Free chapter ยท Read without an account

Free page 5

by A lady with capital *K* ยท BADRIYA

๐Ÿฆ‹๐Ÿพ *BADRIYA* ๐Ÿพ๐Ÿฆ‹


A lady with concealed gender (MX)


~Storie and written by~

*~Unknown Author๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ“–~*


*Da sunan allah mai rahama mai jin kai ina wa allah godiya daya bani ikon kawo muku wanan littafin na BERDRIYA fatan zaku Bini sannu a hankali dan jin mai labarin yake tafe dashi ina fatan yadda allah yasa na fara lafiya allah ya bani ikon gamawa lafiya๐Ÿ˜๐Ÿคฒ๐Ÿป*



*~PAID BOOK 300~*



~Little note!!!~

*Ban yadda wani ko wata ya juyamun labari ta kowacce irin hanya ba littafin BADRIYA mallaki nane sanan ka kaggen labari ne bata yadda zaiyi kama da tarihin ki ko labarin ki domun ban yishi dan cin zarafin wani ko wata ba do mun bada shawarwari ko wani korafi kofa abude take fatan za'a kiyaye nagode๐Ÿ™๐Ÿป*


*FREE PAGE* 5


*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*


Malan sule haifaffan kasar nijar ne cikekken buzu neman kudi ne ya kawo shi nageriya bayan rasuwar iyayansa matan malan sule shida cip daya taba aura daya ta rasu biyu kuma sun fita yanzu saura uku


tafarko ummusalma wadda suke kira da ummu itace matarsa ta farko da yaran ta hudu duka kuma maza sadiku, shine na farko isuhu,bilal da haruna sai ta biyu maman su nadiya data fita yayan ta biyu nadiya allah gafarta mata nadiya itace yarsa ta fari wadda da tana raye zatai shekara 20 yanzu sai kaninta sama'ila amma shi yana wajan maman sa sai matarsa ta uku maman bilki hafsatu kenan yayan ta shida hudu mata biyu maza bilkisu wadda ta kasance itace babba dan sai bayan ta fara haihuwa sann ummusalma ta fara tata haihuwar ta sanu jinkiri sosai, daga bilki a dakin sai hauwa,naima,da kuma fauziya, a maza kuna akwai sulemanu mai sunan malan suna ce masa manu sai audu wanda take goyo yanzu


Sai kuma natarsa ta hudu wadda ta fita ita bata da daya ko daga ita sai ya karo aure wadda itace matarsa ta biyar itama bata ji dadin zama da matan malan ba ummu da hafsatu inda zaman bai wani dade ba ta fita bayan fitar ta da watanni uku ta dawo wa malan da yar sa data haifa badriya inda saida aka sha daru da malan kan ya amince yarsa ce dan har saida akai masa gwajin jini sanan ya karbe ta malan bai hakura ba fa ya kuma auro jumma matar sa ta shida kuma amaryar sa yaranta biyu hadiza da gali gaba daya yayan malan goma sha hudu ne


Kamar yadda kukaga matan malan kaf dinsu basu aje komai ba sai kazanta musamman hafsatu dan dakinta baka isa ka shiga ba dan gadan da sauran suke dashi ita yaran sun karyesa baban damuwar ta kuwa shine yawo dillaliya ce ba abunda bata dillanci kullum tana yawon karbo bashi da tallata haja shiyasa malan yake kiranta da hafsatu kafar yawo a unguwa ma haka ake ce mata ta inda tafi kauri kuwa shine taci kwaskwarimar ta da dare taje dakin malan ๐Ÿ˜‚



Mai biye mata baya itace jumma amarya itama masha allah kazanta gata nan tana gwadawa duda bata jima agidan ba amma dakin ummu yafi nata kyam gani bata aje komai ba sai jin litafi da bacci abu na biyu da zaka dan yabeta akai shine gwara ita da gaba daya matan malan in ana maganar biyayya kenan

Sai uwar gida ran gida wato ummu in akwai wadda malan yake shakka to ta biyo bayan ummu ita ma dai kazantar tana kwatawa amma banda ta jiki koda baza ka sameta da kaya masu kyau a jikin ta ba zaka sameta fes ne koda zani daban riga daban ne uwar wanki kenan yaran ta ma haka tana kwatantawa ko yayane dai agidan malan ita din dole a kirata da mai tsafta amma in ana maganar gyaran gida da daki toh ita bata chiki abunda ta kware akai shine tijara da rashin mutunci bata ragawa kowa daga malan zuwa sauran matan sa abunda take da kyai ashi shine girki akwai girki kam


Sai malan malan gaba daya opposite din matan sane malan akwai stafta barshi da rowa da zafin zuciya fada da sababi abu na biyu da kowa zai shedi malan akai shine sallah da zuwa masallaci shiyasa a wanchan lokacin ake kiransa da malan anso bashi limanci ma amma shi yace sam ba wani karatu yabiya ba, sai kuma bangaran neman halal malan akwai nasa sana'oi daga zuwan sa nan ya gwada sana'oi da yawa,a da malan nada kudi abunsa sosai kan ya dan karye amma ko a yanzu ma da rufin asirin sa tinda ba'a wayar gari a gidansa ba'a ciba ko biyan bukata mai mahimmanci wanan shine malan da matansa

Cigaban labari

Yau ta kama juma'a 23/11/2023

Gidan malan a chike yake taf kai kace mutane sun san da auran tin wata daya baya yaran gidan kuwa kowa yasha A shape dinsa zal wadda iliya mai dinki ya zuba musu iri daya sak kamar anko har ita amaryar kanta sune ajikinta tana ta harkokinta dan bata masan mi ake ba sai dai bata san yadda ake kiranta ana fadin wanann ce amaryar fa sai ace ta tafi ko taga ana nunata da yatsa dake da yarinta ita ko a jikinta ma safgoginta kwai take cikin yan uwanta.

Sai matan malan suma sun goce chikin sabbin din ku nan su zakace basu bane ana ta hada hada su ba'a yar da suna aurar da ya ba sai saukewa da dorawa na tukwane ake matan malan fa ba zama


Achan bakin masallacin kandahar dake kano Benz 2023ix ce fake duwan da yazo wucewa saiya kallah ya kara dan motace da ba'a dade da yin launching din taba, a tachan gefe kusa da motar malan ne sanye da shadda sai iban ido take da gyalli kai kace ahine angon


Masallaci ya cika ya cike liman nata hudubar juma'a bayan hudubar ne kuma ya shaida bayan sallah akwai daurin aure fatan mutane zasu staya a daura tare dasu


alh habu ya bude kofa ya fito sanan ya zaga ya bude dayan barin mai zaman banza kusan minti 3 kan ya sauko da kafarsa sanye chikin takalmin sarauta wadda kallo daya zaka masa kasan ba karamin kudi bane ya siye shi sannan mamallkin takalmin ya baiyano mai martaba ne amma a shiga ta badda kama ta yadda bamai gane sa koda wadan da suka sansa sun ganshi


tare da abubakar suke tafiya a jere shi gaba daya ma abubakar baya chikin yanayin sa farga ta cikasa gaba daya yana tsoron kar wasu susan fitowar shugaban su farmake su far daya gasu su ba wani matai makai kusa ba ba dogaran ba bodyguards din haka suka dau riski dinnan bisa umar nin mai marta ba na biyu kuma ga wanan abu da suka zo kullawa

Bayan duka waliyay sun hallara da goro da kuma kudin sadakin auran bayan gama abubuwa dasuka dace aka sanar da daurin auran

*BADRIYA SULEMANU BUXU da kuma ABUTURAB IBRASHIM ZAโ€™AMOON*

a kan sadaki dubi dari lakadan ba ajalan ba masallci ya dau kabbara kafun ashafa fatiha aka fara gaishe gaishe da taya murna da fatan alkairi ga ahalin biyu an raba alewa da gore har sunyi saura saboda suma su mai martaba sunzo dashi sanan mai martaba ya bada sanar war bawa limamin daya daura auran kujerar ummra nana zan fa ya dauka


Daga chan kuma a dunguma zuwa gidan su amarya achan aka gama wuni mata nata hira masu gulma nayi masu sharhi nayi yara ko nata wasa abunsu

9:00 alhaji buba ya iso daukan amarya malan ya kira wayar jumma yace ta taho da badriya dakin sa


badriya wacce keta murmushi jin ance tazo za'atafi da ita amota ta taho baki washe to balaifi ummu a kwai da hankali wani lokacin ita malan yaba sabbin kayan badriya yace in anzo daukan ta ta bata tasa da sabon hijab dinta hadda takalmin ta shima sabo ita jinta take baya ita gaba daya

Bayan zuwan su jumma malan ya nisa yana kallan alhaji habu yace toh ga amanar badriya nan ko ba komai yanzu ita din surukar kuce


ba damuwa insha allah malan yarka bazata taba wulakan taba dan inda aka kaita bama su san haka ba alkawari nane wannan


nagode sosai allah baku ikon rike amana da kuma alkawari


*badriya*

malan ya kirata yana kallanta baki washe ta ammsa da fadin na'am malan da yake haka suke cemasa


ga sabon baba nan shi zai kaiki gun yayan ki banda kiriniya da rashin kunya sanan arage surutu ko


toh malan ae na dena ma badriya ta bada amsa cike da yarinta


yawwa yar albarka mi dami zaki kawo wa malan dinki staraba in zaki dawo


komai ma zan taho maka dashi daku dasu manu


yawwa toh ayi biyaya sanan ki cigaba da karatunki banda kiriniya


toh malan


yawwa hakan yayi to tashi kuje hanunta na na malan suka fito kofar gidan inda manya da yara suka fito rakiya ana ta bye bye badriya ki taho mana da alawa kitamo mana da biskit ki kawo mana kaza da kaza haka yaran keta ihun fada ita kuma tana ta washe baki tana na amsawa da toh


baki washe take daga ma su malan hannu har saida ta dena ganin su sanna ta maida kanta ga kallan motoci da fitilun kan titi tana ta murmushi abunta dan kusan wanan itace fitowar ta wajan gari karo na farko a haka har bacci ya dauke


ta wani katafaran hotel alhji hubu yay fakin kanya zaga baya ya dauko badriya dake ta sheka bacci abunta har ya isa dakin da suka sauka ba wanda ya hadu dashi bayan ya shiga da mai martaba yafara cin karo dashi wanda yake kishin gide sai wani babban mutun a gaban sa ya rissina saida alhaji huba ya gaishe da mai martaba cike da girmama wa da biyayya kan ya wuce wani kofa dake daga farko ya shinfide badriya akan wani makeke gado sanna ya ja mata barjo ko kalan fuskarta bai tsaya sani ba saboda sanin mastayinta ayanzu tafishi daraja nesa ba kusa ba zai iya kiranta da sarauniyar sa ba karya yayi ba sanan ya ja kofar ya rufe mata ya dawo falo shima ya rissina gaban sarki


kusan 8 minit yana fama da izza da shan kamshi irin nasu Na sarakau kan yay gyaran murya ya fara Magana ina sauraran ka *shek*

wanda ka kira da shek ya dora bayani cike da ba mai martaba girman sa abun da kanema ya sugabana allah kara maka lafiya abune mai matukar wiya inda kai tsaye zan iya cewa allah bai bamu ikon yin abu makaman tan haka ba amma saidai akwai wata hanyar mai kama da abunda ka nema sanan zata fima fiye da maganar farko sai dai hanyar nada matukar wahala amma ina da tabbcin samun nasara fiye da dayar hanyar bayan haka a kwai kalubale da dama


chike da dattako izza da mulki mai martba yace kalu bale achikin sa muke yanzu haka domun take sharadin farko na zaman du wani yarima mai jiran gado da mukai achikin wannan masarauta so inaga......๐Ÿ’…

Inaga nan zamu tsaya muma๐Ÿ˜‚ sai kuma in allah ya kaimu monday da rai da lafiya fatan zaku hutun weekend lafiya

๐Ÿค—๐Ÿ™*My people with ur lovely and sweet comments ina godiya sosai da sosai really appreciate you also kuna karan karsashi da kwarin guwa ina godiya sosai da sosai allah bar zumun ci love u all* ๐Ÿ™

*_Karku manta kuyi sharing a group's group's dinku na WhatsApp nagode da kasancewar ku tare dani taku har kullun_*


*The unknown author๐Ÿ’…๐Ÿ“–*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.