Free chapter · Read without an account
SHIMFIDA
Haƙƙin Mallaka: Ibrahim Musa Gozawa
Gargaɗi:
Ba a yarda wata ko wani su yi amfani da wannan littafi ta kowace siga ba sai da izinin mai shi. Duk mai son yin amfani da shi ta wata hanya ƙofa buɗe take ya tuntuɓi marubucin kai tsaye.
ABUBUWAN DA KE CIKI
TARIHIN MARUBUCI
GODIYA
SADAUKARWA
TARIHIN RUBUTUN LITTAFIN
GABATARWA
DARASI
Menene Darasi?
Ɗaukar Darasi
Manufar Ɗaukar Darasi
Muhimmancin Ɗaukar Darasi
Hanyoyin Samun Darasi
GWALAGWALAN KALAMAI 500
TARIHIN MARUBUCI
Sunana Ibrahim Musa Gozawa. An haife ni a Gozawa, Tudu, Kankara, Katsina State. Na yi primary a Tudu Primary School, Tudu daga 2000 zuwa 2006. Sannan na yi sakandire daga 2006 zuwa 2012 a Government Day Secondary School, Tudu. Sai kuma daga nan na wuce Isa Kaita College Of Education, Dutsinma, Katsina State, Nigeria daga 20 12 zuwa 2015. Anan na na samu NCE a English /Islamic Studies.
Na yi karatun Blogging da WordPress da sauran wasu courses a makarantar yanar gizo ta Flowdiary wadda Muhammad Auwal Ahmad ya kafa.
Ni marubucin litattafan hausa ne. Sannan kuma makarancin litattafai wanda yake mayar da su zuwa audio books. Sannan ni CV da Cover Letter Writer ne.
Domin samun karatuttakan litattafan da na yi ku yi following ɗina a social media handles nawa kamar haka:-
***
***
WHATSAPP GROUP
***
TELEGRAM GROUP
***
***
AUDIOMACK
***
GODIYA
Allah buwayi gagara misali shi ne ya cancanci dukkan wata cikakkiyar godiya da yabo. Ina mika godiya ta gare shi a jumlace akan ni'imomin da yayi gare ni. Kama daga babbar ni'imar imani da musulunci da samun Cikamakin Annabawa Shugaban Manzanni. A taho har a zo kan ƙananun ni'imomi.
Sannan a keɓe godiya nake gare shi da ya bani ikon rubuta wannan ɗan littafi.
Bayan haka ina godiya ga mahaifana waɗanda suka rene ni akan kyakkyawan ɗabi'u. Waɗanda suka koyar da ni darussan rayuwa masu yawa tun daga yarintata har zuwa yanzu da na rubuta wannan littafi. A cikin godiya ta dole ne in ambaci malamina a addini wato Malam Abdullahi Haruna Tudu. Shi ne wanda ya karantar da ni wani abu kuma har yanzu yana kan haka. Yayi ƙoƙari ƙwarai da gaske wajen samun kaina a halin da nake yanzu.
A ɓangaren gwagwarmaya ta fasahar internet kuma, ba zan taɓa mantawa da babban malamina kuma ubangidana a harkar digital skills ba. Wanda ya ba ni horo na musamman da shawarwari masu tarihin yawa sannan ga wata irin kulawa ta daban. Wannan shine Muhammad Auwal Ahmad wanda aka fi sani da Mohiddeen. Shugaban makarantar Flowdiary wato makaratar koyon fasahar zamani ta yanar gizo. Kuma har ila yau shi ne shugaban babban kamfanin nan Alphamega.
Sannan ina mika godiya ga dan uwa kuma abokin gwagwarmaya tun daga sakandire wato Nasiru Adamu.
Daga ƙarshe dai ina mika godiya ga dukkan masoyana da ƴan uwa da abokin arziki na nesa da na kusa. Allah ya saka wa kowa da alheri.
Ibrahim Musa Gozawa
Author
Producer of Hausa Audiobooks
SADUKARWA
Wannan littafi sadaukarwa ne ga mahaifana.
TARIHIN RUBUTUN LITTAFIN
A shekara ta 2023 ne aka gabatar da zaɓe a Najeriya a cikin watan Maris. To bayan an gama zaɓen shugaban ƙasa da kwana daya ne na ga wani posting da Muhammad Auwal Ahmad yayi a shafinsa na Facebook. Posting din yayi shi ne akan darussan da ya fahimta a lokacin gudanar da zaɓen. Ina ganin haka fa abin ya birge ni tare da bani sha'awa.
Daga nan nima na ɗauki wani darasi da na fahimta daga rubutunshi. Darasin kuwa shine yin ƙoƙarin ɗaukar darasi a duk halin da mutum ya tsinci kansa kuma yayi aiki da shi. Tun daga lokacin na ƙudurce a raina lalle zan yi aiki da wannan darasin koda sau ɗaya ne a rayuwata.
Ina akan haka ne sai kuwa na samu kaina cikin wani yanayin da na ga ya kamata ace na ɗauki darasi. Haka kuwa aka yi. Sai na dinga tattara darussan a zuciyata amma ba ni rubutawa a farkon al'amarin. A kullum zan ruwaita a raina na fahimci darasi kaza da kaza a cikin sha'ani na.
Da tafiya tayi tafiya, sai wata zuciyar ta ce mani don me ba zan rubuta wadannan darussan ba? Idan ban rubuta su ba ai zan iya mancewa. Sai kuma na ga haka ne.
Wata rana ina dawowa daga aiki sai na ɗauko biro da littafi. Na fara tunanin darussan da na samu ranar da kuma wadanda zan iya tunawa na baya. Sai kawai na ci gaba da rubutawa. A ranar farko na samu na rubuta darasi 30. Da na ga haka sai na ce to tun da haka ne me zai hana in cike su su zama dari. Sai kuma na yi tunanin to ina zan samu darussa har dari in rubuta. Kawai sai na yanke shawarar a duk kullum in samu darasi ko ɗaya in rubuta shi har su cika ɗari. Ai kuwa sai na ci gaba da yin haka. Wata rana in rubuta da yawa, wata ranar kuma in rubuta kadan. Da haka har na cike dari. Wadannan darussa duka na rubuta su a lokacin don amfanin kaina kaɗai.
Ina kaiwa ɗari sai na ga ai ya kamata in cika su su kai ɗari biyu don wasu mutanen su amfana. Shi kenan sai na cigaba da tattarawa har suka cika ɗari biyun. Suna kaiwa sai na yi tunanin me zai hana in tattara guda dubu ɗaya. Sannan kuma ai ya kamata in rinƙa haɗawa da maganganun wasu malamai da mutane don abin ya ƙara armashi.
Shi kenan sai na ɗora daga inda na tsaya har suka kai ɗari biyar. Sai na haɗa su suka zama matsayin littafi na ɗaya 1. Da kuma nufin idan Allah ya nufe ni da ƙarasawa, zan tattaro wasu darussan 500 sai ya zama littafi na biyu 2. Wannan kenan.
Dangane da saka sunan littafin kuwa, da farko na sa mashi Darussan Rayuwa. Sai da na gama sai na ga ai waɗannan darussa kamar wasu gwalagwalai ne masu matuƙar tsada waɗanda za a yi ado da su. Idan aka yi adon kuma to kwalliya zata biya kuɗin sabulu. Wannan tunanin sai yasa na canja sunan daga Darussan Rayuwa zuwa Gwalagwalan Kalamai 500 Masu Tsada. Saboda haka kalamai ne masu amfani a rayuwarmu ƙwarai da gaske. Idan har ka samu yin amfani da su zaka ƙaru a rayuwarka. To wannan shi ne tarihin rubuta wannan ɗan littafi.
GABATARWA
Littafin Gwalagwalan Kalamai 500 Masu Tsada littafi ne da ya ƙunshi kalamai masu ɗauke da darussa da hikima da ƙarfafa gwiwa. Ya tattara kalamai da suke da alaƙa da Alƙur'ani da lahira da koyi da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Yana da kalamai da za su ƙarfafe ka game da addininka. Sannan kuma akwai kalamai da zasu ƙarfafa maka gwiwa game da sha'ani na duniya.
A taƙaice dai littafin ƙarami ne a jikin shi amma babba ne a ma'ana.
Zaka samu kalamai masu matuƙar amfani gare ka. Waɗanda idan ka yi amfani da wasu zaka samu hanyar cimma wani guri naka a rayuwa.
Littafin na ɗauke da darussa da kalmomi na hikima har guda 500. Wasu kalmomin daga marubucin ne. Wasu kuma daga wasu malaman ne. Dalilin haka kuwa saboda asalin littafin na yi nufin in tattara darussan da na samu ne na rayuwa in kuma yi amfani da su ni kaɗai. Sai daga baya na ga dacewar in ɗauko wasu maganganu na malamai suma su zama mani darussa.
To a duk inda ya kasance kalamai ne na wani malami da na ji to zan rubuta sunan shi a ƙarshen maganar. Sannan kuma zan sanya wa maganar alamar maganar wani "" . Na ɗauki maganganu na Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum da na Sheikh Yahaya Haifan da na Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zariya.
Wasu kalaman ba su wuce karin magana ba. Amma su ma na ɗauko sune saboda na ga akwai wani darasi da za'a iya fitarwa.
Saboda haka maƙasudin rubuta littafin kacokan ya ta'allaƙa ne akan samar da wani darasin da mutum zai yi amfani da shi don ya samu wani alheri ko kuma ya kuɓuta daga wani sharri. Daga ƙarshe ina fatan wannan littafi ya kasance mai amfani ga duk wanda ya ɗauke shi ya karanta ko yayi nazari ko kuma ya saurari karatun shi.
Ibrahim Musa Gozawa
Marubuci