Free chapter · Read without an account

03

by Fareeda Aliyu · KOWA DA ƘADDARARSA

Abin ka da ba-sa-ban ba tun safe nake fita sai marece nake dawowa zancen registration na makaranta, ga shi daga Yaya Zainabu har Yaya Naziru ba wanda yake Kano a lokacin bare su tayani. Rashin kan sanin abubuwan da kuma tsarin makaranta ne ya fi wahalar da Ni sannan ga layi a komai. Wannan jigilar ce ta sanya na mance da littafin da aka ba Ni aro har ma da na Yaya Nazirun da na bayar.

Ranar da zan kammala registration ne na haɗu da 'yan mata biyu tsararrakina, waɗanda course ɗin mu ya kasance ɗaya har muka yi musayar lambobin waya. Watau Zara'u Darma da Fatima. A tare muka kammala komai, muka samo jadawalin karatun 'yan ajinmu sannan muka nemo venue ɗin kafin mu baro makarantar.

Ranar da za'a fara lectures kuwa tun da na tashi sallar asuba ban koma ba don ɗoki, tuni na yi wanka na shirya gudun kar na makara, sannan na je wurin Baba karɓar kuɗin makaranta. Shi da Mama sai tsokanata suke da ganɗoki. Ina isa makaranta Fatima na isowa ita ma, don haka tare muka tafi venue ɗin da ya kamata mu yi lakcar mu ta farko ƙarfe goma, anan muka ƙara haɗuwa da Surayya, muka zauna tare muna jiran lokacin yayi. Zara'u Darma kam sai kusan ƙarfe goman ta zo. Amma haka muka yini ba wata lecture da malamin ya zo. Yanzu mun zama mu huɗu Ummu (Ni), Fatima, Zara'u Darma da Surayya.

Ƙarfe biyar muka baro makaranta ranar, Zara'u da Surayya ɗaukar su aka zo yi, a yayin da Fatima ta ja ƙaramar motar ta Starlet zuwa gida, tayi-tayi ma ta rage mun hanya nace ba damuwa akwai wanda nake jira, ta je zan taho an jima kaɗan.

Sai da na ba ta aƙalla minti ashirin sannan na taho na doshi gate domin tafiya gida. Ina daidai central mosque naji ta baya na ana magana "Ke! Ina littafi na?" Amma ban juyo ba domin ban ɗauka da Ni ake ba. Sai da naji an danne ham ɗin mota, ina dafe da kunne na na juya na ga waye wannan ya cika wa mutane kunnuwa haka, cikin mamaki ganin Ni yake kallo nace "Malam lafiya? Ko na tare maka hanya ne?"

"Ko ɗaya, hasali ma hango ki na yi na biyo bayan ki. Ina littafi na?

A take na dafe kaina sai yanzu na gane waye me maganar sannan nace "Don Allah ka yi haƙuri, wallahi na sha'afa ne. Ban da ma ka tuna mun yanzu, Ni na mance akwai littafin wani a gurina. Ya za mu yi yanzu kenan? Ko a nan kake karatu?"

"A'a, na daɗe da gamawa. Yanzu ma wani abu ne ya shigo da Ni." Ya amsa.

Na ɗan yi jim ina kallonsa ina tunanin ta yanda zan sake haɗuwa da shi don dawo masa da littafin sa. A hankali na sauke idanuwa na ƙasa nace "Ko za ka bari sai weekend na kai maka littafin K/Na'isa....." Irin kallon da yake yi mun ne ya katse Ni daga magana na fara dariya. Kallo ne da ake yi wa wanda ba'a yarda da shi ba, tun kafin ya yi magana na ƙara cewa "Daga gani ba ka yarda da Ni ba, ka zo nan gobe sai na taho da shi kawai."

Kallon har wannan lokacin yana nan a fuskar sa yace " Ai fa ban yarda ba. Yanzu ba gida za ki ba? Ai kawai ki taho mu tafi tare ki ɗauko mun abu na."

Bala'in mamakinsa ya kama Ni yanda ya dage akan littafi. Ban ce komai ba na buɗe motar na shiga ina faɗin kai ashe aron littafi a wurinka tashin hankali ne, ai daga yau ba zan ƙara ba.

Murmushi ya yi bai amsa ba sai kawai yace "Ina muka nufa yanzu?"

A ciki na amsa "Hotoro" sannan na yi murmushin mugunta na ɗora da "Hold Up kuwa sai ka rasa in da za ka sa kanka." Shi ma ya amsa "Ba zan damu ba in dai akan littafi na ne."

Daga haka ba mu ƙara cewa komai ba, ganin shirun ya yi yawa sai ya ƙara kidan da ke tashi a motar amma ba yanda zai damu kunne ba. 

Muna daidai Zoo Road muka gota wasu a bakin hanya suna dambe, har ina waigawa ina ƙare masu kallo sai kawai idona ya faɗa kan litattafan da ke zube a kujerar baya ta motar don haka na miƙa hannu na kwaso su, yana tuƙi bai kula da abin da nake yi ba. Kusan guda bakwai ne, sabbin kuma original copy ba irin wanda ake siya na Sabon Gari ba. Ina ɗaga na biyun ƙarshe, da sauri na juya ina kallonsa cike da tuhuma tare da ɗaga littafin saitin idonsa nace "Explain this."

Ko da ya kalli littafin sai kawai ya ƙyalƙyale da dariya tare da faɗin " Ko ma mene ai duka littafina ne, ke kin ga laifi na? Wannan original ne sak irin na wajen ki, Da Vinci Code ba."

" Shine saboda Allah za ka ɗaga mun hankali akan littafi kaman babu gobe? Kuma bayan ka samo wani. Sauke Ni anan, ba wahalar samun abun hawa zan yi ba." Na fara tattare jakarta da gyaran zaman mayafi na.

"Ai tun da na ɗauko ki sai na ƙarasa lada na, ko kuma ki biya Ni kuɗin mota idan na kai ki gida, ba wanda ba ya son kuɗi ai."

Na yi shiru na ƙyale shi don ban ga amfanin jayayya da shi ba, kuma a daidai nan na tuna in da na fara ganin shi. Shine dai wanda na taɓa tsayawa ina ƙarewa kallo a layin gidan Hajiya, ba mamaki shi ma ya gane Ni shi yasa yake mun ganin dama. A haka muka ƙarasa unguwar mu, na dinga nuna masa hanya har ƙofar gidanmu. Anan ɗin ma ya sake ba Ni wani mamakin.

Na shiga gida domin ɗauko masa littafin sa ko na huta da nacin ɗan ana ce nan, amma ko da na fito babu kowa bakin gate in da na bar shi sai shatin tayar motar sa. Na ja na tsaya ina mamakin yanda yake neman wahalar da Ni babu gaira babu dalili. Na girgiza kaina na koma gida tare da cin alwashin sai na gara shi sosai Ni ma kafin na mayar masa da littafin, ga ƙarin abun haushin ma ko sunan shi ban sani ba.

A haka muka cigaba da zirga-zirgar makaranta, amma sai a sati na uku sannan lectures ɗin mu suka zama stable. Duk in da ka ganni to tabbas za ka ga Fatima, Surayya da Darma. Abun kaman haɗin baki, dukkanin mu tsawon mu ɗaya kaman an auna, Surayya ce ma zan ce ta fi mu jiki shi ma a ɓangaren ƙugu ne da mazaunai amma duk da haka Ni ce siririyar cikinmu. Haka su farare ne tas, Ni kuma ban kai su haske ba duk kuwa da cewa Ni ɗin ma farar ce sai dogon hanci da ke kafe a fuskanta wanda shi ne ya ƙawata fuskar tawa da ke ɗauke da manyan idanuwa d mitsitsin baki (ta Yaya Zainabu idan muka yi faɗa sai tace da baki kaman ta-kashin tsuntsu). A taƙaice dai, su kana kallon su kake ganin kyan su farat ɗaya, Ni kuma sai ka kalleni tukunna za ka gane na fi su kyawun fuska.

Motar Fatima ce ta yawon mu nan cikin makaranta. Idan mun gama lectures kuma Zara'u da Surayya ɗaukar su ake zuwa yi, Ni kuma sai mu tafi tare da Fatima kasancewar gidansu a Gyaɗi-Gyaɗi yake, anan nake sauka sai na hau tasi ta ƙarasa da Ni Hotoro. Amma idan Yaya Muntari ko Yaya Mahmoud na gari, zuwa suke su ɗaukoni.

Ko da jin yanda na siffanta maku kan mu kusan ba za mu rasa samari ba (su ƙawayena na nake nufi, Ni har yanzu ban yi ko guda ɗaya ba), duk da ba mu kasance masu yawaita kula maza ba ko da kuwa 'yan ajinmu ne (tsakaninmu da su gaisawa sai kuma lamarin da ya shafi harkar aji). Amma kusan duk ranar da za mu yini a makaranta ƙwandalar mu ba ta ciwon kai, har makaranta ake kawo take away na abin da za mu ci, in taƙaita maku zancen nan ma, jadawali muka yi masu ba tare da sun gane ba.

Zara'u Darma kuwa akwai wani saurayin ta Umar don kamar ta fi son shi cikin samarin ta, ba ta bari a bashi wahala, don mun ma gama sadaƙarwa shi ne wanda za ta aura. Har tana dakar kirji cewa ba ya kula kowacce mace sai ita kaɗai, gabaɗayanmu muka sa mata ihu, amma ta dage, har tana faɗin ta yarda a gwada shi a gani, don mamaki kawai za mu sha. Nayi-nayi da ita a share maganar nan amma ta dage ita ta san yanda yake kuma ba ta da shakka a kansa. Mun shaida yana bala'in son ta, rashin kula wasu ne ba mai tabbas a cikinmu.

Ranar wata Alhamis muna zaune kan kujerun siminti ƙarƙashin bishiya, motar Fatima na gefe a buɗe don jakar mu na ciki ma, lemo muke sha muna kallon hotunan mu da Fatima ta sa a laptop ɗin ta muna ta hira kaman za mu aro baki. Zara'u tace bari ta kira Umar don kewarsa take yi duk da ta san ma dole yanzu yana kan aiki. Sai Fatima ta ce " Ko cewa kika yi ya zo, kin san tsallake aikin zai yi, wannan shine mijin tace ɗin ai."

Duk muka ƙyalƙyale da dariya har da Zara'u Darma. Surayya da ke gefen mu tana taunar cingam tace "Kar fa ya zo yace sai nan (tana nuna kanta)" da yake ranar ta yi wani matsiyacin kyau, ɗinkin kaman don ya fidda hips ɗin ta kaɗai aka yi shi, har wani extra haske ta ƙara.

A take Zara'u tace "Bari na kirashi yau dai mu kashe wannan maganar, kuma ai kun ga yau ban yi wata kwalliya ba ko sannan ba wani sanin Surayya ya yi ba ko? To za ku sha mamaki."

Cikin dariya Fatima tace "A'a Zara'u, shi namiji ba'a ci masa alwashi, kar ki zo kina yi mana kuka baiwar Allah, don mun san soyayyar Umar za ta iya kashe ki."

Ba ta amsa ba sai gani muka yi ta sa waya a kunne tana magana a hankali tana shagwaɓe masa wai tayi missing ɗin shi, ita so kawai take ta gan shi yanzu. Ko da ba mu jin me yake faɗa mun san cewa yayi ga shi nan tafe. Ta kashe wayar tana cewa Surayya ta ƙara shirya wa.

Zan iya cewa kaf cikinmu ba wanda ya kai Surayya dakiya, duk abin da kake tunanin ba zata iya ba shine abin da ta fi bada ƙarfi a kai don ta nuna she is up to any challenge. Don haka a take ta jawo jakarta ta fara gyara kwalliyarta, jambaki, turare har gyara ɗaurin ɗankwali. Irin ihu da dariyar da muke yi har sai da aka dinga juyowa ana kallon mu, don ma Allah ya rufa asiri ba kusa da lecture hall muke ba, da tuni an kore mu. Gudun gardama aka ce Surayya ta danna recording a wayarta don a ji me ya wakana idan sun dawo (kar ku ga laifin mu, ƙuruciya ce).

Ko da ya kira waya ya iso, Zara'u tare da Surayya suka tafi wurinsa, mu kuma muna dakon jiran yanda za ta kasance. Infact ma Zara'u maiƙon rana take yi ko hoda ƙin shafawa tayi don tana don ta tabbatar mana ta yarda da Umar sosai.

Tun da ya hango ta yake murmushi har suka ƙaraso in da yayi parking, yace " Ya na gan ki haka Saraki (sunan da yake kiranta da shi)? Wani abu na damun ki ne?" Tuni murmushin ya ɓace sai zallar kulawa a madadinsa.

"Ba komai fa, wahalar BUK ce kawai. Ka ga ma yanzu sai da na kira ka sannan aka ce malamin da ya ba mu assignment yana neman 'yan group ɗin mu. Kuma Ni ina son ganin ka shi yasa ban kira na ce ka fasa zuwan ba, ai za ka jira Ni naje na dawo ko?" Ta faɗa cike da shagwaɓa.

Cikin hanzari yace "Ba damuwa ki je zan jira. Dama na cewa Jibrin ya yi covering ɗina a wurin aiki."

Cikin murmushi tace "Bana son barin ka kai kaɗai, bari na bar Surayya ta taya ka zama kafin na dawo."

Sai a lokacin ma ya lura da Surayya da ta ci jambaki tana murmushi don kawai ta nuna manyan dimples ɗin da ke fuskanta, sannan ya juya ya kalli Zara'u tace "No, it's okay, ku tafi abun ku, Ni kar ki damu i can wait, tun da so kike na jira ɗin."

Kawai sai ta juya cikin sauri tana cewa "Shiga motar ku yi hira Surayya, ki tabbata kin kula mun da shi kafin na dawo." Kai tsaye ta dawo wuri mu, muka ci gaba da hira muna kallon lokaci.

KOWA DA ƘADDARARSA


Fadda_banan 


Fdd 0️⃣4️⃣

Don joining Whatsapp group ɗin mu, ga link: ***


Lokacin da agogo ya nuna minti arba'in da tahowar ta sai ga wayar shi yana tuhumar ina ta maƙale haka, shi ya gaji ita kaɗai ya ke son gani. Shewa kawai muke yi kafin ta juya ta tafi in da ta baro su ɗazun.

Chan muka hango Surayya tana tahowa, tsabar ɗokin mu ji me ya faru yasa muka ga ba sauri ma take yi ba kuma sai dariya take yi. Ko da ta qaraso ma cewa tayi a jira Zara'u ta dawo, yanda ba sai ta bayar da labarin sau biyu ba.

Ko minti goma ba'a yi ba sai ga Zara'u ta dawo fuskanta ɗauke da fara'a tace "Surayya ke kuwa ina kissar taki? Kin san me Umar yace? Wai ba ya son ina hulɗa da ke, kaman idonki ya buɗe da yawa. Nayi-nayi ya faɗa mun abin da kika masa da har ya ga hakan, amma ya kafe ba komai kawai dai ba ya son mu tare."

Surayya ta amsa " Ai yanda kika san bulo haka Umar ɗin ki yake. Masifa! Kin san tun da kika bar mu bana jin yayi mun cikakken zancen da ya kai takwas. Bari dai na kunna maku ku ji."

Kaf tsayin lokacin Surayya ce kawai take ƙoƙarin jan sa da hira, sai yayi kaman zai saki jiki su yi magana sai ya yanke maganar, ƙarshe sai ya koma amsa wa da 'ummm', 'uhm-uhm' ko 'hmmm'. Daga baya ma cewa yayi "Wai ke bakin ki ba ya gajiya da surutu ne?". Matuƙa abun ya ba mu dariya, har Surayya na faɗin kawai dai don ya gan ta tare a Zara'u ne, amma da a wani waje ne sai dai a ji sabon labari. Daga bisani muka yanke shawarar Zara'u ta sanar da shi gaskiyar zance, kar yake ganin baƙin Surayya.


*******************************

Ina komawa gida na iske motar mai littafi yana shirin barin ƙofar gidanmu, yana gani na ya dakata yana faɗin "Allah ya taimake Ni ba sai na ƙara dawowa ba, barkan ki da zuwa Ummul."

Mamakin ganinsa nake yi, ashe har sunana ya sami kenan. Na amsa "Yauwa mai-littafi, shine rannan ka yi tafiyar ka ba ka jira na ɗauko maka littafin ka ba ko? Don ma ka sani Ni ba yanzu zan bayar ba."

Ya amsa cikin murmushi "Ni dama ba littafi ya kawo Ni ba, ke kawai na zo gani. Sannan Gadanga ƙusar yaƙi nake ba mai-littafi ba."

"Aliyu?" Na tambaya

"Na'am"

Haka yayi ta ja na da hira har aka yi kiran Sallah sannan ya yi mun sallama ya tafi.


Tun daga ranar kusan kowanne ƙarshen sati yana gidanmu har ba zan ce ga lokacin da muka fara soyayya ba. Bai jima da fara aiki ba tun bayan kammala karatun shi a jami'ar Bayeron.

Shaƙuwar mu ta san ya san duka 'yan gidanmu don suna haɗuwa idan sun zo hutu, amma sun fi sabawa da Yaya Naziru (barin ma yanzu da ya dawo Kano gabaɗaya don ƙarasa bautar ƙasar). Faɗar cewa sun saba da clique ɗina na makaranta ma ɓata lokaci ne, ko bana kusa shi da su Fatima kan zauna su sha hirar su kamar shi suka sani ba Ni ba.


Ranar wata Laraba muna zaune kafin mu shiga lecture ta gaba, sai ga Umar ya zo, har da kawo mana take away ganin rana ta take kuma yau har shida za mu kai. Nan tare da mu ya zauna ana hira gabaɗaya, Surayya ce kaɗai ba ta nan. Kamar haɗin baki sai ga Aliyu shi ma tafe da na shi take away ɗin har Fatima na tsokanar su da cewa so suke mu yi ƙiba dai da alama.

Surayya ita ma ta iso daidai lokacin ta yi sallama. Tana ganin Umar ta kwashe da dariya tana faɗar "An gaida Saraki na Saraki" shi ma dariyar yayi yace da Aliyu "Kasan me yaran nan suka yi mun kuwa?"

Aliyu yana murmushi bayan sauraron Umar yace "Amma fa sun solaka,amma da yake mata ne afuwa za'a yi masu, su a zaton su kyau ne ke ruɗarmu...." 

Umar ya katse shi da cewa " Allah yayi maka albarka ɗan uwana! Abin da nake so su fahimta kenan. Babu ƙarya in an ce kyau ya ɗau hankalin mu, mu mutane ne ai kuma masu jini a jika, amma so ai daban ne."

*****************

A haka lokaci yake ta tafiya har muka gama jarabawar ƙarshen zangon karatu na farko, muka tafi hutun sati Uku kacal. Ranar da na kammala jarabawa ina zaune a falo bayan na yi sallar Isha ina kallo, don tun kafin na fara jarabawar na watsar da komai shine yanzu nake son rama abin da ya wuce mun. Ko nisa ban yi ba sai ga Hussain ya zo kirana wai Aliyu ya zo. Cikin ɗoki na tafi wurinsa don rabona da shi tun kafin na fara jarabawa kasancewar Ni na hana shi zuwa don na samu sararin karatu sosai.

Yana gani na ya tsare Ni da ido yace "Wai duk wannan dogon wuyan na menene? Examz ɗin farko kika yi fa akwai wasu a tafe, bai kamata ki dinga ɗaga hankalin ki ba ga shi tubarkallah kina da ƙwaƙwalwa." Ni kam ban saurari ƙorafin da yake mun ba, dariyar daɗin ganinsa kawai nake yi.


Amma fa abin da ya kawo Aliyu yau wurina yana cike da rikitarwa a gare ni, domin abin da ban zata ba ne ya zo mun da shi. Yana buƙatar na amince da shi ya turo magabatansa gidanmu domin tambaya, idan da sarari ma a taho har da kuɗin gaisuwa. Ban amsa masa nan take ba, domin ban taɓa zaton zai ce zai turo yanzu ba, na fi zaton nan da lokacin da na shiga aji uku yanda kafin a kammala komai na gama makaranta gabaɗaya ko ina gab da gamawa.

Abu ɗaya na sani, son da nake yi wa Aliyu zazzafa ne, zan iya haƙura da buƙata ta don na zauna da shi har ƙarshen rayuwata. Mun bar maganar akan cewa zan faɗa wa Mama buƙatar shi, ko me a ciki zan sanar da shi.

Ko da na shigo gidan kai tsaye wurin Yaya Naziru na wuce don na faɗa masa abinda Aliyu ya zo da shi. Shiru yayi kamar yana nazari sai kuma yace "Ummu za ki iya haɗa karatu da sabgogin da ke cikin aure? Da yake tsakanin mu babu boye-boye sai nace "Ni fa ban sani ba, kawai dai nasan ina son Aliyu da yawa da har zan iya yin abubuwa domin faranta masa. In dai bai ce zai hana Ni karatun gabaɗaya ba, i think I can manage."

A daren Yaya Naziru ya samu Baba da maganar, abin da Baba ya fara tambaya shine"Ita Ummun tana son shi?" Shi kuma ya amsa da cewa "Ai ita ce ma ta kawo zancen tace na sanar da ku, duk abin da kuka yanke sai a faɗa masa."

Baba yayi shiru ɗan jim haka sannan yace "Je ka Naziru, babu komai. Bari na sanar da mahaifiyar ku, ba zai yiyu mu yanke shawara mai mahimmanci irin wannan ba ba tare da ta sani ko ba da gudunmawa ba. Zan sake neman ka."

A kuma ranar aka yanke shawarar ba shi damar fitowa kaman yanda ya buƙata ganin cewa ina son shi Ni ma. Har na kwanta bayan na kora Hassana ɗakinsu na jiyo Mama tana kira na daga falo. Tare da Baba na iske su. Tambayoyi Baba ya dinga mun game da Aliyu da kuma neman tabbacin ko ina son shi ko a'a, daga ƙarshe yace na tura nasa Aliyu yana son ya gana da shi.

Washegari da marece sai ga Aliyu yazo, ni da na gan shi da farko ma na ɗauka ba shi da lafiya don har idonsa sun faɗa yayi zuru-zuru. Shi yasa ma na kasa zama na shiga tambayar shi me ke damun shi. Murmushi mai kama da yaƙe yayi bai amsa ba, sai damuwa da ta ƙaru akan fuskarsa. Gaba na yayi mummunan faɗuwa da wani irin hanzarin na buɗe ƙofar mota ta ɓangaren shi na tsuguna, ƙwalla ta cika mun idanu.... Ganin hawaye a idona ya sanya shi razana, cikin hanzari ya sa hannu yana goge hawayen da ya fara gangarowa daga fuska ta yace "Haba Ummul haba mana, don Allah ki bar kukan nan, ki daina zan faɗa maki abinda ke faruwa, yi shiru, kin ji?"

Hannunsa na sauke daga fuskanta tare da jan hancina, na miƙe tsaye tare da rungume hannayena na jingina jikin motar shi ina kallon ƙasa da nuna alamar sauraro. Ya ɗan yi jim yana kallo a kafin shi ma ya fito daga motar ya tsaya daf da Ni har ina jiyo saukar numfashin sa sannan a hankali ya fara magana "Ki yi haƙuri Ummul fargaban abinda za ki faɗa mun ne ya tarwatsa mun ciki (gudawa) kuma na kasa cin komai. Ban san iyakar soyayyar da wannan zuciyar take maki ba, nasan na so kaina saboda nasan yanda kike son karatu sosai, tsorona ɗaya kar ki ce sai kin gama makaranta tukunna don Allah ma ya sani ba zan iya jira wasu shekaru...." Ya tsaida maganar yana sauke ajiyar zuciya.

Tausayin kan mu ya kama ni, a hankali na juyo na fuskance shi nace "Haba Aliyu! I fall for you before you even knew of my existence, ni kaina ban sani ba sai daga baya. Yanzu haka bana tunanin son da kake mun ya wuce nawa. Na riga na sanar da su, Baba yace dama idan ka zo na faɗa maka yana son ganin ka tukunna kafin ka turo....." Juyowar da yayi da sauri ne ya sanya na yi shiru, sai kawai ya fara hamdala "Idan Baba na ciki ki faɗa masa gani na zo." Ina dariya na amsa "Sun fita da Yaya Naziru kuma ban san lokacin da za su dawo ba."

Muna tare har aka yi magriba amma quaker oats na samu na dama masa, yana ta mita bakinsa ba daɗi ba zai sha ba, haka na dinga lallaɓa shi har ya sha da dan yawa. Ya yi baya da kujerar motar ya jingina sosai, ba yanda ban yi da shi ya je gida ya kwanta ba amma ya ƙi wai ganina ma magani ne, idan ina son ya warke na bar shi yayi ta kallona ko da ba za mu yi hira ba.

Mun yi sallama kenan yana shirin tafiya sai gasu Baba sun dawo. Ai kuwa ya maƙale ya ƙi tafiya, tare suka yi Sallah a masallacin layin mu kafin ya samu damar tattaunawa da Baba. Ko da ya gama bai nemi Ni ba sai tashin motar sa naji kawai kuma ya figeta kamar me tashi zuwa sama.


Yaya Naziru ne ya faɗa mun yanda Baba suka yi da Aliyu. Kawai tambayoyi ne da suka danganci aikinsa, danginsa da sauran tambayoyi dai da suka dangancesu. Ina kitchen ma na jiyo Baba yana faɗawa Mama ya yaba da hankalin yaron, Allah ya sa kuma ba pretending yake yi ba. Mama tayi dariya tare da faɗin "In shaa Allah babu damuwa, Allah kuma ya haɗa kansu." Farin ciki ya lulluɓeni ganin ya samu karɓuwa.

Washegari wurin ƙarfe goma na safe sai ga Yaya Zainabu ta bugo waya, mamaki kawai take yi domin ta san alwashin da na ci akan karatu tare da faɗin sai na gama zan yi aure. Na amsa da cewa "So ne Yaya Zainabu, Allah wani banzan abu ne da yake rushe dukkanin wani ƙuduri, just wish us well kawai."

Dariya tayi tace "Yau na ga ta kaina Ni Zainabu, wai Ni Ummu ke yi wa lecture akan so." Ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya tare da katse kiran.

Kwana biyu bayan nan 'yan gidansu Aliyu suka zo tambaya da kuma kawo kuɗin gaisuwa sannan sun ce a kusa za su dawo sa rana.

Tun bayan nan kusan kullum da marece ko dare Aliyu na gidanmu, shaƙuwa tsakanin mu sai ƙara yawa take yi. Ranar wata Litinin yana tasowa daga aiki kai tsaye ya taho gida wurina, kallo ɗaya za ka yi masa kasan a gajiye yake hakan ya sa na koma gida na ɗauko masa abinci da lemo. Zan koma ɗauko darduma ya hana ni wai zai ci a mota kawai.

Ya fara cin abincin muna hirar mu, garin dariya sai wanda ya ɗebo a cokali ya ɗan zuba gefen rigar shi, da saurina na sa hannu na fara goge masa wurin amma sai ya sa hannun shi ya riƙe nawa hannun tare da maido su jikina sannan ya mayar da nashi bisa ƙafarsa. Shiru ya biyo baya kowa da abinda yake zagayawa a cikin ransa.

Ni kam kaina a ƙasa yake, kunyar duniya ta rufeni sai tambayar kaina nake me yasa nayi hakan ma tun farko? Shikenan mutuncina ya girgiza kenan, yanzu haka ma ɗauka zai yi na saba yin hakan da wasu, wayyo Ni, ƙasa tsage kawai na shige...

Tunanina ya katse saboda maganar da ya yi cikin murya mai matuƙar sanyi "Ummu ki yi haƙuri, i can guess me kike tunani probably ma kin ɗauka wulaƙanci ne ya sa na sauke hannunki haka amma ko kusa ba haka ba ne, i did it for your own good and safety. Bari na faɗa maki wani sirri da ba ki sani game da Ni ba." Ya juya tare da ajiye farantin abincin a bayan mota sannan ya juyo da nufin kama hannuna amma sai yayi sauri ya mayar da su kan ƙafarshi. Ya cigaba da magana "Allah ya yi ni mai matuƙar ƙarfin sha'awa amma ke Ummul tsananin so nake maki shi yasa kika ga ko attempting na riƙe ki bana gwadawa, domin ji nake kaman kina passing electric current yana ratsa dukkanin jikina. Ranar da nazo ba Ni da lafiya har na goge maki hawaye a wahale na kwana, ciwon ciki kaman ba zan kai safiya ba kuma idan kin tuna za ki ga sai da kwana biyu bayan nan ban zo ba ai ko? Bana son ɓata pure alaƙarmu, besides ma shine ƙarfin ɗago maganar auren mu a wannan lokacin. Na roƙe ki ki yi mun afuwa, amma na fi kowa son na kasance tare da ke. Ummul Pleaseeeeeeee?! Ya ƙura mun ido yana jiran amsa.

Ni kuma yanda ya ja kalmar Pleaseeeeeeee ɗin nan ta saukar mun da wani yanayi a jiki na da ba zan iya kwatanta wa ba, ga kunya kamar na ɓace daga wurin kawai, da kyar na iya cewa "it's okay" na juyar da kaina ɗayan ɓangaren, wannan wane irin katoɓara ne a bakin Aliyu saboda Allah?

Tun daga ranar ban ƙara yarda na yi kusa da shi sosai ba bare na kai ga taɓa shi, shi ma ya lura amma ba shi da bakin maga

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol