawo da kallonsa akanta cikin zallan kaduwa da kalamanta.
Duka hanayyenta ta daura akai yayin da take kallon Salim a cikin TV yanda ya rame ya kare baka ganin komai nasa sai kasusuwa ma'ana ya koma kamar skeleto. Cigaba da jero salati take tana kuka kasa kasa idanunta cike da hawaye masu dumi . Kokarin barin falon take izuwa dakinta , taji daga cikin TV ana fadin dan Allah ataimaka ma wannan yaron dan rayuwarsa tana cikin hatsari , ga Mai buƙatar taimaka masa yazo Asibitin Aminu Kano". Tana jin karshen zancen ta fara sauri sauri wajen yin sashinta. Azafafe taji ƙarfin iko ya rike hannunta wanda yayi sanadiyar juyowarta ba shiri , yanda ya rike hannun nata take kallo da kuma yanda ya tsareta da idanunsa masu kwarjini. Dago kai tayi tana kallonsa , cikin sassaita nutsuwa ta ce " ka sake min hannuna wlh rikon da kamin akwai zafi". Ta magana cikin sanyin murya ..
Kyawawa fuskarta yake karewa kallo na tsanaki , kana cikin damuwa kasar zuciyar , saman fuskar ba yabo ba fallasa ya ce " waye salim? meye alakarku kuma meyasa kike masa kuka , meyasa zaki ambaci Salim dinki a gabana , Amatullah kinsan me kike fadi kuwa ayanzu fa kin kama hanyar zama budurwa kuma wanda ze aureki kike yabon wani agabansa". Ya karashe zancen yana hura kofar hancinsa.
Ita kuwa hannayen da yasa ki take kallon yanda yayi ja , bata kara yarda sun hada idanu ba kanta a kasa ta ce " Salim yace inna girma ze zauna damu ya gina min gida ni da papy". Tana kai karshen wannan zancen Ƙarfin Iko rintse idanunsa ya yi da karfi domin sosai yaji tsananin kishinsa ya motsa.
Taci gaba da fadin " shine wanda ya taimaka muna Lokacin da aka nemi aka kashemu , dole nayi kuka domin ina tabbacin wannan halin da yake ciki saboda mu ne , kuma bakina ni da papy baze iya fadin Alkhairan da Salim ya mana , dole nayi kuka yana cikin wani hali banda ikon taimaka masa ". Ta karashe zancen tana mai jin tsayuwar ta isheta.
" Zan bada millon goma a masa magani , ki saurareni zuwa gobe , amma a daren yau zan kawo kudin su kwana adakin ki ". Ya yi furucin yana mai jin tsananin kishinta, amma kuma yana son taimakawa Salim kodan ya faranta mata rai.
Amatullah bata tsorata jin ze bada kudin ba dan tasan yana kudin da basuda iyaka yanda ta samu labari gun Hasina , murmushi mai sanyi tayi wanda yakara bayyana zallan kyawunta , cikin jin dadi ta fara masa godiya shi kam hakan da ya ganta ba karamin sanyasa cikin nishadi ya yi ba.
Bayan magrib
Amatullah zaune a tsakiyar dakinta muraja'a takeyi na karatun da Papy yake koyar da ita na surori.
Shigowar Hasina hannunta dauke da jaka ne yasa ta kai dubanta akanta tana sanye cikin doguwar riga mai tsantsi baki tare da bakin hula akanta , cikin jin dadi takai ayar karatun ta tare da mata sannu da zuwa cikin fara'a. Hasina ta ce .
" Amatullah yar gatan Haruna karatu ake ?".
"Eh karatu nake , kuma nakai aya". Cewar Amatullah.
" Ma sha Allah , Allah ya bada lada " .
" Ameen Nagode sosai". Fuska dauke da yalwatccen murmushi.
Numfashi Hasina ta fesar tana karewa Amatullah kallo na musamman kana cikin muryanta ta dabi'a ce ta ce " muga kitson da Nana ta miki , sannan ga sako Haruna yace in kawo miki zakuyi Magana". Ta karashe zancen tana mai kallon kitson kan Amatullah data bude mata cikin hanzari ta furta.
"Ma sha Allah".
" Nagode kwarai ". Takai karshen zancen tana mai amsar jakar daga hannun ta .
Sun shagala suna hira tsakaninsu wanda har yasa Amatullah darawa dan sosai Hasina ke ɗebe mata kewar Papy .
.................................
Umar Faruk bakin sa na rawa yaje gun mai gidansa tare da fada masa buƙatarsa na son tafiya garinsu , Alhajin ya tausaya masa matuka hakan yasa ya ba shi kudin mota tare da fadin " in komai ya daidaita dan Allah ya dawo ze kama masa aiki a kamfaninsa. Sosai Umar yaji dadin hakan ya kuma masa godiya tare da zama a cikin shirin gobe asabar ze bar garin ..
_______________________
Ridwan sosai yake shiri bayan Sallah isha'i yanda kasan ze je wurin shakatawa , wandon treequater ya sanya tare da brown din rigarsa cotton , mai daukar idanu , anutse tattare da kamalarsa ya gama shirinsa tsaf , gaban mirror yaje yana taje kansa kana cikin hanzarinsa ya fesa turaruka masu kamshi ajikinsa ta cikin madubi yake kallon kansa shi kansa yasan yayi kyau , jin wayarsa na rîng ne yasa shi hanzarta sanya flat din takalminsa hade da fita domin yasan be wuce Mansur ne ...
Cikin sassarfa yake taka matakalan step din , wanda ya jawo hankalin dukan kannensa da suke falon kallon sa , yana saukowa ya yi dai-dai da fitowar Mamy ita da Madina da idanu suke binsa ganin yana gaisawa da kannensa, kana ya tsaya su na dan taba hira da kaninsa Faisal tare da fada masa ya shirya gobe tare da zasu fara fita aiki. Kannensa mata kuwa bayan gaisuwa be kara ce dasu komai ba . Kokarin ficewa yake daga falon ya ji murya Madina tana fadin " Haba Ridwan baka ganmu bane". Cak ya tsaya ba tare da ya waigo ba , cikin kasa da murya ya ce sannunku da fitowa iyayena ". Tare da fara yunkurin fita falon.
Murya Madina yaji again tana fadin " naga kamar sauri kake dan Allah ka saukeni gida , motata ta lalace". Tayi magana cikin jiran amsa.
Cak ya tsaya yana nazarin kalamanta kana cikin muryansa ta dabi'a ya ce " zan baki kudin Napep zan baiwa me Gadi ya baki , dan ba hanyarmu daya ba". Yana kai karshen zancen ya fice daga falon.
Da idanu suke bin keyarsa da kallo daga su har kannensa , Faisal ne yayi murmushi domin ba karamin burgesa takun Ridwan yake ba.
Madina rike da baki suke kallon juna da Mamy , kana cikin hanzarinta ta ce " Mamy bari nabi sahunsa nasan ma ze saukeni". Tayi furucin tare da fita ba tare da ta jira amsa ba.
Su Anisa me zasuyi in ba dariya ba , ita kuwa Mamy ta fara tsorata da Lamarin Madina akan Ridwan kasa magana tayi hakan yasa ta samu wuri ta zauna cikin ya'yanta.
Madina tana karasowa ya yi daidai da kunna wutar motarsa ze fice daga Gidan , hannun da take masa ne ya bashi damar danna madanni sauke gilashin motar , kana ya dawo da kallonsa akan ta jin tana fadin " Dan Allah Ridwan ka sauke ni diyar antina ce ba lafiya kafin na samu napep da aiki ". Ta karashe zancen cikin magiya ".
Kallonta yake tuno da ai ita ma kamar Uwarsa take hakan yasa ya ce " to shiga kofar baya ".
" Haba dana kai ba drever ba gwamma in zauna gaban zefi ". Ba ta jira cewarsa ta shige ta gaban motar , tare da cika kujerar da manyan mazaunata.
.
Yakai mintuna biyu be tada motar ba lissafi da nazarin matar yake , barin wannan tunanin ya yi tare da tada motarsa , daman yasan Gidanta a lugwai yake hakan yasa be tambaye ta kai tsaye ya fita da hancin motar daga cikin gidan.
Sun sha tafiya da yakai akalla minti ashirin , wayarsa ta hau ruri yana dubawa yaga Mansur ne daga wayar ya yi yana mai cigaba da tukinsa cikin kasa da murya ya ce" Mansur ina hanya zan ajiye Mamata Madina Gida ne , ka jirani ina nan zuwa kace wa Mama pls aidole inzo cin abinci". Ya karashe zancen tare da katse wayar.
Madina sosai ranta ya bace jin ya ce mata Mama , cikin boye damuwar ta kakalo murmushin dole tare da fadin " wai kai yaushe zaka yi Aure ne Ridwan?". Tayi magana domin tasan amsarsa be wuce baya son jin zancen aure kamar yanda ya saba.
Cikin tsantsan mamaki da rudewar tunani a bazata ta ji ya furta .
" Ai na kusa Aure kwanan nan , baki ga na fara gyaran dayan sashin cikin gidanmu ba to anan zata zauna Amarya". Yayi furucinsa cikin tabbatarwa.
Zazzare idanu Madina tayi kokarin yin magana take , taji yana fadin " mun fa iso". Yayi furucin yana mai nuna mata da jiransa ake .
Jiki a sanyaye ta sauka tare da rufo kofar, muryanta na rawa ta ce " Rid Nagode Allah ya maka Albarka ".
Be bata amsa da Ameen ba sai dai yabita da kalmar sai anjima. Daga haka yafice daga unguwar.
Ita kuwa cikin hanzarinta ta karasa gida tana mai jin takaicin tambayar da ta masa tana kuma rantsewa da buwayar Ubangiji sai ta Auri Ridwan ko ana ha maza Ha Mata.
Rid mintina sha biyar ya dauka kafin ya isa Unguwar su Mansur , me Gadi na ganin motarsa ahanzarce ya wangale masa babban gate din Gidan.
Cusa hancin motar yayi yana mai daga mai Gadi hannu , tare da zarcewa farfajiyar Gidan.
Parking space ya ajiye motar , fitarsa daga motar ya yi dai-dai da karasowar Mansur shi ma irin shigar Ridwan din ya yi komi irin daya , murmushi kwance a fuskokinsu suka kama hannayen juna , bakin Mansur na rawa ya ce " kai Abokina har gida kaje kai kawar Mamarka ka barni da jiranka gashi ina jin yunwa".
" Wallahi matar ce ta cika naci ".
" To ai ita ma Mamarka ce dole tayi iko dakai ".
" Hummm ni karshe ma saida tasa na fadi abinda bashi ne ba" .
" Ahaf kace kayi kwaba tunda kasan karya ba dabi'arka bace Lallai ka tabbatar kayi abinda ka fada mata ". Ya karashe zancen suna mai karasowa falon kusan a tare.
Suna isa falon ya yi tozali da Mansura dake sanye cikin doguwar riga atamfa ba karamin kyau tayi da shigarba.
Cikin sakin fuska da walwala take fadin " oyoyo yaya Ridwan har ka iso". Furucinta ya yi dai-dai da fitowar Mama cikin riga da zani atamfa Mai kalan ruwan kasa .
Ita ma da murmushi take fadin .
" Lale marhaba da Dana ". Murmushi ya sakar musu dukansu yana mai cigaba da tafiya izuwa kayataccen falon , cike da ban girma ya gaishe da Mama kana cikin dan sakin fuska yake amsa gaisuwar Mansura.
Bayan taba yar hira da Mama ne yake fada mata Aure zeyi cikin satin nan kuma sha'awar yin Aure ya zo masa ne a daren .".
Mansura dake kokarin shan lemun acikin kofin glass ba tare da ta ankare ba ta saki glass din ya fadi saman tayis jika kake ..............
Makauniyar Shari'a taku ce
Share and comment pls