Free chapter · Read without an account

Chapter 21 , 22 , 23

by Ikilima Adam · Makauniyar sharia

[10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: Makauniyar Shari'a


_Sai a Lahira_




NA


*IKILIMA ADAM*


_(Kyauta daga Allah)_

_***_



_Jarumait writ associations_




SHAFI NA ASHIRIN DA DAYA




Cikin gigita da fitar hayyaci ta fara ihuuu tana zabga salati , hannayenta na rawa kamar ana kadata da ganga , wani irin kyaikyayin azaba ta fara ji dukan sassan jikinta , cikin azaba take kallon Mamy da ta tashi zaune tana salati , Fauziyya bakinta na rawa ta ce .


" Mamy wayyo azaba zan mutu , Mamy ki agazan ". Waiwaya tayi wajen Firdaus da su kayi caa akanta suna zabga salati ganin yanda jikinta nan da nan ya fara canza halitta , hatta fuskarta wasu kuraje kamar marurai suka cikasu har wani jini jini suke yi . Safiyya banda" Innalilahi" ba abunda take maimaitawa , kana cikin rawar murya da kadawar harshe ta ce .


" Wallahi Tallahi idan na amince da cutar Fauziyya shegiya nake , haba wannan abun da take sai kace sammu aka mata , wallahi idan na yarda ba Mamy ta haifan sai na ci kutumar bura uban duk wanda yake son gigita min yar uwata ". Ta karashe zancen agigice hannunta na kan Fauziyya dake ihunn neman agaji. Firdaus gabakidaya kanta ya kulle ta rasa wannan wani irin iftila'i ne suke fuskanta daga wannan sai wannan , fuskar babu digon rahma takai hannunnta kan Fauziyya dake kururuwa , ganin Mamy na hawaye bibbiyu daga zaune , ba karamin shiga tashin hankali suka kara yi , a kidime Firdaus ta dau waya domin kiran Jibrin .


Bangaren Jibrin yana zaune a office dinsa shida abokan sai hirar Shari'a da akayi a kotu suke , cikin yakini yake jaddada in sha Allah sai ya taimaki Mamy , dan zaluncin ya yi yawa , karar wayarsa ce tasa shi ɗan murmusa ganin kiran Firdaus ya san Fauziyya ce ke son magana dashi hakan yasa ya amsa kiran fuskarsa dauke da annuri , soma zazzare idanu ya yi jin kururuwar Fauziyya ta cikin waya yana jin muryan Yasmin cikin kuka tana fadin " anti Fauzy kiyi hakuri , wlh bamu san maganin da zamu baki ba ki samu sassauci ba ".


Zumbur Jibrin ya mike tsaye yana zagba salati , kasa tsayawa ya yi ya saurari maganar da Firdaus take masa , abokansa ne suka yi caa akansa sai tambaya suke "lafiya kuwa" ? be basu amsa ba illah cigaba da zagba salati, zufa na keto masa a fuska , bakinsa na rawa dakyar ya iya furta " Fauzy na jama'a ku taimakeni dan Allah karta mutu , wlh zan mutu inna rasa Fauzy". Ya karashe zancen a dimauce.


Abokansa duk sun gigice su kansu basu san me yake faruwa ba , amma sun tabbatar ba ƙaramin Matsala bane , gani suka kayi ya saka wayoyinsa a aljihun wandonsa , ji yake kamar sam baya sauri hakan yasa be tsaya ko sauraren abokansa ba , ya ja mashin dinsa aguje yabar office din ko tsayawa rufewa beyi ba . Abokansa kam suna ta sakawa da kwance daga hakan suka fara fatan Allah yakawo sauki.


Cen Bangaren Basma duk abinda yake faruwa suna kallo ita da Bokan nata , ba karamin dadi ne ya lullubeta ba , cikin shauki ta ce " Boka wannan Yarinyar anya cutar nan bazeyi ajalinta ba ?".


Murmushi keta Boka ya yi tare da fadin " ko dai kina son a kasheta ne ? ". ya karashe zancen cikin son jin amsa.


Guntun murmushi tayi tana taunan cingam da ta sanya a baki , tare da fadin .


"Ni in har zata mutu zan fi kowa farin ciki , na tsani yarinyar nan wlh , saboda tana kama da munafukar uwar mijina , ni in har zeyu a fara kasheta wlh". ta karashe zancen cikin tsanani bukatuwa.


Boka dan jim ya yi alamun tunani kafin ya kara kai dubansa akanta , dauke idanunsa akanta ya yi yana mai ci-gaba da kallon kwaryan dake gabansa , kana ya kara kallonta a karo na biyu , cikin sassaita nutsuwa ya ce .


" Ba zeyu mu kasheta ba , saboda Uban Mijinta gangarumin malami ne , yana gani kamar hanji , in har ze san kasheta akayi to tabbas ze dawo da aikinmu akaina ko akanki ko akan yayanki ". ya karshe zancen cikin tabbaci .


Ya kara da fadin " Zaman kotu da za'a koma baze masu kyau ba , hatta alkalin mun fara aiki akansa , ita kanta Hadiza Ibrahim zamu sanya mata cutar mantuwa , kwata kwata zata manta da wannan case din , ko binciken ba zata samu damar yi ba , bare har ta tuna zuwa kotun ". Ya idasa zancen yana bushewa da dariya mai tsoratarwa.


Basma kwalalo idanu tayi a waje tana mai rike bakinta , murya na rawa ta ce " A'a in har sai abun ya dawo kanmu a kyaleta da ranta a iya hakan ma ai gwamma mutuwarta , kokan Surukin nata ya gane meke damunta ai tasha jiki , gaskiya Barister Hadiza zata gane kurenta shegiya mai farar kafa , malam zan tafi kar yaga na dade ban dawo ba ". tana kai ayar zancen nata ta mike cikin dan saurinta.



************


Jibrin na isa kokarin shiga daga cikin Gidan yake ya ci karo da Alhaji Isah Sharifai yana kokarin shiga motarsa a harabar Gidan , kallon kallo sukewa juna , kana Jibrin ya yi karfin halin fadin " Ina wuni " be damu da jiran amsa daga bakinsa ba , in da sabo har ya saba .


Alhaji Isah kauda kai gefe ya yi kamar be ji gaisuwar ba , hanzarta shiga motarsa ya yi , kokarin tada motar yake ya ji sautin ihuu Fauziyya ya karade kunnennsa wanda ya sa cak ya tsaya be tada motar ba , a kidime ya furta "Fauziyyata". kana ya saka dukan hannayensa kan sitiyarin motar yana sauraren kururuwan dake cika dodon kunnensa , nan da nan ya shiga tariyo shekarun baya duk sanda beda lafiya Fauziyya ce take dawainiya da shi bata iya barci inhar yana cikin tsananin rashin lafiya , ita ce mai zuwa yin wankau dan ta samo kudin da za'a sai masa magani ko zuwa asibiti , nan da nan ya fara tariyo lokacin haihuwarta da yanda ya haifeta babu kudi ko ragon suna be yanka mata saida ta shekara bakwai , da wayonta ta ci naman sunan haihuwarta . " innalilahi wa'inna ilairajun' ya shiga maimaitawa jin cikin kururuwar da fauzy keyi tana fadin.


" Ya Allah !! Ka taimakeni ya Allah !! Ya Allah ka shiga lamarina ya Allah !! ".


Muryan Jibrin ya ji yana Faɗin " Fauzy nine Jibrin dinki ki tsaya ki mun bayani mana , gayamin ina ke miki ciwo ya Fauziyyata ".


Yanda yake jiyo muryan Jibrin cikin fitar hayyaci yasa shi bude motarsa ya fito zumbur , hanzarta rufe motarsa ya yi ya kama hanyar da ze sada shi da sashin su Mamy , dai-dai lokaci Motar Basma ya kunno kai Gidan , me Gadi na wangale mata babban get babu bata lokaci ta shigo harabar gidan , cikin tashin hankali take kallon Isah ya bi sashin Mamy , ko tsayawa daidaita parking din motarta ba tayi ba ta bi sahunsa a guje sai kiran sunansa take tana fadin .


" Isah!! " amma ina sam be san tana yi ba , hankalinta a tashe ta fara gudu _gudu sauri sauri har ta kusa cimma masa , cikin rawar murya ta ce.


" Is..a...h ". ta karashe cikin daga murya , sautin muryanta har cikin dakin Mamy , daga Mamy har yayanta da surukinta kowannensu mamaki ne ya cika su jin muryan Basma a sashin su.


****


Isah kuwa , cak ya tsaya yana kallonta tana karasowa hannunsa na kan handle Kofar , tana karasowa bakin ta na rawa ta ce ..........



Ayi hkr dakyar nayi editin banjin dadi ina barar addu'a.




Makauniyar Shari'a


_Sai a Lahira_




NA


*IKILIMA ADAM*

_(Kyauta daga Allah)_

_***_


_Jarumai writ association_



_SHAFI NA ASHIRIN DA BIYU_


_Saura page uku in gama free page , wa'yanda basu payment ba ku hanzarta kada ayi babu ku



Tana karasowa bakinta na rawa ta ce.


" Kayi batar hanya ne ?".


Hada rai ya yi cikin hanzari ya ce " kamarya kenan? ".


Wani irin tsorone ya shige Basma lokaci daya , cikin aro jarumta ta ce .


" karka je dakin nan yanzu haka wani sabon makirci ne ake shirya maka" ta karashe zancen tana kallon reaction dinsa.


Kallonta yake kamar me nazartan wasu abubuwan, kana ya sauke nauyayyan ajiyar zuciya mai zafi , karamin macijin tun daga nesa yake tahowa cikin sauri sauri gudu gudu , kamar walkiya ya shige cikin babban yatsarsa na kafarsa na dama , wanda nan take Alhaji Isah ya dafe kansa , yanda macijin ke bin sansan jikinsa haka yake jin yanayinsa na sauyawa , saida macijin yazo kwanyar kansa ya kara yabi ta hancinsa , kana ya samu mazauni akan harshensa , cikin tafasar zuciya Isah Sharifai ke kallon Basma da duk ta tsorace da lamarinsa .


Jin ya kamo hannunta yasa ta kallonsa kamar wata tabbabiya sake da baki .


" Alhaji daman nazo in hanaka fadawa ga ha.....".


" Shiiihhh " Alhaji Isah ya mata tare da hanata karasa abinda take shirin fadi , kama hannayenta ya yi cikin ban hakuri ya ce" Basma bansan ma nazo ba , kiyi hakuri my baby " ya karashe zancen cikin kashe murya .


Basma kuwa sauke ajiyar zuciya mai sanyi take yi akai akai domin ta tabbarar macijin ya shigo jikinsa.


Cen Cikin dakin kuwa duk hirar da Basma da Isah suka yi duk akan kunnensu , Allah yakyauta suka furta tare da dawowa kusa da Fauziyya da barci barawo ya yi awon gaba da ita.


Jibrin fifita yakewa Fauzy cike da kulawa , sai fadi yake.


" Wannan lalurar Fauzy bata asibiti bace , zan kawo Abbana yanzu ya dubata ze iya gane me yake damunta " ya yi furuci cike da kulawa.

Mamy girgiza kai kawai take ita kaɗai ta san halin da take ciki.

Cikin karfin hali ta ce.


" Jibrin Alhaji yasaka maka da Alkhairi , samun irinka babban saa ce arayuwa " karashe zancen tayi cikin sanyin murya.

Da" Ameen " suka amsa dukansu dakin .



*****************



Bayan kwana biyu


Tun bayan sallah asubahi Ridwan be koma ya kwanta ba , safa da marwa yake ta yi cikin dakinsa , sakawa da kwancewa yake ya rasa ta inda ze kamo bakin zaren abinda ke damunsa , samun damar makalewa jikin bangon dakinsa ya yi yana tuno abinda ya faru shekarun baya , dode kunnuwansa ya yi sakamakon jin kamar harbin bindiga yake ji anayi agabansa , duk da shi ɗan sanda ne amma wancen harbi da yake jin sautinsa na rikirkita tunaninsa yana nuni da alokacin shi ba dan sanda bane yana nuni kamar bakon abu ne a wajensa a wannan time din , jujjuya kansa yake yana ganin kamar abinda ya faru shekarun baya sune yake faruwa yanzu haka reality agabansa .


Cikin fitar hayyaci da tsoro yake fadin " Abba an kasheka ko? Abba ka bude idanunka , Abba ni ne Ridwan dinka , ga Faisal dinka cen yana barci ". Azauce yake sassaka kalamansa, wanda ya ja hankulan gabakidaya all din yan Gidan har ma da ma'aikatansa da masu aikin gidan.


Mamy da sautin maganganun sa ya fito da ita dakinta , tana fitowa taci karo da Anisa da Amina , sun fito daga dakunan su , Faisal da dukan alamu daga barci ya tashi dan idanunsa na dishi dishi , cikin hanzari suka haura sama domin zuwa ganewa idanunsu.


Me aikin Gidan wacce suke kira da Dumbaru yar matashiya ce kalarta kalan Dumbaru na industry yarinya ce wacce bazata haura shekaru Ashirin da biyar ba . Salati take yi da dogon bakin nata tare da fadin.


" oh Shugaba Ridwan lafiya yake surutai , shi dai kullun duk yanda nake ado dan in burgeshi sam baya kallona, anya yana da idanu kuwa , yanzu ma fa nasaka doguwar riga wanda ta matseni. ,karshenta yana fitowa ya watsa min harara tunda shi be san abun arziki ba , bari dai in bi bayansu dan in ji me ke faruwa da Honey na ". ta karashe zancen cikin dan sauri saurinta tana tafiya tana kwarkwasa.



Cen Cikin Dakin Mamy sosai ta rikice dan jin yanda yake kalamai daga bakinsa , Mamy na kokarin dafa shi ahanzarce ya bude idanunsa da suka kada jajir, hannu ya mata alamun kar ta kuskura ta taba shi . Cak ta tsaya tana kallon Anisa da Amina dake suke taba shi be ce komi ba , Faisal ma hannunsa ya rike shi ma be ce komi ba , sai ita ce ze hana ta taba shi , take tambayar kanta yanzu fa Ridwan yana nufin bata isa ta rabe shi ba ? rasa me bata amsa maganar zucin da take yasa ta kallonsa yanda ya bude idanunsa yana kallon kannensa da suke masa magana cike da kulawa , ba karamin dadi ya ji ba , hakan yasa ya kama Anisa da Amina ya rungume su atare , shi ma Faisal janyosu ya yi yana kara matse su ajikinnsa , fesar da numfashi ya yi sannan ya sake su , kallon Mamy yake yanda tashin hankali ya bayyana karara afuskarta , har ya taho ze rungumeta yana tuna wani abu da baya baya ya koma yana mai kokarin shiga bandaki domin ji yake komi ze iya faruwa .


Dumbaru abakin Kofa ta tsaya tana kallonsu , cikin kasa da murya ta ce.


" Mijina Ridwan be son ana takura masa dan haka kowa ya fita yabar mana dakin". Cikin mamaki ta ga Mamy ta wuceta tana sheshekar kuka , ahanzarce Faisal da Anisa da Amina suka take mata baya , koda suka zo kusan Dumbaru sun zata tazo gyaran dakin Ridwaan ne , bayan sun san in yana ciki be yarda a masa gyara ba , ba su bi ta kanta ba suka wuce ta dukansu , suna barin wurin kwabe baki Dumbaru tayi , sai leka dakin take tana tunanin kar ta shiga ya korota kamar yanda ya saba , ahankali ta fara taku tana tura kofar dakin , Ridwan da yake zaune yana amsa waya da dukan alamu da Mansur yake waya , fuska babu annuri , lumshe idanunsa ya yi kamar me barci yana sauraren Mansur , ahankali ya fara bude idanunsa tare da sauke su akan Dumbaru , kwalalo idanu waje ya yi yana mai kallon kansa da ko riga babu ajikinsa , sosai Dumbaru take kallon gargasan jikinsa yanda gashin jikinsa ya kwanta gwanin ban sha'awa , ganin jikinsa take kallo yasa shi hada rai tare da katse wayar..


Tsawar da ya daka mata , gigitar da ita ya yi har saura kadan ta yi tuntube ba .


" Me kike nema adakina bayan kinsan ban fita ba?". ya yi tambaya yana kallonta da idanunsa masu kwarjini.


" Wallahi yallabai Ina sonka ".ta fada saman labbanta.


" Me kike fade ne ? Kin yi shiru ni fa ban son iskanci ya zakiyi ta Magana kasa kasa ba'a ji ".


" Yi hakuri Yallabai daman ,ina bukatar kudi ne , Mamata cen gida ba lafiya na kai sati ban sanin fitarka da shigowarka shiyasa dana ga su Mamy sun zo shine nazo ko Allah zesa asamu."


Shiru ya yi yana kallon kasa alamun tunani kafin ya iya furta


" Ok ki je wurin Mai Gadi zan bar masa kudi , ze baki, Allah ya sauwaka ya bata lafiya , dan Allah karki sake shigomin daki bana so " ya ƙarashe zancen cikin tsanani ɓacin rai.


Ita kuwa ba karamin jin dadi tayi ba ganin yau tayi fira da Ridwan har tsawon wasu mintuna.

Hanzarta barin dakin tayi , shikuwa yana ganin fitar ta , tashi ya yi yaje da kansa ya rufe kofar , tare da yin hanyar bandaki domin yin wanka da bukatun sa .


_______________________




Karfin Iko sosai yake Safa da marwa a cikin babban Falonsa , gefensa Malam ne , hagunsa kuwa Hasina ce , cikin tsananin damuwa karfin Iko ke fadin .


" Amatullah tana hannun Dsp Ridwaan mai Nasara , taya zan kwato ta , wallahi bazan iya barinta ba , nasan halinsa ze iya yimun tarko da ita , Ridwaan babban Jami'i ne mai ƙwaƙwalwa kamar Computer yanada wayau fiye da tunani , ko tafiya yake baya barin sawayensa a fili , baya tafiya sai da waiwaye , ai tunda Ridwaan ya yi nasarar kama wani dan ta'adda da ake nema sama da shekaru ashirin, ina tabbatacin kamani , ba ze masa wahala ba , sai de inda matsalar take yarinyar dake hannunsa badan ita ba , wallahi yanda na zama duhu agaresa ahaka zeci gaba da tafiya " ya karashe zancen cikin tsananin tashin hankali.


Malam cike da damuwa ya ce " Haruna na fika shiga damuwa Yarinyar nan nasanta wallahi !! Bansan samu damar yin Magana da ita , kaddara ta sake rabawa" ya ƙarashe zancen rai a dagule.


Karfin Iko ahanzarce ya ce " karfa kace kana son Amatullah fa? .

Malam ne ya yi hanzarin fadin " ni in so Amatullah kake nufi?".


" kwarai kuwa , haka nake nufi ". Cewar Karfin Iko .


"Haba !! Amatullah ai kamar ya ce a wurina kadaina wannan zancen a samu mafita kawai ta yanda zamu sato ta daga hannun Ridwaan Mai nasara ". Ya ƙarashe zance yana kallon Hasina da ke jînjina gaskiyarsa.



Hasina cikin karfin hali take fadin .


" Akwai hanyoyi da dama da zamu gwada domin kwato Yarinyar nan hannun Ridwaan , barinta hannusa zeyi yanda zeyi ganin yasan siririnmu dan shegen wayau da naci gare sa.".


Karfin Iko fesar da numfashi ya yi yana mai kallon Hasina cikin huci tare da fadin .


" Ai babu wani sirrinmu da Amatullah ta sani " ya yi magana cikin babban murya.

Hasina cikin dukar da kai ta ce .


Wallahi Haruna na sanar mata da sirrin Gidan nan hatta gidan nan sai da na karanto mata sunan Unguwar , dan Allah ka yafe mun bansan hakan ze faru ba " ta karashe zancen cikin neman afuwa da nadama.


Karfin Iko kallonta yake cike da tsoro da takaicinta , kasa magana ya yi ya dunkule hannayensa yana dukar iska.


Malam ne ya numfasa yana mai samun kansa da zama kan lallausan kujerar falon , kallon Ƙarfin Iko yake cikin tausasa lafazi yake fadin.


" Haruna ka daina damuwa da zancen Amatullah karta tona asirin Gidan nan , nasan bata da wayon yin haka , abinda ya fi cancanta shine ka amso ta daga hannunsa dan gudun kar ya cutar mana da ita kasan shi yana da fadin rai " Malam ya karashe zancen yana jin babu abinda yake bukata da gani sama da Amatullah. Zama suka yi dukansu suna nazarin yanda za'a shiryawa Ridwan tarko domin kwato Amatullah daga hannunsa.



****************

Ridwaan zaune a office dinsa rubutu yake kan wani file gabakidaya ma'aikata sun zagaye shi , knoking da akayi daga waje ne yasa , sakatariarsa shigowa cikin shigarta na dogon riga abaya mai adon stone , kasantuwa abayar ja ne ba karamin kyau ya yi da dan madaidacin jikinta ba , siririyar muryanta ta doka sallama kana cike da Respect ta ke sanar masa da sakon Commission da kuma tana neman yiwa mansoor iso a garesa , duk maganganun da take kallonta yake rike da habarsa , kana ya dan yi gajeran tsaki , tare da fadin " Rakiya duk wata ma'aikaciyar yan sanda irinki sun san waye Mansoor a wurina , daga yau karki sake gangancin hana shi shigowa da fatan kin gane ?".


Cikin hanzari ta gyada masa kai kamar kadangaruwa .

Ya kara da fadin .


Shi kuma Commissiner zan kira wayarsa , kin hanzarta barin Mansur ya shigo , kina fita ki rufe min kofa " ya karashe zancen yana mai maida hankalinsa kan aikinsa.


Gabakidaya ma'aikata soma fita suka ringa yi dan sun san in har Mansoor ya zo office baya son ganin kowa kusa da su .


Suna fita , Mansoor ya shigo Office din cikin shigarsa boyel maroon colar ba karamin kyau ya yi da hular kansa da takalmi ba , fuskarsa dauke da murmushi ya zauna suna face din juna , musabaha suka yi cike da girmamawa kana Mansur ya yi saurin fadin .


". Ridwan haka ake Rayuwa kasa ankai yarinya gida kai baka ce komi ba , yarinya bata da aiki sai kuka ".


Kif kif da idanu Ridwan ke kallon Mansur , cikin mamaki yake maimaita" kuka kuma?".


" kwarai kuwa , kukan take sai kiran sunan Papy take , kuma kai bakamin bayanin komi ba akanta bare har na baka shawara akanta". Cewar Mansur cikin damuwa.


" Ridwaan mikewa tsaye ya yi yana mai tafiya kamar ingarman doki , taku yake irin nasu na yan sanda kana ya nufi wurin window office din idanunsa na kallon farfajiyar ma'aikatan. Cikin kasan zuciyarsa da tsananin damuwa a bayyane a saman fuskar , cike da raunin sa ya ce .


" Mansur ka gafarceni na Daura Aure ".


Zumbur Mansoor ya mike daga zaune yana kallon keyarsa , cikin tsananin tashin hankali domin ya zo ne ya sanar masa da yanda Mansura take sonsa . Cikin surprise din zancen har bakinsa na rawa ya ce.


". Ridwaan dan Allah kasan bamu saba irin wannan wasan ba , Please dan Allah karka fara a yau ". Ya karashe zancen cikin kaduwa.



Ahanzarce Ridwaan ya waigo yana murmushi mai ciwo bakinsa cike da yakini ya ce .


" Dagaske nake nayi aure, zan iya wasa akan komi banda irin wannan ".


" wacece matar ka my Rid".


Ridwaan cikin gaskiya da gaskiya ya ce..


Na duri diyar.........






*Makauniyar Shari'a*


_Sai a lahira_



*NA*


IKILIMA ADAM

(Kyauta daga Allah)

_***_



*Saura page biyu in gama free page , ki hanzarta biyan naki domin ayi tafiyar dake*





Zaku samu complete din makauniyar sharia da aauran littafaina



_Jarumai writ associations_



SHAFI NA ASHIRIN DA UKU



" Na auri diyar... " sai kuma ya yi shiru be karasa ba , yana taune lip dinsa.


" Kayi shiru ina magana haba Ridwaan ka gayamin abin da yake faruwa , ni shakikinka ban sani ba " cewar Mansur cikin tsananin mamaki da jiran amsa.


Ridwaan kallonsa yake kamar wanda sam beda damuwa tattare da shi , cikin dabiarsa da na yau da kullum tare da tattara nutsuwarsa akan Mansur , cikin rashin sanin makama ya fara fadin.



" Wallahi Mansur auren nan na wucin gadi ne aiki na ne ya biyo ta hakan domin kama tarkona , Commissioner shine yabani bani Umarnin yin haka , kai ma kasan in har zanyi abu dan kare kasata komin wahalarsa ina yi , ba kowace yarinya bace na aura sai wannan Amatullah dake tare daku a gida" ya karashe zancen yana mai jin zafin hadin Commissioner da kulla alakar aure.



Mansur sankaka sake da baki yake juya wai Amatullah ya aura in har ze iya tunawa yarinyar ta masa kama da wacce suka taba gani a kauye , sannan kuma ta ina ta bullo ta iso Abuja . dafa shi da Ridwan ya yi hakan yasa shi dawowa hayyacinsa a firgice .


" Zauna muyi magana don naga kamar abin be maka dadi ba , kamar yanda nima be min dadi ba " cewar Ridwan cikin rauninsa.


Mansur fesar da numfashi ya yi yana kallon Ridwan ya kawo kujera biyu ya hade su wuri daya . Jiki babu kwari ya zauna kujerar dake kusa da wanda Ridwan din ya zauna . Kallon Ridwan yake yanda yake kallon sama kamar me tunani , kana ya yi saurin sauke kansa kasa yana kallon sa kana ya furta.


" Mansur a jiya aka daura kuma yarinyar tana da masaniya dan Commissioner da kansa ya mata magana ta amince duk da nasan be kai ciki ba , naga tsananin tsoro tattare da ita , auren yarinyar nan da kuma fitar da sanarwar aurenta ze sanya Karfin Iko yin yunkurin yin komi domin nayi bincike na tsananta bincike karfin Iko yana tsananin son yarinyar nan akanta ne ze shigo hannu , shi kansa ba tare da ya ankare ba" cewar Ridwan cikin damuwa.


" To me meyasa ba zaku yi karya ace ka aureta ba , tunda kunada damar yin hakan " cewar Mansur cikin soma yarda da maganganun Ridwan din, yasan karya ba dabi'arsa bace.


" Eh bazan iya yin karya ba Mansur sashina zata zauna , kuma kai kasan ajiye ta babu aure ze kawo zargi akan yan gidan mu , bare kuma daga majiya me karfi suka san ba gaskiya bane , za'a min kallon mutumin banza bayan nasan bazan iya aikata komi da wannan yarinyar ba". ya karashe zancen yana mai rike hannun Mansur .


Numfashi Mansur ya fesar shima damke hannun Ridwan ya yi sosai cikin nasa , kana ya murmusa cikin fara'a da sakin fuska ya ce.


" Wallahi na gamsu dari bisa dari kuma wannan hanya ce ka ɗauka domin kawo nesa kusa " cewar Mansur yana kallon Ridwan.


Ridwan murmushi ba dabi'arsa bace amma yau kam saida ya yi na gefen baki , kana suka dauko hirar Mansura akan yanda take son Ridwaan din.


Ridwaan cikin damuwa ya ce


" Abokina kai kasan in har zan iya aure da tuntuni nayi , Mansura bazata gane ba , bazan iya aurenta ba , ni fa kwata kwata bansan me Ma'aurata suke ji in sunyi aure ba da zasu shafawa kansu lafiya da sun zauna kalau , aure sunnah Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne , amma da sai ince a zamanin Annabi akayi me dadi da ni'ima , ni auren wucin gadi nayi kai kasan bazanyi aure ba , ita ma wannan zaka ga yanda zan sallameta cikin sauki " cewar Ridwan cikin yakini .


Murmushi Mansur ya yi yana juya kalaman abokinsa , kana ya yi karfin halin fadin.


" Humm bazance komi ba amma su Mata ba'a musu hakan ita ma wannan din bar ganinta kwaila wallahi tafi Mansura baiwa da komi" ya karashe zancen cikin yakini.


Tsaki Rudwan ya dinga jerowa akai akai yana kara jin haushi furucin Mansur , cikin yatsine fuska da takaici ya ce ..


" Ni fa ka daina hadani da wannan yarinyar saboda ko lissafin Mata ban sanyata ba , ai gwamma Mansuran in har dagsk Auren zanyi ita ce ta fi cancanta, kawai ma abar zancen nan , Mansura kuma Please kar mu sake Maganarta a barta bana so " ya karashe zancen cikin tsanani jin haushi.


Mausur kuwa murmushi yake dan yasan Ridwan komi a duniya in ya nema ze masa in har ya halarta amma banda ba shi shawara akan aure , fesar da numfashi ya yi hakan yasa suka fara wani hiran da ya shafi aikin Npower da Mansur ke jagoranta in har babu Ridwan a kusa.



***********



Abokin Umar a Gidan me Gidan Umar ya sauka me suna Alhaji Abdullahi , sun yi sintiti har sun gaji basu samu damar ganin Umar ba , Alhaji Abdullahi da kansa ya nemi ahada da Dsp Ridwan Muhammad Mai nasara domin ance case din a hannunsa yake , sun samu damar zuwa koda suka zo yan sanda dake kai kawo sunce in har me gidan nasu yana tare da shakikinsa Mansur baya amsar kowa in har ba Umergency matsala bane ya taso.


Sun dade Zaune Usman sai sakawa da kwancewa yake hannunsa rike da carbi tunawa ya yi yau yau befi saura kwana goma a kotu ba , hakan yasa shi girgiza kai yana tunanin yanda zata kaya a zaman da za'ayi na gaba.


Har sun fidda rai da fitowar Ridwan din , sai gani suka yi ya bude kofar office dinsa , Alhaji Abdullahi cikin zazzare idanu yake kallon Ridwan din , ya ganshi fari tass karfafan Namiji a tsaye , duk wani abu da ake kiran namiji mai haiba duk ya tattara uwa uba kyakkyawan ne fari sangiri , gefe daya kuma sosai yake kallon yanda suka yi mugun kamannin da Muhammad Mai Nasara duk da yasan Ridwan din ze mance shi ɗan tun yana yaronsa suke zuwa gidan , dayan kuma zuciyarsa tunowa da Mamy ya yi nan da nan ya ji ransa ya sosu akanta , karasowar Ridwan gabansu yasa shi dawowa hayyacinsa firgit .


Murya na rawa Dr Abdullahi ya ce .


" Ridwan mai Nasara dan Jagindi dake jahar Kaduna , Ko ba haka ba ?" ya yi tambaya yana tsare Ridwan da idanun.


Be bashi amsa ba duk da ya ji abun da yake fade , illah son ya wuce kusa dasu ya yi , shi da Mansur , ahanzarce Usman da Alhaji Abdullahi suka take masa baya , ganin yana musabaha da jama'ar wajen , hakan ya nuna kamar ya tashi daga aiki kenan . Ahanzarce suka sha gabansu shi da Usman ...


Ridwan kallon kallo suke wa juna shi da Alhaji Abdullahi , kana ya fesar da numfashi , hannun Alhaji ya mika masa suka yi musahaba , kana suka gaggaisa har da Mansur din .


Alhaji Abdullahi cikin sakin fuska ya ce " Haba Ridwan ni abokin mahaifinka ne tun kana yaro na sanka kuma dani da Mahaifinka akaje neman auren Saratu a Jagindi watau Mahaifiyar ka .


Ridwan sosai yake nazartan kalaman sa jin ya ambaci mahaifinsa cike da girmamawa ya kara basa hannu suka yi musabaha , bakinsa na rawa ya ce .


" Abba ka yi hakuri , akwai dayawa masu zuwa damuna ba tare da wani dalili ya kawosu ba , nasan yanda nake sannanne ba abu me wuya bane dan ansan garin mahaifiyata ba , shin Alhaji lokacin da Mahaifina ya rasu kana ina? ina ga banga fuskokinka cikin wa'yanda suka zo zaman makoki ba , abar wannan zancen yanzu akwai taimakon da zan maka ne ?" ya yi magana cikin ladabi.


Alhaji Abdullahi girgiza kai ya yi domin yanda Ridwan ya jero masa tambayoyi ya tabbatar ba yaron yanada zurfin ilimi da hangen nesa.


" Ridwan daman nazo ne akan yaron nan da aka kama watau Umar Isah Sharifai , sam anki bamu damar ganinsa hakan yasa nasa ahadani dakai dan zatin Ubangiji ka mana hanyar ganinsa , sannan muna so mu zauna dan jin irin laifin da ake zarginsa da shi , sannan kayi magana akan Mahaifinka ina ina ya rasu banzo gaisuwa ba , bana kasar ma bakidaya , amsar wannan tambayar yana bakin Magaifiyarka ko kuma in ce in lokaci ya samu zan fada maka komi akan Mahaifinka nasan bakasan wasu dayawa daga ciki ba "


Numfashi Ridwan ya sauke yana kallonsa hade da nazartansa yanayinsa da kalamansa , cikin hanzari ya ce.


" Umar Faruk ku bari zuwa gobe karfe goma zaku gansa da kunzo ku nemi sakatariya ku ce mata ni ne nace afito da Umar , dan Allah zan iya tafiya dan akwai inda zan je sauran maganganun zamu karasa in mun sake haduwa " ya karashe zancen yana juya kalaman da Alhaji Abdullahi ya fada masa da ya je ya tambayi Mamy , barin wani tunanin ya yi suka barsu nan tsaye shi da Mansur.



**********



Mansura zaune a farfajiyar Gidan ita da Amatullah dake goge hawaye dan tunda ta ji wai andaura mata aure da dan Sanda tasan ajalinta ne yazo dan ta yi imani kuskure kadan zata aikata ya harbe mata kai , Mansura dake mata kallon yar yarinya matashiya cikin sakin fuska ta ce..


" Wai ke Amatullah ba zaki saki jikinki ba , nan fa kamar Gidanku ne , bakiga inata koyamiki abubuwa ba , kuma fa yaya Mansur har Makaranta ya ce ze sanyaki , ki nutsu daman banda yar uwa mace tunda na sameki ai dadi naji kafin lokacin aurena da yaya Ridwan ya yi shine kawai ze rabamu" ta karashe zancen cikin shauki sai da dimple dinta ya lotsa.


Zazzare Idanu Amatullah tayi jin wai Murna take in har akayi aurenta da wannan malakun maut din , dayar zuciyarta take fadin...


" kenan ni da Mansura ze hada ya fallewa kai kenan? " rasa me bata amsa yasa ta mayarwa Mansura da murmushi.


Sosai idanunta ke kallon yanda tsuntsaye ke shawagi a sama kana yanda tsakar gidan yake a tsare babu wasu motoci sai kwaya daya kacal wanda da dukan alamu motar Mama ce .


Mansura sai zuba take ita kam Amatullah da idanu take bin ta da shi tana yar murmushi.



***************



Salim yana kwance ya dan fara samun sauki , likita ne ya shigo dakin , cikin shigarsa na likitoci hannunsa dauke da file , cikin fara'arsa ya ce .


" Mama congrat an samu wanda ya dau nauyin fitar da Salim kasar waje dan haka mun tattara takardu ranar Monday zaku tafi , dan haka zan bada kudi a muku password Umergency , sannan in ya samu lafiya ya dauki nauyin karatunsa acen kasar waje ze iya karasawa tunda ya yi nisa" cewar likita cikin jin dadi.


Mama cikin hanzari ta durkushe kasa , kuka take sosai iya ranta dan sun fidda tsammani , murya na rawa ta ce.


" Dan Allah wani dan Aljanna ne ya taimaka mana ? Ina son in masa godiya , Allah ya rabasa da kunci da baƙin ciki Allah ya daurasa akan makiyansa" ta karashe zancen cikin muryan kuka.


Docto kallonta yake yi ,cikin sanyin murya yace .


" Me yi dan Allah ne baya son a sani baya fadar sunansa , baya son godiya ke dai ki gode wa Allah , dan ni kaina cikin takardan ansa Fisabidillah babu suna akai sai yawan kuɗaɗen da kuma bayanan wanda ake son ataimakawa " ya karashe zancen cikin jin dadi.


Mama dake kallon Salim yana murmushi , tashi ta yi zaune cikin farin ciki ta rike hannun Salim tana fadin.


"Kaga dan Aljanna ya taimaka mana Allah ya biya masa da bukatunsa duniya da lahira " dukansu da Ameen suka amsa har salim din , shi da a saman labbansa ya amsa amma kana ganinsa kasan yana cikin farin ciki.

Da jim ya yi gefe daya na zuciyarsa yana tunanin in har ya samu dawowa ta ina ze fara neman Amatullah domin ya cika mata burinta na gina mata gida ya kuma aureta domin cire ta cikin wahalar rayuwa , ya dade yana tunani har Likita ya bar dakin be sani ba..



*************




Bayan sati daya


Kwanaki na shudewa inda ya rage be fi saura kwana uku a koma zaman kotu ba .


Barister Hadiza Ibrahim bincike take yi babu kama hannun yaro , sosai Hajiya Basma ta tsorata jin wai Hadiza Ibrahim har cikin gidan nasu ta zo yin bincike , kenan Boka yana nufin aiki be kama Hadiza Ibrahim ba kenan take tambayar kanta , rasa me bata amsa ne yasa cikin hanzari ta shirya ta tafi wajen bokanta. Tana zuwa ta iskesa da baki , bakin na tafiya ta zauna cikin damuwa ta zayyane masa damuwarta shi kuwa yana bugawa kasa cikin rawar murya ya ce.


"Kyale Hadiza Ibrahim na lura mace ce wacce bata wasa da adu'oi , ai in ita be kamata ba Alkali dole ne ze kamashi tunda shine me yanke hukunci. Kuma karki damu dan Fauziyya ta warke na gayamiki surikinta maye ne , abinda za'ayi kawai ayi yanda kika ce wajen sanyawa mijin nata sha'awar karin aure anan ne zata gane ƙurenta " cewar boka cikin yakini.


Basma ta ji dadin haka inda ta ajiye masa makudan kudade kana ta bar wajen gudun kada Alhaji Isah ya dawo be ganta ba.


Tana komawa gida iske Nasara diyarta da Basira da Badariyya tayi har ma da Laila suna tikar rawa , tsakiyar falo ko ina sashin tashin hayaniyarsu ake ji .

Tana kallonsu tana dariya tare da wuce su bata ce musu komi ba , su ma ko sannu da zuwa basu mata ba suka ci gaba da tikan rawa cikin kananun kayansu riga da wando dake jikinsu.


Nasara sai fadin take .


" Allah yakaimu Kotu a kora mana ya'yan awaki daga gidan nan" tayi furucin tana tikar rawa.


Laila ce ta dan bata rai cikin yar murya ta ce.


" Su da Gidan Ubansu za'a koresu , ai tunda muma muna zaune ciki , su ma babu inda zasu je " ta karashe zancen tana cigaba da rawar ta.


Sosai kalaman ya ratsa kunnuwan sauran yan Uwan nata , ahanzarce suka kashe kidar dake tashi tare da matsowa kusa da Laila suna juya kalamanta cikin tsanani ɓacin rai.


Nasara ta ce " ke amma Laila bakida hankali ko ? ni kike gayawa ba zasu bar gidan ba ? ". ta karshe zancen cikin fada.


" kwarai kuwa ba zasu bar gidan ba ai suma ya'yan Daddy ne , kuma bakiga yanda Yasmine take kama da Kakan mu Muhammadu ba , kuma Anty Fauziyya tana kama da Daddy " ta karashe zancen cikin turo baki .


Caraf kalamanta cikin kunnen Alhaji Isah da Hajiya Basma dake saukowa daga kan matakalan step saboda jin tashin hayaniyar fada.


Zazzare Idanu Basma ke yi jin yanda Laila ta yi furuci babu tsoro , bata ankare ba sai ji ta yi Nasara ta dauke Laila da zafafan maruka guda biyu. Tana kokarin kara mata wani marin ne ta ji kakkausar Muryan Alhaji Isah yana fadin.


" Dakata " karki kara marinta , in har ta yi laifi gyara mata za'ayi kuma abinda ta fada ina ga fahimtarta ce sai kuma barta a hakan tunda kunsan yarinya ce , dudu bata fi shekaru 15 ba , kunsan bana son ɓacin ranta " ya karashe zancen tare da kama hannun Laila ya yi sashinsa da ita tana kuka , ko magana beyi wa Basma ba dan yaga ranta a bace yake.


Nasara cikin takaici take fadin .


" Laila zata sani ne har ta fito " ta karashe zancen tana hura hanci , sun dade suna hira da Basma tana basu hakuri kana suka dan manta da batun , cigaba da rawa sukayi bayan sun kunna kida.


***************



Mamay Zaune a dakinta daga ita Kaka da Yasmin dan sosai ta ji sauki ta warware kamar ba ita ba , soma lissafin inda zata je take yii , bayan kotu ta koresu , cikin sanyin murya ta ke fadin.


" Kaka yanzu in har bamuyi nasara ba ina zamu je ne ? "


Kaka cikin rawar murya ta ce " A'isha ai keko kike da wurin zuwa kedai bari akai karshen zaman kotun zamu samu mafita , wallahi mazan yaran nan suna da kokari wlh , saboda su muke cin abinci " ta karashe zancen cikin jinjina kokarin su .


Mamy cikin rashin walwala ta ce " ni a kotu zan sa a raba Aurena da Isah , in sha Allah aure zanyi dan Isah ya fita araina kwata kwata , kiyayyar da yake nuna min yasa banko kaunar ganinsa " ta kai karshen zancen cikin damuwa.


Kaka dake kallon Yasmin dake shan garin kwaki da suga a kofi , cikin damuwa ta ce" Wallahi Isah ze..........




Karku Manta saura page biyu a gama free page kin hanzarta ki biya kar ayi babu ke .



Taku har kullum Kyauta daga Allah

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol