Free chapter · Read without an account
7
🌹 SHEIKH IMAM🌹
By
YAR LELEN ROYAL STAR
Page .....7
Turarensa na Viktor &Rolf Flowerbomb Haute couture da ya zauna masa a jikinsa y kara fesawa, leather slippers masu kyau ya sa, cikin natsuwa ya fito daga bedroom nasa, bai tsaya a parlournsa ba ya wuce k'asa, kofar parlon gidan gaba daya ya bude ya fita , securities ne ta ko ina suna ta zagaya gidan, bai tsaya a tsakar gidan ba sai ya nufi get, tun kafin ya karasa Mai gadi ya bude masa get din gidan, hakan yasa ya fice , kai tsaye masallaci ya nufa, cikin natsuwa ya cire takalminsa , yasa Kai cikin masallacin , daga chan gaba gurin da aka tanadar domin ajiye littafai ya karasa, bude glass din da akai domin adana littafan ya yi, Al-qur'anin da shigowarta ta ci karo da shi a cikin masallacin ya mayar gurbinsa.
Gefe daya ya koma, da hasken wayarsa yay amfani gurin haskaka masallacin, ya fi 1 yana zaune , yana karatun Al-qur'ani a zuciyarsa, lokacin da zai Kai karshen suratul Ankabout lokacin Sallah ya yi, addu'a ya yi , ya shafa , a hankali ya Mike Kiran Sallar farko ya yi, bayan wani karamin lokaci ya kira Sallah, sai a sanan mutane suka fara fitowa.
..
Bakwai dai² ya fito cikin shirinsa tsaf, kamar kullum dai sanye yake da Jallabiya fara, bakin takalmi, sumar Nan ta ji gyara ta kwanta luf a kansa, hannunsa kuwa kamar kullum dai Agogo ce mafi k'ololuwar daraja wato Rolex watch, sai baza kamshin turarensa ba Viktor&Rolf Flowerbomb Haute couture da yake.
Kamshin turarensa da karar takun takalminsa ne suka fara shaidawa mazauna parlourn isowarsa, cikin natsuwa ya sauko, idanunsa like da farin siririn eyeglasses mai kyau irin na Manyan likitoci , masu ji da boko.
D'ago da idanunsa yay ya kalli Ummie da take masa magana, muryarsa a tausashe yace "Barka da safiya Ummie", ya fada a hankali, murmushi tayi tare da cewa "barka dai Sheikh, tea za'a kawo ko coffee .?", Agogon hannunsa ya kalla, Yana cewa "Ummie yau Litinin", dafe kanta ta Dan yi, a hankali ta Dan daki kanta da yatsun hannunta, "shaf na manta," jinjina mata kai ya yi ba tare da yace komai ba.
Ya dan jima a gurin kafin ga kalleta, cikin natsuwa yace "Ummie akwai abun da kuke so ?, "Shiru ta dan yi kafin tace "Ina Jin kamar fruits ne kawai babu a gidan, Amma komai akwai, don na watan baya ma ba'a fasa ba", girgiza kansa ya yi, kafin yace "ki fitar da wanchan ki bayar, za'a kawo sababbin", Yana fada ya fice, bin bayansa tayi da murmushi tana sa Albarka.
A Fili tace "oh mutumin Saudi, ya saba da ganin duk karshen wata an fitar da kayan da ba'a ci ba an bayar, to ubangiji ya kara rufa Asiri, " ta fada tana mikewa, store dinsu ne , kaya ne sosai a cikin store din, don buhunhunan shikafa kawai sun fi goma, carton² na taliyar, makaroni, cous², noodles, su doya, dankwali ,da sauran kayayyaki.
Baxa ta iya fitar da su ba, dole tasa ta je ta nemi taimakon Yan aikinta da suke mata aiki, Wanda basa shigowa side nata sai zasu yi aikinsu, shima shara ne sai mooping parlour, da sauran gyare², Amma ita take musu Abin ci da duk wani abun buk'ata Wanda bai fi karfinta ba.
Fiffitar da kayayyakin da suke ciki gaba daya suka yi, hatta da kayan cikin fridge duka aka fitar, rarrabawa Yan aikin ta yi, sauran kayan kuma ta bayar a raba a chan wajen Anguwa inda suke da mabuk'ata....
JAMVALY HOTEL RESORT KATSINA.
Room â„– 5 VIP side.
Zaune take cikin room din ta kure kanta chan kuryar d'akin, cikin Yana yin fita hayyaci take goga hodar ibilis din da take cikin wani dan plate din glass da yake hannunta, idanunta sun yi jaazir sosai a'lamar tana cikin matsanancin b'acin rai, shakar cocaine din take tana karawa, bata damu da yarda yake shiga jikinta ha burinta kawai ya bugar da ita, sai da ta shak'ata sosai kafin ta koma chan kan bed din room din ta fada, ribbon din da aka sa aka rike kitson attachment din da yake kanta ta zare, tare da baza gashin nata, a pillow ta sa kanta, tare da baza gashin nata, kwanciya tayi amma sam kwanciyar ta kasa mata dadi, tashi ta yi zaune shima zaman ya gagara yi mata dadi, tashi tayi ta fice a d'akin tana tafiya tana layi cikin fita hayyaci...
Katsina psychiatrist hospital Gabas III.
Ciki natsuwa yake tafiya cikin Asibitin, wasu Doctors ne biyu mace da namiji, namijin na kusa da shi sai macen na dan bayansu kadan, tafiya suke suna dan tattaunawa, sai dai maganganunsu duk sun fi yawa, bai fiye magana sosai ba, sai dai ya jinjina kai ko ya lumshe iso ya bude, karshen amsar da take basu ita ce "eh , aa, uhmm, uhmm²", su kenan amsoshin, da haka har suka karasa jerin gwanon ofisoshin Likitocin cikin Asibitin, daga nan ma tafiya akai mai dan tsayi kafin a k'araso wasu jerin sababbin office, Wanda da gani sababbin yi ne, wata kofa suka karaso in da a bakin kofar aka sak'ale wani dan allo Mai kyan gaske, an rubuta 'Dr Muhammad Aleeyou Imam ', in bracket kuma aka rubuta (Sheikh Imam).
Da sauri dayan Dr din yasa key ya bude cikin office din, da sallama sannan da addu'o'i a bakinsa suka shiga office din da ya gama tsaruwa sosai, office din kamar parlour, don wata lafiyayyiyar kujera ce Mai kyawun gaske doguwa aka sa , chan gefe kuma kawataccen table ne da yake kallon kofar shigowa, kujera ce irin Mai juyawa a bayansa, sai daga gefe loka ce ta ajiye files , ga tulin files a ciki.
Duk da daga wata sai wata a watan ma bai fi yay zuwa biyu ko ukku ba, amma komai na nan kitse, kamar yana nan.
Ja masa kujera Dr din ya yi ya zauna, shi Kuma ya zauna a kujerar da yake gabansa , dayar Kuma ta zauna a doguwar kujerar da take chan farkon shigowa.
Lumshe idanunsa yay, Yana saurarar yarda likitan yake kora masa bayani akan cutar wata Yarinya da aka kawo musu, sai da ya gama masa bayani tas, ya ajiye files na yarinyar, gyaran muryar ya yi, a'lamar dayar ma ta ci gaba da nata bayanin, cikin natsuwa da yanga itama ta fara nata bayanin, sai da ta gama itama ta ajiye files nata, a tare da dayan likitan suka fita.
Jan yo files din ya yi ya dudduba, sai da ya nazarci komai sosai, kafin ya tattarasu ya ajiye , system nasa ya fara daddanawa cikin natsuwa, kaco kam Kuma hankalinsa da natsuwarsa ya mikasu wa abun da yake da a'lama yana da matukar muhimmanci, don Sallah ce kawai abun da take tayar da shi a gurin, har maraice tayi.
5pm
Maraice lilis ya fito daga cikin office nasa, anan ya tarar da Drs , gaisawa suka yi , da sauri massager nasa ya karbar masa brief case nasa, suka fito , a mota ya sa masa kayansa kafin ya kara so, yana zuwa yasa hannu a aljihunsa, wallet nasa ya fitar, dubawa yay , fasar da numfashi ya yi, ganin babu naira ko daya a cikin wallet din sai dollars, kallon mutumin da yake gefensa yay wanda yake Jira a miko masa ya cikawa wandonsa iska , rasa yarda zai yi ya yi, sai kawai ya d'ibi dollars din da shi kansa bai San nawa bane saboda yawansu ya mika masa.
Da sauri mutumin ya karb'a yana kallon kudin , murna ya fara Yana masa godiya kamar zai duk'a masa, don shi tunda Allah ya haliccesa bai tab'a ganin dollar ido da ido ba sai yau , Kuma wai gashi mallakinsa.
Bai bi ta kan godiyar da yake masa ba, don shi bai bayar Dan a gode masa ba, ya bayar ne don a godewa Allah, da sauri securities nasa suka bude masa mota ya shiga, rufewa aka yi suka tafi. Wayarsa da take cikin aljihunsa ya fita, zubawa number Asrat da ya jima da tura masa sak'o ido ya yi, bayan ya gama karanta sak'on ya mayar da wayar ,
Har sun wuce ta gurin Suhal Store, ya bawa Drivern da umarnin komawa, a kawataccen parking lot din Sahal store suka yi parking, in da tulin motoci birjik suke, Bude masa mota aka yi, ya Kai 5 minutes kafin ya ziro k'afafunsa.
Idanunsa da suka dan fada ya lumshe , lips din sa da yake a bushe a'lamar Yana Jin k'ishi ya taune, kafin ya fara tafiya cikin natsuwa da dattaku, tun kafin ya shiga cikin store din yake Amsa gaisuwar mutane, sannan Kuma Akai waje da mutane da yawa , saboda ya samu natsuwa yin abun da yazo yi cikin Kamala.
Cikin store din ya shiga, Yaransa na bayansa suna take masa baya...
Hadadiyar mini Cooper red colour ce ta yi parking a lot din, ta Saman motar ta fito, sanye take da wasu bakaken kaya riga da miniskirt rigar iyakarta cibiyarta, ta bayyana mata cibinta da kuma waist chain for women gold body belly chain.
Classic anklet bracelet leg chain jewelry ne daure a kafarta ta dama , kafarta sanye da ladies fashion high heel casual leather shoes_black , tayi kyau sosai Kuma shigar ta bayyanar da asalin farar fatar jikinta da take wani shek'i, black p-cap ne a kanta , kafadarta ta haggu na rataye daMouawad 1001 nights diamond purse Mai kyawun gaske, sai tsadaddiyar agogonta da ta dace da tsintsiyar hannunta.
A hankali take tafiya , ta Dane idanunta da Sunglasses, tana tauna chewing gum cikin ja aji da yanga, tafiya take fuskarta a haÉ—e, sai dai duk da hakan bai hana kyan da tayi kasa bayyana ba.
Sai da ta zo zata shiga, Security din gurin ya tsayar da ita, a hankali ta zare glass din da yake idanunta, da idanunta masu dauke da manya Manyan eyes ball bak'ak'e ta watsa masa.
Bata duba tsufa da darajarsa ba ta ware hannayenta tare da watsa masa mari, wanda yasa ya dafe gurin da ta maresa, tsaki ta ja tare da shigewa ciki.
Idanunsa da suka kad'a suka yi jaazir ya zuba mata har ta shige, murmushin bakin ciki yay, cikin kaushin harshe da riketa a zuciyarsa ya furta "in sha Allah sai kin yi nadamar wulakanta Dan Adam, sannan sai kin yi kuka marar yankewa, sai kin so yin nadama a lokacin da bata da amfani a gare ki, sai kin wulakanta, sai kin gwammace dama a wani jinsi aka halicce ki ba Dan Adam ba", ya fada yana komawa ya zauna gurin daka tanadar domin zaman masu tsare gurin, zuciyarsa kuma cike da kunci.
Tana barin gurin ta mayar da glass din ta, tana Jin kanta a wani sama, dama Kuma ga abun da ta sha bai gama fashe mata ba.
Bangaren jewelry ta nufa , nan ta shiga zabar top expensive waist chain for women gold body belly chain da classic anklet bracelet leg chain jewelry masu kyan gaske ta zab'a,Gurin biyan ta nufa, tana zuwa ta bayar da ATM card nata aka cire kudin..... kanta a kasa take tafiya so bata iya ganin abun da yake faruwa gabanta ma ba sosai take kallo ba, zuciyarta ce ta ji ta tsinke take kamshin turaren Viktor&Rolf Flowerbomb Haute couture, ta ji ya cika mata hanci, a hankali ta dago da dara²n idanunta, kai tsaye a bak'ar sumar kansa da take kwance ta sauke idanunsa, bata iya ganin fuskar wanda take gani, amma daga ji shi ne mamallakin wannan kamshin turaren mai dadi da ta ji ya cika mata hanci.
Tsare bayansa da idanu tayi, dai² lokacin ne kuma ya juya bayansa, Cikin kad'uwa ta zubawa masa idanu tana kallonsa, da manyan idanunta, cikin natsuwa ta taka in da ya ke, cikin harshen turanci ta Mai magana, sai dai bai juyo ba balle yay mata magana, sai da tayi sallama kafin ya Amsa mata duk da haka bai yi magana ba, don sallamar ma don ta zama dole amsata ga ko wanne musulmi shi ne kawai dalilin da yasa ya Amsa mata, gabansa ta koma tana murmushi tace "SHIEKH IMAM ko?", Ta fada tana kallonsa da murmushi a fuskarsa, kallo daya yay mata ya dauke kansa ba tare da ya Amsa mata tambayar da yay mata ba, don shi ba mutum ne Mai yawan magana ba , musamman ma da mata, hakan yasa bai ce da ita komai ba, "Sunana Maryam Muhammad (Asneeeh) ya ga Gwamnan Garin nan ", bai kalleta ba sannan bai Amsa maganar ta ta ba.
Sai ma ya chanja hanya tare da ci gaba da siyayarsa, Yana zubawa a kwandon da daya daga cik Yaransa yake ja.
Sai da suka gama, ya mikawa Yaron ATM nasa, shi kuma ya yi hanyar waje, cikin sauri ta je gabansa, "Yallabai in ba damuwa a bari na biya kud'in wannan soyayyar", ta fada tana kallonsa, daga sama har k'asa ya kalleta tare da dauke idanunsa a kanta, ba laifi tana da dan kyau, gashi bata yi shigar banza ba doguwar rigar Abaya ce a jikinta tayi rolling da dankwalin abayar, Wanda y Kara fito da asalin fari da kyanta.
Ficewa ya yi ba tare da ya kulata ba, haka ta ringa binsa tana masa magana, sai da ya shiga mota tace, "zan iya samun number ka don Allah ?", Ba don ta Kai ko don ta isa ba, ba Kuma don ta birgesa. Ko wani Abu ba sai dai don girman abun da ta hadasa da shi, compliment card nasa ya bata, karb'a tayi tana godiya kamar zata mai sujud.
Lokacin da suka kama hanyar gida shida saura, lokacin da suka karasa lokacin Sallah ya yi, hakan yasa sai da ya fara tsayawa a Masallacin ya yi Sallah kafin ya shiga gida.
Zaune ya samu Ummie da Amaya a parlour suna kallon wa'azinsa a TV, cikin kauna da tausayi tace "Barka da shan ruwa Sheikh", ta fada tana kallon bakinsa da ya bushe a'lamar Yana tare da matsanancin k'ishi, a hankali yace "barka Ummie", ya fada yana shigewa ciki.
Bai tsaya a parlournsa ba, sai ya wuce ciki, wanka ya yi tare da wanke baki, yasa wata jallabiyar , ya fito jikinsa na baza kamshi, dining room ya nufa don yasan already an gama shirya masa abun buk'ata......
YOUR ƳAR GABAN GOSHI 😂.
YAR LELEN ROYAL STAR......