Free chapter · Read without an account
4
BINTUN BATUUL
E1
Da farko dai sunana Bintu, a gidan mu na Zama tamkar wata shadow ce, wato idan nace shadow Ina nufin Inuwa, shi ne dalilin da Kai tsaye baa Kira na Bintu, sede ace BINTUN BATUUL. Da farko ban gane hakan ba se daga baya da nayi wayo na gane dalilin Kira na da hakan.
Kamar yadda kuka sani, a kasar mu ta gado, wato kasar Nigeria mu nada arewaci da Kuma kudancin kasar, mu din Yan arewa ne Kuma arewar ma north west, wato arewa maso yamma. Da bana gane wannan intersection din se a hankali na Fara fahimtar yadda suke da Kuma me suke nufi. A jahar jigawa akwai wani daddaden gari me tarin tarihi, wanda ake tunanin suna daya daga cikin Hausa bakwai, wannan gari masarauta ce cikin daya daga cikin masarautu biyar da suke a garin na jigawa. Wannan garin kuwa shi ne Hadejia ginsau birnin Doki.
Kamar yadda kowanne gari zaka ga Allah ya hallitta musu irin mutane, yaren su da Kuma abincin su, ways of living, norms din su day values din su, to Suma a Hadejia suna da wannan! Na farko dai idan ka fiye Baki a jigawa we consider you Bahadeje (No offense, this is the reality) Yan garin bakake ne, saboda suna da asali da barebari, Amma Kuma akwai farare tunda ana samun auratayya tana hada su day wasu! Akwai Kuma miyar kuka, ban sani ba ko sune founders din miyar kuka, Amma mu a jigawa kirarin da ake ma kuka is always "Bahadejiya kin fi giya tsiya" Wai kuka fa ake cewa Haka, gaskiya justice for miyar kuka....lol
Suna da ruwa, shiyasa suke da kifi, garin Hadejia akwai kifi akwai Kuma ruwa, I remembered duk shekara Kawu zai ce ya tafi Yi musu jaje, either flooding ko Kuma garin is about to flood. Haka dai maganar take. Mahaifi na Dan asalin Hadejia na, tun daga mahaifiyar shi har mahaifin shi, tun mahaifi na Yana karami Allah yayi Masa son fararen mata, hajja tana yawan fada Mana ko bakuwa akai in dai Fara ce, to ko an aike shi sai saa zai je, da ya Fara girma kuwa kusan duk wadda ya gani Fara se yasan yadda yayi yayi Mata magana, se Kuma yasan yadda yayi ta kula shi ya Fara zuwa gidan su. Wannan shi ne mahaifi na!!
Bansan me yasa maimakon Baba ko Kuma Abba ko ka Daddy, da ywanacin ake Kiran iyaye mu a gidan mu Kawu muke cewa, Haka muka tashi muka hi sauran yayin mu na Kiran shi muma Kuma muka dauka. Asalin sunan mahaifi na Hamisu, mutum ne dogo da Kuma jiki, irin mutanen nan da ake Kira da giant, Kuma Baki ne sosae, Dan kuwa Bai bar gida ba. Labarin da na Baku na rashin son bakaken Mata yasa yake da nacin nema, tun da mahaifiyar shi tace Masa ai fararen Mata masu kyau tsada ne da su, shikenan ta birkita wannan bawan Allah, karatu yayi na primary anan cikin Hadejia, kafin da ya Gama ya taho minjibir yayi makarantar maza ta karamar secondary! Da ya kammalla se ya dawo nan tsohuwar makaranta me cike da tarihi wato Rumfa college da ke cikin birnin na Kano. Anan Yana zaune gidan wani kanin mahaifin shi Kawu Sabaru, daga can yake Hawa Keke yaje makaranta, idan aka tashi ya cire uniform ya kulle a Leda ya tafi kasuwa inda nan ne yake yaron shago cikin kasuwar kwari, idan yamma tayi Kuma ya tuko Keke ya dawo gida. Yana ta fama har Allah ya nufe shi da kammalla secondary School, kamar ba zai cigaba ba Amma uban shagon ya nuna masa muhimmanci da yake gani a tattare da karatun Boko, cikin saa da kullum yake fada, Yana Kuma alfahari da shi din me sa'a ne a rayuwar shi. Ya samu gurbin karatu nan cikin bayero University, dukda Haka Yana kasuwancin shi, Yana Kuma yin taro yadda Baku tunani, a kwana a tashi , karatun shi yayi nisa haka ma kasuwan cin shi, mahaifin shi ya aike Masa da sakon komawa gida Dan an zaba Masa Mata. Kunsan dai ya Riga da yayi alkawarin mace in dai baka ce to Bata da gurbi a cikin gidan shi, Bai Yi musu ba ya tafi Hadejia Dan ganin Mata, Yana zuwa ya tarar da Yar kanin baban shi ce Salamatu, shi yarinyar saboda bakin ta ko magana ba yayi Mata, kuji fa gwano baijin warin jikin shi, shi ma da bakin ne. Ya nunawa mahaifin shi rashin son auren Amma mahaifin shi yace Babu fashi, shikuwa ya tattara na shi ya nashi ya dawo Kano ya cigaba da sabgar shi, aka daura aure kamar yadda aka saka rana, Amma ango har amarya tayi wata guda Babu shi Babu dalilin shi, Haka mahaifin shi ya dakko Salamatu ya taho da ita Kano, ya aje Masa ita dakin shi na zaure Dake gidan Kawu Sabaru. Se dare ya dawo kamar kullum, da bredi na kullum da yake tahowa da shi da Kuma alawa saboda Yara. Yana zuwa ya shiga dakin shi Kamar yadda ya saba, ya cire Kaya ya fito zuwa wani shago Dake makwabtan su yayi wanka sannan ya dawo, se da ya saka Kaya sannan ya lura da dankwali an kulle Kaya da shi, ya saka kafa ya shura dankwalin se Kuma ya dauki biredi da sauran kayan shi yayi cikin gida, Jin sallamar shi yaran Suka taho da gudu, dukda ba kula su yake can sosae ba, Amma dai Yana Basu alawa, shi Kuma alkhairi Yana saka mutum ya Shiga ran Wanda yake bawa, shiyasa kayi kokarin ganin ka kyautatawa mutane.
Ya Mika musu ledar alawar su, sannan ya bawa babbar biredi Dan ta kaiwa mahaifiyar su, anan zaune yayi Ido hudu da Salamatu, da taimakon aci balbal din Dake gaban ta wadda aka kunna Dan ta haska gidan, ya Bata fuska Yana ayyana wannan mayyar har nan ta biyo shi ko ko me? Suna gaisawa da Inna talatu matar Kawu Sabaru, se ga Kawu Sabarun ya shigo, Suka gaisa da Kawu Dake kokarin juyawa Amma Kawu Sabaru ya dakatar da shi, tabarma Salamatu ta shimfida musu Suka wanke hannu Suka ci tuwo tare, wannan cin tuwon tare implies alot, ya tabbatar akwai gagarumar magana a kasa Yana Kuma fata Bata danganci auren Salamatu ba, Dan kuwa ba zai aure ta ba, ba zai zauna da bakar mace marar wayewa irin ta ba. Idan Kuma suka matsa to gaskiya ba zai jure ba, zai bijire duk abin da zai faru ya faru, wannan shi ne tunanin da yake yawo a cikin kwakwalwar Kawu. Bayan sun Gama cin tuwo an wanke hannu, Bayan Gama sude sude saboda Inna talatu ba dai girki ba, matar nan da ace a wannan zamanin take, to tabbas zata buge food content Creators da yawa!
Cikin lallami, da Kuma tsara kalamai Kawu Sabaru yayi wa Kawu bayanin halin da ake ciki, na an Riga da fa an daura Masa aure da Salamatu, shi ne dalilin dawowar ta nan, ya kada Baki da fadin Kuma Yana son yayi hakuri ya zauna da matar shi lafiya su samu zuri'a dayyiba. Kawu da yake ta auna kalaman cikin Kan shi, like for real shi akaiwa auren Dole? Ko Kuma bashi Hamisun ba? To su wanne digimi ne ya kaisu entrusting Yar su gare shi, bayan he clearly said it, baya so, baya son ta ba Kuma zai aure ta ba. To fa cikin Abu biyu Dole zaayi daya, ko dai ayi Abu cikin lumana ko Kuma hatsaniya ta biyo baya domin shi dai Bata da space cikin rayuwar shi!
" Kawu Sabaru, gaskiya maganar Allah bana son yarinyar can, bana kaunar ta ba Kuma Zan zauna da ita ba!"
Kawu yayi saroro Yana kallon shi da mamaki a fuskar shi yace
" To Hamisu waye yayi auren soyayya? Ai dukka Hadi akai Mana Kuma gashi mun manta cewa ba soyayya mukai ba! Ka da kake neman albarka..."
"Wannan fa ya wuce Kawu! Ni na fadawa malam (mahaifin shi) ni ba Zan aure ta ba, saboda ni matar da Zan aura ba irin wannan suffar nake so ba"
Mamaki ya Kara kama Kawu Sabaru, ai se ya Fara fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, Amma wannan fadan Bai saka ya janye kalaman shi ba, Haka suka rabu baran baran, ya koma daki Yana ta pacing cikin tsukakkaen dakin Yana Kuma nemawa Kan shi mafita, a karshe se ji yayi an turo kofar an shigo, ya dago idanun shi Yana tunanin wanne isashen ne? Se gata a tsaye ta Sha lullubi Wanda ya Bata Masa Rai, maimakon Barin ta ta shigo se ya maida kofar ya barta a nan tsaye.
A takaice kowa baccin bacin Rai yayi, kowa jira yake safiya tayi ya dauki mataki. Asuba nayi ya hade kayan shi tas saboda yasan idan ya aiwatar da abin da yayi niyya to tabbas zaman shi gidan Kawu Sabaru yazo karshe,shi Kuma saboda gurin Zama ba zai cuci rayuwar shi ba. Ana idar da sallah yayiwa Tasha tsinke ya hau mota se Hadejia, shima Kawu Sabaru Yana idar da sallah wanka ya dawo yayi a gida sannan ya dauki hanya se Hadejia!
Ko da yaje gidan su ya wuce, ya samu mahaifin shi ya dawo daga su, wato kamun kifi saboda sanaar shi kenan, Bayan sun gaisa aka kawo Masa tuwon buski da miyar kuka, ya zauna yaci yayi hani'an kafin mahaifiyar shi ta Fara tambayar shi wajen su Inna talatu da Kuma amaryar ta shi? Lafiya kawai yace Mata sannan ya fice zuwa wajen baban shi, ya samu har Kawu Sabaru ya iso Kuma an Kira Kawu Mamman wato mahaifin Salamatu, dukka suna zaune suna sauraron abin da Kawu Sabaru yake fada musu. Ko dar baiji ba yaje ya zauna, malam ya Fara fada se Kawu Mamman ya dakatar da shi yace
" Hamisu baka son Salamatu ko?"
Ya gyada Kan shi, ba tare da yaji ounce of rashin dacewar abin da yayi ba
"Bana son ta Baba, ban shirya aure ba. Ku gafarce ni, bana son zumunci ya lalace, ba Kuma nasan Bata muku, ko Kuma na zalunce ta shiyasa nazo nace muku ni na sawwake Mata igiyar aure na daya dake kanta idan ta samu miji tayi aure"
To be continued...