Free chapter · Read without an account

#33

by Aunty Mamee · FANSA KO ƘIYAYYA

*FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔


*©️AuntiMamee*


_Page33 _


   A ƙalla ta kusan minti uku a wannan yanayin, sannan ta buɗe idanunta da suka canza launi, tareda sakin ajiyar zuciya, ta riga da tasan tabar kari tun ran tubani, ba abinda zata iyayi a wannan lokacin wanda zai goge ta'asar da ta aikata masa.

Wani tunani ne tayi, hakan yasa jiki a mace ta miƙe da ƙyar ta lalubo inda ta ajiye wayarta.

Kunna wayar tayi, ta batta ta gama loading sannan ta nemo nombansa, ta jima tana nazarin sunan tana kallon sunada shi da kansa yayi saving da hannunsa, a yanzu taji sunan nada muhimmanci gareta dukda ma'anar sunan a yanzu baida wani amfani gareta,WhatsApp inda bata taɓa amfani dashiba a yanzu ta shiga, dan yanzu taji tana sha'awar chart in , saƙo ta rubuta masa masu kalmomi guda Shida "NA SAUKA ƊAZU AN SAMU MACE" saida ta karanta saƙon sau kusan goma sannan ta tura masa tareda runtse idanunta.   

Tana shirin ajiye wayar ne, taga alaamun nomban Umma an turo mata saƙo "Naja" ta faɗa a fili cikin sanyin murya tanajin ƙaunar yarinyar da tausayinta na ratsa zuciyarta, tasan dolene Naja taji ba daɗi idan ta samu labarin ainihin abinda ya faru tsakaninta da ƴaƴanta.

  "Aunty kina ina wai? gashi har gida an fara farautar yaya kuma wallahi anja ra'ayin Umma tunda har ta amince da tayin da akayi mata, a yanzu dai so ake Yaya ya ƙara aure, dan Allah ki dawo".

Saura kaɗan ta damƙo jaririyar dake kwance kusa da ita, Allah yasa hannunta ya kauce ya damƙi gefen shimfiɗar yarinyar sakamakon wani irin amsawa da ƙirjinta, kanta, da gaɓbanta sukayi mata lokaci guda, da ƙyar ta samu ta daidaita numfashinta da yake kokawar ɗaukewa.

"Ya Allah kada ka jarabceni da abinda bazan iya ɗauka ba".   Ta faɗa tareda sakin wani irin siririn kuka, haka kawai taji zuciyarta nayi mata ƙuna da zafi ba tareda ta tantance dalilin faruwar hakan ba.

Cakk! ta tsaya da kukanda takeyi sakamakon wani tunani dayazo ranta, da sauri ta ɗauki wayarta ta shiga WhatsApp ta goge saƙonda ta tura masa, dan gani take a yanzu saƙon ba shida wani amfani kwatakwata dan haka kawai taji tana sha'awar chart Kuma da shi kaɗai, shi yasa ta zaɓi sanar masa da haihuwar ta whasapp sai gashi wai har an farayi masa zancen aure Ko idda bata gama ba? to ita mai tayiwa umma mai zafi har haka da zata yimata wannan mummunan shigar wurin? "Saboda kin tsani ɗanta" zuciyarta ta bata amsa. Girgiza kanta tayi cikin ƙunar zuciya da wani abu mai Kamada nadama da yake rugurguza zuciyarta. Hawayen idanunta da basu gama fita ba, ta share tareda kallon ɓarinda 'yarta take, wani ninkin ƙaunar 'yar tata ne tareda tausayinta ya shiga zuciyarta, tasan ta cuci jaririyar da ace tana tareda mahaifinta tasan irin gatanda zata samu ita shaidace akan hakan amma gajen haƙurinta da harshenta ya jawo musu kaɗaici da sabon maraici.  Ji tayi a yanzu mutuwar Dady ta dawo mata sabuwa, dan sai yanzu taji tayi rashi, rashi na har abada a yanzu zata iya faɗawa duniya bayan Dady da yake mahaifinta, ba namijin da yake ƙaunarta sama da shi, kuma shine zai iya cike mata wani abu daga gurbin rashin Dady.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda ɗauke idanunta daga kan yarinyar ta gayara kwanciyarta badan tanajin bacci ba saidan hakan zaisa ta samu tayi tunaninda kecin zuciyarta.

Wayarta ta ɗauka tareda tura saƙo wayar Umma.  "Ki kirani Naja'atu idan kin samu lokaci" .

Ajiyar zuciya ta sauke ta shiga kogon tunanin irin abubuwanda tayi masa, da irin yadda yake bayyana mata zafin ƙaunarsa da soyayyasa a fili amma zuciya da ɓacin rai sun haneta ganin hakan, a duk sanda tayi masa laifi ko kuma ta faɗa masa magana hukuncinda zai mata a jikinta yake ba tareda duka ko zagi ba amma idanunta ya rufe ta kasa fahimtar hakan wani al'amarine mai girma, tabbas yau ta tabbatar itace MAJANUNIYAR ba shiba. ************


Allah ne kawai ya kaishi gida lafiya dan gaba ɗaya neman rasa tunaninsa yakeyi, yana zuwa gida kai tsaye ɗakinsa ya nufa tareda faɗawa kan laifinda. Wanne irin ƙiyayya takeyi masa dahar zata kasa kiransa ta faɗa masa zuwan gudan jininsa duniya? Me yayi mata mai zafi har haka? a duk sallarda zaiyi Nafila ko farilla, baya taɓa tashi daga sallaya ba tareda ya sakata a cikin addu'ar sa ba kan Allah ya sauketa lafiya kuma a jikinsa shi yakejin ko mahaifiyarta bata yimata irin addu'ar da yakeyi mata, dan shi su dukan sune shi, shine su haka yakeji a zuciyarsa, dukda ta zaɓi rabuwa da shi amma shi ko kaɗan ba abinda ya ragu na daga ƙaunarda yake mata sai tarin kewarta data barmasa a zuciyarsa.

Bai cancanci irin wannan shariyar da hukuncin ba, ai shine uban abinda ke cikin jikinta kuma koda ace rabuwar kotu kota police station sukayi yanada haƙƙin a faɗa masa samun ƙaruwar gudan jininsa balle shi baima zaɓi rabuwar ba, itace ta zaɓi ya bata takaddata, gudun matsala ya nema musu masalaha dan yasan ta fishi iya hauka yana kuma tsoron abinda zata aikatan.

Sai ɓacin ransa na biyu yadda yaji umma na jaddada bataga amfanin tambayar abinda aka haifa ba, duk wani abinda Umman ke masa gameda Bishira bai taɓa jin komai a ransa ba gani yake ita mahaifiyace dolene taso maison ɗanta, amman a yau Umman ta bashi mamaki matuƙa gaya ga wani abu mai kamada haushin Umman da yakeji a zuciyarsa, taya za ayi a kiraki a faɗa miki haihuwar gudan jininki sannan kuma kice bikiga amfanin tambayar abinda aka haifaba dan kawai zuciyarki ta raya miki anyiwa ɗanki ba daidai ba?

Shi a iya saninsa tunda yake da ita, bai taɓa jin ta aibanta wani nasa kota wulaƙanta wani nasa ba, kuma yasan ko abayan idanunsa hakan takeyi dan bata iya ɓoye abu a zuciyarta ba, tana girmama umma fiyeda zaton mai zato wanda har mamakin hakan ya sha yi shi kaɗai dan baiyi tsammanin hakan daga gareta ba dukda ba ƙyaleta zaiyi ta wulaƙanta masa ahali ba amma ta bashi mamaki wanda hakan ya ƙara ninka darajar ƙaunarta a zuciyarsa, amma sai gashi Umma ta fara sauya ra'ayinta a kanta.

Ajiyar zuciya ya sauke tareda miƙewa a daddafe ya shiga toilet haɗida sakarwa kansa ruwan sanyi, saida yaji ya fara attishawa sannan ya kashe ruwan ya fito tareda shirin kwanciya amma sai yaji baccin ya kasa zuwar masa, kuma bayason cigaba da tunanin laifinda Ummansa da Binazir ta aikata masa dan yasan tsaf zuciyarsa zata iya bugawa muddin yasa abin a ransa wai ace ayiwa mutum haihuwa amma a kasa kiransa a waya a faɗa masa and mahaifiyarsa ta nuna haihuwar bai dameta ba? how could he hold such victim in his mind? Numfashi ya furzar tareda janyo wayansa ya kunna data dan ganin labaran duniya.

Zuciyarsa ce ta harba sakamakon sunanda ya gani a notification bar, hannunsa har wani rawa yakeyi wajan buɗe WhatsApp insa.   Wani irin hucin takaici ya fitar ta bakinsa tareda wuri da wayar, Allah yasa bata kai ƙasa a ta tsaya iya kan gadon, har yanzu tana nadamar saninsa a rayuwa kenan kamar yadda ta taɓa faɗa masa?  mene dalilinta na goge masa saƙonda yanada tabbacin zancen haihuwar ta rubuta masa? Kenan baida wata ƙima tunda har zata iya kasa faɗa masa haƙƙinsa.  Wani yawu ya haɗiye mai ɗaci tareda runtse idanunsa, Yana fitarda numfashi a hankula*****************


Washegari da safe Naja ta dauki wayar umma dan tura wa Ƴaƴanta saƙo sai taga alamun message, da har zata share sai kuma ta shiga inbox, wani irin farin cikine ya kamata, da sauri ta lalubo nombar tareda yi mata flashing.

  Binazir na zaune shiru ita kaɗai a ɗaki sakamakon babyn Aunty lubabatu ta ɗauketa ta goya a bayanta dan Binazir ta samu isasshen bacci.

Tunani ne daban-daban a ranta amma wanda yafi tsaya mata a ranta shine nasa tunanin, jita batayi wani baccin kirkiba dan duk juyinda zatayi, shi ne a ranta, haka zalika mafarkinta duka kanshi tayi, gaba ɗaya zuciyarta tayi mata nauyi, ba abinda ke ciki sai nadama da fargabar auran da Naja tace anasan ayi masa.

Ƙarar flashing inda tajine yasa ta waigowa ta kalli wayar, can kuma saita miƙa hannu da sauri ta ɗauka dan tunawa da Naja zata iya kiranta.

Kiran layin tayi, bugu ɗaya Naja ta ɗauka cikin zumuɗi da farin ciki. Sosai suka gaisa tareda tambayar lafiyar juna. ...

 "Me aka samune wai Aunty?" Naja ta tambaya cikin jin kunya.

Murmushi tayi da faɗin "mace ce mai kama dake, amma ta fiki kyau" wata dariyar daɗi Naja ta saki da faɗin "na yarda ta fini wallahi, ai kyaune ya haɗu da kyau"

"Allah ya shiryeki" Binazir ta faɗa sai kuma kowa yayi shiru.

Ajiyar zuciya Binazir ta sauke da tambayar "mene sanadin mutuwar NAFISA da labarinta?" 

Wani irin bugawa ƙirjin Naja yayi wanda Saida ta waiga ko zataga wani kusa da ita , ajiyar zuciya ta sauke da faɗin "yaya ne ya faɗa miki akwaita ko?" Ta tambaya kamar mai raɗa.  Cikin son jin cikakken labarin Nafisar ta amsa da "umm".

Ajiyar zuciya Naja ta sauke "Yaya tace ita nakebi, Yaya yanasonta fiyeda Ni, dan yace tafi ni kyan hali, kuma da gaske hakanne dan bata taɓa musawa ko saɓawa umarnin Yaya ko Umma ba, saɓanin ni wanda hakan ya haifarda tarin soyayyarta a cikin zuciyarsu Kuma tanada rauni sakamakon ciwon ASMA da take dashi" 

"Inaji ci gaba" Binazir ta faɗa danjin Naja tayi shiru.

"Nafi shine sunanda Yaya ya samata wanda yabita kowa da kowa yake kiranta da hakan.

Wata rana ne wata ƙawarta tazo har gida neman izini wajan Umma kan ta amince Nafi ta rakata gidan yayarta amso saƙo, da Umma kamar bazata bari ba, amma ganin yadda ƙawar ta tako har gida tana neman izini yasa Umman amincewa da sharaɗin kada su jima.

Da shike itama tanason fitar haka ta shirya cikin farin ciki ashe tafiyar tata kenan daga gidannan ba dawowa" Naja ta faɗa cikin raunin murya amma taƙi bari tayi hawayen da keson tarar mata dan tanada taurin zuciya.

  "Innalillahiwainnailaihirrajiun, hasbinallahu wa ni'imal wakil" Binazir ta faɗa cikin rawar murya.

 "Kamar yadda ƙawarta ta faɗawa Umma, suna zaune gidan yayarya saita miƙe da cewa ƙawar Yanzu zata dawo taga wani fili mai kyau tanason yin hoto a wajan kasancewar unguwar duk yawanci filayen ne saɓanin namu unguwar dake cike da jama'a.

Wai jin shiru bata dawoba shine yasa ƙawar fitowa tana nemanta, a wajan wani kewayen fili ne taji kamar ƙarar waya hakan yasa tabi sautin tana zuwa taganta yashe numfashi baya fita a yadda ta faɗa wai ta koma da gudu gidan yayarta, shinefa suka dawo kiɗime harda wasu maƙotan ta kuma har lokacin wayar na ringing Shine wata tayi jarumtar ɗaukar wayar, ta kuma faɗi halinda Nafin ke ciki..." Naja ta faɗa a hankali dan ji takeyi zuciyarta nayi mata wani irin ɗaci kamar yanzu abin yake faruwa.

 "Ya akayi kuka sani? Ya akayi yayanki yaje wajan?" Binazir ta tambaya murya a raunane.

Numfashi Naja ta ja sannan ta cigaba.

  "Lokacinda umma ta shiga ɗaki taga inhalern Nafi, cikin tsoro ta kirani ina ɗakin yaya ina masa bincike kozan samu kayan kwaɗayi, banso ba na tawo ina ɓata raina, inajin abinda Umman ke faɗa nayi saurin faɗa mata kawai ta kira Nafin ta cemata ta dawo gida gudun matsala. da sauri Umman ta bani wayarta kan na kirata amma inata kira bata ɗauka ba hakan yasa Umman tace na kira Yaya na faɗa masa abinda ke faruwa ba yareda ya ce komaiba ya kashe wayan, munsan ita zai kira hakan yasa muka dakata da kiran layin nata, shikuma yaci gaba da kiran layin nata har akaci sa'ar wata mata ta ɗauka shine ya umarceta da kada a taɓata a barta har saiya ƙaraso. wannan shine duka labarin mutuwar Nafi, bayan sadakar bakwai  Yaya ya roƙi Umma da kada a ƙara labarin Nafi a gidan har saiya gama binciken wa'yanda suka aikata hakan gareta, nima kuma ya haneni da zancenta ya kuma lallashemu kan muci gaba da yimata addu'a amma muyi haƙuri da labarinta har zuwa sanda zai gama binciken mutuwar."

Naja ta ƙarasa murya a sanyaye.

 "Me yasa bayason zancen nata?" Zancen ya suɓuce mata ba tareda ta shirya hakan ba.

"Ban saniba amma munfi zaton kawai bayason a dinga zancen ne saboda ransa zai dinga ɓaci ya kuma zargi kansa a matsayinsa na mai binciko mai laifi ya kasa binciko wanda ya aikata mata hakan ya kuma hukunta suba". Najan ta faɗa a hankali.  

Shiru sukayi kowa da abinda ke saƙawa a zuciyarsa.

  "Anuty dan Allah ki dawo wallahi Bishira ban yarda da itaba ba haka kawai tabar Umma ba, dan wallahi Umma ta matsa lallai Yaya saiya aureta" Naja ta faɗa dan kawarda raunin da keson shiga zuciyarta na gameda labarin Nafisa data faɗawa Auntynta.

Ajiyar zuciya Binazir ta saki murya a sanyaye tace "ina muku ta'aziyar mutuwar NAFISA ku duka Ubangiji ya gafarta mata yasa kuma ƙarshen wahalar kenan, shikuma Allah ya tabbatar da alkairi tsakaninsa da Bishiran" tana gama faɗa ta kashe kiran tareda kashe wayar gaba ɗaya tai jifa da ita sakamakon wani irin ɗaci da zuciyarta tayi mata, kukanda take ƙoƙarin riƙewa ne ya kufce mata, kuma haka ta sakeshi. badan zuciyarta ta huce ko kuma kukan ya isheta ba, jin sautin Muryar kukan halittarda ta kasance mafi soyuwa a gareta ne yasa ta share hawayenta dan tasan yanzu Aunty Lubabatu zata shigo ɗakin.

Naja kam wayar hannunta tabi da kallo bayan ta cireta daga kunnenta, ƙara danna layin tayi dan sakeyi mata Flashing, amma sai taji layin a kashe, hakan yasa ta cire wayar a kunnanta ta fita tsakar gida dan jin Muryar Umma na kiranta.








*Contact me 👇

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.