Free chapter 路 Read without an account

#24

by Aunty Mamee 路 FANSA KO 茦IYAYYA

FANSA KO 茦IYAYYA?* 馃挃


*漏锔廇untiMamee*


_Page24 _

   

   Hawa kan gadon yayi sosai hannunsa ri茩eda kofin, 茩ara 茩an茩ame jikinta tayi 茩irjinta na bugawa, bai kulata ba har ya matsa kusa da ita, tean ya 蓷ebo a cokali ya hura sannan ya nufi bakinta dashi, ba musu ta bu蓷e bakinta ya saka mata, ahaka yayita bata har ta kauda kanta gefe, ganin hakan yasa ya ajiye kofin kan bedside tareda fuskantarta.

Ita dai kanta na gefe jin kuma alamun idanunsa a kanta yasa ta muskuta dan kwanciya, da sauri ya ri茩ota da fa蓷in "karki kwanta yanzu amai zakiyi" murya a sanyaye,  runtse idanunta tayi cikin takaici wai yanzu wannan mugun ne ke juyata son ranshi har yana 茩o茩arin rabata da rayuwarta le蓳anta ta tauna cikin jin 蓷acin abun idanunta na fitar da ruwa.

Shi dai baisan me takeba dan ta juya kanta gefe amma kuma tana ri茩e a hannunsa ya茩i 蓳arinta, da yaga yamma ta kawo sosai ne ya cikata ya sauka daga gadon tareda tsayawa a saitinda take ya mi茩o mata hannunsa da fa蓷in "palo zamu koma magrib ta kawo kai ba kyau kwanciya a wannan lokacin" hawayen idanunta ta share tareda sakkowa a hankali ba tareda ta kama hannunda ya mi茩a matanba a haka harta lalla蓳a ta bar 蓷akin, sai a lokacin ya janye hannunsa ha蓷ida sosa gashin girar sa tareda sakin ajiyar zuciya Sannan shima yabar 蓷akin

 nasa 蓷akin ya nufa, kai tsaye toilet ya shiga yayi wanka sannan ya gabatar da alawala.

Jallabiya kawai ya zura a jikinsa ya nufo palon, a 茩asan carpet ya sameta ta mimmi茩e 茩afafunta Naja na matsa mata yatsun 茩afar, tsayawa yayi na wani lokaci yana kallonsu sai kuma ya shafa saman sumarsa tareda sakai yabar palon.

Bayan fitarsa ne tasa Naja ta kamata dan komawa 蓷akin dan sam batajin da蓷in zaman tafison ta kwanta, koda suka shiga toilet ta wuce ta 蓷auro alwala tana fitowa ne taji kiran sallah hakan yasa Naja mi茩a mata hijabinta ta bar 蓷akin dan yin tata sallar.

Al茩ibila ta fuskanta, da 茩yar ta idarda sallar dan wani wahalallan baccine ke nu茩ur茩usarta, tana idarwa ta 蓳ingire anan, koda Naja ta dawo ta ganta tana bacci, bata tasheta ba waje ta samu tana tilawa a hankali a haka har aka kira sallar isha, sai alokacin ta tasheta, ido rufe tace "fara ha蓷amin ruwan zafi tukuna" ba 蓳ata lokaci ta ha蓷a matan ta dawo ta shaida mata, da 茩yar ta mi茩e ta nufi toilet,  wani irin sakayau taji jikinta sakamakon gasa jikinta da tayi da 茩warinta ta fito alokacin bata samu Naja a 蓷akin ba, 

Cikin kayan baccin da suke cikin akwatin ta shirya kanta sannan ta gabatar da sallar ta, tana idarwa ta shafa man zafi tareda 蓷aukar wayarta data gani kan mirror ta haye kan gado. 

Nomban Mummy ta dannawa kira, bugu 蓷aya Mummy ta 蓷aya cikin muryar shagwa蓳a tace "Mummy saura ka蓷an yau na mutu amma ke ko ajikinki bikiji ba dan banga misscall inkiba"   

"Subhanalla! meya faru?" Mummy ta tambaya cikin kulawa amma ba ru蓷ewa ba dan tasan tayu abin bai taka kara ya karyaba amma ake masa wannan uban shelar

蓳ata fuska tayi da fa蓷in "menema Mummy bai faruba? ai yau naga zallar gaskiyar hauka wallahi"

Cikin bawa zancen mahimmanci Mummy tace "ki fa蓷amin abinda ya faru mana" 

ta bu蓷e baki zatayi magana kenan sai gashi ya shigo 蓷akin, 蓳ata fuska tayi dukda bugawar da 茩irjinta yakeyi mata "zazza蓳ine Mummy amma yanzu nawarke kuma insha Allah Ubangiji na tare dani Mummy ba abinda zai sameni da Allah na dogara dan shine gatana kuma shi zai isarmin a dukkan wani sha'anina"

"Ikon Allah" Mummy ta fa蓷a a fili dan wannan bayanin baiyi kamada bada labarin mara lafiya ba tana 茩o茩arin magana taji 蓷iff ta kashe wayar zare wayar tayi daga kunnanta tana kallon fuskar wayar, kamar ta kira sai kuma tayi wani tunanin ta barshi zuwa asuba lokacinda suke waya.

wani miskilin murmushi ya saki dan tsaf ya fahimci wannan zaurancen dashi takeyi ya kuma amsa hakan yasa ya shafa saman kansa tareda barin 蓷akin, dama ya shigone yaga ko tayi sallah, sai kuma gashi ya ganta cikin kayan bacci harda su habaici any way shi hakan is okay dama lafiyar Tata yake bu茩ata.

Wani dogon tsaki ta saki bayan fitarsa 蓷akin, 茩wafa tayi tareda gyara kwanciyarta.

Naja ce ta shigo 蓷akin hannunta 蓷auke da plate sai tururi yakeyi, 

Mi茩ewa tayi cikin fara'a da fa蓷in "sannu Naja'atu da hidima kedai Allah ya nunamin ranar auranki" kunyane ya kamata tayi 茩asa da kanta tana murmushi.

Saida ta bari ta gama cin abincin sannan ta kawo mata magungunanta, bayan tasha ne Naja tabar 蓷akin tareda yimata saida safe.

************************************A haka har jikinta ya murmure ta dawo da sabgoginta kamar da, ammanfa ta bala'in yiwa bakinta training da wankan tsarki, yadda bai fasa kunnata ba, haka bata fasa gaya masa magana ba amma bamai ciwo ba, saidai yanzu an koma da Allah, maganganun nata basa wuce "Akwai Allah" ko kuma "Akwai ran hisabi" kuma kosuma idan ta fa蓷a masa saiya gurji bakinta son ransa. 

Ranarda ta cika wata, tun da asuba ta shaidawa Mummy zataje wajan Dady yau "ki dai nemi izinin mijinki tukunna" abinda Mummy ta gaya mata kenan tareda kashe wayar a lokacin bin wayar tayi da ido, sai kuma ta saki ajiyar zuciya tareda mi茩ewa ta nufi kitchen.

Ko bacci bata komaba yau, dan tare sukayi komai da Naja, bayan sun shirya komaine taga ya fito palon ya zauna kasancewar yau weekend a gidan zai yini, harta gifta shi, sai kuma ta tsaya, jiki a mace ta dawo da baya zuwa cikin palon nesa dashi ta tsaya da fa蓷in " Yau zanje wajan Dady",  shiru yayi baice mata komaiba, saida ta 茩ara maimaitawa sannan cikin isa da aji ya furta "da izinin wa?" idanunsa a kanta.

Wani 茩ullutun ba茩in ciki ta ha蓷iye mai 蓷aci, cikin nuna ita ba komai bace ta furta "da izinin ka" ido cike taf da hawaye.

Gashin girarsa ya sosa tareda 蓷auke kansa daga gareta da fa蓷in "kin taimaki kanki"

Tsayawa tayi tana kallonsa ido taf da hawaye "shege, mugu azzalumi, mahaukaci, fasi茩i " shine sunayanda ta fa蓷a a zuciyarta sanna ta share hawayenta tareda barin wajan ta nufi 蓷akin Naja dan shaida mata sunada fita unguwa, murna ce ta bayyana a fuskar Naja danjin zasuje unguwa.

Cikin mintuna 茩alilan suka shirya, kusan a tare suka fito palon, har zuwa lokacin yana zaune a palon hannunsa 蓷auke da waya yana daddannawa.

Naja ce ta nufi wajansa da fa蓷in "yaya sai mun dawo" dakatawa yayi da abinda yake tareda 蓷ago kansa yana kallon Naja, sai kuma ya maida idanunsa gareta yana 茩are mata kallo daga sama har 茩asa ajiyar zuciya ya sauke ganin kayanda ke jikinta ba 茩aramin sa'a taciba data saka kayan danko tsaf zai sauke tafiyar dukda yasan muhimmancin inda zataje in kallonsa ya dawo dashi ga Naja dake du茩e a gabansa sai kuma ya maida idanunsa ga abinda yakeyi "zuwa ina?" ya tambaya tareda maida kansa ga wayarsa.

茒ago kanta tayi tana kallon Binazir da ta kafe yayan nata da ido tana masa kallon takaici sai kuma tayi 茩asa da kanta da fa蓷in "Aunty zan raka nima bansan ina zamuba"  

 "Bikisan ina zakuba amma shine kike zumu蓷in fita? and kin manta yau kinada hadda?" ya tambaya ba tareda yabar abinda yake akan wayarba.

ita dai shiru tayi kanta a 茩asa, batace komaiba 

Binazir kam tasan wannan wula茩ancin ya tanadesa ne badan komaiba saidan ya musguna mata ya 茩untata mata, ajiyar zuciya ta sauke tareda kallon Naja da fa蓷in "saina dawo Naja" ta fa蓷a a sanyaye tareda nufar hanyar fita.

"Tashi ki bita" Naja ta tsinci muryarsa cikin dodon kunnenta sanda yake mi茩ewa dan barin palon zuwa 蓷akinsa.

   "Ko ni kikeso na mi茩ar dake?" ya 茩ara fa蓷a wanda hakan ya tabbatar mata lallai da ita yake aiko da sauri ta mi茩e ta fita, a lokacin Binazir na dafda fita daga gate in ta fito, hakan yasa ta 茩wala nata kira.

    "wai ya akayi ya barki ?" Binazir ta tambayi Naja bayan sun fito daga gidan.

Murmushi Naja tayi da fa蓷in "ai daman Ni ba hanani zaiyi ba dake yake kema kin sani" Najan ta fa蓷a cikin kunya.

  "Ban fahimceki ba?" Binazir ta tambayeta cikin mamaki

茒an kallonta ta gefen ido Naja tayi sannan ta kauda kanta gefe da fa蓷in "Allah Aunty kinsan yau weekend Yaya zaiso ki kasance a gida amma kawai sai kika tsiri tafiya kuma kofa sallama bakiyi masaba Ni nasan haushin hakanne yasa ya huce a kaina" ta fa蓷a cikin kunyar Binazir tareda 茩ara 茩asa da kanta

"La'ilaha illallahu yanzu Naja dama sa ido kikemin ban saniba?" ta tambaya cikin sallallami da mamakin kalaman Najan.

da sauri Naja taci laya da fa蓷in "Allah Aunty ba haka bane bana sa miki ido kawai dai nayi wannan tunaninne amma kiyi ha茩uri".

Bata tanka mataba a haka har suka isa bakin titi inda zasu hau napep inda Binazir zata iya rantsuwar ta 蓷au shekaru rabonta dashi.

  "Prison fa zamuje" Binazir ta fa蓷awa Naja kalamanda suka tarwatsa zuciyarta

"Mmme me zamuyi a can?" Naja ta tambaya cikin in'ina  

"Wajan mahaifina" Binazir ta amsa mata kai tsaye, daga nan kuma ba wanda ya 茩ara magana har suka samu abin hawa auka hau .

Ita dai Naja bakinta ya kulle amma sai idanu data zubawa Auntyn tata tana binta duk inda ta nufa. 

Bata wani sha wuyaba wajan neman Dady dan yawanci an san sunasa 

Sanda taga Dadyn mamakine ya kamata ganin yadda ya koma kamar ba wanda yake prison ba, ba wani alamun shan wuya a tattare dashi, saidai kallo 蓷aya zakayi masa ka fahimci tarin damuwa lullu蓳e a fuskarsa.

  Gaishesa tayi tareda 茩o茩arin maida hawayenda yake 茩o茩arin zubo mata.

Ha蓷ida gabatar masa da Naja , sosai ya fa蓷a蓷a fara'arsa yana amsa gaisuwar Najar cikin sakin fuska tareda tambayarta mutanen gidansu.

Bayan sun gama gaisawa ne ya kalleta cikin halinsa na tsokana da fa蓷in "daughter an samu gidan miji da蓷i an manta dani" shagwa蓳e fuska tayi da fa蓷in "kai Dady kaifa kace karna sake na fara fita harsai nayi wata 蓷aya"

Ajiyar zuciya ya sauke da fa蓷in "Ni nama manta Amma hakan da kikayi yayi daidai Ubangiji yayi miki albarka daughter"

A sanyaye ta amsa da "Amin uba na gari" murmushi kawai yayi tareda sukuyar da kansa 茩asa. Suna a haka har lokacin ziyara ya wuce, kayanda ta ha蓷o kasane da aka ga hargitsawa wajan checking ta ajiye gabansa, idan mutanen wajan ta daka tareda danna masa ku蓷i cikin ledar kayan sannan ta mi茩e ta fara tafiya ba tareda ta juyoba, ganin haka yasa itama Naja mi茩ewa tayiwa Dady sallama ta nufo bayanta.

Tafiya suke zuwa 蓷aya 蓳arin inda zasu hau abin hawa anan ta ha蓷u da wani shgon siyayya ta shiga ta siyi abubuwan bu茩ata na yau da kullum ita dai Naja na binta da idanu.

" Gidanku fa zamuje mu gaida Umma" maganar ta sauka cikin dodon kunnen Naja.

da sauri ta 蓷ago kai tana kallon Binazir fuskarta fal murna, tana shirin yin magana ne wani mai Napep ya tsaya a gabansu hakan yasa Naja fuskantar shi tana fa蓷a masa inda zasuje.

"Wai ai inaji yau gidanmu yayi ka蓷an Aunty dan Umma saita kusan neman inda zata ajiyeki ta rasa daga 茩arshe dai a banka蓷a Miki labule a saukeki a 蓷aki"

duka Binazir takai mata tana murmushi "Allah ya shiryeki Naja naga a duniyannan ba wanda kika raina sama da Umma"  dariya tayi kawai sannan ta fara bata labarin dramarsu da Umma wani tayi dariya wani kuma ta naimawa Naja shiriya a haka mai Napep yabi kwatancan Naja ya saukesu a matsakaicin gidan Umma.

Lokacinda suka shiga tana tsakar gida a zaune suka shiga da sallama jin kara蓷in muryar Naja ne yasa ta mi茩ewa da sauri tana kallon hanyar shigowa sai kuma ta tsaya cakk fuska fal fara'a tana fa蓷in "masha Allah sannunku da zuwa" dan ko ba'a fa蓷aba tasan wacece tunda ta ganta da Naja.

Binazir kam sai murmushi take zabgawa Naja ma an wani sunkuyar dakai irin ba茩innan masu kawaici.

Ilai kuwa maganar Naja ta tabbata dan Umma dube dube ta farayi inda zata samar musu wajan zama daga 茩arshe dai ta nufi 蓷aki da fa蓷in  "ku shigo daga ciki dan Allah" kallon Naja Binazir tayi suka ha蓷a idanu sai kuma sukasa dariya 茩asa 茩asa.

Umma ina kasa ka ajiye sirika 蓷aya tilo ta kawowa gidan ziyara duk tabi ta rasa inda zata saka kanta ga Naja ta wani maze Kamar wata ba茩uwa, da Umma ta gaji da iskancin Najanne ta shammaceta sanda tazo wucewa ta kai mata duka da fa蓷in "zaki tashi kizo ki siyo min abu a kanti ko saina 茩arasa karya wuyanda kike karkatarwa?" da sauri Naja ta mi茩e tana sosa wajan da ta daketan da fa蓷in "kai Umma daga zuwana?" bata kulata ba ta yi waje hakan yasa Naja binta tana 蓳ata fuska. Ita dai Binazir murmushi kawai takeyi tareda tuno tata draman da Mummynta.

"Ke dan gidanku kinsan zakuzo ba saiki kirani a waya ki fa蓷amin ba? dagake har babban mutum bansan wayafi wani a cikinku ba" ta fa蓷a cikin takaici sanda suka 茩araso tsakar gidan

"Umma nimafa daga Unguwa muke har zamu hau abin hawa ya kaimu gida tace wai nan zamuzo"  

"ai shikenan" Umman ta fa蓷a tareda mi茩a mata ku蓷in hannunta tana lissafa mata abinda zata siyo mata.

Cikin 蓷akin ta dawo ta zauna suna sabuwar gaisuwa itada Binazir, sosai Binazir ke magana da Umma kanta tsaye kamar sun saba ita dai Umma a kunyace take.

"Nace Allah yasa Naja Bata Miki shirme nasan hali zama da Naja akwai gundara"

"Wallahi Umma ko 蓷aya kedai takewa haka kuma kema dan tasan itace auta, nima haka nake a gidanmu amma idan a wajene sai kiga har wani manyance ne ke zuwarmin"  murmushi kawai Umma tayi da fa蓷in "masha Allah to Allah ya 茩ara ha蓷a kanku"

 " Wai Umma kinaji anata sallama lafiya?"  ya fa蓷a lokaci guda tareda 蓷aga labulen 蓷akin.

Zaro idanunsa yayi waje Sakamakon tozali da sukayi da wadda baiyi zato ba.

     








*Contact me 馃憞

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol