Free chapter · Read without an account

8&9

by Aishatu Abdullahi Idris · Sawun Giwa

*SAWUN GIWA*

_Ya take na Raƙumi_





 _By_

*Aishatu Abdullahi Idris*

_REAL ESHAA_



 *F-R-PG 8&9*

“Tabbas Wanda ya faɗa miki wannan maganar akwai la'ananne kuma tsinanne Watanin ko da kuwa wanene shi”.

Cikin sauri suka kalleta musamman Imraan Amma bai ce komai ba Baba kuwa cikin sanyin murya da dattako ya kalleta tare da cewa.

“Haba Saude meyesa zakiyi ƙoƙarin la'antar mutum bayan kinsan hakan haramun ne ko a musulunci”.

Ya mutse fuska tayi tare da faɗin.

“Watanin in ban la'ance ko uban waye ba mai kake so inyi Malam,Uyum nace me kake so inyi?,irin wannan ɗiban albarka har ina idan ba kaine Ubanta ba to waye ne to amma ai na tajiyo wannan maganar wani ko wace Gafalallune suka sanar mata?”.

Kai Baba ya girgiza cikin sanyin murya da kamala ya kalli Imraan da Indu kana yace.

“Toh mungode Imraana Allah ya saka da alkhairi gwara ku hanzarta komawa gida saboda hadari amma maganar cewa kyauta tsintacciya sam ba gaskiya bane nine Mahaifinta Mahaifiyar ta kuwa tana haihuwanta Allah ya mata rasuwa”.

Numfashi Imraan ya fesar tare da lumshe idanunsa kana yace.

“Toh Baba mun gode Allah yaƙara girma”.

Kallon Indu dake durƙushe kusa da Neenah yayi kana yace.

“Taso mu tafi”.

Asanyaye Indu ta miƙe tana shesh-sheƙa kallon Mamawo Imraan yayi kana yace.

“Toh sai da safe”.

Cikin sauri tace.

“A'a tsaya-tsaya mana Malam Soja,Watanin me kuma wani sai da safe kamar dai Gaulaye ka samu babu wani cikekken bayani”?.

Cikin takaici Baba ya girgiza kansa halin Saude sai Allah cikin yamutse fuska ta cigaba da cewa.

 “Watanin daga ina kuke acikin wannan tsohon daren ba bayani bakomai kuma sai kujuya ku barmu kamar dai kun samu gafalallu?”.


Cak Imraan ya tsaya anutse ya juya ya kalleta.

Gyaran mayafinta tayi kana tace.

“Watanin ai amsa zaka bani Malam soja bawai ka tsareni da ido kamar kaga sabon halitta ba tun yamma hankalin mu ke masifar tashe ba muga dawowarta daga Islamiyya ba kana ganin tsohonta ya kasa zaune bare tsaye duk ya wani fiffige duk da cewa dama ba ƙiba bane dashi to ni dai har zuciyata ta shiga saƙe-saƙe akan ku kunsan fa ance zuciya bata da ƙashi”.


Wani irin kallo Imraan ke binta dashi da idanunsa masu kaifi da ƙwarjini kana haiba lokaci ɗaya tasha jinin jikinta murmushi ta ƙirƙo kana tace.

“Watanin duniyar ce babu yarda Malam soja abin dai sai addu'a to amma wai Malam Soja daga ina kuke a wannan tsohon daren kamar wata muharramar ka?.”.

Kallonta kawai Imraan keyi kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya maida kallonsa kan Baba da kansa ke ƙasa numfashi ya fesar tare da faɗin.

“Baba”.

Ahankali Baba ya ɗago kansa muryarsa cike da rauni yace.

“Na'am Imraana”.

Iska mai sanyi Imraan ya fesar tare da kallon Neenah da har zuwa lokacin take wani irin kuka me tsuma zuciya cike da kamala yace.

“Baba ɗazun bayan dawowa na daga aiki misalin Ƙarfe Biyar da minti ashirin ina shiga falo na tarar da Neeraan asume ganin halin da take cikine yasa na Kaita asibiti batare da nanemi izini daga gare ka ba amma ina neman yafiyar ka domin nasan dole hankalin ka zai tashi akan rashin dawowarta kuma sai yanzu aka bamu sallama”.

Ya mutse fuska Mamawo tayi tare da taɓe baki kana ta watsa masa kallon banza cikin sauri tace.

“Amma dai ko awaya zaka kira kasanar masa ba lallai sai kazo ba ai,Watanin badan dai kasame mu masu sauƙin kai da takko ba ai wallahi sai muce baɗala kuke aikatawa aɓoye in ba haka ba yaushe zaku keɓe da yarinya sama da Awa da awanni kana baligi tana baliga”.

Cikin sauri Neenah ta ɗago idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kalleta cike da mamakin kalamanta.

Kai Baba ya girgiza tare da kallon Imraan daya tsirawa Mamawo ido cike da dattako yace.

“Imraana ku tashi ku tafi nagode Allah ya saka da alkhairi”.


Kai Imraan ya Jinjina cike da takaicin matar aransa kana ya furta.

“Toh nagode Baba sai da safe”.

Daga haka ya riƙe hannun Indu suka shiga Mota ya tayar har ya isa ƙofar gidansa zuciyarsa ba daɗi.

Ajiyar zuciya Baba ya sauƙe tare da tsugunnawa ya ɗago kafadar Neenah suka shiga gida.

Tsaki Mamawo tayi tare da wucewa ɗakinta tana surutai.

Cike da kulawa Baba ya kalli Neenah tare da cewa.

“Kyautana kije ki kwanta sannan ki cire damuwa aranki duk wanda yace baki da asali ƙarya ya miki”.

Lumshe idanunta tayi hawaye masu zafi suka zubo mata cikin rawan murya tace.

“Na yarda da kai Baba to amma wacece mahaifiyata dan Allah koda hotonta ne ka nuna min ko zan samu nutsuwa wallahi ji nake tamkar zuciyata zata fashe”.

Kai Jinjina yayi kana yace.

“Ina Zoben dana baki!?”.

Cikin shesh-sheƙan kuka tace.

“Yana nan?”.

Numfashi ya fesar tare da faɗin.

“Ki cigaba da adana wannan zoben dana baki, daga yau ina so kisa shi ahannunki komai rintsi komai wuya kada ki cire”.

Kai ta gyaɗa hawaye na kwaranya daga idanunta tace.

“In sha Allahu Baba”.

Murmushi ya sakar mata tare da shafa kanta kana yace.

“Yanzu kina bukatar hutu tashi kije ki kwanta banaso kisa damuwa aranki kuma kada ki sake yimin tambaya akan hakan”.

Kai ta gyaɗa tare da shiga ɗakinsu kallon Maryam dake bacci tayi agefenta ta kwanta hawaye Masu masifar zafi suka zubo mata asaman kuncinta lokaci ɗaya hadarin ya taso aka fara ruwa tamkar da bakin ƙwarya miƙewa tayi ta zauna kana ta kife kanta akan cinyarta tashiga rera kuka ganin Maryam tayi juyi yasa tayi saurin toshe bakinta,

Ahankali ta miƙe ta buɗe Ghana Masgonta tare da cusa hannunta can ƙasa ta laluma wani ƙalle data ɗaure buɗe wa tayi ta ciro wani Round Zobe me ɗauke da wani irin ado ajiki ta sanya ayatsarta tare da fashewa da sabon kuka sai misalin ƙarfe uku da rabi bacci yayi nasaran ɗaukar ta kana har zuwa lokacin ana tsuga ruwan sama tamkar da bakin ƙwarya...


Acan cikin barcinta kuwa kwance ta hangota abakin wani tangamemen rami mai masifar zurfi,tsayi kana da duhu yayin da take ƙoƙarin faɗawa cikin ramin cikin tsananin ɗimuwa gami da galabaita take ihu da duka ƙarfin kana tana neman agaji yayin da daga can nesa ta hango Sir Abdallah ya nufo inda take cikin sassarfa yana mai miƙa mata hannu tun kan ya isa gareta kafin ya ƙaraso gareta wani irin santsi mai azaban sulɓi yajasa nan take ya faɗi.

Idanu ta zuba masa hawaye na kwaranya ganin duk yanda yaso tashi ya gagara sai hannu yake miƙa mata amma ya gaza ceton kansa bare ya iya cetonta.

Cikin tsananin galabaita ta ɗaga idanunta sama ga mamakinta sai ta hango Imraan ya nufota gadan-gadan da niyyar temako amma shima kafin ya ƙaraso tuni wani irin santsi da yafi na Sir Abdallah ya kwashesa ya faɗi agaban Sir Abdallah cikin sauri ya riƙo hannun Sir Abdallah 

Ba zato ba tsammani ta hango wani mutum da bata iya gane fuskarsa ya sanya hannu da niyyar janyota kawai shima ya zame agaban Imraan cikin sauri ya riƙe hannun Imraan ya zamana Sir Abdallah na gaba Akuma dai-dai lokacin ta saki ɗan abinda ta riƙe ta nufi ainihin cikin ramin da wani irin matsanancin sauri Sir Abdallah ya riƙo hannunta tare da janyota waje...


Akuma dai-dai lokacin ta ƙwalla ihu tare da farkawa arazane kanta ta dafe da duka hannunta biyu yayin da hawaye ya wanke fuskarta wani irin zufa ke fita daga jikinta duk kuwa da yanda gari yayi sanyi.

Kanta ta cusa acikin cinyarta jikinta na rawa.


   Acan ɓangaren Baba tun da ya shiga ɗaki ya kasa runtsawa jinginga bayansa da jikin bango yayi,zuciyarsa na bugawa cike da tsoro da tarin fargaba irin wannan ranan yake tsoron zuwanta kamar yanda Neenah bata samu wadatacciyar bacci ba haka shima Baba ya kwana cikin zullumi...


**

   Bayan kwana biyu haka nine ta kasance cikin zullumi da tunani ko Islamiyya taje bata fahimtar abinda ake Indu na ƙoƙarin ganin ta kwantar mata hankali Imraan na bakin ƙoƙarin sa wajen ganin ta samu nutsuwa....


Washe gari Monday.

Maryam dake zaune kan sallaya bayan ta idar da Sallar Asbah ta juya ta kalli Neenah da har zuwa lokacin take bacci kusa da ita ta matsa tare da bubbuga kumatunta ahankali tace.

“Sister Neenah!, Sister Neenah!!, Sister Neenah!!!? lafiya kuwa har ƙarfe bakwai fa ko dai ba zakije school bane?”.

Kamar amafarki Neenah ke jin sautin muryanta sake bubbuga bayanta Maryam tayi kana tace.

“Ko dai baki da lafiya ne Sister amma ko Sallah fa bakiyi ba”.

Neenah kuwa ahankali ta miƙe tare da buɗe idanunta da suka ƙanƙance kana ta sauƙe ajiyar zuciya tare da faɗin.

_“Alhamdulillahil Lazi ahyana bada ma amatana Wa'ilaihin nushur Astagfirullah Wa'atubu Ilaik”_.


Cikin sauƙe numfashi Maryam tace.

“Wai meke damunki kwana biyu nan ina lura dake ko dai baki da lafiya ne?”.

Kai Neenah ta girgiza kamar bazata ce komai ba sai kuma tayi ƙasa da idanunta tace.

“Lafiya”...

  Ido Maryam ta tsira mata tana nazartar yanayinta cikin sauri Neenah ta sun kuyar da kanta ƙasa kana Ahankali ta miƙe ta fita daga ɗakin jikinta sanye da hijabi kai tsaye bakin rijiya ta nufa ta ɗauki buta kana ta zira guga arijiya tajanyo ruwa.

Cikin sauri ta saki gugan ta damƙe ƙasan maranta da yayi wani irin murɗawa da azabebben ƙarfi..

Mamawo data fito daga kitchen hannunta riƙe da Kwanon ɗumame ta zare ido cikin ɗaga sautin murya tace.

“Kutuma dan Allah Idan kin cika Gafalalliya, Watanin kibar gugan ya ƙarasa faɗawa rijiyar nan wlh sai na nuna miki ƙaryan iskan ci kike dan sai kin bishi”.

Aruɗe Neenah ta tsugunna tare da riƙe igiyar gugan da saura kaɗan ya ƙarasa faɗawa cikin rijiyar still hannunta na hagu na dafe da ƙasan maranta yayin da hawaye ke kwaranya daga idanunta cikin rauni ta durƙusa ƙafafunta abakin rijiyar Kasancewar irin rijiyar nan ne dake kewaye da taya ji take ƙafafunta tamkar ba ajikin ta suke ba.

Cike da takaici Mamawo tace.

“Watanin tunda Uwata ta haifeni nazo duniya ban taɓa ganin Gafalalliyar yarinya mara nutsuwa da hankali gaula irin kiba sai kace wacce aka Ƙanwartace ta raineta”.


  Araunane ta lumshe idanunta hawaye Masu ɗumi suka zubo muryanta na rawa tace.

“Mamawo cikina!Ƙafana!Bayana!Kaina!,Ƙuguba Ji nake kamar ba ajikina suke ba”.


Kai ta Jinjina kana tace.

“Allah ko!,to ai sai ki dawwama awajen tunda kince baki da aiki sai bin gindin maza Watanin baki ma ga komai ba tukunna sai kin kasa tafiya sun ɗurka miki ciki”.

Maryam dake sanya hijabin Uniform ɗinta tayi saurin ajiyewa ta leƙo jin abinda Mamawo ke faɗa kallon Neenah dake durƙushe abakin rijiya yasa tayi saurin nufarta cike da kulawa ta furta.

“Subhanallah ya dai Sister Neenah Meke damunki!?”.

Dogon tsaki Mamawo taja tana ƙoƙarin shiga ɗaki tace.

“Rabu da baƙar Annamimiya taje ta buɗe wa wancan Munafuki me fuskar kafirai ƙafa ya gama ƙaƙuleta shine yanzu zata zo tana non-noƙewa to wallahi idan ma wani abin kika ƙunsu tun wuri kisan yanda zakiyi dashi”.


Cikin yanayin ɓacin rai da takaici Maryam ta juya ta kalleta tare da cewa.

“Haba Mamawo meyesa bakin ki baya faɗan alkhairi akanta ne? Fisabillah? Manzon Allah (S.A.W) yace _Falyaƙun Khairan Au'liyastumu_ idan har kinsan ba zaki faɗi magana wacce ta dace ba ai sai ki haƙura”.

Ta ida maganar tare da ƙarasawa bakin rijiyar ta karɓi gugan da har zuwa lokacin ke riƙe ahannun Neenah kana ta janyo ruwan ta juye mata abuta cike da kulawa tace.

“Sannu ga ruwan”.


Haɓa Mamawo ta riƙe cikin ya mutse fuska ta furta.

“Toh sannu ƴar gidan Liman ƙutu,Watanin da zaki tsareni da cewa in faɗi alkhairi ko inyi shiru ai yanzu ma ba ƙarya nayi ba sannan ba mugun fata na mata ba amma in dai tace maza zata biyewa to ina mai tabbatar miki kaita za suyi su barota?”.

Kai Maryam ta girgiza cike da takaicin abinda ta faɗa ta zuba mata ido kana tace.

“Amma dai kinfi kowa sanin duk wata haka take fama da azabebben ciwon cikin amma yau ki bijiro da wata magana mara ma'ana?”.

Sheƙeƙe Mamawo ke kallonta sai kuma ta laluma jikinta ta ciro wata koɗaɗɗiyar Naira goma tace.

“Toh Ash-sheikiya Maryama ga abin sadaka amma da zaki tafi bakin masallaci inaga zaifi dan inaga zaki samun wadatacciyar sadaka”.

Kai Maryam ta gyaɗa tare da kawar da kanta gefe mai hali baya fasawa sam bata kaunar abinda Mahaifiyarta keyi.


Neenah kuwa numfashi ta fesar tare da kife kanta Jikin butar tana jin yanda cikinta ke murɗawa da wani irin azabebben ƙarfi yayin da ƙafofinta suka riƙe gam takai minti biyu ahaka kafin taji cikin ya ɗan sake da ƙyar ta yunƙura ta miƙe.

Maryam dake kallonta cike da tausayawa ta matsa tare da cewa.

“Ko dai in tallafa miki ne zuwa ban ɗakin?”.

Cikin sauƙe numfashi ta girgiza mata kai kana ta ɗauki butar tana ta fiya ahankali har tashiga bayin.

Butar ta ajiye kana ta tsugunna da niyyar kama ruwa taga jini lumshe idanunta tayi ganin period ɗin ta ne yazo sai dai sam ba tayi tsammanin a irin wannan lokacin zai zo ba da ƙyar ta yunƙura ta miƙe kana ta zuba rabin ruwan butar a ƙasa jinin ya wanke alwala tayi wanda ya kasance ɗabi'arta ce koda bata Sallah takanyi alwala saboda falala da kuma kariyarsa.

Ahankali take ta fiya har ta isa dakinsu dai-dai lokacin da Maryam ta fito kafadar ta rataye da jaka baƙi me kyau cike da kulawa tace.

“Sannu Sister amma dai yau ba zakije makaranta ba duk da cewa farkon Satine?”.

Cikin sanyi murya da sauƙe numfashi tace.

“A'a zanje”.

Saurin kallonta Maryam tayi kana tace.

“Bangane zaki jeba?da ciwon cikin zakije ko me?,dan Allah ki haƙura zan bi in sanar wa Indu idan taje sai ta sanar baki da lafiya”.

Kai ta gyaɗa kana ta shiga ɗakin ita kanta tasan baza ta iya zuwa makaranta ba sai dai kuma Case ɗinta ance yau za'ayi kai tsaye jikin Ghana Masgon ta tanufa ta buɗe wani leda ta ɗauka tare da buɗewa ta ciro wani tsumma mai haske ta naɗa sannan tayi ƙunzugu dashi.


Maryam kuwa ɗakin Mamawo ta nufa a Kofar ɗakin ta tsaya tare da ɗaga labulen dake maƙale jikin ƙofar tace.

“Mamawo na tafi”.

Shayin data kurba ta hadiye kana tace.

“Kishigo ki sha shayin mana”.

Kai ta girgiza tare da yamutse fuska kana ta furta.

“A'a zan tafi sauri nake bakwai da rabi yayi”.

Jinjina kai tayi kana tace.

“Toh Ubangiji Allah ya tsare min ke ya rabaki da sharrin mutum da Aljan adawo lafiya Maryama sarauniyar mata”.

Kai ta gyaɗa kana tace.

“Ameen ya Allah”.

 Har ta juya zata tafi sai kuma ta tsaya tace.

“Ina Baba ne tun daya buga mana kofa da asuba ban sake jin motsinsa ba”.

Ƙaragon ta kai bakinta ta tauna kana tace.

“Ya tafi gaishe da abokinsa ko kuma ince yawon Maular tasa da yasa ba duk safiya”.

Cike da takaici Maryam ta girgiza kai kana tace.

“Dan Allah ki kula da Sister Neenah tana kwance ki dama mata kamu”.

Baki ta taɓe tare da cewa.

“Toh Makarantar fa?”.

Kai Maryam ta girgiza tare da cewa.

“Baza taje ba ai komai sai da lafiya”.

Cikin sauri ta katseta ta hanyar cewa.

“Bangane baza taje ba Watanin Ubanwa zai warware mata Jagwal data haɗa a lallai dole tace baza taje ba ta fake da munafikin ciwon ciki”.


Cikin rarrashin walwala Maryam tace.

“Wani irin Jagwal kuma?wai dan Allah Mamawo meyesa wani lokacin kike abu kamar yarinya?”.

Zare ido Mamawo tayi kana tace.

“Ubanki Audu shine yake abu kamar yaro bani ba shegiya fitsararriya Watanin na lura nan gaba ma dukana zaki fara”.

Juyawa Maryam tayi ta fice duk ranta ba daɗi a ƙofar gidan su Indu ta tsaya tare da kallon mai gadin kana tace.

“Yawwa Malam Idi dan Allah idan Indu ta fito kace mata yau Neenah ba zata samu zuwa Makaranta ba bata da lafiya”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Ash'sha toh Allah ya bata lafiya da yake kwana biyu babu makarantar shiyasa ban sani ba”.

Kai Maryam ta gyaɗa tana ƙoƙarin barin wajen tace.

“Aikam”.

“Toh Allah ya bata lafiya”.

“Ameen”.

ta amsa tare da barin wajen.


****

Anutse ya fito daga toillet ƙugunsa ɗaure da towel me ɗan girma faffaɗan ƙirjinsa dake ɗauke da ƙiran jarumtaka da gargasa kana da damshin ruwa ya bayyana kai tsaye gaban dressing mirrow dake cike da kayan shafa da turaruka ya nufa stool yaja ya zauna tare da ɗaukan ɗaya daga cikin lotion ɗin ya shafe jikinsa kana ya ɗauki mayukan kansa da turaren kai mai daɗin ƙamshi ya shafa ahankali ya miƙe ya nufi jikin tan gamemen siff dinsa daya cinye bango daya na ɗakin wani danyen Boyel sky blue ya ɗauka irin ɗinkin samarin zamani mai masifar kyau ya sanya kana ya sanya baƙin hula ya feshe jikinsa da turarukansa masu daɗin kanshi ahankali ya ɗauki wayarsa da breafcase dake kan gadon ya nufi kofa ya fita kai tsaye sashen Ammie ya nufa bayi da Ma'aikatan gidan sai durƙusawa suke suna gaishesa cike da kamala da kuma ƙasaita yake amsa musu yayin da ƙwarjini da kuma haibarsa ya cika idanunsu.

Kallo ɗaya zaka yi masa kasan Ubangji ya zuba halitta Sir Abdallah kyakkyawa ne na karshe ba fari bane amma kalarsa na da wuyar samu ya kasance chocolate colour ne da wasu irin ido masu masifar kyau da ƙwarjini yana da dogon hanci da ƙaramin baki kana ga saje ɗaya ƙawata kyawun fuskarsa...


Anutse ya murɗa handle ɗin ƙofar falon tare da cewa.

“Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarkatuhu”.

Lallausan murmushi Ammie dake zaune ƙasan Capet gabanta ɗauke da kayan Breakfast ta sakar masa kana tace.

“Wa'alaikum Salam Auntana duk ka kwashe ladan ai”.

Murmushi yayi tare da ware Manyan idanunsa dake lumshe kana ya ƙarasa gefenta ya zauna kansa ya ɗaura akafadarta cike da shagwaɓa yace.

“Kai Ammie na aikema na bar miki naki”.

Murmushi ta sakar masa tace.

“Uhm haka dai kace”.

Zamansa ya gyara kana ya daidaita nutsuwarsa tare da cewa.

“Ina kwana Ammie na ya ruwa ya kuma ƙarfin jiki?”.

Kallonsa tayi da murmushi afuskarta tace.

“Ruwa Alhamdulillahi jiki kam ai kai za'a yiwa nikam ina lafiya ya raunin ya daina zafi kam?”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe kana ya maida kansa kafadar ta yace.

“Nikam Alhamdulillah Ammie amma naji tsoron kada wani abu ya sameki”.


Numfashi ta fesar cikin sanyin murya tace.

“Da izinin Ubangiji babu abinda zai sameni tunda ina da jarumin ɗa kuma sadauki kamar ka?".

Ware idanunsa yayi tare da sakin murmushi kana yace.

“Kasancewar ki Uwa tagari kuma tsayayya shi yasa na zama Jarumi kuma Sadauki”.

Jinjina kai tayi kana tace.

“Tabbas ina alfahari da kai ɗa ɗaya tamkar da dubu tabbas albarkar haihuwa ake buƙata ba taran yun-yu-yu-ba”.


Murmushi yayi wanda ya bayya nar da fararen hakoransa tare da cewa.

“Tabbas maganar ki gaskiyace ada idan naga bani da ƙanne na kanji ba daɗi musamman idan na tuna bani da Yayu maza sai mata asamana na kanji ba daɗi amma yanzu Alhamdulillah Yayu mata biyu sunfi min Goman maza hakan kuma yana da alaƙa da tarbiyyan da kika bamu”.

Ammie kuwa ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

“Autah na ina alfahari daku ƴaƴa uku Allah ya bani amma kun fiye min ƴaƴa dubu sai dai duk haka ina buƙatar ganin jikoki masu yawa kaga Aunty ka Aysha da Zainab ni suka ɗauko shekarunsu kusan shabiyar agidan miji Amma ƴaƴan Aysha biyu na Zainab uku”.

Numfashi ya fesar cikin sanyin murya yace.

“In sha Allah zan tara miki jikoki masu tarin yawa da albarka sannan na baki kiyi musu tarbiyya kamar yanda kika min”.


Murmushi tayi tare da shafa saman fuskarsa tace.

“Ina fatan haka Autah na shiyasa nake so kayi Aure da wuri kar ka tsufa agauranci”.

Baki ya tura kana Ashagwaɓe yace.

“Tsufa kuma Ammie ai namiji baya tsufa”.

Murmushi tayi kana tace.

“Haka dai kace tun yaushe zaka tsufa har ka tsofe.

Dariya ya sanya wanda ya bayyanar da Fararen haƙoransa kana ya furta.

“Kai Ammie ba wani tsofewa”.

Martani murmushin ta mayar masa tare da faɗin.

“Amma ya jikin Meerah da Fa'izah yau kwana biyu kenan tunda abin ya faru babu wacce ta shigo kuma jiya ƙafana na ciwo ban samu na shiga na duba su ba?”.

Atake yanayin fuskarsa ya sauya ya mutse fuska yayi sai kuma ya girgiza kai tare da kallon agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa yace.

“May be da sauƙi Ammie dan Ni tun ranar Friday ban sake komawa ba bari na tafi kada in makara”.

Zama ta gyara tare da fuskantar sa da kyau tace.

“Bangane may be da sauƙi ba,kana nufin ba kashiga ka duba jikinsu ba kenan tun shekaran jiya!?”.

Kai ya girgiza batare daya kalleta ba yace.

“A'a Ammie amma ai da ace akwai wata matsala zaki ji?”.

Cikin sauri ta girgiza masa kai kana tace.

“A'a Auntana wannan ba hujja bace Akan idon ka komai ya faru, sannan ƙarfe takwas ne yanzu kana da sauran time da zaka shiga ka duba su”.

Langwabar da kai yayi cike da shagwaɓa ya furta.

“Please Ammie Allah ina dawowa zan shiga but now nayi letti”.

Bayanta ta jingina da jikin kushin kana tace.

“Ahaka zaka kula da ɗawainiyar ta bayan Auren ku?,Ina kula da halin ko in kula da kake nuna mata Auntana ka rage wannan ƙiyayyar da kake nuna mata domin zakuyi rayuwa na har abada ne”.

Wani Abu mai masifar ɗaci ya haɗiye cikin sanyi ya ɗago idanunsa ya kalleta cikin sauƙe numfashi yace.

“Ammie sam Meerah bata cikin quality irin matan da nake son Aure sam bata dace dani ba Ammie yanzu fa kika gama cewa kina so kiga na haifa miki yara masu tarbiyya”.

Ido Ammie ta tsira masa ganin yanda yake magana cikin sanyi Idanunsa alumshe ya cigaba da cewa.

“Ammie sam Meerah bata cancanci zama mata kuma uwar ƴaƴa agareni ba domin bata da wadatacciyar tarbiyya da zata tarbiyantar min da ƴaƴa dan Allah Ammie ki fahimceni”.

Ahankali ta shafa sumar kansa cikin rarrashi tace.

“Autana kada fa ka manta kai ne ke da iko akanta da zaran kunyi Aure duk dokar da ka shimfida mata ba zata tsallake ba muddin tana son zama da kai”.

Cikin sauri ya girgiza mata kai kana yace.

“Ammie taya kike tunanin zan bata tarbiyyar da bata samu awajen iyayen ta ba?,Nasan koda kun Aura min ita ba zata taɓa jin daɗin zama dani ba domin bana ƙaunarta”.


Kafin tace wani abu tuni ya fice kai tsaye inda motarsa ke fake ya nufa buɗe mazaunin driver yayi ya shiga ya tayar kana ya danna Hong mai gadi ya buɗe masa ahankali yake driving zuciyarsa na wani irin zafi arayuwarsa ya tsani a alaƙantasa da ita bare kuma har maganar Aure. Cikin minti goma sha biyar ya isa harabar makarantar anutse yayi parking ya fita kai tsaye Office ɗin Principal ya nufa jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi yayin da ƴan matan ke aikin kallonsa.


**

Acan ɓangaren Imraan kuwa zaune yake akan 3sitter jikinsa sanye da kakin sojoji da yayi masifar Amsar jikinsa yayin da wasu kyawawan yara mata biyu ke zaune agefensa wanda aƙalla shekarunsu bazai gaza Goma ba aƙage ya kalli haɗaɗɗen agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa me launin Kore da baƙi kana ya girgiza kai tare da jan siririn tsaki.


Ɗaya daga jikin yaran ce ta ɓata fuska cikin tura baki tace.

“Daddy zamuyi letti fa kuma Security zai samu punishment”.

Kallonta yayi tare da fesar da numfashi sai kuma ya kalli ɗayar wacce ta cure baki kana ya furta.

“Yanzu zamu tafi Auntyn ku muke jira”.

Wacce ta cure bakin ne ta kallesa tare da cewa.

“Dad to kasa driver ya kaimu Please ni dai wallahi na gaji gwanda ma Reehana zata iya daukar punishment Amma ni bazan iya ba”.

Harara Wacce ta kira da Reehana ta watsa mata kana tace.

“Iyeee lallai ma Reeyana wato ni jikin ƙarfe ne dani ko?”.

Miƙewa Imraan yayi tare da kallon Reehana yace.

“Oya kicewa Indu idan bata fito ba zamu tafi”.

Kai Reehana ta gyaɗa tare da juyawa da gudu ta nufi bedroom ɗin Indu dai-dai lokacin da Indu tafito hannunta riƙe da hijabinta.


Cikin tura baki Reehana tace.

“Aunty Indu Daddy yace kiyi sauri ko kuma mu tafi mu barki dan yagaji da zaman jiranki”.

Indu na sanya hijabi tace.

“Toh ku tafi mana dama kunji nace ku jirani ne?,Ina ce kuka ɓata min lokaci wajen shiryaku amma yanzu kinzo kina Min kwainane".

Ta ida maganar tare da ƙarasawa falon.

Imraan kuwa harara ya watsa mata babu walwala atare dashi ya kalli agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa kana yace.

“Ke ko!,Ke ko!!,Baki da aiki ai ɓatawa mutane lokaci ki duba time fa ƙarfe nawa yanzu?”.

Langwabar da kai tayi cikin sanyi murya ta haɗe hannunta waje ɗaya tare da faɗin.

“Ayyah Yah Imraan Allah Reehana da Reyaana ce suka ɓata min lokaci wajen shiryasu”.

Dai-dai lokacin Lateefa ta fito hannunta riƙe da lunch box guda biyu yayin da ɗaya hannu ke riƙe da ƙaramin yaro wanda shekarunsa baza su gaza biyu ba murmushi tayi kana tace.

“Ai lalli dai kam keda Twins ɗinki duk lazy ya muku yawo shiyasa zaku ta makara”.

Banza Indu tayi mata tare da nufar ƙofa ba tare da bata amsa ba bata taɓa jin haushinta irin na ranar juma'a ba har ƙasan ranta takejin zafin maganganun data faɗawa Neenah cikin sauri Reehana da Reyaana suka bi bayanta.


Cikin mutuwar jiki da sanyin murya Lateefa ta kalli Imraan dake ƙoƙarin fita kana tace.

“Sojana kaima fushi kake dani kamar yanda Indu ke fushi dani?”.

Wani banzan kallo ya watsa mata tare da nufar ƙofa cikin sauri ta ajiye Rayyan dake hannunta tabi bayansa dai-dai lokacin daya fita daga falon rungume sa tayi ta baya tare da fashewa da matsanancin kuka cikin rauni da shesh-sheƙa tace.

“Am so sorry dan girman Allah Sojana ka yafemin nasan Ni mai laifi ce awajenka sai dai bazan iya juran fushinka ba na tuba ka yafemin”.

Numfashi ya fesar kana ya janyeta daga jikinsa ya juyo da ita gabansa kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa ya nufi ƙofa ya fita.

Lumshe idanunta tayi hawaye Masu ɗumi suka zubo asaman kuncinta ahankali ta jingina bayanta da jikin ƙofar falon tana jin wani irin tsanar Neenah fiye da komai arayuwarta.

Imraan na fita ya samu duk sun shiga motar batare da yace uffan ba ya buɗe ya shiga. mazaunin driver ya tada motar tafiyar minti goma yayi ya isa wani tsare-tsaren gate da asaman sa aka rubuta _(Brilliant Primary & Secondary Academic)_

Parking yayi kana ya fita ya ɗauki lunch box dinsu fita Reehana da Reeyana sukayi tare da ɗagawa Indu hannu itama hannu ta ɗaga musu.

Bayan sun shiga cikin makarantar kai tsaye ajinsu ya nufa ya ajiye kana ya juya ya shiga motar asanyaye Indu ta kalli Imraan kana tace.

“Ayyah Yah Imraan Neenah fa baza mu biya mu ɗauketa ba?”.

Yana daidaita hancin motar akwalta yace.

“Saboda nasan Shiriritan ki yasa nace da Bana kafin ya wuce gwonan ya kaita idan zan dawo sai inn biya in ɗauku”.

Murmushi tayi kana tace.

“Kai Yah Imraan Allah ba haka bane duk shirya twins ne ya ɓata min lokaci kuma itama Neenah haka take har na fita kazar-kazar”.

Ware ido yayi kana yace.

“Uyum in ma Twins sunyi haka aike suka gado Neeraan kuwa ta fiki kazar-kazar kada ma ki haɗa kanki da ita”.

Ya ida maganar yana lumshe idanunsa ahankali zuciyarsa ya shiga tariyo masa abubuwan da suka faru atsakanin su murmushi ya saki.

Ware ido Indu tayi tana nazartan yanayinsa kafin tace wani abu wayarsa dake gaban motar ya hau ruri batare daya kalli wayar ba yace.

“Duba kiga wake kiran”.

Kai ta gyaɗa sai kuma ta saki murmushi kanatayi picking call ɗin tare da cewa.

“Laa Aunty Muna ina kwana”.

Daga daya ɓangaren tace.

“Lafiya lau Autah ina Imraan ɗin?”.


Tura baki Indu tayi kana cike da shagwaɓa tace.

“Aunty Muna ko gaisawa fa ba muyi ba kike tambayarsa sai kace ba kiyi missing ɗina ba”.

Cikin sanyin murya tace.

“Zamu gaisa Autah amma fara bashi wayar”.

Fuska ta ɓata kana ta mikawa Imraan wayar murmushi yayi kasancewar yana jin duk abinda suke faɗa cike da zolaya yace.

“Lallai yarinya zaki sha wahala indai kishi kike dani ba kisan na fiki Fan's ba”.

Ƙin tanka masa tayi girgiza kai yayi kana yayi sallama awayar.

Bayan Aunty Muna ta amsa sallamar tace.

“Imraan ku taho yanzu kai da Auntah”.

Jin yanayin muryanta yasa Imraan daidaita nutsuwarsa kana ya furta.

“Lafiya kuwa Aunty Muna ya naji muryanki hana?”.

Kai ta girgiza tare da cewa.

“Kuna ina ne yanzu?”.

Da damuwa asaman fuskarsa yace.

“Ina hanya ne zan ajiye Indu a makaranta sannan na wuce wajen aiki,Wai Meke faruwa ne?”.

Kai ta gyaɗa kana tace.

“Jikin Ummu ce ya tashi kuzo yanzu”.

Da ƙarfi ya taka burki kana yace.

“Innalillahi gamu nan zuwa”.

Aruɗe Indu tace.

“Yah Imraan lafiya meyafaru?”.

Bai iya cemata komai ba sai juya akalar motar da yayi cikin tsananin tashin hankali zuwa unguwar tasu...


****


Acan ɓangaren Sir Abdallah kuwa kansa ya dafe da hannunsa na dama yayin da hannunsa na hagu ke saman deks ɗin kana idanunsa alumshe yana bubbuga ƙafarsa na dama ahankali...

  Principal dake kallonsa ya sauƙe ajiyar zuciya cike da girmamawa yace.

“Bundi aƙalla mun kai awa ɗaya da rabi da zama amma har zuwa yanzu babu yaran nan babu dalilinsu anya akwai ƙamshin gaskiya amaganarsu?”.

Ya ƙarasa cikin sigar tambaya.

Anutse ya buɗe idanunsa dake lumshe kana ya fesar da numfashi mai ɗumi jin idanu na yawo akansa yasa ya kalli ƙofa akan Malam Saidu dake zaune da uban tumbi ya sauƙe idanunsa wani murmushi Malam saidu ya sakar masa.

Ya mutse fuska Sir Abdallah yayi tare da kallon sauran Malaman da dake zaune a Office ɗin Wanda baki ɗaya idanunsu ke kansa.


Cike da Izza da ƙasaita yace.

“Bana tunanin akwai alamun rashin gaskiya atare dasu domin banga dalilin da zaisa suyiwa wannan mutumin sharri ba muddin babu abinda ya haɗa su”.

Cike da borin kunya Malam Saidu ya miƙe ya kalli Principal kana yace.

“Malam Hassan na lura da bawan Allah nan kwara-kwata baya ƙaunar ganina acikin makarantar sa ya tsaneni ƙofar da zai koreni kawai yake nema saboda yana da karfin faɗa aji amma na dogara ga Allah”.

  Wani kallo Sir Abdallah ya watsa masa cike da tsanarsa lallai ɗan Adam sai Allah to kuwa tabbas zai saita masa tunaninsa...


Hannu Principal ya ɗaga masa cike da kamala yace.

“Ya isa haka Malam Saidu ba abinda ya tara mu ba kenan mu ba ƙananun yara bane da zamu riƙa maimaita magana ka kama kan ka”.

Komawa Malam Saidu yayi ya zauna yana huci.

Anutse Principal yace.

“Bundi ina ganin ya kamata abar wannan maganar domin ga dukkan alamu yaran nan basu da gaskiya tunda gashi cikinsu babu wacce tazo bayan kuma sun san da maganar sannan kaima kada aɓata maka lokaci”.


  Afusace Sir Abdallah ya miƙe tare da bugar table ɗin yana huci yace.

“Im Possible babu ta yanda za ace wannan yaran basu da gaskiya na tabbata suna da gaskiya dan haka wallahi wa rabbul ka'aba muddin yaran nan suka sake tabbatar mana da abinda suka faɗa saina ɗauresa sai dai ya gama rayuwarsa a Prison domin babu amfanin irin wa'annan adoron ƙasa”.


Wani irin kaɗawa hanjin cikin Malam Saidu yayi tare da bada sautin ƙururu-ƙurrr ƙurrrr.

Cikin ƙoƙarin ɓoye tsoronsa yace.

“Ni san akan gaskiya ta nake kuma nan bada jimawa ba gaskiya za tayi halinta gashi tun kafin aje ko ina gaskiya ta fara bayyana”.


Ɗaya daga jikin Malam man ne ya kalli Principal tare da cewa.

“Aganina ya kamata idan akwai Number gidansu Akira aji dalilin rashin zuwanta sannan idan da hali aturo ta”.

Jinjina kai Principal yayi tare da faɗin.

“Ƙwarai kuwa wannan shawarar ita za abi tun da akwai Address da Number ko wani ɗalibi ajikin file ɗin sau aduba nata akira.

Malam Saidu da zufa ya karyo masa ya shiga zazzare ido.


Sir Auwal dake tsaye gefen Sir Abdallah ya jinjina kai tare da cewa.

“Tabbas haka za'ayi idan yarinyar tazo komai ya ƙare”.

Jinjina mai Principal yayi cike da gamsuwa ya kalli Sir Auwal tare da cewa.

“Auwal duba mana File ɗinta”.

Kai Sir Auwal ya gyaɗa kana ya nufi jikin cabort ya fara bincika files ɗin ya kai minti ashirin yana dubawa kafin Allah yasa ya gani file ɗin ta ya ɗauka ya buɗe number biyu ya gani ajiki ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗago files ɗin ya miƙawa Sir Abdallah.

Karɓa Sir Abdallah yayi ya ɗauki Number na farko yayi dealing awayarsa.

Kai tsaye baturiyar dake magana tace switch Off sake dearling ɗayar yayi shima still swich off dogon tsaki yaja kana ya miƙe atake yanayin fuskarsa ya sauya.


Malam Saidu dake zaune ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.

“Nifa wannan ƙazafi da cin mutunci da kuma daraja da kimata da wata ƙaramar yarinya ke neman zubar min bazan lamunta ba bayan haka kuma ina zargin sata akayi domin ta wulaƙanta furfurata”.


Wani banzan kallo Sir Abdallah ya watsa masa ji yake tamkar ya shaƙesa ya mutu ya tsani mutum mara kamun kai da sanin ciwon kansa.

Malam Saidu kuwa kallon Principal yayi tare da faɗin.

“Malam Hassan ina da lambar da zan kira asameta kai tsaye idan ka amince sai na kira?”.

Kai Principal ya gyaɗa tare da cewa.

“Ok zaka iya kira”.

Cikin sauri Malam Saidu ya ciro wayarsa a aljihu tare da dearling number Mamawo yana jin kiran ya shiga ya miƙe ya fita da kallo suka bisa.

Sir Auwal ya kalli Sir Abdallah tare da cewa.

“A.A Zaman nifa ba. Yarda da fitan mutumin nan ba Akira sa ya dawo yayi waya agaban kowa in dai har ba wani abu yake ƙullawa ba”.

Kai Principal da sauran malaman suka gyaɗa alamar haukane.

Sir Abdallah kuwa numfashi ya fesar kana yace.

“No ku barshi”...


   Lokacin da kiran Malam Sa'idu ya shiga wayar Mamawo tana ƙoƙarin fita daga gidan.

Ganin kiransa yasa ya tsayawa azauren ta gyara Robalin dake jikin wayar kana ta kai kunne tare da cewa.

“Yah Saidu ina kwana”.

Cikin ƙasa da murya yace.

“Lafiya Saude Ina Neenah tazo yanzu ana buƙatar ganinta amakaranta akan wannan maganar da mukeyi ina fatan kin ja mata kunne domin kada asamu matsala”.

Zare ido Mamawo tayi cikin alamun tsoro tace.

“Yah Saidu nifa wallahi tsoro na keji,Watanin kada ta canza magana yasa akore mu agari ko kuma asa wa'annan dogarawan marasa imani su zane mu”.

Fuska ya ɓata tare da faɗin.

“Babu abinda zai faru ke dai ki tsawatar mata sannan ki jadda da mata kada tayi kuskuren kiran sunana akan ƙazafin data yimin kuma alƙawarin kuɗin mu yana nan”. 

Bai jira cewarta ba yayi saurin katsewa.


Da kallo tabi wayar sai kuma ta juya ta koma cikin gida kai tsaye ɗakin su Neenah ta nufa.

Daga bakin ƙofar ta tsaya ta ɗaga labulen zaune ta hangota hannunta dafe da cikinta idanunta na tsiyayar da hawaye.

Ya mutse fuska tayi cikin halin ko inkula tace.

“Ke kuma fa kika zo kika takure kamar wata babanin akuya ba zakije makaranta bane?”.

Araunane ta ɗago idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kalleta muryanta na rawa ta furta.

“Mamawo ciki na ciwo yake sannan ƙafofina sun ɗaure bazan iya zuwa ba”.

Bakin zaninta ta since ta curo Naira ɗari ta wurga mata kana tace.

“Ze wuce yunwa ne kije ga can guntun ɗumame atukunya sai dai ba miya ki duba akwai gauta akan murfin kwano kije daki ki ɗauki ƙaragon hamsin Kisha da koko kina gamawa ki tafi makaranta ina fatan kin riƙe maganar dana faɗa miki jiya wallahi tallahi idan kika kuskura ki kayi ganganci ƙin bin maganata Hmmm?”.

Ta ida maganar tare da juyawa har ta fita ta dawo ta ɗaga labulen tace.

“Kada fa ki bari in dawo in same ki maza ki wuce ki tafi dan ko kin zauna babu abin arziƙin zaki tsinanamin sannan idan kinje an tambayeki wani abu akan dan Uwana ki tozarta shi wallahi sai dai ki nemi wani gidan”.

Araunane ta gyaɗa kai kana ta miƙe da ƙyar ta buɗe Ghana Masgon ta ɗauki Uniform ɗinta ta sanya kallon agogon dake bangon dakin tayi karfe goma da minti arba'in..

Numfashi mai zafi ta fesar tare da ɗaukar jakarta ta rataya ta fita kofar gidan taja ta rufe ahankali take tafiya yayin da cikinta ke sake damkarta sai da ta fita bakin hanya ta samu adaidaita ta shiga banda tsinkewa da bugawa da masifeffen karfi babu abinda zuciyarta keyi.


Suna isa bakin makarantar mai adaidaitan yayi parking fita tayi ta miƙa masa Naira ɗarin kana ta nufi cikin makarantar dai-dai lokacin da Sir Auwal ya fito daga Office ɗin ganinta yasa ya ɗaga mata hannu alamar tazo ba musu ta nufi inda yake zuciyarta na cigaba da bugawa kallonta yake har ta iso kusa dashi baice da ita komai ba har suka shiga office ɗin.

Ganin mutanen dake Zazzaune a Office din yasa cikinta sake murɗawa da masifeffen karfi cikin sauri ta rintse Idanunta cikin raunin Murya tace.

“Ina kwanan ku”.

Principal da Sir Auwal ne kaɗai suka amsa Sir Abdallah kuwa goshinta ya tsirawa ido yana kallo.

Ajiyar zuciya Principal ya sauƙe kana yace.

“HeadGirl sake maimaita abinda kika faɗa shekaran jiya akan Malam Saidu”.

Ahankali ta ɗaga kai ta kalli Malam Saidu kana ta kalli Principal zuciyarta na tsinkewa da masifar ƙarfi!.

Zaman farin eyeglass dake fuskarsa ya gyara yace.

“Head girl kinyi shiru ki sake maimaita abinda kika faɗa akan Malam Saidu domin musan matakin da zamu ɗauka akansa”.

Kai ta girgiza hawaye na kwaranya daga idanunta kana ta kife akanta cinyarta ta shiga rera kuka me tsuma zuciya shin taya zata fara shawo bakin zaren shin taya zata ƙaryata kanta da kuma mutumin dake ƙoƙarin cetonta.

Duk ido suka zuba mata suna jin yanda shesh-sheƙan kukan ta ya karaɗe cikin Office ɗin.


Sir Auwal dake tsaye yace.

“Neenah ke ake sauraro kuma kinyi shiru ki faɗi abinda ya kawo mu kowa ya watse”.

Cikin rauni da tsinkewar zuciya ta ɗago idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kallesu ɗaya bayan ɗaya ahankali ta maida idanunta kan Sir Abdallah daya zuba mata idanunsa da suka sauya launi lumshe idanunta tayi muryan Mamawo ya dawo sabo acikin Dodon kunnenta ciki sallamawa da gajiyawa da rayuwar kana da karaya tace.

“Ƙarya nayi muku duk abinda na faɗa muku ba gaskiya bane ƙazafi nayi masa sannan saka ni akayi”.

Cike da mamaki suka kalleta Malam Saidu kuwa wani miskilin murmushi ya saki yana kada ƙafarsa.

Principal da mamaki ya gama cikasa yace.

“Ban fahimci me kike nufi ba kamar ya saka ki akayi sannan waya saki?”.

Neenah kuwa lokaci ɗaya jikinta ya kama ɓari idanunta suka fara lumshe wa duhu na mamaye su da ƙyar ta iya ɗaga hannunta kana tace.

“Wannan shine ya sani!”.

Da sauri suka kalli saitin hannunta atare suka zare ido cike da dumbin mamaki suna kallon wanda ta nuna...


*@AREWABOOKS REALESHAA*


*@WATTPAD REALESHAA*



_Ya Allah Ubangji kajiƙan mahaifina ya Allah kagafar ta Masa zunubansa ya Allah ka kai haske kabarinsa_


_Ayi shearing saboda Allah ƴan Uwa masoya da Abokan arziki_


*👭GARKUWAR MATA👭*

*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka  kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*

*GA*

*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*

Rage tumbi💯

Nono💯

Sanyi💯

Karin kiba💯

girmar hips💯

Ni'ima💯

Sabulai💯 

Humra💯

Turarukan wuta💯

Matsi💯

Miski💯

Dilka💯

Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki

GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI

***

***


         *ESHAA CE*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.