Free chapter · Read without an account

12

by Aishatu Abdullahi Idris · Sawun Giwa

*SAWUN GIWA*

_Ya take na Raƙumi_




_By_

*Aishatu Abdullahi Idris*

_REAL ESHAA_



*F-R-PG 12*

Wani irin gudu Sir Abdallah ke shararawa akan titin tamkar zai tashi sama duk wata mota dake gabansa ko bayansa ƙoƙarin kauce masa yake saboda yanda yake zuga gudun tamkar zai tashi sama babu abinda ke tashi acikin motar face hucin numfashinsa da kuma bugun zuciyarsa daya tsananta sosai yake gudun yayin da baki ɗaya ilahirin jikinsa ke fidda zufa tamkar an watsa masa ruwan Zafi gudu yake batare da yasan Ainihin inda yake saka motar ba...

Abakin wani tan gamemen gate da aka rubuta City Hospital ya danna hong da masifar ƙarfi cikin sauri mai gadin ya buɗe masa yana shiga yayi parking atsakiyar asibitin kana ya fito batare daya rufe gaban motar ba ya buɗe baya tare da sanya hannunsa duka biyu ya janyo gangar jikinta da babu alamar numfashi atare da ita kana ya rungumota jikinsa tare da manna kanta aƙirjinsa da gudu ya nufi haraban asibitin cikin ɗaga sautin murya yake faɗin.

“Dr!,Dr!!,Dr!!,Norse!,Norse”.


  Da gudu Norse's dake reception suka fito daga cikin Ward kasancewar private hospital ne ga kuma dare yasa babu hayaniyar mutane sai ɗai-ɗaiku dake waje sai kuma wanda suka san fuskar Sir Abdallah suka bisa da kallo ganin daga shi sai Singlet kana ga yanda duk jikinsa ya ɓaci da jini ga kuma mace rungume aƙirjinsa wacce ke sanye da rigarsa daya gama ɓaci da jini da gudu ya nufi stair yana haɗa hanya yayin da yake taka stair ɗin bibbiyu batare da yasan ainihin inda yake sanya ƙafarsa ba da gudu Norse's din suka bi bayansa tare da turo godo kana suka haɗa baki wajen cewa.

“Yallaɓai ka ɗaura ta anan”.

Wani irin kallo ya musu tare da sake ƙanƙameta ajikinsa ya nufi wani office yana cigaba da cewa.

“Dr!,Dr!”.


Aruɗe Dr Khameel ya zare ido cikin tsananin kaɗuwa ya nufi kansa tare da cewa.

“Innalillahi wa'inna ilahai rajiun _A.A Zaman_ lafiya meke faruwa?Wacece ba lafiya?”.

Cikin tsananin tashin hankali da raunin murya irin na wanda ke gab da zub da hawaye yace.

“Dan Allah kaceci rayuwar ta kada ka bari ta mutu dan Allah ka ceceta Dr Khameel!”.

Cike da al'ajabi da kuma tausayawa Dr Khameel ya kalli Norse da suka turo gadon yace.

“Calm down A.A Zaman be a Man In sha Allah babu abinda zai sameta ka ɗaura ta anan”.

Kai kawai Sir Abdallah ya iya gyaɗawa tare da kwantar da ita akan gadon ya yunƙura da niyyar tashi yaji hannunta acikin nashi cikin wani irin yanayi yabi hannunta dake sarƙafe da nasa da kallo ƙoƙarin janyewa yayi amma ya kasa wani irin ruƙon tsauri tayiwa hannu.


Cikin sauri Norse guda biyu suka tura gadon Sir Abdallah na biye dasu anutse Dr Khameel ya ƙarasa wajen tare da buɗe hannun Neenah da ƙarfi ya janye hannun Sir Abdallah acikin nata kana ya juya ya kallesa cikin tausayawa yace.

“A.A.Zaman ka fita zamu fara aiki”.

Wani irin kallo Sir Abdallah ya watsa masa da idanunsa da suka sauya launi zuwa ja tamkar babu fari aciki kai ya girgiza kana yace.

“No Dr bazan iya fita ba duk wani abu da zaku mata kuyi mata agaban idona but babu inda zanje ina so inga numfashinta ya dawo!”.

Numfashi Dr Khameel ya fesar ganin yanda Sir Abdallah ya jingina bayansa da jikin bangon alamar bazai fita ba.

Anutse Dr Khameel ya fara dubata cike da tsantsan ƙwarewa da sanin makaman aikinsa cikin minti goma sha biyar ya samu numfashinta ya daidaita.


  Wani iri zazzafan ajiyar zuciya Sir Abdallah ya fesar tare da ƙarasawa bakin gadon ya durkusa ƙafafanun sa kana ya janyo tafin hannunta ya riƙe acikin nasa sai kuma ya manna goshinsa akan hannunta atake hawaye masu ɗumi suka zuba masa cike da tsananin tausayawa yake kallon kyakkyawar fuskarta da tayi fayau ta kumbura.

Idanu Norse's mata biyu dake tsaye suka zuba masa sosai ya burgesu ganin yanda yake bata kulawa domin duk zatonsu matarsace kuma wannan shine First night ɗin su.


Dr Khameel kuwa cike da damuwa yace.

“A.A.Zaman tunda numfashinta ya dai-dai ta dan Allah ka fita zamuyi mata abinda ya kamata domin aikine babba zamu gudanar akanta”.

Da wani irin sauri Sir Abdallah ya kallesa tare da girgiza masa kai muryarsa araunane yace.

“No Dr babu inda zanje idan har banga ta buɗe idanunta ba,Kuma ba zaiyu ace kaine zaka dubata sai dai ka samu ƙwararriyar Dr mace ta dubata saboda wa'annan ma ban yarda da aikinsu ba”.

Ya ƙarasa maganar tare da nuna Norse's biyu dake tsaye.


Atare Dr Khameel da Norse's suka kallesa zaiyi magana Sir Abdallah yayi saurin ɗaga masa hannu alamar yayi yanda yace hakan yasa ya tsuke bakinsa tare da kallon ɗaya daga cikin Norse's dake tsaye yace.

“Ruƙayya ki duba Dr Hajja Adama idan tazo kice tazo ta dubata”.

Kai wacce ya kira da Ruƙayya ta gyaɗa kana ta juya ta fita kai tsaye Office dake Upesite dana Dr Khameel tayi knowking daga ciki wata sanyayyar murya mai cike da nutsuwa ta amsa tare da cewa.

“Come in”.

Buɗe ƙofar Ruƙayya tayi tare da kallon kyakkyawar matashiyar dake zaune tana rubuce-rubuce cike da ladabi tace.

“Dr Hajja Adama Dr Khameel na kiran ki akwai wata Emargancy percien da aka kawo yake so ki du bata”.


Numfashi ta fesar tare da cewa.

“Subhanallah Haihuwa ce ko accident naga har ƙarfe 2:00am?”.

Kai ta girgiza cikin ƙasa da murya tace.

“No Dr inaga case na fyade ne,ko kuma sabon Aure Saboda yanayin da aka kawota kamar macacciya da ƙyar Dr ya samu numfashinta ya daidaita abin tausayi!”.

Azabure ta miƙe cikin yanayin tashin hankali da razani kana da tarin tausayi ta furta.

“Innalillahi wa'inna ilahai Fyaɗe kuma?”.

Kai Ruƙayya ta gyaɗa kana cikin ƙasa da murya tace.

“Kuma sai kin ganta yarinya ƙarama abin gwanin ban tausayi duk da dai ban tabbatar ba”.

Cike da tausaya tace.

“Ubangiji Allah ya ƙwato mata hakkinta in dai har fyaɗe ne Ubangiji ya wulaƙanta duk wanda yayi wa ƴaƴa mata fyaɗe”.

Bata jira cewar taba ta nufi kofa kai tsaye ɗakin da ake kwantar da masu irin wannan matsala tashiga.


Nannauyan Ajiyar zuciya Dr Khameel ya sauƙe kana yace.

“Dr gata nan ki du bata kai ta gyaɗa tare da kallon Ruƙayya dake biye da ita izini ta bata data gyara labulen wajen wanda ze kewaye gadon kana ta kalli Sir Abdallah da har zuwa lokacin ke durƙushe gaban Neenah kana tace.

“Dr dole tana buƙatar jini da za'a ƙara mata cikin gaggawa”.

Cikin sauri Sir Abdallah yace .

“Muje aɗibi nawa asa mata”.

Kallonsa Dr Hajja Adama tayi kana ta kalli Dr Khameel tace.

“Ok Dr aje agwada nashi idan yayi dai-dai da nata sai asa mata”.

Kai ya gyaɗa kana suka fita da kansa ya rakasa aka ɗibi jinin cikin sa'a jinin yayi dai-dai da wanda za'a ɗiba ba ɓata lokaci aka ɗibia Dr Khameel na son tambayarsa ainihin abinda ya samu yarinyar da kuma wanda yayi mata haka sai dai babu damar hakan ganin bashi da nutsuwa.


Bayan sun koma Dakin da aka kwantar da ita Sir Abdallah ya durƙusa agaban gadon tare da riƙe tafin ƙafanta hawaye masu ɗumi suka zubo asaman kuncinsa.

Ajiyar zuciya Dr Hajja Adama ta sauƙe tare da kallon Sir Abdallah kana tace.

“Please yallaɓai ka fita zamu fara aiki”.

Ba musu ya miƙe ya fita Dr Khameel na biye dashi direct office ɗin Dr Khameel suka shiga.

Suna shiga ya zauna akan kujera tare da tallafe kansa yana jin wani irin azabebben ciwo azuciyarsa tabbas duk wanda ya keta mata haddi ya gana cutar da rayuwar cuta mafi muni.


Dr Hajja.Adama kuwa cike da tsantsan ƙwarewa da sanin makaman aikinta tashiga duba Neenah sosai ta tausaya wa yarinyar wacce s shekaru bazata wuceta ba duk wani rauni dake jikinta sai da ta gyara tayi mata dressing.


Acan Office kuwa kafaɗar Sir Abdallah Dr Khameel ya dafa tare da cewa.

“Cslm dawn A.A Zaman me yasameta?”.

Uffan Sir Abdallah bai ce masa ba sai ma Runtse idanunsa da yayi ganin kamar bai son magana yasa Dr Khameel tsuke bakinsa...


    Cikin tsananin tashin hankali Baba ya kalli agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa wanda ke nuni da ƙarfe 2: 30am araunane ya juya ya kalli Maryam da idanunta suka kaɗa sukayi Jawur dasu alamar taci kuka ta gode Allah kana ahankali ya maida idanunsa kan Mamawo dake tsaye jikin gwafa ta riƙe fuskar nan nata babu Annuri kona misƙala zarratin sunkuyar da kai ƙasa yayi zuciyarsa ba daɗi.

Cike da takaici da ɓaci rai Mamawo ta kalli Baba tace.

“Watanin ni dai wallahi duk wanda yayi sanadiyyar hanani bacci ban yafe masa ba wannan ai zalunci da ɗaukar hakki ne yarinya ta tafi yawon Gaulancinta agari saboda tsabar tsagoran wulakanci sai asamu zaman jiranta tana can tana holewa”.

Cike da takaici Maryam da muryanta ya dishe saboda kuka tace.

“Mamawo wannan wace irin rayuwa ce kin tura Baiwar Allah makaranta acikin halin jinya sannan yanzu kin dawo kina jifanta da mugayen kalamai wanda kinsan ba halayyar ta ko ɗabi'unta bane shin ba addu'a ya kamata kiyi mata ba”.


Cikin sauri ta tari numfashin ta tare da faɗin.

“Kulll Maryama Allah ya sawwaƙa na yiwa wannan Gafalalliyar Addu'a to idan ma nayi addu'ar ai nayi abanza tunda Uwarta ma ayawon gantali ta ƙare dan haka itama a gantale zata ƙare”.

Cikin wani irin fushi da tsananin ɓacin rai kana afusace Baba yace.

“Saude!”.

Tsabar yanda zuciyarsa ke ta farfasa yasa ya kasa tuna cewa tsakiyar dare ne yasa ya ɗaga sautin muryarsa.

Da mamaki ta kallesa jin yanda ya buga mata tsayuwar ta ta gyara kana tace.

“Na'am Malam Audu”.

Sunkuyar da kansa ƙasa yayi cikin raunin murya yace.

“Idan har ba zaki iya bin Kyauta da Addu'ar alkhairi ba to dan Allah kije ki kwanta babu amfanin tsayuwar ki anan!”.

Baki ta taɓe kana tace.

“Yo ai yafi Nono fari haba jama'a Watanin irin wannan jaraba da rashin son gaskiya da mai yayi kama yarinya budurwa ta tafi makaranta taƙi dawowa sannan atsaya ana wani zubar mata da hawaye har da wani gadi na banza da wofi saboda rashin mafaɗi”.

Cikin shesh-sheƙan kuka Maryam ta kalli Baba da har zuwa yanzu kansa ke ƙasa tace.

“Fisabillahi Baba kana tsaye kana jin tana jifanta da muggan kalamai amma ba zaka dakatar da ita ba sannan ba zaka ɗauki matakin daya dace akanta ba!?, Wallahi idan har na rantse bazan yi kaffara ba akan tana dasa hannu acikin abinda ya samu Sister Neenah”.

Kai ya girgiza cike da rauni yace.

“A'a Maryama Ni duk wannan ba damuwa ta bace damuwa ne be wuce duk inda ake tunanin Kyauta zata je anje bata nan ba ina tsoron wani mugun abu ya sameta ayanda duniya take ba gaskiya gata ƴa mace”.


Tsaki Mamawo taja tare da shigewa ɗakinta cikin ƙasa da murya tace.

“Kada Allah yasa ta dawo har gaban Abada kowa ma ya huta haba jama'a wannan jaraba da mai yayi kama.


    Awannan dare haka zuciyoyo da dama suka kwana cikin tashin hankali da ɗimuwa Musamman Sir Abdallah duk da cewa duk wani temako daya kamata anbawa Neenah amma bata farfaɗo ta dawo cikin hayyacinta.

Haka zalika Imraan,Indu da Aunty Munah suka kwana akan Ummuh da numfashinta ke kai komo yayin da tsananin firgici da abinda Dr yace zai iya faruwa akanta ya hana su runtsawa.

Acan ɓangaren Lateefa ma hakance ta kasance yanda mijinta ke fushi da ita da kuma yanda take kiransa baya dagawa yayi masifar ɗaga mata hankali domin Aduk sanda yayi irin wannan fushin takan ɗauki tsawon lokaci batare data shawo kansa ba domin yakan ɗauki ɗauki lokaci mai tsayi batare daya kulata ba Ayanda sukaga rana haka suka ga dare.


Washe gari:Kiran sallar Farko acikin kunnen Sir Abdallah nufashi ya fesar tare da kallon Neenah da hannunta ke ɗauke da ƙarin jini ahankali ya tsirawa fuskarta da yayi fayau Idanu hannu yasa ya shafa goshinta dake naɗe da bandeji dogon gashinta na kwance akafadarta kamar me tsoron wani abu ya maida hannunsa saitin bakinta dake kumbure lumshe idanunsa yayi tare da kallon shatin yatsu biyar akuncinta wanda har zuwa yanzu bai baje ba.

Zazzafar ajiyar zuciya ya fesar tare da miƙewa ya cire ƙarin jinin kasancewar ya ƙare miƙewa yayi tare da ɗaukar ta kamar Baby ya rungumeta aƙirjinsa ahankali numfashinta ke sauƙa akan faffaɗan ƙirjinsa dake ɗauke da lallausan gargasa yayin da ya ya sakala hannunta asaman wuyarsa ahankali yake tafiya ba tare da yayi wani hayaniya ba.


Karo suka kusa bugawa da Imraan daya fito daga dakin da Ummu ke kwance domin kiran Norse cikin sanyin murya Imraan yace.

“Kayi haƙuri”.

Ya ida maganar yana ƙoƙarin leƙa fuskarta domin wani irin bugawa da zuciyarsa yayi haka nan ya tsinci kansa da son ganin fuskarta...


  Cikin sauri Sir Abdallah ya girgiza masa kai alamar bakomai kana ya nufi waje.

Da kallo Imraan ya bisa yana ji kamar yaje ya buɗe fuskar wacce ke hannunsa.

Cikin sa'a har ya fita haraban asibitin bai sake haɗuwa da kowa ba...


 Agaban motar ya ajiyeta gefen me zaman banza kana ya zagaya yashiga mazaunin driver sit ɗin ya kwanta tare da ɗaura mata belt kana ya tayar anutse ya danna hong cikin sauri mai gadin dake bacci ya miƙe tare da buɗe masa gate din ahankali ya cinna hancin motarsa waje tare da dai-daita hancin motarsa akan Kwalta zamewa kanta yayi agefe cikin sauri ya gyara parking tare da janyota jikinsa ya rungumeta kana ya cigaba da driving ahankali.

Yana Isa ƙofar tangamemen gidansu ya danna hong lokacin har anfara kiran Assalatu cikin sa'a babu kowa aharabar gidan sai masu gadi su biyu.

Ahankali ya fito bayan yayi parking gani yayi ɗaya ya zagaya ban ɗaki ɗayan kuma yana rufe gate kana security dake gadin ƙofarsa yana bacci ajiyar zuciya ya sauƙe cikin sauri ya buɗe gefen da take kwance ya ciro ta kana ya nufi sashen sa akuma dai-dai lokacin mai gadin ya juya da kallo ya bisa.

Bayan yasa mukulli ya buɗe yashiga falon bakinsa ɗauke da sallama kai tsaye bedroom ɗinsa ya shiga ya kwantar da ita akan gadon lokaci ɗaya zuciyarsa yayi baƙiƙƙirin ganin yanda jini ya bushe arigarsa dake jikinta

Juyawa yayi yashiga toillet zuciyarsa na ƙuna ya daɗe yana wanka kafin ya fito agurguje ya shirya cikin Pjmas Neavy blue da ya amshi fatar jikinsa kana ya nufi masallaci lokacin har anyi raka'a ɗaya cikin gaggawa ya ida shiga cikin masallacin tare da jona jam'i kana ya tada kabbara bayan an idar liman yayi sallama yayi saurin miƙewa ya fita batare da ya zauna yayi azkhar kamar yanda ya saba ba ya miƙe ya fita bakinsa ɗauke da sallama yashiga falon farko duk da yasan cewa babu kowa amma yasan muhimmanci amsa sallama,kana kai tsaye ya wuce na biyu tare da shiga bedroom kwance ya hangota har zuwa lokacin bacci take yayin da rigar ya zame ya koma sama santala-santalan cinyoyinta Chocolate suka Bayyana.


Lumshe idanunsa yayi tare da fesar da numfashi mai ɗumi kana ya nufi gefen gadon ya zauna tare da sanya hannunsa ya shafa lallausan gashin kansa daya baje asaman kafaɗarsa ya kai kimanin minti talatin ahaka kafin ya saki ajiyar zuciya.


Tunanin taimakon da zai bata ya fara yasan koda giyar wake yasha bai isa ya fara tunkarar sashen Ammie da ita ba duk da cewa Ammie macece mai sauƙin kai da kamala amma bata yarda da zalunci ko rashin gaskiya muddin ya Kaita can zata kai maganar gaba zuwa wajen hukuma wanda zai sa dole maganar ta fita wanda basu sani ba su sani wannan dalili yasa ya daukota daga asibitin kafin Dr Khameel ya cigaba dayi masa tambayoyi har akai ganin Wacece ita.


Iska mai zafi ya furzar tare da dafe kansa da duka hannunsa biyu sai yanzu yake jin takaicin daya kori Hadimai mata dake sashensa amma yanzu ya zama dole ya nemo Amintattiyar Hadimarsa mai suna Mama Asabe itace kaɗai zata iya kula da ita cikin aminci da sirri.

Idanunsa ya lumshe kana ya miƙe tare da shiga toillet tamkar kazar da ƙwai ya fashewa aciki ruwan zafi ya tara mai yawa acikin Bathtub kana ya ɗauki Dettol ya zuba kallon towel ɗinsa dake rataye yayi ya ɗauka ya fice.


Tsayawa yayi akan ta tare da tsira mata manyan idanunsa dake ɗauke da tsantsar damuwa ya kai minti uku atsaye yana tunanin ta inda zai fara ajiyar zuciya ya sauƙe tare da bin shawarar zuciyarsa hawa tsakiyar gadon yayi ahankali ya sanya hannunsa ya janyota jikinsa idanunsa ya rintse tare da ɓalle botiran gaban rigar ya cire mata,Towel din ya laluma ya ɗaura mata sai alokacin ya sauƙe numfashi kana ya buɗe idanunsa ya ɗauketa ya nufi toillet yana shiga ya sanya ta acikin ruwan zafin batare daya cire mata towel ɗin ba duk da cewa bacci take bata cikin hayyacinta sai da taja dogon numfashi tare da sakin ajiyar zuciya mai nauyi.


  Ahankali ruwan ya riƙa ratsa ko wani lungu da saƙon dake jikinta kana riƙa sauya launi daga fari zuwa ja kafin minti goma ruwan ya canza baki ɗaya ya koma jajawur cikin wani irin yanayi yake kallonta ɗaya daga cikin towel din dake rataye ya ɗauka ya naɗota aciki kana ya zare wancan batare daya yarda ya kalli tsaraicinta ko kuma taɓa wani sashe na jikinta ba duk abinda yake mata yana matane amstsayin ƙanwarsa wacce yake ji tamkar ciki ɗaya suka fito kwantar da ita yayi akan gadon ido ya tsira mata yana tunanin kayan da zaisa mata yasan koda ya fita yanzu ba zai samu wani shago da zai siyo ba haka zalika kayansa ba za suyi mata ba bare kuma na Ammiensa wayarsa ta ɗauka tare da turawa Manager sa dake Dubai saƙo ya faɗa masa Samfurin kayan da yake so.


Numfashi ya fesar tare da juyawa ya fita lokacin har gari ya fara haske bayi da ma'aikata sun fara zirga zirga jefi-jefi kai tsaye sashen Gimbiya Fa'izah ya nufa yana tunanin rabonsa da shigowa sashen tun ranan da Aljanun Meerah suka tashi ahankali ya murɗa handle ɗin ƙofar cikin sa'a ya samu ƙofar abuɗe cikin sanɗa yashiga da kallo yabi falon ba kowa sai AC dake aiki ajiyar zuciya ya sauƙe tare da nufar Corridor kana ya murɗa handle ɗin bedroom ɗin Meerah ya shiga wutan dakin akunnen yake hakan ya bashi da mar kallon Meerah dake kwance jikinta sanye da Sleeping drees riga da wando fari sol ta ɗage ƙafafunta sama cikin sauri ya kawar da kansa tare da jan siririn tsaki cike da nutsuwa ya nufi jikin Siff ɗinta ya buɗe ido ya tsirawa kayan baki daya babu Suturar arziki aciki kamar Atamfa,Less,Ko Shadda,duk English wears ne wanda mafi yawa top marasa hannu ne wasu kuma hannu ɗaya sai wando Crazy sai kuma skirt wanda mafi yawa pencil ne nasu tsagu da half gownt wasu kuma dogine amma marabansu da babu kaɗan ne rufe Siff ɗin yayi tare da juyawa zai bar wajen dan baiga kayan da zai iya ɗauka mata ba wata zuciyar tace to idan baka ɗauka ba kana da wanda zaka sama tane tuna hakan da yayi yasa ya tsaya ya dauki wani half gownt Maroon me hannun Sphagetti,da wani farin dogon riga kala biyar ya ɗauka me hannu kana ya buɗe gefen Pants dayawa ya gansu wani rabin dozen ya ɗauka da always.


Meerah dake kwance ta buɗe idanunta tare da miƙewa ta zauna cikin muryan bacci tace.

“My Prince?Mekakeyi acikin kayana?”.

Dum-dum haka ƙirjinsa ya buga ahankali ya juya tare da ɓoye hannunsa abaya sai kuma ya ɗaure fuska tare da nufar ƙofa.

Cikin sauri ta diro gadon tare da shan gabansa cikin tsaresa da ido tace.

“Me kake yi acikin kayana ko dai?,Ko dai?”.

Idanunsa dake lumshe ya ware babu walwala atare dashi yace.

“Ko dai mai?”.

Ido ɗaya ta kashe masa tare da cewa.

“Ko dai Nunnura(Bita zai-zai) zaka min ajikin kayana kasan fa ance idan mutum na neman wani abu sai ya samu kaya ya maka sammu ajiki domin yafi saurin kamawa toh amma dai kar ka damu ni ba sai kamin komai ba aini mallakin kace”.

Ta ƙarasa tare da kai hannunta bayansa tana kashe masa ido.

Baya yaja cikin haɗe girar sama dana ƙasa yace.

“God forbid!, Nayi wani abu akan ki aini ko ɗaura min ke akayi aƙafa ina mai tabbatar miki da zan since in jefar domin bakya cikin jerin irin matan da zan Aura”.

Afusace tace.

“Wallahi kayi ƙarya babu Lafiyayyan ɗa namiji da zai ganni yace baya so kuma kaima nasan faɗa kake dan kaji daɗin bakin ka”.

Baki ya taɓe tare da cewa.

“Hmmm tunda makafi ne ko?domin babu cikekken Namiji mai hankali, nutsuwa da zai ƙyasa ki”.

Aƙufule tace.

“Kuma ahakan zaka aure ni ka zauna dani sannan in haifa maka ƴaƴa koda kana so ko baka so”.

Wani kallo ya watsa mata tare da juyawa ya fita cikin sauri domin bashi da lokacin shirmenta.


Da mamaki tabi bayansa da kallo sai alokacin ta tuna da abinda ke riƙe ahannunsa cikin sauri ta leƙa shi ko alamar sa bata gani ba tsaki taja tare da komawa ta shiga toillet tana jin zafin kalamansa.



Acan Asibiti kuwa ahankali Ummu tayi murmushi tare da girgiza kai kana tace.

“Na ƙoshi Autana ko so kike cikina ya fashe?”.

Langwabar da kai Indu tayi tare da tura baki tace.

“Ayyah Ummu ko rabin cup din fa baki shaba gashi kuma Yah Khameel ya bada magungunan ki idan har ba kisha tea da yawa taya zaki sha maganin”.

Aunty Munah dake gefen hagunta ta zuba Perpersoup a plate Wanda tasa mai aikin Ummu ta dafa a cokali ta ɗiba ta kai mata baki cike da kulawa tace.

“Ummu ki daure kisha Perpersoup din ko ba yawa”.

Kallon fuskar Indu tayi taga idanunta ya ciko da ruwan hawaye.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da sakar musu da murmushin ƙarfin hali tace.

“Bana sha'awar cin komai amma bani kaɗan Autana kada kiyi kuka”.

Kai Aunty Munah ta gyaɗa kana ta fara bata.

Ba laifi taci ya kai rabi kafin ta ture hannunta kallon Indu da har zuwa yanzu jikinta ke sanye da Uniform tayi tace.

“Autah meyesa Baki bi Yayanki kinje kin canza kaya ba!?”.


  Cikin sanyin murya da tausayawa tace.

“Ummu bana son tafiya in barki nafi so idan aka sallame mu mu tafi tare”.

Murmushin ƙarfin hali Ummu tayi Allah ne kaɗai yasan yanda take ji ajikinta cikin sanyin murya tace.

“Hmm Autah kenan ai dole wataran in tafi in barki bari na har abada koda kuwa ace kuna so ko bakwa so to dole zan tafi gwara tun yanzu ku fara sabawa kanku da rashina akusa daku!”.

Atare Indu da Aunty Munah suka haɗa baki wajen cewa.

“Haba Ummu wannan wace irin magana ne haka?”.

Lumshe idanunta tayi kana ta jingina bayanta ajikin Pillow cikin sauƙe numfashi tace.

“Maganar gaskiya shi na faɗa muku inaji ajikina rayuwata tazo ƙarshe bani da wasu sauran kwanaki masu yawa Ni dai burina ku cigaba da haɗa kanku sannan kuyi ƙoƙarin ganin kun cika min burina”.

Cikin yanayin tashin hankali da rauni Indu ta fashe da kuka kana tace.

“Dan Allah ki daina fadar haka In sha Allah zamu rayu tare har sai kinga ƴaƴana da jikokina kin aurar dasu amma idan kina irin wannan maganar karya min zuciya kike!”.

Ta ida maganar tare da kallon Aunty Munah da idanunta ke cike da ruwan hawaye ta cigaba da cewa.

“Aunty Munah dan Allah kice ta dai na fadar haka wallahi karya min zuciya take”.

Ahankali Aunty Munah ta share hawayen da suka zubo mata kana ta kalli Ummu da har zuwa lokacin idanunta alumshe suna tsiyayar da hawaye tace.

“In sha Allah ba zaki mutu yanzu ba Ummu da sauran lokaci”.

Cikin sauri ta katseta ta hanyar cewa.

“Zuciyata zafi take min ni kaɗai nasan me nake ji ajikina ku kira min Imraana yazo kafin na mutu!”.

Cikin tsananin tashin hankali Indu ta faɗa jikinta haka ma Aunty Munah rungumeta suka yi suka cigaba da kuka.


Dai-dai lokacin Dr Khameel ya shigo ganinsu ahaka yasa yayi saurin ƙara sawa bakin gadon tare da cewa.

“Subhanallah Ummu,Aunty Munah,Autah lafiya!?”.

Ɗagowa Indu tayi tare da faɗawa jikinsa tana shesh-sheƙan ahankali yasa hannu ya shiga bubbuga bayanta cike da kulawa yace.

“Me ya faru?”.

Cikin sarƙewar murya tace.

“Ka kira Yah Imraan”.

Cikin rashin fahimta yace.

“Meyafaru?”.

Cikin shesh-sheƙan kuka tace.

“Ni dai ka ki rashi Please kace yazo Ummu nason ganin sa”.

Ba musu ya janye ta jikinsa kana ya ciro wayarsa yayi dearling number Imraan amma har ya katse bai ɗauka ba sake dearling yayi still har ya katse bai ɗauka kallon Indu data tsira masa ido yayi kana yace.

“Bai ɗauka ba”.

Kai ta gyaɗa”.

Tare da koma gefen Ummu ta daura kanta akafadarta tace.

“Ummu Yah Imraan bai amsa kiran ba”.

Ummu kuwa lokaci ɗaya numfashinta ya fara hawa da sauƙa yana fusga yayin da bakinta ke fitar da kumfa idanunta suka kakkafe asama jikinta ya saki.

Aruɗe Dr Khameel ya ƙarasa kusa da ita yashiga bata temakon gaggawa.

Banda kuka da addu'a babu abinda Indu da Aunty Munah keyi.


  Acan ɓangaren Imraan kuwa anutse ya murɗa handle ɗin toillet ya fita ƙugunsa ɗaure da towel faffaɗan ƙirjinsa na ƙiran Zaratan maza ya bayya ahankali ya sauƙe idanunsa akan Lateefa dake zaune bakin gado idanunta na kofar toillet din.

Atake yayi kicin-kicin da fuska ya nufi gaban dressing Mirrow batare daya zauna ba ya ɗauki lotion ya fara shafawa.

Cikin sanyin jiki ta miƙe ta isa wajensa hannu ta miƙa da niyyar karɓan roban yayi saurin matsarwa gefe alamar baya buƙata.


Durƙusawa tayi akan gwiwoyinta tare da haɗe hannayen ta waje ɗaya cikin raunin murya tace.

“Am so sorry Sojana nasan Ni mai laifi ce awajenka wacce bata cancanci yafiyar ka ba amma dan Allah ka yafemin bazan iya juran fushin ka ba Aduk sanda kake fushi dani na kan rasa nutsuwata!”.

Batare daya ce Uffan ba ya janye ƙafarsa ya koma gaban Siff ya buɗe Wando kakin sojoji ya ɗauka da farin T-shirt mai gajeran hannu batare daya kalleta ba yace.

“Please ki bani waje zan canza kaya”.

Da wani irin mamaki ta kallesa kana ta maimaita abinda ya faɗa aƙasan ranta wato ma ta fita.

Jin batace komai ba sai kallonsa da take yasa ya buga mata tsawa cikin wata kakkausar murya yace.

“Are You a deaf??,I say Get out!”.


  Miƙewa tayi ta nufi kofa dogon tsaki yaja tare da zira dogon wando dai-dai lokacin ta dawo da gudu rungumesa tayi ta baya tare da manna kanta a gadon bayansa kana ta sanya hannunta ta zagaye bayansa ta fashe da matsanancin kuka cikin muryan kuka tace.

“Am so sorry”.

Sake ɗaure fuska yayi tare da sanya hannunsa ya ɓanɓare nata batare da yace uffan ba ya sake nuna mata ƙofa.


Kallonsa take still hawaye na Rollin a idanunta cikin tsawa yace.

“Kada kisa raina ya ɓaci Lateefa zanyi miki abinda bakya zato wallahi idan har baki fita”.

Bata bashi damar ƙarasawa ba tayi saurin fadawa jikinsa tare da haɗe bakinsu waje ɗaya cikin wani irin salo ta kamo lallausan harshensa ta shiga tsotsa yayin da take ɗan gatsa lips ɗinsa kaɗan-kadan kana hannun ta na yawo afaffaɗan ƙirjinsa zuwa tsakiyar bayansa tana yi masa tafiyar tsutsa.

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da sake rigar sa ya faɗi ƙasa hannunsa na dama ya sanya ya riƙo ƙugunta yayin da na hagun ya cusa acikin ƴar yaloluwar rigar dake jikinta ya sanya aramin cibiyar ta yana wasa dashi cikin wani irin salon ɗaukar hankali yake jujjuya ya tsarsa acikin ramin cibiyarta baya sukayi luuu cikin sauri ya janye bakinsa daga nata tare da janyeta daga jikinsa ya tsugunna ya ɗauki rigarsa yana ƙoƙarin sanyawa tayi saurin sake rungumesa tana shesh-sheƙan kuka mai cike da kissa.


Ahankali ya juya ya zuba mata idanunsa da suka fara sauya launi zuwa tsantsar jaraba da bukata acikin nata.

Cike da shagwaɓa da rauni tace.

“Sojana har yanzu fushi kake dani baza ka yafemin ba!??”.

Banza ya mata ya ɗauki turarensa ya shiga fesawa.

Sosai tashiga tashin hankali ta lura fushin gaske yake da ita cikin sauri ta durƙusa akan ƙafafunta ta rungumesa cikin shesh-sheƙan kuka tace.

“Na tuba Dan girman Allah dan darajar Manzon Allah (S.A.W)kaji kaina ka yafemin nasan nayi kuskure agareka amma ka yafemin bazan sake aikata irin wannan laifin ba idan har na sake ka ɗauki duk matakin daya dace akaina na tuba!.

Anutse ya kalleta ganin yanda take kuka tsakaninta da Allah yasa yaji tausayinta tsugunna wa yayi ya ɗagota kana ya share mata hawaye muryarsa adake yace.

“Its ok kukan ya isa haka”.

Cike da shagwaɓa tace.

“Ka yafemin sannan ka dena fushi dani?”.

Kai ya gyaɗa tare da nufar ƙofa cikin sauri tabi bayansa aɗaya daga kujerun falon ya zauna tare da dafe kansa.


Cike da kulawa ta zauna daga ƙasan ƙafafunsa kana ta ɗaura kanta akan cinyarsa tace.

“Sojana jiya nayi kwanan tsoro,kewa damuwa da tashin hankali kun barin Ni kaɗai baki ɗaya daren ya min tsayi da nauyi”.

Bayansa ya jingina da jikin kushin kana ya taɓe baki ataƙaice yace.

“Uhm dake baki saba kwana ke kadai ba ko?”.


Kai ta girgiza tare da tura baki asanyaye tace.

“A'a saboda kewar ka da nayi da kuma tsoron halin daka ke ciki naga duk lokacin da kake da night duty kana faɗa min sannan tunda kuka fita da Indu baku dawo ba sai yanzu da kashigo”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe ba yabo ba fallasa yace.

“Ummu ce ba lafiya time da muka fita Aunty Munah ta kirani shine muka wuce Hospital dake jikinta yayi tsanani yasa muka zauna asibitin acan muka kwana”.

Aruɗe ta zare ido tare da cewa.

“Innalillahi wa'inna ilahai rajiun shine baka faɗa min ba? yanzu ya jikin nata?Meke damunta?".

Ta ida maganar tare da miƙewa cikin sauri ya riƙe tsintsyar hannunta yace.

“Ki nutsu mana Ina zakije?”.

Idanunta na zubar da hawaye tace.

“Hijabi zansa mu tafi ina so insan halin da take ciki agaskiya baka kyauta min ba ace Ummu na asibiti har ta kwana amma ban sani ba”.

Hannunta ya janyo ta faɗa kansa rungumeta yayi lokaci ɗaya wani irin soyayyar ta da tausayinta ya lullubesa cikin sassauta murya yace.

“Ki kwantar da hankalinki In sha Allah taji sauƙi dan time dana taho ma ta tashi”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da taɓe baki kana ta cusa kanta aƙirjinsa.


Kanta ta ɗago cike da shagwaɓa tace.

“Amma kayi breakfast kuwa?naji cikin ka babu komai”.

Ta Ida maganar tana shafa shafeffen cikin sa”.

Kai ya girgiza idanunsa a lumshe yace.

“Um-um banci ba bana tunanin zan iya cin wani abu”.

Zare ido tayi tare da langwabar da kai tace.

“Sha biyu fa shine baka ci komai ba?”.

Bata jira cewar sa ba ta miƙe daga jikinsa tashiga kichen soyayyen dankalin turawa(Patoto)ta zuba masa da Perpersoup na kayan ciki ta shirya akan faranti ta fito dashi agabansa ta ajiye tare da cewa.

“Saƙƙo kaci”.

Ba musu ya sauƙa dan rabonsa da abinci tun Breakfast da yayi jiya anutse ya fara ci ba lefi yaci da yawa kana ya ture gefe.


Miƙewa tayi ta kwashe plate ɗin kana ta kallesa cikin lankwasa harshe tace.

“Sojana ka kwanta ka huta mana naga duk agajiye kake”.

Kallon agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa yayi tare da fesar da numfashi yace.

“No dear yanzu zan koma”.

Murmushi ta ƙirƙira kana tace. 

“Bari na saka hijabi mu tafi ko dama nayi tunanin ko zaka huta ne shiyasa?”.

Kallon kayan dake jikinta yayi fallen zani ne da top mara hannu wanda ta daure igiyar awuyanta numfashi ya fesar kana yace.

“Ahaka zakije asibitin?”.

Kai ta gyaɗa cike da damuwa tace.

“Koda nace zan shirya na tabbata babu abinda zan iyayi baki ɗaya hankalina na kansu kuma ma ai dogon hijabi zansa”.

Jinjina kai yayi tare da kallon lokaci yace.

“Yanzu sha biyu da Rabi idan su Reehana da Reeyana suka dawo fa”.

Aƙage tace.

“Zan kira Meenah idan taje ɗaukan Abeed ta tafi dasu”.

Baice komai ba sai jingina kansa da jikin kushin da yayi cikin sauri tashi ta wuce ba daɗewa ta dawo jikinta sanye da Maroon hijabi har ƙasa.

Atare suka fita yana gaba tana biye dashi suna fita ta kulle kofar falon gefen drive ya buɗe ya shiga dai-dai lokacin hasken wayarsa ya ɗauke ahankali ya kai hannunsa ya daga cike da mamaki yake kallon 30 Misscall cikin sauri ya buɗe nan yaga Misscall din Dr Khameel goma na Aunty Munah sha biyar sai kuma number da ba suna guda biyar.

Atake zuciyarsa ta buga da masifeffen karfi cikin sauri Lateefa dake gefen me zaman banza tace.

“Lafiya Sojana me ya faru”.

Kafin ya bata amsa wayar ta sake ɗaukar ruri ido kawai ya tsirawa screen ɗin wayar yana kallon sunan dake yawo yayin da bugun zuciyarsa ya cigaba da ƙaruwa.

Lateefa dake kallonsa tace.

“Sojana ka ɗauka kaji menene kada kiran ya katse”.

Kai ya gyaɗa ya rasa dalilin da yake jin bugun zuciyarsa na tsananta hannunsa na rawa yayi picking tare da kaiwa kunnensa cikin yanayin tashin hankali yace.

“Aunty Munah lafiya”.

Daga ɗaya bangaren Cikin matsanancin kuka Aunty Munah tace.

“Imraan kazo Ummu”.

Da sauri ya dafe saitin ƙahon zuciyarsa yace.

“Meyafaru?”.

Cikin kuka tace.

“Ummu”.

Kafin yace wani abu wayar ta katse da wani mahaukacin gudu ya figi motar ya fice daga gidan ko sauraron abinda Lateefa ke faɗa baya ji ita kam tsoro da fargaba ne ya lulluɓe ta bawai na halin da Ummu ke ciki ba sai na ganin yanda yake sharara gudu tamkar zai tashi sama.

Ikon Allah ne kaɗai ya kaisu asibitin lafiya ko Parking bai gama ba ya fita da gudu ya nufi ɗakin...


   Acan ɓangaren Sir Abdallah kuwa tsaye yake a gaban Fridge kunnensa maƙale da waya cikin yanayin damuwa yace.

“Dr har yanzu fa bata farka ba ko akwai wani abinda za'a mata?”.

Daga ɗaya bangaren Dr Hajja Adama tace.

“Am sorry to say yallaɓai da baka ɗauke ta kun tafi ba domin halin da take ciki ya nuna mana tana buƙatar kulawar daya dace amma sai ka ɗauketa kuka tafi batare da ka jira mun baku sallama ba bayan kasan wannan babban case ne mu kayi kasa dan karɓa”.

Cikin sauri ya ɗaga mata hannu kamar tana gabansa yace.

“Enought Please ba cewa nayi kiyi min tsari ba yanzu me zaku iyayi akai sannan ina Dr?”.

Numfashi ta fesar kana tace.

“Agaskiya yanzu bazan iya cewa komai ba Dr Khameel kuma suna kan Maraya lafiya ya bar wayarsa s office amma Shawarar ”.

Ƙit ya kashe wayar tare da dafe kansa da hannunsa ɗaya...


Da damuwa ya juya ya fita kai tsaye BQ dake kusa da sashen Ammie ya shiga daidai lokacin da wata dattjuwar mata mai cike da kamala ta fito tana ganinsa ta ɗan risina tare da cewa.

“Bundi Barka da safiya”.

Ahankali yace.

“Yawwa Mama Asabe fatan kin tashi lafiya”.

Kai ta gyaɗa shiru ne ya biyo baya ya rasa ta inda zai fara mata bayani.

Ganin haka yasa tayi Murmushi kasancewar tasan halinsa tun yana yaro agabanta ya taso sai dayawa wani abin bazai faɗa ba sai da ka fahimta ayanayin mu'amalarka cike da kulawa tace.

“Bundi ko akwai abinda kake buƙata?,Dama yanzu zanje sashen Ammie".

Numfashi ya fesar tare da gyada mata kai kana ya motsa laɓɓansa da cewa.

“Dan.Allah sashena za muje kiyi min wani taimako”.

Kai ta gyaɗa masa kana ya shiga gaba tana biye dashi har suka shiga bedroom ɗin.


Cak Mama Asabe ta tsaya da mugun mamaki take kallon Matashiyar budurwar dake kwance akan gadon sai kuma tayi saurin maida kallonta kan Sir Abdallah irin kallon Wacece wannan.

Numfashi ya fesar tare da harɗe hannunsa aƙirji kana ya zauna abakin gadon muryansa cike da sanyi da kuma rauni yace.

“Mama Asabe kada zuciyar ta kulla Miki zargi ne wannan yarinyar da kike gani amana ce agareni sannan an keta mata haddi ne”.

Da sauri Mama Asabe ta zare Idanu cikin tsansnin tashin hankali da tsoro kalmar fyaɗe yana masifar gigita mata tunani.


Sir Abdallah kuwa Manyan Idanunsa ya ɗan tsira tana nan kamar yanda ya barta har yanzu gefen bakinta da goshinta yana nan akumbure.

Ahankali yaga ta motsa idanunta sai Kuma ta motsa hannunta da ƙafafunta da sauri ya matsa kusa da ita.

Neenah kuwa Ahankali ta ɗaga hannunta dake zugu ta dafe saitin kanta kana ta ƙwalla ƙara da ƙarfi tana fusge-fusge

Aruɗe ya matsa gefe tare da tsira mata ido yana kallonta afirgice ta miƙe tare da shaƙe wuyansa da wani irin karfin ta juya sa ƙasa hannunta ta ɗaga ta wankesa da mara.

Cike da matsanancin mamaki da al'ajabi yake kallonta haka ma Mama Asabe lokaci ɗaya idanunsa suka sauya launi da tsantsar ɓacin rai wannan shine karo na farko a rayuwar sa da aka fara marinsa kafin ya dawo daga duniyar tunanin da yake ta sake kwaɗa masa wani marin da yasa yaga gilmawan taurari da wani irin fushi ya ɗaga hannunsa...



_Sawun Giwa na kuɗine 500 zaki tura ta wannan account number 6030406548 Abdullahi Idris Aishatu keystone bank ko kuma katin Mtn ta wannan number *** tare da tura shedar biya ta wannan number ***..._


_Ya Allah Ubangiji kajiƙan mahaifina ya Allah kagafar ta masa zunubansa ya Allah ka haske kabarinsa ya Allah kajiƙan duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya_


_Ayi shearing saboda Allah Ƴan Uwa masoya da Abokan arziƙi_.



     *ESHAA CE*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol