Free chapter · Read without an account
#14
FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔
*©️AuntiMamee*
Free pages
_Page14 _
Lumshe idanunsa yayi sanda yake tauna goron, ji yake kamar wani abu na daban yake taunawa ga zuciyarsa dake cike da nishaɗi, duk wani damuwa da ɓacin rai na zuciyarsa jiyake ya yaye, tun bayan shigarsa prison wannan ranan kawai yake jira da zullumi kuma Alhamdulillah gashi ubangi ya cika masa burinsa.
Dukkansu kallonsa sukeyi cikin tausayi Binazir kam maida kanta tayi jikinsa tareda rungumesa idanuwanta na zubarda hawaye.
Saida ya gama tauna goron duka sannan ya buɗe idanunsa tareda saukesu kan Samir da shima nasa idanun a kansa yake.
Huci Samir ya saki tareda ɗauke idanunsa daga kan Dady ya maidasu gefe.
Girgiza kansa Dady yayi tareda jin tausayin Samir a zuciyarsa, shi kansa yasan yaron kome yakeyi dauriya kawai yake dan Allah ne kaɗai yasan me yakeji a zuciyarsa wuta biyu ce ke ruruwa ya sani a zuciyar yaron da wutar Binazir da kuma wutar abinda shine sanadin faruwar komai.
Shima numfashin ya fesar tareda maida dubansa gasu Barrister buɗe baki yayi zaiyi magana Barrister yayi saurin dakatar dashi da faɗin "Ni bana sonjin komai ai duk yiwa kaine Alhaji fatana ɗaya kawai ka yawaita istigifari Allah yasa mu dace"
"Ameen" Dady da ƙanin Mummy suka faɗa a tare.
Samir ne ya juya yabar wajan tareda fita waje ya jingina da jikin motarda sukazo, idanunsa ya lumshe tareda fitarda iska ta bakinsa.
Da kallo Dady ya bishi sanda yake fita har saida ya ɓacewa ganinsa sannan ya saki ajiyar zuciya tareda ɗago Binazir dake jikinsa yana kallonta cikin ƙauna irin ta ɗa da mahaifi.
"Amarya kinsha kyau" Dady ya faɗa cikin tsokana hakan yasata sakin dariyar kuka tareda bin jikin ta da kallo ba komai a jikinta sai wani ƙaton hijabi da batasan na wane ba ta zullubo sa.
"Dadyyyy" ta kira sunansa cikin Muryar kuka.
"Oya zo mu tafi tunda bazaki daina kukan ba" ƙanin Mummy ya faɗa tareda fara taka ƙafarsa, da sauri ta share hawayen tareda tsaida kukanta.
"Ko kefa gashi har kin ƙara Kumari" Dady ya gaya mata cikin zolaya.
Wani kukanne yazo mata zuciyarta amma ta danne sa, taya za ayi bazatayi kewar wannan mahaifin da akoda yaushe babban burinsa ya tsokaneta dan yasata nishaɗi? Mahaifin da indai yana a tare da ita ajiye shekarunsa yake a gefe ya fuskanceta matsayin ƙawa harsai ta gama faɗa masa damuwarta sannan zai dawo da matsayinsa na uba wajan mata hukunci ko adalci kan hirar da sukayi? Taya bazata tsani mutuminda ya zama silar shigar mahaifinta wannan halin ba?
Tana cikin tunani ne taji Gandiroba na faɗama su Barrister lokacin ziyara ya wuce, da sauri takai dubanta ga gandiroban tareda maida dubanta ga Dady.
Murmushi yayi mata da faɗin "Allah yayi miki albarka, Allah ya kawo takwarana baɗi iwar haka" yana faɗa ya juya yabar wajan.
Har saida ya ɓacewa ganinta sannan ta ɗauke idanunta a kansa tareda haɗiye wani abu daya tokare mata ƙirjinta. Maida idanunta tayi kansu Barrister da suke magana da wani gandiroba, da sauri ta juya tareda fita waje, a jikin motan ta gansa har lokacin idanunsa a rufe.
"Da fatan ka fara irga awannin ƙarewar zaman lafiyar ka?" Ta tambayesa sanda ta ƙaraso wajan idanunta a kansa.
Buɗe idanunsa yayi ya sauke a kanta na tsawon second uku sannan ya janye tareda maida kansa gefe " am not in the mood woman!" ya faɗa tareda lumshe idanunsa.
"But i am" ta amsa masa a zafafe.
Buɗe idanunsa yayi tareda saukesu a kanta yana karantar yanayin ta, ajiyar zuciya ya sauke tareda buɗe marfin motar yana mata nuni data shiga da ciki.
Hararar ta wurga masa sannan ta zagaya ɗaya ɓarin tareda buɗewa ta shige.
"Hummm" yace tareda girgiza kansa sannan ya shiga motan ganin su Barrister sun nufo wajan.
Ba wanda ya ƙara magana a cikin su motar ta ɗau shiru, har saida sukazo Darmanawa sannan Barrister ya sauketa da faɗin "ku shiga ciki angon naki zamu kai gida" kanta kawai ta sunkuyar ba tareda tace komaiba ta fice daga motar.
Tana shiga mutane sukayo caaaa kanta da tambayar ina taje daga ɗaurin aure? "Wajan Dadyna" shine amsarda take bawa Kowa kuma amsarda ke sanyaya jikin masu tuhumar inda taje da haka ta samu aka rabu da yimata mita ɗakin Mummy ta nufa inda take kyautata zaton ba mutane acan, kuma taci sa'an hakan dan bata samu kowa a ciki ba, kan gadon ta faɗa tareda duƙunƙune kanta cikin hijabin ta shiga tunanin yadda zata gudanar da babin sabon ƙaɗɗarar ta da ya buɗe a yau, ita da zuciyarta cike take da FANSA, da fargaba dolene Majnun ya ɗanɗani ɗacin rayuwa idan ba hakaba kam taga alaman yana dabda haƙo rufaffen ruhinda ta daɗe da binnewa a tarihin rayuwarta.
ANGO
Har gida su Barrister suka kaisa, cikin mutumtaka sukayi sallama da juna tareda godiya, kamar jira danginsa suke, yana shigowa gida ya kacame da guɗa har saida ya ɗan ja baya dan ba ƙaramin tsorata yayi ba dan shi zatonsa wani mummunan abune ya faru, ajiyar zuciya ya sauke fahimtar ma'anar guɗar sannan ya ɗan saki ransa yana gaisawa da 'yan uwa abokan wasa kuma sai tsokanarsa sukeyi shidai nashi murmushi ne kawai tareda shafa sumar kansa.
Maman Bishira ce dake zaune can daga gefe take wurga masa harara dan haka kawai taji tayi mugun tsanarsa tareda ƙudurin ɗaukar FANSA kan abinda yayiwa 'yarta da kuma kasancewarsa dalilinda yasa mijinta yayi mata dukanda rabonta dashi tun Bishira na shekara goma sha biyar. Yanzuma batayi niyar zuwaba Baba Garba ne ya rantse muddin bataje bikinnan ba ita da 'ya'yanta saiya bata mamaki, hakan yasa ta tattaro kan 'ya'yanta amma banda Bishira dan ko Bishirar bata rantse ba kan zuwannata bikin ita batada niyar takura mata dan koda bata shiga zuciyarta ba, tana jin irin raɗaɗinda take ciki.
Kauda kanta tayi gefe tareda taɓe bakinta.
Naja kam ai sune biki dan idan ka ganta sauka rantse itace amaryar dan kam Yayan nata ya tsaya mata komai tace tanaso ya siyo mata zai siya matan, idan kuma bai siyoba to zai tamayeta kuɗinne ya bata.
Umma ce ta jashi gefe take faɗin
"Babban mutum anya 'yan ɗakko amarya bazasu haɗa da lefebe inyaso idan danginta sun gani sai a dawo dashi tareda amarya?" ta tambayesa idanunta akan nasa, dan ya haɗa laifinsa daidai gwargwadon iyawarsa da kuma gudummawar dangi a haka ya tada akwatina takwas, amma tun ana saura sati biyu umma ke masa zancen kai lefe saidai yace a dakata akwai abinda yakejira, gashi har an ɗaura kuma tasan har iyanzu a cikin dangin amaryar baza'a rasa mai zuba idon ganin laifanba a yau dan tasan al'adar mu ta mata na son ƙwaƙwƙwafi da ɗaukar magana.
Gashin girarsa ya sosa da faɗin "Umma yanzu a ɗebi akwatunan kawai akai can sabon gidan duk wanda yaje gidan ya gani" yana faɗa ya juya yabar wajan, yana tuna yadda sukayi da Binazir yana gama haɗa lefe ya taka har gidansu yasa aka kira masa ita a fusace ta fito dan daga idanunta ya gane ko bacci ko kuka takeyi aka katse mata hanzari, Numfashi ya sauke da faɗa kan za'a kawo lefe don fita haƙƙinta , alokacin wani kallo ta bishi dashi sannan tayi rantsuwa da muddin matsiyatan kayansa suka shigo musu gaida ta kuma rantsuwa da saitabi dare ta ƙonasu alokacin kasa control in kansa yayi dan sosai kálamnta suka taɓa masa zuciya shima a take yayi nasa kyakykyawan rantsuwar kan bazai kawo kayanba tunda ya fuskanci shi practically ya gwada hauka amma ita physically and mentally ta fishi iya haukan kuma yasan tsaf zata aikata hakanne yasa ya amsa mata da baza'a kawoba amma shima ya rantse idan ta shigo gidansa sati biyu ya bata ta gama amfani da dukkan wani kayanda tazo dashi daga gidansu, sati biyun na cika da lefenda ta kira matsiyata zata cigaba da amfani da, yana gama faɗa mata yabar gidan shima zuciyarsa na ƙuna, dan bata taɓa ƙona masa rai irin na ranar ba.
Da mamaki take kallonsa na inda ya samo asalin wannan ƙwarin gwiwar da har zai lulluɓeta da masifa? " The hidden secret" zuciyarta ta bata amsa, ajiyar zuciya ta sauke tareda shigewa cikin gidan jiki a mace.**
Da kallo Umma ta bishi kallon mamaki, ita dai tasan komai 'ya'yanta zasuyi sai sun sanar da ita amma ta fuskanci tunda ya fara kawomata zancen Binazir cikin gidan ta ɗan nuna rashin goyon bayanta, tun daganan taga ɗan nata ta fara ɓoye mata abubuwa dan ko zancen yarinyar ta ɗakko cikin hikima zai kauda zancen tareda sako wani batun daban.
Ajiyar zuciya ta sauke "Allah ga amanar marayanka nan mai biyayya ga umarni ka , mai ƙaunar ma'aikinka ya Allah ka shiga lamuransa karka barshi ya wulaƙanta" ta faɗa a fili tareda komawa cikin dangi dan cigaba da hadahada, dattadawan da zasu ɗakko amarya ne ta shaida musu kan a nemo Naja a tafi da ita dan zata yi musu jagora zuwa gidan Samir dan za a fara kai akwatunan gidan kafin a ɗakko amarya, bata basu damar jin ba'asi ba ta ɗakko wani zancen.
Naja da taji zancen da ita za akai amrya ai wani rawar daɗi ne ya cika zuciyarta na zataje taga gidansu matar yayan nata harda koda watarana idan jar miya ta ratsata tayi mata iskanci ta goranta mata dan ta gano mafakar tsofaffi.
Gidansu amarya shirye-shirye ya kankama dan masu ɗaukar amarya sunzo suna main palo zaman jira Aunty Lubabatu ta zage sai gyara amarya takeyi itadai komai akace mata bata musawa wani lokacin ma idan aka tsokaneta har maida martani takeyi hakan ba ƙaramin faranta ran Mummy yakeba, dan saika yi mata kallon ƙurilla ne zaka fahimci rashin nutsuwar da ke tare da ita haɗe da ramarda tayi amma a bayyane kam tana ƙoƙarin danne komai ta na ƙoƙarin nunawa duniya ba wani manufa a autanta haɗine na Allah ita da angon nata.
Su Naja da tun sanda sukaje gidan yayan nata idanu suka fara raina fata ganin yadda aka jera gidan dan musamman Mummy ta Kira Barrister a waya kan ya tambayi Sameer makullin gida za suyi jere.
sun kuma jeran dan dukkanin wani bedroom dake gidan saida aka saka masa saiti haka zalika toilet komai na buƙata an jera amma iya toilet biyu na bedrooms inda suke manne da juna ɗayan ne kawai basu sa komai a toilet inba amma ansa saiti madaidaici dan sun fahimci nanne zai kasance ɗakin baƙi, kitchen kam ba'a magana ga store da aka shaƙesa da kayan Gara kobam faɗa ba nasan kinsan yadda palon aminiyar Mummy zai kasance, saida keys in sukayi kusan two weeks a wajansu sannan aka maidawa da Barrister ya bawa Samir kuma ko kaɗan baije yaga gidan ba dan ana gobe ɗaurin aure Barrister ya kirasa yaje ya karɓa kuma yana dawowa ya damƙawa Umma mukullin ajiya.
Wani kallon abin mamakin ga Naka, sai da mai gadi ya zuge gate ta buɗe idanu da hanci harma da baki tana kallon ikon Allah, bata shiga tashin hankali ba saida taga motocinda ke jere guda huɗu a gidan, tun daga nan ta raina kanta, ai data shiga palo har riƙe takusa da ita tayi sakamakon sanyin AC daya daki fuskarta. wani numfashi taja ta sauke sanda ka nuna musu wajan zama. Yadda take wannan tunanin haka abokan tafiyarta keyi na mamakin inda Samir ya samo 'yar masu kuɗi har haka, tunaninsu ne ya yanke a abu ɗaya "'yar Ubangidansa ce" da haka kowa yabar gulma da zuciyarsa ya shiga bawa idanunsa haƙƙinsa.
Tarba ta mutumci akayi musu ga uban abinci da naman kaji da aka baje musu a gabansu ana basu haƙuri kan su jira kafin a kawo musu amaryar, cikin jin daɗin girmamasu da akayi suka amsa da bakomai wallahi "ai jira kam dolene muyi dan dole sai an kakkaita ga uwayenta kowa tayi mata faɗa" wata yayar Umma ta faɗa cikin raha.
"Aiko Mun gode sosai da fahimta Baba" wata cousin in Mummy ta faɗa tareda barin wajan.
Nana sai zabga murmushi takeyi na asan da zamanta a wajan amma ina ba wanda ya kawo hankalinsa gareta.
Tsaf Amarya ta fito cikin kyakykyawar shigarda komai hasaadarka baka isa ka kusheba.
Aunty Lubabatu ce ta kamo hannunta tayi mata jagora har zuwa ɗakin Mummy.
Sanda akazo wucewa da ita ta main palo Naja da idanunta ke zagaye cikin palon ta hango giftawar amaryar yayan nata. Wani yawu ta haɗiya tareda jinjina kai sai kuma ta maida idanunta jikinta tana ƙarewa kayan jikinta kallo, duk saitaji ta raina kanta, itada take fankama ƴaƴanta ya saimata leshin dubu goma sha biyar sai gashi tana ganin na jikin amaryar tasu tayi laƙwas, lallai yaya ya kankaro mata daraja wajan 'yan islamiyar su, aiko duk sati zata dunga kawo musu ziyara itada ƙawayanta dan itakam taga wajan zuwa, duk zumuɗinta na yaya yayi aure ta tare a gidansa, ita da kanta bayan ganin yadda aka tsara gidan sai taji zaman cikinsa bai kamacetaba daɗinsa dai ta kawo musu ziyara ta tafi a marmarce.
Ɗakin Mummyn cike yake da 'yan uwanta, dan kowa na shirin kai amarya, Aunty Lubabatu ce ta roƙesu kan dan Allah suyi haƙuri su shiga wani ɗakin abar 'ya da uwar zasuyi sallama.
Ba wanda yaji ba daɗi dukda suma sunada haƙƙin yimata faɗa amma sun fahimci Aunty Lubabatu macece mai hikimomi da dama kuma sunga alamar gamsuwa da zancen nata a fuskar 'yar uwar tasu, haka yasa cikin raha suka fara faɗin itama ta fito kar tayi laɓe, da raha su duka suka bar ɗakin cikin fahimtar juna.
*Contact me 👇
****
*Comment*
*Vote*
*Share*
*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*