Free chapter · Read without an account

6&7

by Aishatu Abdullahi Idris · Sawun Giwa

*SAWUN GIWA*

_Ya take na Raƙumi_




_By_

*Aishatu Abdullahi Idris*

_REAL ESHAA_




*F-R-PG 6&7*

Cikin wani irin yanayi na tsananin azaba da raɗaɗi ya dafe gefen kansa da hannunsa na dama wanda yaji yana barazanar tarwatsewa gida biyu kana cikin dauriya da jajircewa ya nufi kanta yana Isa ya sanya hannun sa na dama tare da rintse idanunsa da karfi kana ya furta.

_“Bismillahir Rahmanir Rahim,Hasbiyallahu La'ilah ha'illahuwal alaihi tawakallatu wahuwa rabbul arshil azeem”_.


Yana Ida addu'ar ya sanya hannunsa na dama ya fisgota da karfi tare da wurgata da jikin bango kanta ya bugu da jikin karfen plasmer atake wajen ya loɓe...


 Wani razanen'niyar ƙara ta sanya wanda yasa ɗakin amsa suwwan muryanta daya girgiza ɗakin kana ya firgitar da duk wani mahaluki dake numfashi kana ya razanar da duk wasu dabbobi da mutane dake cikin gidan.

Cikin rauni da azabebben raɗaɗi daya ratsa hannunta ta sulale kasa Tana wani irin gurnani mai kama da magagin mutuwa.


  Azabure ta yunƙura da ƙarfi ta Miƙe kana ta nufi kansa gadan-gadan tana cigaba da gurnani tamkar zakanya yatsun hannunta ta ware atake suka Kara tsayi da tsini tamkar mashi kana idanunta suka sake sauya launi izuwa kore da ja babu alamar fari acikinsu.

Sir Abdallah kuwa tsayuwar sa ya gyara babu alamar tsoro ko karaya atare dashi ya tsira mata manyan idanunsa ganin yanda ta dumfaro kansa gadan-gadan tana wani irin gurnani mai firgitarwa yasa ya cigaba da karanto addu'oin neman tsari...


   Tana Isa gabansa ya sanya hannunsa na dama ya shaƙe wuyanta da ƙarfi tare da zaunar da ita aƙasa cike da jarumtaka yace.

_“Allahu la'ilah ha'illah huwal hayyul ƙayyum lata'ahuzuhu sinatu walau nau lahu mafissamawsti wama fil'ard manzallazi yashfa'u indahu Illah bi'izni ya'alamu ma bayna aydihim wama halfahum Wala yuhiɗuna bi'shay'in Min ilmihi Illah bima sha' Wa'asiyya kursiyyuhus samawati wal'ard Wala yahiɗuhu hizbuhuma wahuwal aliyul Azim”._


Wani razanen'niyar ƙara ta saki akaro na biyu wanda yafi na farko rugugin tashin hankali.

Agalabaice ta yunƙura da niyyar tashi cikin sauri ya sanya tafin hannunsa ya maidata ta zauna tana wani irin numfashi da gurnani.


Rintse idanunsa yayi da ƙarfi kana cikin dauriya ya zuba mata manyan idanunsa masu kaifi da kwarjini yace.

“Wacece ke!,mekike buƙata meyesa kika shiga rayuwar mu!!?”.

Ɗago kanta tayi tare da watsa masa wani kallo Amma batace komai ba.

Jijjigata yayi da ƙarfi kana cikin tsawa yace.

“Wacece ke!, me kike bukata atare damu!!?”.


  Wata mahaukaciyar dariya mai kama da kukan jaki ta sheƙe dashi akaro na farko amma batace komai ba sai zazzare ido da take tana ƙoƙarin janye hannunsa acikin nata.

Cikin wani irin karfi ta fisge hannunta na dama dake rike da nasa ta ɗaga dogon yatsanta ma nuniya ta caka masa ahannunsa aruɗe ya janye hannunsa cike da azaba yake kallon yanda wajen ke tsirtar da jini lokaci ɗaya hannun ya kumbura ya fara sauya kala.


Ganin haka yasa ta sake kece da wata mahaukaciyar dariyar kana ta miƙe da karfi ta bugi kasa da ƙafarta na hagu tayi sama tana jujjuyawa tamkar tsuntsuwa cike da al'ajabi yake kallonta hannunta ta ziro dai-dai saitin idanunsa daya tsira mata da niyyar tsiyayewa.

Cikin hanzari ya tsugunna ƙasa ta samu jikin kofar falon atake wajen ya bule yana fitar da koren hayaƙi da wani irin mamaki yabi wajen da kallo ganin yanda ya ɓule kafin ya Ankara ta sake kawo hannunta ta dai-dai maƙogoronsa azabure yayi saurin tsugunnawa amma tuni ta samu bayan wuyansa ta yanka da wani irin sauri ya kalleta dariya ta sheƙe dashi tare da cewa.

“Tabbas kayi Kuskuren shigowa cikin abinda bai shafeka ba nayi alƙawarin gana maka azaba mai raɗaɗi tunda ka shigo gonata”.

Afusace ya ɗago kansa hannunsa na hagu na dafe da ƙeyarsa yace.

“Ƙarya kike ke baki isa kiyi abinda Allah baiyi ba saina tarwatsa duk shirin ki sannan na kawo ƙarshen zaluncinki”.

Dariya ta sheƙe dashi kana tace.

“Tabbas jarumtakar ka ta burgeni ɗan saurayi sai dai ka sani agabana tamkar ɗan tsiyako nake ganin ka abisa wannan taurin kai da neman gogawa dani dakake ƙoƙarin yi kuwa nayi alƙawarin gana maka azaba mai raɗaɗi!”.


Ta ida maganar tare ɗaga hannunta na hagu sama atake wani karamin ƙoƙo ya sauƙo hannunta mai ɗauke da farin abu kamar kumfa tasanya ta damƙi abin kana ta watsa masa ahannunsa da ƙeyarsa inda ta cakesa atake duk inda abin ya taɓa ya fara fitar da farin kumfa yana tarwatsewa.


Rintse idanunsa yayi sakamakon wani azabebben zafi da zugi daya ratsasa kallon abin yayi wanda ke kama da gishiri hannunsa ya kai saitin idanunsa dan tabbatarwa ko gishirin ne da sauri ya kalleta ganin tabbas gishiri ta watsa masa akan raunin data masa.

Cike da taƙama ta sauƙo ƙasa tare da tsayawa akan ƙafarta na hagu ta sheƙe da wata mahaukaciyar dariyar daya sanya duk wani abu na tangaran ko glass dake cikin falon tsagewa ya tarwatse a ƙasa.


Hannunta ta buɗe atake faratunta suka sake tsayi da tsini fiye da tunanin mai tunani ganin haka yasa Sir Abdallah zabura ya Miƙe kana cikin dakewar zuciya da rashin tsoro atake zuciyarsa ta tuno masa da aya ta (102)dake cikin Suratul Bakra numfashi ya fesar tare da fin cikota yakai bakinsa dai-dai saitin kunnenta kana ya fara furta.

_“Wattaba'u Ma tattalush Shayadinu ala mulki Suluiman,Wama kafara Suluimana Wala kinnash shayadina kafaru wayu'allimunan nasas sihra Wama Unzila alal Malikaini bi babila haruta wamarut,Wama yu'allimuni min ahadin hatta yakula innama nahnu fitnatun fala takfur,Fayata Allamuna minhuma ma yufarrikuna bihi baynal mar'i wazauji,Wama hum bidarriyna bihi min ahadin Illah bi'iz Nillah,Waya ta Allamuna ma yadurruhum Wala yanfa'uhum,Wala Ƙad alimu limanish tarahu malahu fil akhirati Minal khalki,Wala bi'isa ma sharau bihi anfusahum,Laukanu ya'alamun”._


Aruɗe tayi ihu kana jikinta yashiga ɓari yana fitar da zufa tamkar ba AC afalon cikin sarƙewar murya da azaban dake ratsata tun daga ƙwaƙwalwar kanta har zuwa tafin ƙafanta kana cikin rauni tace.

“Wayyo zafi kana ƙonani ka bari kana yimin lahani ka cire hannunka daga jikina kada ka lalata min jiki”.

Numfashi ya fesar kana cikin tsawa yace.

“Ki bani amasa wacece ke meyesa kika shiga jikinta kike cutar da ita!?”.

Cikin haki da fesar da numfashi tace.

“Zan faɗa!,Zan faɗa!!, amma ka daina ƙonani kana lalata min surar jiki”.

Wani kallo ya watsa mata still yana riƙe da wuyanta yace.

“Kin tabbata?,idan har kika ce zaki yaudareni zan ƙona ki da izinin Ubangiji”.

Kai ta girgiza cikin haki da rawan murya tace.

“Nayi alƙawari zan faɗa maka bazan yaudareka ba”.

Kallon Ammie da Gimbiya Fa'izah dake yashe babu alamar numfashi atare dasu yayi laɓɓansa na ƙasa ya cije cikin dakewar zuciya da rashin tsoro ya furta.

“Muddin kika yaudareni,ko kuma karya min alƙawari zan shayar dake mamaki”.

Kai ta gyaɗa cikin tsananin azaba kana da raɗaɗi ta risinar da ƙwayar idanunta tare da cewa.

“Na amince”...


  Acan ɓangaren Imraan kuwa sai da ya idar da sallar isha'i ya fita daga masallacin kai tsaye jikin motarsa ya nufa cikin rashin kuzari ya buɗe gaban motar ya shiga mazaunin driver ahankali ya jinginar da kansa jikin kujeran ya lumshe idanunsa tare da fesar da numfashi yana jin yanda bugun zuciyarsa ke ƙaruwa fiye da kaso Cassa'in da Tara cikin ɗari Fatansa ɗaya kada wani abu ya samu ƴar mutane idan har wani abu ya sameta yayi alƙawari ba zai ƙyale Lateefa da Meenah ba saiya ɗauki matakin daya dace.


Ahankali ya buɗe idanunsa dake lumshe jin vibration ɗin wayarsa daya karaɗe motar ahankali ya ɗago wayar ganin sunan Wife na yawo a screen ɗin wayar yasa yaja siririn tsaki tare da ajiyewa Kiran na katsewa wani ya sake shiga ƙin kallon wayar yayi.

Ƙaramin wayarsa ya dauka tare da dearlin number Baba amma switch off ya kira yafi sau uku amma duk amsa ɗaya suke bashi akashe. Iska mai zafi ya furzar daga bakinsa kana ya yiwa motar key kai tsaye cikin gari ya nufa yana Isa babban Cros yayi parking motarsa tare da ziro kafarsa na dama ya fito kai tsaye inda ake gasa gashash-shun kaji ya nufa ya siya guda biyu bayan ansa masa aleda ya juya kana ya shiga wani Mall ya siya Faro water da 5alive da Freshyou ya fita har ya nufi motarsa ya tsaya tare da juyawa ya tsirawa wani Boutique ido haka nan wani Maroon abaya dake cikin wani farin glass ya ɗauki idonsa yakai minti biyar yana kallo daga ƙarshe ya nufi cikin Boutique din kamar ba laka ajikinsa yana shiga ya nuna Abaya mai shagon ya faɗa masa kuɗin atake ya masa transfer kasancewar babu cash ahannunsa godiya mutumin ya masa tare da miƙa masa.

Anutse ya fita daga Boutique ɗin yana Isa wajen motarsa ya buɗe gefen mai zaman banza ya jefa ledar kana ya shiga mazaunin driver ya yiwa motar key.


Anutse yake driving ɗin kana yana cigaba da kiran layin Baba amma har zuwa lokacin akashe yana Isa hospital ɗin parking motar yayi ya fita kana ya buɗe ɗaya side ɗin ya ɗauki ledan kajin ya shiga zaune ya samu Indu gefen Neenah da har zuwa lokacin bata farka ba.

Ahankali Indu ta ɗago kai ta kallesa cikin sanyin murya tace.

“Sannu da dawowa”.

Kai ya gyaɗa mata yana kallon agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa yace.

“Har yanzu bata farka ba?”.

Kallon Neenah Indu tayi idanunta cike da ruwan hawaye ta gyaɗa masa kai tare da faɗin.

“Eh Yah Imraan har yanzu shiru bayan fitar ka na Kira Dr yazo ya sake dubata yace in sha Allah ba matsala lafiya zata farka”.

Numfashi ya fesar tare da Jan kujera ya zauna gaban gadon kana yace.

“Kinyi sallah?”.

Kai ta gyaɗa masa tare da gyara zamanta tace.

“Eh nayi”.

Ledan kazar ya miƙa mata tare da faɗin.

“Gashi kici”

Kai ta girgiza muryanta na rawa tace.

“Na ƙoshi”.

Kallon mamaki ya mata tare da cewa.

“Me kikaci?”.

Kafin tace wani abu suka ji motsin Neenah cikin sauri suka kalli gadon.


Juyi take tare da shush-shura ƙafafunta yayin da bakinta ke motsi tana sauƙe ajiyar zuciya akai-akai sannu ahankali ta fara buɗe idanunta da taji sunyi mata mugun nauyi ahankali tabi ɗakin da kallo tana ƙokarin tuna inane Kanta ta ɗaga sama jin ƙaran fanka ido ta tsirawa fankar dake jujjuya tana ƙoƙarin tuna inda take amma ta kasa Kanta ta juya gefenta na dama akan Imraan dake zaune tallafe da kuncinsa ta sauƙe idanunta.

Kallon second uku zuwa biyar tayi masa tana ƙoƙarin tuna Ina ne nan da sauri ta dafe kanta da yayi mata mugun nauyi.


  Araunane Indu ta riƙe tafin hannunta tare da faɗin.

“Sannu Blue eyes kin tashi?”.

Saurin juyawa Neenah tayi tare da kallon Indu ahankali ta yunƙura daniyar miƙewa amma ta kasa cikin muryanta da baya fita sosai tace.

“Ina ne nan Indu me mukeyi anan?”.

Ajiyar zuciya Indu ta sauƙe kana tace.

“Ba komai ki kwanta ki huta”.

Kai ta girgiza tare da bin ɗakin data kasa tantance Ina ne kana tace.

“Ya zaki ce bakomai bayan ga Yah Imraan atare damu sannan bansan inda muke ba”.

Kasa cewa komai Indu tayi.


  Kallon Imraan daya tsira mata ido tayi cikin muryan kuka tace.

“Yah Imraan me mukeyi anan?”.

Shiru yayi baice komai ba sai aikin kallonta da yake sake kallon Indu tayi cikin raunin murya tace.

“Dan Allah kuce wani abu kun barni aduhu meke faruwa dani meke damuna?”.

Da sauri ta dafe kanta tare da jingina bayanta da jikin Pillow sannu ahankali ta fara tuna abinda ya faru ɗaya bayan ɗaya lumshe idanunta tayi wasu hawaye masu masifar zafi suka zubo akuncinta kife Kanta tayi akan cinyarta ta fashe da kuka me gunji tana shesh-sheƙa tare da cewa.

“Nashiga uku ashe tsintacciya ce ni!,wacce bata da galihu ƴar kwaroro Innalillahi wa'inna ilahai rajiun”.


Miƙewa Indu tayi tare da rungumeta ajikinta kana tashiga bubbuga bayanta cike da rarrashi ta furta.

“Baki shiga uku ba Neenah dan Allah kiyi haƙuri ki daina kukan nan kada ki yarda da maganganun Aunty Lateefa babu komai aciki face shirme da ƙazafi sannan kalamanta ba za suyi miki tabo ba!”.

Cikin sauri ta janye kanta daga jikinta cikin shesh-sheƙan kuka tace.

“A'a Indu tabbas kalamanta sun riga sunyi min tabo azuciya da gangar jiki ta jefeni da kalaman da suka fi duka da bulalar ƙaya zafi kana sunfi garwashin wuta raɗaɗi da ƙuna azuciya”.

Zama Indu tayi agefen gadon ta riƙe tafin hannunta cikin sanyin murya tace.

“A'a Neenah kada ki ɗauki kalamanta da muhimmanci duk abinda ta faɗa ƙaryane ba gaskiya bane”.

Murmushin da yafi kuka ciwo tayi kana tace.

“A'a Indu a yanda Aunty Lateefa tayi maganar Ina hango tsagoron gaskiya acikin kalamanta ya kamata in koma gida yanzu Baba ne kaɗai zai tabbatar min”.

Ta Ida maganar tare da sauƙa akan gadon ta tsaya cikin sauri ta dafe kanta da duka hannunta tana jin jiri na ɗibarta Amma yanda zuciyarta ke wani irin zafi da tafarfasa yasa ta kasa Zama.


Numfashi Imraan ya fesar tare da lumshe idanunsa sai alokacin yayi gyaran murya cikin tsira mata Ido yace.

“Koma ki zauna”.

Kai ta girgiza araunane ta kallesa tare da cewa.

“Ya kamata inje gida akan lokaci”.

Still idanunsa na kanta yace.

“Ai zakije gidan Amma kafin nan ki nutsuwa”.

Kallonsa tayi da idanunta da suka sauya launi tamkar wata zautacciya ta furta.

“In nutsu fa kace!? Yah Imraan?,Taya kake tunanin ruhina da gangar jikina zai samu salama da nutsuwa muddin ban samu tabbaci akan kalaman Aunty Lateefa fa?”.

Anutse ya miƙe tare da harɗe hannunsa aƙirji kana ya tsira mata ido yana kallon yanda take layi tamkar ƴar maye cikin shesh-sheƙan kuka ta cigaba da cewa.

“Ina son sanin asalin wacece ni Ina son sanin wacece mahaifiyata Ina son sanin sirrin da mahaifina ya ɓoye min Ina buƙatar sanin meyesa Aunty Lateefa ta jefeni da irin wannan kalaman masu tarwatsa lissafi da ruguza farin cikin zuciya”.

Ajiyar zuciya Imraan ya sauƙe kana cikin sassauta murya yace.

“Ok na fahimci zafin da kike ji aranki amma yanzu ki koma ki zauna kina buƙatar hutu”.

Kallonsa tayi da idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye tace.

“Hmm-Hmm Yah Imraan baza ka taɓa fahimtar zafi da raɗaɗin da ƙirjina keyi min ba,Bazan taɓa samun nutsuwa a irin wannan halin da nake ciki ba!,Ai nayi sallama da nutsuwa da kwanciyar hankalin muddin ban samu amsar da nake buƙata ba”.


Ahankali ya jingina bayansa da jikin bangon kana ya ɗaure fuska tare da cewa.

“Koma ki zauna nace ko”.

Neenah kuwa wani irin kallon ta masa batare da tace uffan ba ta nufi ƙofa hawaye na cigaba da kwaranya daga idanunta bata tunanin zata iya ƙara koda minti ɗaya awajen da yanzu take iya fahimtar asibiti ne hannu tasa da niyyar buɗe ƙofar wani irin duhu ya mamaye Idanunta baya tayi luuuuu cikin wani irin sauri ya zabura taku biyu yayi ya Isa gareta kana ya rungumota jikinsa.

Ajiyar zuciya Indu ta sauƙe tare da furta.

“Alhamdulillah”.

Asaman laɓɓanta.

Neenah kuwa jin bata kai ƙasa ba yasa ta saki sanyayyar ajiyar azuciya tare da gyara zamanta ajikinsa tana shaƙan daddaɗan ƙamshi ahankali ta buɗe idanunta ya sauƙa acikin nasa daya tsareta da ido wani irin kallo yake binta dashi cike da kunya ta lumshe idanunta tare da janye jikinta daga nasa shikam ɗaukar ta yayi kamar Baby ya nufi gadon da ita...


**

Wani irin kallo Sir Abdallah kebin Meerah dashi cikin tsawa yace.

“Ba zakiyi magana ba ko?”.

Harara ta watsa masa cikin ɗaga sautin murya ta amsa da.cewa.

“Dakata!,kada ka sake ɗaga min murya!,Ina so kayi gaggawan rufe min baki domin bana buƙatar jin sautin muryar ka sannan duk abinda za kayi sai dai kayi Amma bazan yi magana ba”.

Kallon mamaki ya mata tare da cewa.

“Ok haka kika ce ko?”.

Kai ta jinjina cike da gadara da ƙasaita tace.

“Tabbas haka nace badan kaci darajar Alkur'ani mai girma ba koda silin gashina ka Isa ka cutar ne bare kuma ni akaran kaina?,Kasan waceceni Ni kuwa?”.


Hannu ya ɗaga mata afusace yace.

“Daka ta ban damu da sanin wacece ke ba,Kana da kinsan darajar Alkur'ani mai girma kamar yanda kika faɗa to da baki cutar da kowa ba sannan da baki karya alƙawari ba!?”.

Murmushi tayi tare da harɗe hannunta aƙirji cike da gadara da ƙasaita tace.

“Anyi ɗin idan da abinda ka Isa kayi to kayi yanda kake ji da taƙamar sarauta da mulki haka nake ji da nawa,Sarauta na ma yafi naka sannan na fika shu'umanci da miskilanci badan kaci darajar ance kada in taɓa ka ba,Da tuni nayi kilishinka dan tsire ma da sauƙi”.


Numfashi ya fesar tare da tsira mata ido tabbas ita ɗin shu'uma ce kamar yanda ta faɗa ahankali ya fara takawa yana Isa kusa da ita.

Wata mahaukaciyar dariya ta fashe dashi kana lokaci ɗaya ta haɗe fuskarta tare da cewa.

“Idan ma za kayi tafiya kai tsaye gwara kayi ka daina ƙumbiya-ƙumbiya domin duk wani numfashin ka akan idona yake bare kuma tafiyar ka”.

Ƙin tanka ta yayi ya cigaba da kusantar inda take tana ganin ya Isa gareta tayi saurin buɗe yatsun hannunta azabure ya kai hannunsa na dama tare da furta.

_“Bismillahi Rahmanir Rahim”_.

Kana ya damƙi gefen cikinta na dama tare da sanya idanunsa acikin nata kana yace.

_“Bismillahir Rahmanir Rahim (1)Wassama Izatin burujj(2)Wal yaumil Ma'ud(3)Washahi diu Wama sha huud(4)Ƙutila Ashabul Uhdud(5)Annari zatil Waƙud(6)Izhum alaiha ƙu'ud(7)Wahum Alama yaf'aluna bil muminina shuhud(8)Wama naƙamu minhum Illa an yu'uminu billahil Azizul Hamid(9)Allazilahu mulkussamati wal'ard,Wallahu alakulli shay'in shaheed(10)Innalazina fatanul muminina wal muminati thumma lam yatubu falahum azabhu jahannama walahum azhabul jaheem”._


Wani razanen'niyar ƙara Meerah ta saki wanda suwwan muryanta ya amsa baki ɗaya ilahirin gidan kana ya farkar da Ammie da Gimbiya Fa'izah daga dogon sumar da sukayi.

Afirgice suka miƙe suna zazzare ido cike da firgici da kuma ɗimuwa.

Cike da rauni tace.

“Na tuba Dan Allah ka daina ƙonani nayi alƙawari zanyi magana”.

Afusace yace.

“Da kinsan girman Allah da baki saɓa alƙawarin da kikayi a farko ba ba Dan haka kada ki sake haɗani da girman Allah zan ƙonaki da izininsa kamar yanda kika buƙata”.

Aruɗe ta girgiza kai tare da faɗin..

“Nayi alƙawarin sanar da kai wacece ni Sunana Hamjariyya saurauniyar Matan Aljanu mace mafi kyau da ƙasaita acikin jinsin Aljanu wacce gasar neman aurenta ya zama abin kwatance a duniya Aljanu da Iblisai”.

Cikin sauri ya ɗaga mata hannu cikin haɗe girar sama dana ƙasa yace.

“Ba abinda nake buƙatar jiba kenan,meyesa kika shiga jikin Meerah kike cutar da rayuwarta da kuma Wanda ke tare da ita??”.

Kallonsa tayi tana haki da sauƙe numfashi tare da cewa.

“Ni ba cutar da ita nake ba temakon ta nake ƙasaitarta da kuma Izzarta ne yake burgeni wannan dalili yasa na shiga jikinta saboda mu Zama aminai”.

Afusace ya watsa mata wani irin kallo cike da rashin tsoro yake faɗin.

“Ƙarya kike ba wannan dalili bane yasa kika shiga jikinta kin taɓa ganin bil Adam da Aljan sunyi abota tabbas kina da wani buri akanta domin masoyinka baya taɓa cutar da kai”.


Cikin rawan jiki Ammie da Gimbiya Fa'izah ke kallonsa musamman Gimbiya Fa'izah wani irin rawa da kyarma jikinta keyi na tsananin tsoro da firgici har juyewa kanta keyi tunda uwarta ta haifeta bata taɓa ganin tashin hankali irin na yau ba.

Ammie kuwa cike da dauriya ta shiga karanto duk wata adduar dake bakinta.

Meerah kuwa wani mahaukaciyar dariya ta feshe dashi kana tasa hannunta na dama ta tallafi kuncinta sai kuma ta haɗe yatsunta biyu alamar jinjina tace.

“Tabbas kana da kaifin basira da wankekkiyar ƙwaƙwalwa ɗan kyakykyawan saurayi sai dai kasani basirar ka da tunaninka ba zaiyi amfani akaina ba domin na wuce tunaninka”.

Tsayuwarta ta gyara tare da ɗaure fuskarta tamkar bata taɓa dariya ba kana tace.

“Tabbas muna da ƙuduri da manufa akanta sai dai wannan ba abinda ya shafe ku bane wannan sirrin mune domin kai ance kada mu taɓa ka shiyasa badan haka ba tuni nayi bandarka kada ka sake Kuskuren tambaya ta wani abu”.


Atsawace Sir Abdallah ya buɗe baki da niyyar magana tayi saurin watsa wani abu kamar Powder atake hayaƙi ya lulluɓe ɗakin wata mahaukaciyar dariya ta kece dashi wanda yake amsa kusurwa huɗu na ɗauki.

Sannu ahankali hayaƙin ya fara washewa da sauri Sir Abdallah yabi falon da kallo akan Meerah dake yashe ƙasa koren hayaƙi na fita ta hancinta ya sauƙe idanunsa numfashi ya fesar tare da ƙarasawa kusa da Ammie data yunƙura da niyyar tashi cikin sauri ya tallafo ta jikinsa rintse idanunta tayi kana ta riƙe hannunsa gam acikin nata.


Da gudu bayin dake shawagi acikin gidan suka nufi sashen Mai martaba suna isa suka nufi falonsa Fadawan dake tsaye bakin kofa sukayi saurin tare sa tare da cewa ina zakuje cikin haki daya daga cikinsu yace.

“Ina mai martaba saƙon gaggawa ne ke tafe damu babu lafiya”.

Ɗaya daga cikin masu tsawon yace.

“Ku faɗi abinda ku keson faɗa in isar muku amma babu inda zaku shiga”.


Dai-dai lokacin da aka buɗe ƙofar falon cike da nutsuwa da kamala wani Kamilin Dattijo Mai cike da,Haiba,kamala da nutsuwa ya fito cikin shiga ta alfarma wanda aƙalla shekarun sa baza su gaza sittin ba yana da matsakaicin tsayi da ƙiran jarumtaka kana baƙi ne cike da kamala da dattako yace.

“Lafiya sarkin gida Meke faruwa?”.

Kafin Sarkin gida yayi magana Bafaden da yazo ya zube aƙasa cike da girmamawa ya furta.

“Allah yaja zamanin adalin sarki Ubangiji ya tsare gabanka da bayanka Sashen Gimbiya Fa'izah babu lafiya Sai kururuwa da gurnani dake tashi”.

Jinjina kai Sarki Aliyu Ahmad Zaman yayi cike da alhini ya furta.

“Toh muje”.

Cikin sauri Fadawan suka shiga gaba saura kuma na biye dashi Abaya 


Cike da tausayawa Sir Abdallah ya kalli Ammie kana yace.

“Sannu Ammie ina ke miki ciwo”.

kai kawai ta iya girgiza masa batare da tace uffan ba baki ɗaya jikinta yayi tsami ko Ina ciwo yake mata.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da miƙewa ya riƙe hannunta tare da faɗin.

“Muje ɗaki ki huta”.

Kai ta gyaɗa kana ta yunƙura ta miƙe.


Da sauri Gimbiya Fa'izah ta kallesa tare da cewa.

“Abdallah wa zai kai Meerah ɗakinta idan ka tafi?Sannan yakamata ace ka zauna tare da ita kada ka tafi wani abu ya biyo baya kaga dai yanda abubuwan suka faru a idonka”.


Batare daya juya ya kalleta ba yace.

“Babu abinda zai faru da izinin Ubangiji ki kunna mata ƙira'a”.

Yana gama faɗin haka ya riƙe kafadar Ammie har sunyi taku biyu Gimbiya Fa'izah tayi saurin cewa.

“Abdallah idan ka tafi kabarta anan waye zai kaita ɗaki kasan dai ni ba iyawa zanyi ba sannan kasan bazan bari ƙasƙantattun ma'aikata su taɓa mata jiki ba daga baya ta riƙa fesar da ƙuraje!”.


Kallon mamaki ya mata jin abinda ta fada tabbas me hali baya fasawa duk wani girman kai da wulaƙanta mutane daga wajenta Meerah ke koya sam bata ganin mutuncin kowa.

Siririn tsaki yaja babu walwala atare dashi ya kalleta tare da cewa.

“Ok sai ki barta awajen lokacin data farka ta shiga da kanta domin bani da kuzarin ɗaukar ta.

Kai Ammie ta girgiza cikin sanyin murya ta kallesa kana tace.

“Kar kayi haka Autah na gaskiya ta faɗa idan ka tafi ka barta ba zata iya shigar da ita ba!”.

Saurin kallon Ammie yayi har ya buɗe baki da niyyar magana tayi saurin girgiza masa kai kana tace.

“Ban sanka da musu ba kayi yadda nace Dan Allah”.


Numfashi ya fesar kana ya juya tare da komawa cikin falon ya tsugunna akanta ya mutse fuska yayi ya rasa Ina ta samu wannan Gafalallen rigar anutse ya sanya hannu ya ɗauketa kamar Baby ya nufi bedroom dinta.

Wani shegen kallo me cike da tsana Gimbiya Fa'izah ta bisa dashi kafin ta taɓe baki.


Kai Ammie ta girgiza tare da juyawa zata fita dai-dai lokacin Sarki Aliyu Ahmad Zaman yashigo.

Da sauri ya riƙe ka faɗar Ammie kana yabi falon da kallo ahankali ya maida kallonsa kan Gimbiya Fa'izah da tayi narai-narai da ido saurin kallon Ammie yayi tare da cewa.

“Subhanallah Hafsat me ya faru me ya sameki dubi yanda wuyanki ya kumbura baki ɗaya jikin ki yayi zafi ko hari aka kawo muku ne?”.

Kai Ammie ta girgiza cikin sanyin murya tace.

“Ka kwantar da hankalin ka Abiey Abdallah ina lafiya ba wani babban ciwo bane”.

Hararan Gimbiya Fa'izah ta watsa masa cike da takaicin abinda yake.

Cikin sanyin murya yace.

“Toh wai meyafaru ne?”.

Ahankali Ammie ta janye jikinta daga nasa tana lumshe idanunta tace.

“Faizah zata yi maka bayani jiri nake ji”.

Hannunta ya sake riƙewa tare da cewa.

“Ok muje in kai ki ɗaki”.

Kai ta girgiza kana tace.

“Um-um zan iya ka kula da Fa'iza”..

Tana gama fadar haka ta juya ta fice.


   Anutse ya ƙarasa gefen Gimbiya Fa'izah kana yace.

“Wai meyafaru ne?”.

Kuka ta fashe tare da faɗawa jikinsa tashiga faɗa masa abinda ya faru.

Cike da al'ajabi kana da mamakin yake bubbuga bayanta ahankali ya furta.

“Yanzu ina Meerah”.

Cikin shesh-sheƙan kuka tace.

“Ta samu bacci”.

Kai ya gyada kana ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.

“Babana fa?”.

Sai da ta galla masa harara ta ƙasan ido kafin tace.

“Tun ɗazu ya tafi ba tare daya damu da halin da muke ciki ba sam wannan yaron baya ƙauna ta na rasa me natsare masa aduniyar nan kwata-kwata ya tsani ya buɗe idanu ya kalleni”.

Cikin sanyi Murya ya dafa kafaɗarta tare da faɗin.

“Ki rabu dashi zan ɗauki matakin daya dace akansa muje in kai ki ɗaki”.

Kai ta gyaɗa kana ya tallafa mata zuwa dakinta.


Ahankali Sir Abdallah ya kwantar da ita akan raound bed ɗin da yasha shimfida na alfarma sosai bedroom ɗin ya tsaru komai Jaa da ratsin baƙine numfashi ya fesar tare da juyawa zai fita.

Da mamaki yayi saurin juyawa ya kalleta ganin kamar gezo idanunsa ke masa tabbas ba gezo idanunsa keyi ba kayan jikinta sun sauya daga Jan doguwar riga zuwa Boomshort fari da riga sky blue iya cibiya gashin kanta atufke yana sheƙi fuskarta ɗauke da simple make-up kamar me tsoron wani abu ya dawo bakin gadon yana kallonta baki ɗaya kansa ya kulle da lamarin ya ɗauki minti uku yana kallon kyakykyawan fuskarta dake ɗauke da siririn zanen kanuri ahankali ya fesar da numfashi me sanyi kana ya juya da niyyar fita yaji ta riko tsintsiyar hannunsa.


Anutse ya zuba mata manyan idanunsa.

Ahankali ta buɗe idanunta tare da kashe masa ido ɗaya kana ta fisgosa kasancewar jikinsa ba karfi yasa ya faɗa kan gadon cikin sauri ya sanya tafin hannunsa akan katifar hakan yasa bai faɗa kanta ba gira ta ɗage masa tare da sanya tafin hannunta ta saƙalo wuyansa tana shaƙan numfashinsa.

 

Ɗaure fuskarsa yayi tamkar bai taɓa dariya ba yace.

“Me haka?”.

Fari tayi masa da ido tare da kai bakinta kan nasa ta gatsa lips ɗin.

Cikin sauri ya kawar da kansa gefe kana yace.

“Kinyi haukane?”.

Gira ɗaya ta dage masa tare da sakar masa da lallausan murmushi tace.

“Of cause my Prince indai akan soyayyarka ce na daɗe da zama zautacciya wannan ba sabon abu bane musamman idan ina kallon wannan idanun naka sai naji na gama zaucewa akan ka”.

Jin abinda tace yasa ya watsa mata kallon banza tare da faɗin.

“Tabbas kuwa daf kike da fara tsince-tsince abola Dan na lura haukar taki ba ƙarama bace”.

Atake yanayin fuskarta ya sauya daga murmushi zuwa ɓacin rai still hannunta na maƙale da wuyansa tana shaƙan numfashinsa ta furta.

“Me kake nufi da hakan?”.

Baki ya taɓe kana ya fincike hannunta daga wuyansa tare da cewa.

“Duk abinda kika fassara aranki haka nake nufi”.

Ya Ida magar tare da ficewa daga ɗakin.

Miƙewa tayi ta zauna atsakiyar gadon kana ta tallafe kuncinta tana shaƙan kamshin sa daya bari adakin yayin da soyayyar sa ke ratsa duk wani lungu da saƙo dake jikinta miƙa tayi jin yanda jikinta ya mata nauyi baki ɗaya.

Tsaki taja tare da miƙewa sai kuma tabi ɗakin da kallo ganin yanda ya hargitse da mamaki tashiga toilet tare da watsa ruwa...


**

Acan gidan Imraan kuwa

Miƙewa Meenah tayi tare da rataya Jakarta aka faɗa kana ta kalli

Lateefa dake cika tana batsewa tace.

“Dan Allah ki kwantar da hankalin ki Lateefa Sam bana son ganinki haka yana ɗaga min hankali”.

Kai Lateefa ta girgiza tare da kallon agogon dake screen ɗin wayar ta Wanda ke nuni da karfe 10:5pm araunane tace.

“Taya kike tunani hankali na zai kwanta Meenah ki kalli time fa har yanzu Sojana bai dawo ba sannan na Kira wayarsa yafi sau goma ba respond idan na rantse ba zanyi kaffara ba yana tare da wancen karuwar yarinyar”.

Kai Meenah ta girgiza cikin ƙoƙarin kwantar mata da hankali tace.

“Meyesa zakiyi irin wannan tunanin Lateefa ki kyautatawa kanki zato mana yaushe zaki alaƙanta mijinki da wancan kucakar yarinyar may be asibiti ya kaita tunda kinga dogon suma tayi shi kuma ya wuce wajen aiki”.

Har Lateefa ta buɗe baki da niyyar magana wayar Meenah ya hau ruri hakan yasa tayi shiru.


Ciro wayar Meenah tayi tare da picking ta kai kunnenta ataƙaice tace.

“Am so sorry My Dr gani nan fitowa”.

Janye wayar tayi tare da katsewa kallon Lateefa tayi kana tace.

“Daddyn Abeed na jira na zamu ƙarasa maganar awaya duk yanda ake ciki sai ki sanar min”.

Kai Lateefa ta gyaɗa batare data iya cewa komai ba Banda suya da tafarfasa babu abinda zuciyarta keyi taya Imraan zai mata haka.

Ita dai Meenah ficewa tayi ta lura Lateefa bata jin rarrashi tun yamma take abu ɗaya amma kamar tunzura ta take sai kace tafi sauran mata kishi.


**

Acan ɓangarensu Imraan kuwa anutse yake driving yayin da Neenah da Indu ke baya Banda shesh-sheƙan kukan Neenah babu abinda ke tashi acikin motar cike da tausayawa Indu ke rarrashinta yayin da itama hawayen ke kwaranya daga idanunta Uffan Imraan bai ce musu ba har suka Isa unguwar kai tsaye ƙofar gidansu Neenah ya nufa yana Isa yayi parking.

Cikin sauri Kamilin dattojin dake tsaye jikin gidan sanye da rigar shadda kore da wando milk color ya tsirawa motar ido zuciyarsa na bugawa da masifan karfin kallo ɗaya zaka masa ka fahimci babu nutsuwa da kwanciyar hankali atare dashi.

Anutse Imraan ya buɗe murfin motar ya fita tare da ƙara sawa kusa dashi cike da ladabi ya risina tare da miƙewa dattijon hannu yace.

“Ina yini Baba”.

Cike da kamala da nutsuwa dattijon yace.

“Lafiya lau Imraana ya gida ya aiki ya kuma ɗawainiya?”.

Imraan kuwa sake sunjuyar da Kansa yayi kana aladabce yace.

“Alhamdulillah Baba mun gode Allah”.

Har Baba ya buɗe baki da niyyar magana Neenah da Indu suka fito daga motar ajiyar zuciya me nauyi Baba ya sauƙe tare da tsira mata ido cike da ladabi Indu ta risina ta gaishesa.


Neenah kuwa tana Isa gabansa ta zuba gwiwoyinta aƙasa cikin rauni da sarƙewar murya ta haɗe hannunta waje ɗaya tare da cewa.

“Baba Dan girman Allah ka faɗa min wacece ni meyesa ka ɓoye min Asalinsa Meyesa tun ta sowata baka sanar dani waceceni ba?”.

Cikin sauri Baba ya kalleta zuciyarsa na bugawa da karfi kana yace.

“Subhanallah Kyautana meya faru Meyesa kike irin wannan maganar?”.

Kamar jira take ta sake fashewa da sabon kuka me tsuma zuciya cikin shesh-sheƙan kukan da sarƙewar murya ta furta.

“A'a Baba yanzu ba lokacin tambaya bane lokacine daya kamata ka bani amsa Dan Allah ka faɗa min wacece ni su waye asalin Mahaifana?”.

Ahankali Imraan ya jingina bayansa da jikin motar tare da tsira mata ido yana jin yanda take shesh-sheƙan kuka.

Indu kuwa kusa da ita ta tsugunna kana tashiga rera kuka cike da tausayinta tana fatan ace Baba ya ƙarya ta Lateefa tana fatan ace duk kalaman Lateefa ƙarya ne.


Mutuwar tsaye Baba yayi ya kasa koda ƙwaƙw-ƙwaran motsi sai wani irin bugawa da zuciyarsa keyi da masifar ƙarfi lokaci ɗaya zufa ya wankesa duk da Iskar hadari dake kaɗawa.

Cikin rauni da tsinkewar zuciya kana da fargaba tace.

“Baba da gaskene ni tsintacciya ce?,Da gaske ne agefen akwararo aka tainceni atsakiyar dare da gaske ni ƴar zina ce!Da gaske ne ba'asan Asalina ba? ,Dan Allah ka bani amsa Baba kada ka ɓoye min”.


Mamawo dake safa da marwa atsakiyar gidan taji hayani da alamun muryan Neenah yasa cikin sauri ta nufi ƙofar dai-dai lokacin da Neenah tace.

“Dan Allah Baba ka faɗa min kada ka ɓoye min komai ashirye nake da karɓan ƙaddara aduk yanda tazo min ni musulma ce na yarda da kadda mai kyau ko akasin sa”.

Ahankali Baba ya sanya hannu ya sharce zufan dake tsats-tsafowa daga goshinsa kana ya kalli Imraan da har zuwa lokacin ke jingina ne jikin motar kana ya kalli Neenah da Indu dake durƙushe gaban ƙafafunsa muryarsa na rawa yace.

“Waya faɗa miki wannan maganar?”.

Kai ta girgiza cikin zubda hawaye ta furta 

“A'a Baba Dan Allah ka faɗa min na roƙe ka ka kada ka ɓoye min komai da gaske ni tsintacciya ce ko?”.

Kallon Baba Mamawo da fitowar ta kenan tayi kana ta kalli Indu da Neenah sai kuma ta kalli Imraan cikin wata irin murya me cike da tabbatarwa tace.

“Tabbas”.


_@Follow me on Arewabooks realeshaa_


_@Follow me on Wattpad realeshaa_


_Ya Allah Ubangiji kajiƙan mahaifina ya Allah kagafarta masa zunubansu ya Allah ka kai haske kabarinsa ya Allah kajiƙan duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mu cika da imani._


_Ayi Shearing saboda Allah ƴan uwa Masoya da Abokan arziƙi._


*👭GARKUWAR MATA👭*

*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka  kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*

*GA*

*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*

Rage tumbi💯

Nono💯

Sanyi💯

Karin kiba💯

girmar hips💯

Ni'ima💯

Sabulai💯 

Humra💯

Turarukan wuta💯

Matsi💯

Miski💯

Dilka💯

Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki

GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI

***

***

          *ESHAA CE*🤙

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol