Free chapter · Read without an account

15

by Fareeda Aliyu · KOWA DA ƘADDARARSA

Ƙarfe takwas na jiyo muryar Mama tana kira na daga falo, ina zuwa ta miƙo mun wayarta wai an kira ni. Da sauri na karɓa sanin cewa Yaya Zainabu ce me yin haka, idan sun gama magana da Mama sai tace a ba mu idan da daddare ne sanin kowa na gida a wannan lokacin. Ina sa wayar a kunnena na fara cewa "Yaya Zainabu? Tun jiya nake neman ki wayar ki a kashe...."

"Ba Zainabu ba ce" aka katse bi

Na juyo na kalli Maman da hankalin ta na kan TV, sannan a tsorace nace "Yaya Munnir?"

"Rufa'i ne, tunda ke ba kya gane Muryar mutane."

Da hanzari na bar falon zuwa ɗakinmu don bana son Mama ta jiyo abinda zan faɗa. Ina rufe ƙofar na fara cewa "Me yasa ka kira ni ta wayar Mama? So kake ka ja mun faɗa ko me?"

"Ba ɗaya. Kawai sanin hali ne yasa domin nasan a wayar ta kaɗai zan kira na samu mu yi magana."

"Maganar me? Ga shi har wulaƙancin 'yan matan ka ya gangaro kaina. Yanzu wai har nice zan....."

Ya katse ni "Babban abin da yasa na kira ki ta nan kenan. Don Allah Ummu ki saurareni bana son misunderstanding ɗin mu ya haɗo da Mama, domin idan ba ki saurareni ba ita zan faɗawa."

"Barazana kake yi mun?" Na tambaya

"A'a. Roƙin arziki nake daga gare ki don Allah ki saurareni."

"Ina saurare"

"Kin san wallahi, kin ji dai na rantse, ɗazun ban san kin kira ba sai bayan da nayi sallar Isha sannan naga nayi missing call ɗin ki."

"A haba? Shi yasa da na kira ka da farko naji busy ashe." Na faɗa cikin rainin wayo.

"Tsaya nayi maki bayani dalla-dalla. Akwai wata Rahma da take damu na da waya kwanan nan, ɗazu da aka kira ina kwance a falo ina kallo da na duba naga ita ce sai kawai nasa wayar a silent na ajiye. Ina ga ba tantama kiran ki ya faɗo lokacin da ita nata ya shiga shi yasa kika ji busy, domin na tabbata ba call waiting kika ji ba. Kin san dai ba ki da hujjar yi maki ƙarya ko? Don Allah ki fahimta."

Duk cikin abin da ya faɗa ba wanda ban yarda da shi ba don haka nace "To! Naji abin da kace na kuma saurara, sai an jima to."

"Tsaya manaaaaaaaa. Na fi kowa sanin kin gaji da magana da ni amma haka kawai ba wani abu Ummu ba za ta kira ni ba. Faɗa mun abinda zan yi maki ran ki ya daɗe your highness."

Duk wata ƙwarin gwiwa tawa da na haɗa ɗazu don yi masa magana yanzu ko kashi ɗayanta babu. Bansan ta inda zan fara ba, ni gudu nake kar na kwafsa don haka na amsa da "Abun ya wuce, ba shi da wani amfani yanzu sai dai ko wani lokaci a gaba kawai."

Ya sauke murya ya dinga lallashi haɗi da magiya, kasancewar Yaya Rufa'i mai wayo ne, cikin mintina uku ya shawo kaina. Nace "Um....umm....ummm cewa nayi...me.....me yasa ba ka faɗawa su Mama....um....ummm we are no longer together ba? As in ka fasa aurena. Ina ga da ya fi sauƙi ai."

Yayi ɗan jim kaɗan sannan yace "Shawarar ki mai kyau ce, amma ai kin ga bai dace na faɗa mata a waya ba ko? Kar ki damu next zuwa na Kano zan sanar dasu. Hakan yayi maki?"

A sanyaye na amsa "Eh, yayi. Sai da safe." Na katse wayar zuciya ta na rawa.

Maimakon ɗimbin farin ciki sai naji kamar an cire wani abu daga gare ni da ya sanya naji ni ba cikakkiya ba ce. Nasan ko banza sai nayi kewar salon nacin Yaya Rufa'i, wannan wane irin lamari ne wai?


Daren haka ya wuce ba tare da naji daɗin shi ba, na dinga kallon waya ta ko zai kira ni domin canza zancen da yayi amma har bacci ya ɗauke ni shiru. Da asuba ma ina tashi Sallah wayar na fara dubawa, haka na iske babu kira babu saƙo. Duk wata ƙarfin zuciya ta a ranar narkewa tayi, ban taɓa tunanin zan yi nasara akan shi ba, ga shi nayi yanzu kuma na kasa farin ciki. Naci sabon abu ne gare ni da yake bani ƙwarin gwiwar duk inda nake zan iya dawowa gare shi don ba zai gaji ba. A da kenan ban da yanzu.

A makarantar ma yau shiru shiru na yini, su Surayya sun gaji da tambaya sun sa mun ido. A haka na warware kasancewar karatun zango na biyu na kuma aji biyu ya fara zafi, ga shi har muna shirye-shiryen gwaji (test) don sun ƙara matse mana lokacin.

A gida ne kawai nake ɗan kewar Yaya Rufa'i, ganin bai ƙara kira na ba ya sanya nasan da gaske yake an bar maganar. Sai kawai na kwantarwa da kaina hankali da cewa tunda na rasa Aliyu ma ba abin da zai ƙara ɗaga mun hankali, ga kuma ƙarin cewa ba son Yaya Rufa'i nake ba (anya ban fara ba kuwa?), amma sai na bar shi a cewa nacin shi ke burge ni.

Ranar Alhamis sai ƙarfe bakwai na dare na shigo gidan saboda lakcar yamma har shida da motar shi na fara cin karo da na shigo, ai kuwa cikin sassarfa na ƙarasa cikin gidan domin naji irin labarin da yazo da shi na dangane da fasa auren mu amma sai na iske falon ba kowa, nasan duk an tafi yin Sallah don haka ni ma sai na bi layi.

Naƙi yarda na fito falo don nasan ko me zai faru Sauda za ta faɗa mun idan ta shigo. Bana son ganin shi a yau nasan kuma zai yi hakan ne domin ya faranta mun. Ko ƙwaƙwaran motsi na kasa yi, na kasa kunne ina saurare ko zan ji ko da alamar zancen amma shiru ko muryoyin su bana ji, sai da yake yin sallama zai tafi ne ma naji ana ta bashi saƙon gaisuwa wurin su Ummi da su Khadijah.

Washegari kuma da na gama lakcar shi yazo ɗaukana har yayi Sallar juma'a a central mosque kafin mu taho. Ni da mamaki fal zuciya ta amma sai na basar na cigaba da magana da Surayya ta chatting, damu na take akan shi ni kuma ina bata amsa daidai ita.

Maimakon mu wuce gida sai ya wuce da mu save mart da ke Ahmadu Bello Way, sai da muka zauna sosai bayan siyan abubuwan da za mu ci sannan ya fara magana "Ki taimaka ki ajiye wayar nan ki ban ɗan few minutes mana Ummu"

Na ɗan kalle shi sannan na lura ɓangaren da muke zaune babu mutane, ba mamaki don yau juma'a ne ko kuma ma saboda ko la'asar ba tayi ba ne.

Ya cigaba da magana "Har yanzu ba ki da feelings for me?" Ya tsare bi da ido.

Daram dam! Shine bugawar da zuciya ta tayi a take, na zuba masa ido "Ya muke mayar da hannun agogo baya Yaya? Na ɗauka ka faɗa masu tun jiya ai."

"Ummu ba da shirin rabuwa da ke nazo ba, na zo ne da niyyar ɗaga maganar daga gare mu zuwa ga iyayenmu. Na sha faɗa maki farin cikinki yana tare da ni, kin rufe ƙofar ne shi yasa kika kasa ganewa."

"Wai Yaya Rufa'i me kake so ne?" Ina jin wani iri a jikina da kaina ba zan iya fassarawa bare na faɗa maku (maman fannana ban da sa ido dai).

"Ke! Ke kaɗai nake so Ummu, ke kaɗai kika rage mun a cikar rayuwa ta, ina samun ki na gama samun abubuwan da nake buƙata."

Irin kallon da yake mun bana jin zan iya mancewa da shi har ƙarshen rayuwa ta, a take tsigar jikina ta fara tashi na kuma ɗauke idona daga kan shi ko zan samu bugun zuciya ta ya sassaita.

Ba mamaki abin da nake ji, shi ma shi yake ji a lokacin, domin shi ma shirun yayi yana kallon hannun shi da ke bisa teburin.

"Ummu ki yi haƙuri, na fi son na faɗa maki ne da kaina amma yau ɗin nan za su sanya ranar bikin mu kuma na roƙe su kar su tsawaita, ji nake kamar zan iya rasa ki." Ya wani kalan marairaice.

Tsananin mamaki ya kama ni, ashe ba neman izini na yake ba, so yake kawai ya faɗa mun wannan baƙin labari (duk da zuciya ta bata yarda da cewa baƙin labari ba ne). Na ɗago idanuna na tsare shi da su amma ya ƙi yarda ya kalle ni, sai kawai nace "Maida ni gida."

A hanyar mu ta komawa duk iya lallashin Yaya Rufa'i ranar ya sarawa taurin kaina domin ko uffan ban ce masa, ina sauraron shi (daɗi lallashin yake mun fa) ƙarewa ma har numfashin sa ina jin saukar shi tsabar hankali na gaba-daya yana kan shi. Ina ta jin ƙarar shigowar saƙonni a waya ta amma hankali na baya kan wayar yana kan shi duk kuwa da cewa ta gefen ido nake kallon shi. Wata irin hamshaƙiyar damuwa ce shimfiɗe bisa fuskar shi, irin wadda ban taɓa gani ba, domin duk tambotsena na ba ya taɓa nuna damuwa sai dai ka ga kamar ma jin daɗin faɗan yake.

A kwanar layinmu muka haɗu da Baba yana shirin ficewa, amma sai da ya ɗan tsaya fuskar shi cike da fara'a ya sanya mana albarka, alamun jin daɗi zayyane a fuskar shi. Haka ma da muka koma gida muka iske fuskar Mama, yana sauke ni kuma ya yi tafiyar sa. Yaya Zainabu ta kira ni tana murna tare da yi mun gargaɗi kar na sake na ɓata ran manya akan abin nan domin ta san hali na, na cigaba da addu'a domin mafi yawancin lokutta abun alheri baya zuwa ta hanyar da mutum yake so.

Shi kuma Yaya Rufa'i tun daga ranar bai ƙara zuwa gida ba amma yanayin wayar shi ya sauya, kamar cin abinci watau safe, rana da dare sannan text messages ɗin shi basu da lokacin shigowa, duk da wuya na karanta amma wannan karon ba na gogewa. Haka don ban amsa wayar/saƙon shi yanzu ba, hakan ba zai hana an jima ya sake yin wani ba.

A haka sai da aka share wata guda ban sa shi a idona ba kafin ya zo Kano. Kallo ɗaya nayi mashi gabana ya faɗi, ya ƙara ramewa akan ta ɓaya da nake gani, babu komai akan fuskarshi sai hanci har ya so yayi wa fuskar yawa. Duk wurin da nayi idon shi na biye da ni amma sam ya ƙi mun magana, abun ya dame ni sai dai kawai yayi murmushi idan mun haɗa ido.

Wani irin tsoro ya shige ni, na tuna irin wahalar da na sha akan rabuwa ta da Aliyu, kar dai abun ya ta'azzara shi ma abinda ke faruwa da shi kenan? Bansan ya aka yi ba, kawai gani na nayi na tsallake su Mama na doshi wurin da yake zaune na tsugunna gaban shi tare da leƙa fuskarshi a hankali nace "Yaya Rufa'i? Ba ka da lafiya ko?" Na waigo wurin da Mama ke zaune taɓa kallon mu nace "Mama Allah Yaya Rufa'i ba shi da lafiya, ku tashi mu kai shi asibiti, ji yanda ya koɗe fa."

A hankali nake jin maganar shi yana cewa "Ummu, Ummu, Ummu kalleni ki ga, I'm fine, kin ji?" Sai ya juya wurin Mama "Ayyuka ne suka yi yawa da rashin zama wuri ɗaya amma ni lafiya ta ƙalau." Sai ya miƙe ya fice daga falon.

Ko ɗankwali ban tsaya ɗauka ba na biyo shi a guje, hakan ya sanya ya rage saurin tafiyar shi tare da juyowa fuskarsa babu walwala, duk da hakan ya sa gaba na ya faɗi bai hana ni faɗin "Yaya Rufa'i don girman Allah ka faɗa mun abin da yake ramar da kai, zan yi iya bakin ƙoƙari na wurin taimakawa, idan ya wuce ƙarfi na zan baka comfort duk da ba son auren nake yi ba ai kai ɗan uwana ne. Bana buƙatar damuwar ka ko da kuwa nice."

Ya bani dogon kallo kafin ya juya tare da cewa "ba zaki iya ba Ummu." Haka na dinga bin shi ina magoya bai juyo ba sai ma sauri da ya ƙara ya shiga motarsa ya bar gidan.

Ɗakin mu kai tsaye na wuce kawai, wani irin tsoro da damuwa mai tsanani ya kama ni har na gaza jurewa, don haka can yamma kawai na shirya domin bin sa gidan su. Ina fitowa na hango Yaya Naziru zai fita da sauri na tsayar da shi da roƙon shi ya sauke ni can gidan, ina jin shi ma ya lura a kiɗime nake don bai ce komai ba.

A tsattsaye na gaishe da Ummi ko ta kan su Sister Samiha ban bi na wuce ɓangaren shi da hanzari na, ina jiyo Ummi na faɗa mun wani abu amma ban ma san mene ba. Ko da ban juyo ba nasan duka kallo na suke yi.

A kwance na same shi da alamu ma bacci yake yi don haka gefen gadon na samu wuri na zauna ina nazarin fuskarshi yayin da bugun zuciya ta ya ƙaru da sauri. Gashin idon sa yayi masa rumfa har ina ganin inuwar shi, a hankali na miƙa hannu na taɓa gashin wanda sanadin haka ne ya farka. Kallona yake cike da mamaki sai kuma ya fara ƙoƙarin zama yana faɗin "Ummu? Ke ce? Me ya faru?"

Da saurina na sauka ƙasa tare da tsugunawa alamar roƙo "Don Allah Yaya Rufa'i ka faɗa mun me ke faruwa, zuciya ta har wani ɓal-ɓal take yi saboda tsananin damuwar da na karanta a fuskar ka...." Ban ƙarasa ba ya sa hannunshi domin ɗago ni daga tsuguno zuwa bakin gadon.

Yace "Ummu ai idan ina da damuwa a rayuwa ta ɗaya ce, kuma kin san ke ce ai."

"Me kake so yanzu to? Ka faɗa mun ni kuma da izinin Allah zan yi."

"Ke ɗin dai ke ce"

"Yaya Rufa'i zan aure ka bisa son raina ba kaman yanda ka yi zaton tursasawa ne yasa na amince da auren ba."

Fuskar shi bata sauya ba sai ma tsare ni da ido da yayi "Kina so na?"

Ni ma na ɗora idanuna bisa nashi a wani yanayi da ke nuna alamar kamar maganaɗisu ne ke riƙe da idanuwanmu nace "Ina son ka, Ina son Yaya Rufa'i. Ka ji ko na sake maimaitawa?" Kamar walƙiya sai naga kamar an janye mayafi daga fuskarshi, wani sabon annuri yana fitowa. In dai ba gizo idanuna ke yi ba har wani haske ki fita daga idonshi. A take wani farin ciki da bansan ana iya jin irin shi ba ya lulluɓeni. Sai ga shi zube a gabana yana faman nanata "da gaske kike Ummu?" Ni kuma har gajiya nayi da amsawa.

Ummi ce ta leƙo tare da ba mu umarnin dawowa falo don bai kamata mu zauna ɗaki mu kaɗai ba. Subhanallahi! Ranar na ga kulawar soyayya, wani irin salalan tsiya na kusa yi wa kaina? Da ƙyar ya daure ya je yayi wanka domin ya maida ni gida bayan anyi Isha. Abban su sai da ya iske ni a gidan kafin mu taho, kowa murna yake yi da wannan auren namu, ni kaina murnar nake yi yanzu.

A hira mai daɗi muka dawo gidan mu, mun daɗe a haraba muna magana kafin ya raka ni bakin ƙofar falo, wai ba zai shiga ciki ba shi zance ya zo yi yau."

Bayan ya je gida sai ga saƙon muryarsa (voicenote) yana ta shigowa waya ta yana faɗa mun irin yanda yake ji na a zuciyarsa. Ni fa ranar ko bacci sai da ya ƙauracewa idanuwana, sauraren kalaman shi ne kawai a gabana. Kuma ya ƙi yarda mu yi waya, so kawai yake yi na dinga saurara. Biyun dare bacci ya ɗauke ni a wani irin yanayi mara fasaltuwa, zan dai iya cewa ji nayi kamar a gajimare nayi bacci.

Kashegari da wuri na tashi na fara shirya mashi karin kumallo saboda jiya mun yi zai zo gida ƙarfe goma na safe. Gaba na naji ya faɗi, ina dafe da shi ina tunanin menene haka kuma sai hankali na ya kai da cewa gidanmu yayi extra quite wanda ban saba ji ba.

A hankali na ajiye kayan hannuna na leƙo farko, Mama na zaune 'yan biyu kuma sun saka ta tsakiya, kowanne kan shi na kwance jikin ta. Gefe guda ta wurin window na hango Sauda tana kallon waje. Kafin na kai ga magana sai Yaya Naziru ya shigo a gaggauce yana cewa "Mama na fito da motar"

Dukkansu ba wanda ya lura da ni a bakin ƙofar kicin sai da nayi magana sannan su duka suka juyo suna kallona "Ina zaku tafi ku duka haka?" Idon Yaya Naziru da na kalla bansan lokacin da nayi baya ba saboda tsoron da suka ba ni, a firgice kamar wadda lantarki ya kama nace "Me ya faru?!"

"Kawu Habibu ne aka kwantar a asibiti." Faɗar Hussein

Na dafe ƙirjina ina addu'a sannan nace Allah ba shi lafiya, idan na gama girki Yaya Rufa'i zai kawo ni anjima kafin su dawo.

Da kyar na kammala girki nayi kwalliya kafin na koma kan waya ta. Saƙon duka na Yaya Rufa'i ne, saƙo biyar na magana (VN) sai missed call ɗaya, ban ma tsaya sauraron saƙon ba sai na kira shi kawai ganin tun bayan asuba kaɗan duka yayi saƙon da kiran. Jin tana ƙara bai ɗauka ba sai kawai nasa a raina yana kan hanyar zuwa ne.

Baba ya shigo gidan yace na fito mu je dubiyar nan (don dai Baba ne amma da tuni nace a'a sai an jima). Don haka sai na bar mashi text message ɗin na ajiye masa breakfast akan dinning table nan babban falo, idan ya gama ci ya same mu a asibitin. Sannan na ƙara da faɗa mashi wurin da zan bar makullan idan ya ƙaraso.

Ina ta danna waya ta, labari nake bawa munafukan aminaina masu son jin komai a ɗan ƙaramin group ɗin da muka buɗe mu kaɗai, yanda na fara son Yaya Rufa'i. Suna ta tsokanata wai dama can fulako nake yi. Da naji yayi parking sai na rufe wayar da nufin sauka daga motar amma kuma nan ba asibiti ba ne, gidan su Yaya Rufa'i ne!

Tunda daga waje nake ganin jama'a, 'yan uwa ta ko'ina but ni burina na cimma sister Samiha naji taron menene wannan? Manta me ake kira gaisuwa nayi. Falon Abba na hango a buɗe don haka can na dosa kai tsaye ganin mutane da yawa a can. Idon kowa a kaina yake don haka kaina a ƙasa nake ƙarasawa.

Turus na tsaya! Yaya Rufa'i na gani a kwance a ƙasa ga mutane nan 'yan uwa a zaune, a take naji ba ni da sauran nutsuwa. Yayi matashi da pillow me farin yadi, da na ƙara ƙifta idona sai naga kaman darduma ce fara, sai a hankali kuma abun ya fara rikiɗe mun zuwa mayafi fari fat!

A hankali na fara matsowa gare shi tunani na yana barin jikina har na ƙarasa na zauna gefe sa nace "Yaya Rufa'i?" Shiru ya biyo baya.

Na juya ina neman Mama tare da cewa "Dama ai na faɗawa Mama ba shi da lafiya, nace mu kai shi asibiti kuka ƙi, yanzu ga shi kun jawo yana kwanciya a ƙasa. Yaya Rufa'i ka tashi, yanzun nan na gama haɗa maka abinci kuma duka favorites ɗin ka ne, ka tashi ka ci sai ka sha magani, ka ji? Ina girgiza shi a hankali.

Sister Samiha ce tazo ta fara ƙoƙarin janye ni tana cewa "Ummu hakuri za ki yi, babu...babu....babu.....Yaya....babu Yaya Rufa'i." Tana gursheƙen kuka.

"Babu Yaya Rufa'i? Wannan kan ki ne? Nace wannan kan ki ne? Iye?! Wai kai kukan me kuke yi ne gabaɗayan ku? Kun zazzauna a falo kun kasa koma mene ya kawo ku kuna yi wa mutane kuka......." Sambatu ke fita da baki na mai ma'ana da mara ma'ana don ni kaina bansan me nake faɗa ba.

Wani zafi naji a kumatu da ya dawo da ni hankali na, Yaya Zainabu ce tsaye idanunta sun kumbura saboda kuka, sai kuma na ga ta tsugunna ta rungume ni tana cewa "ki yi haƙuri Ummu, Allah ya karɓi Yaya Rufa'i, ya rasuuuuuuuuuuuuuuuu......" Ta ƙara fashewa da wani kukan.

Na ji abinda tace Amma bana son yarda don haka na ƙara matsawa kusa da fuskarshi tsoro na daɗa shiga ta nace "Yaya Rufa'i ka tashi don Allah su gani, ai ba ka mutu ba ko?" 

Shigowar Yaya Naziru ce tasa na rarrafa na isa gare shi domin kafar tawa ta ƙi yarda na tashi tsaye nace "Yaya Naziru ai an kusa yi mana aure ko? Ai ba zai iya mutuwa yanzu ba ko? Ka taimake ni ka faɗa masu ba mutuwa yayi ba, rashin lafiya ce kawai."

Motsi naji daga bayana na juya sai naga ana ɗaga shi a makara, wanann karon bansan ta yaya na miƙe ba kawai na ganni riƙe makarar ina faɗin "wai ina zaku kai shi ne, jiya cewa yayi gajiyar aiki ce ba rashin lafiya ba, ku bar shi ya tashi. Na shiga uku! Wayyo Allah na! Yaya Rufa'i kar kayi mun haka don Allah!" Rirriƙe ni aka yi ina ji ina gani aka ɗaga makarar sama, wannan ya tabbatar mun da gaske rasuwar ce sai kawai sulale na sume a wurin.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol