Free chapter · Read without an account
38
BAYAN WATA BIYU
Mun yi jarabawar zango na farko har na ƙare mun shiga na ƙarshe. Alhaji Hamisu ya fara maganar a sa rana, nice ma nake ta jan lamarin tunda nasan yanda yake so a sa ɗin. Abinda zai buƙata ba zai wuce sati biyu zuwa uku ba, idan ya ɗaga mana ƙafa ya bari mu kai wata guda.
Na fi kowa sanin sa ranar ba za ta dami su Baba ba, ko banza duka yayyena kowa na aiki, ba ma sai an ce wani abu nasan ko su sun isa su shirya mun ɗaki na ba tare da jiran Baba ba, suna da matuƙar zumunci. Balle ma ni kaina da kuɗina a account. Kuma daga take-taken Alhaji Hamisu ma, shi yake niyyar ɗaukar nauyin komai domin har faɗa mun yayi kwanakin baya cewa "UmmalKhairi kaɗai nake bukata a kawo mun, domin a gida na babu wurin kaya, ki taimaka mu taru a inuwa ɗaya gurin Baba yanda zai yi saurin yarda." Menene yake hana ni ba shi damar turowa ne ban sani ba amma na dangana hakan da cewa nasan ina cewa eh na gama zaman gidanmu, amma ai ina son Alhaji Hamisu, ko ba don komai ko don sauƙin kanshi da kuma yanda ya kan biye mun a abubuwa da dama.
Akwai ranar da na mance ban sa mai a mota ta ba, kuma wanda ya rage a ciki da na dawo da shi, Hussein ya ɗauke motar ya je ya sha yawon shi tare da kunna AC ya ƙarar mun. Duk a zato na ina da ragowar da zai fitar da ni sannan na sha a hanya. Raina a ɓace da naga ya ƙarar da man ga shi lokacin tara saura minti goma sha biyu. Tara ya kamata a ce ina ofis, Hussein ɗin kuma tun bakwai da rabi ya fita yau don haka daga ni sai mama a gidan.
Samun kaina nayi da zaro waya ta na kira Alhaji Hamisu, sai da ta fara ƙara sannan na dawo hayyacina, to me zan ce masa da safiyar nan? Ba ni da mai ko me? Kuma kafin ya zo ya kai ni wurin aikin ma lokacin ya ƙure, domin lokacin da zai ishe shi ya zo ai ya ci ace na isa ofis ɗin ma har nayi nisa a aiki. Na katse kiran kawai na doshi hanyar fita daga gidan ina ta tsaki, Allah ne ya so Hussein ya riga ya fita amma irin masifar da take ci na da sai ya raina kan shi yau.
Tunda naji waya ta ta ɗau kara nasan shine ya biyo bayan kirana bayan ya ga missed call, ina tafe zuwa bakin titi ina faɗa masa dalilin kiran da nayi masa, wani a gaba na har ƙara juyowa yayi ya kalle ni saboda yanda nake magana a shagwaɓe. Alhaji kam dagewa yayi akan cewa na jira shi, don yanzu haka ya fito daga gida zai je ya samu wasu mutane, but they can wait. Duk da sanin cewar zan yi latti hakan bai sanya na tafi ba, zuciya ta shi take son gani da alama.
A hanya bayan ya ɗauko ni ya lura sai kallon shi nake yi, bai juyo ya kalle ni ba yace cikin murmushi "sabo na zamar maki ne yau?" Ganin bai juyo ba sai ni ma ban ɗauke idanuwa na ba nace "ai ni har kullum sabo kake a wurina, amma kasan me yass nake kallon ka yanzu?"
"A'a."
"Kawai daɗin yanda kake mun ne ya sanya na ɓaci, kawai so nake kodayaushe na kasance tare da kai. Sai na dinga ji na kamar sarauniya." Na faɗa.
"To ai ke sarauniya ce Madam, komai kike so za'a yi maki sai dai idan ba ki nema ba."
Maganar shi ta sanya ni dariya nace "Hmmm! Allah ka koyi ce mun a'a tun yanzu, domin idan ban saba ba yanzu, idan ka fara faɗa bayan mun yi aure za ka wahala da yawa."
"Haka kike gani?"
"Hakan ne ma ai, haka mu mata muke. Tun daga waje a ke fara ɗora mu akan yanda rayuwar gidajen mu za ta kasance, idan ba haka ba, sai a yi ta rigima bayan an yi aure."
Yana murmushi alamar ɓoye dariya yace "Zan kiyaye UmmalKhairi, amma ba ni da buƙatar canza ki daga yanda kike yanzu haka har zuwa alaƙarmu. Kina da tunani kafin ki aiwatar da abubuwa da yawa, na san ba zan yi nadamar tafiyar dake da nake yi yanzu haka ba." Ya sauke ni a wurin aikina a gurguje muka yi sallama ganin cewar na makara ya wuce.
Watarana muna zaune a falo Mama take tambayata "Ummu sai naga kamar Alhaji ya ɗauke ƙafarsa daga gidan nan ko? Yaushe rabon da naji kin ce za ki je harabar gida wurin shi."
Na amsa "Ya kwana biyu rabon shi da gidan nan kam, amma ba laifin shi ba ne, ni ce nake hana shi zuwa."
Cikin mamaki tace "Saboda me? Ya yi maki wani abun ne?"
"Ni haka kawai idan yace zai zo sai naji raina na suya saboda ɓacin rai. Idan kuma na ɗan daɗe bangan shi ba sai naji kamar ina kewar shi, abun ne kawai ga shi nan a cukurkuɗe."
Mama tace "Kina amfani da maganin ki kuwa?"
Na amsa "Au! Ya ƙare fa. Wallahi kullum sai na zo zan faɗa ya ƙare sai na manta me zan faɗa."
Ta cigaba "Su kuma addu'o'in fa?"
"Kin san kwana biyu na zama busy, ga ƙarin project ɗin makaranta akan sabgogin nawa. Kullum a gajiye nake dawowa gidan nan, ina fara yin addu'o'in sai bacci ya ɗauke ni ko farkawa bana iya yi sai asuba. Kuma da safe kin san da wurwuri nake fita."
Ba ta kalle ni ba, ni na ɗauka ma faɗa za tayi mun na yin wasa da lafiya ta amma sai na ga ta duƙar da kanta ƙasa tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah ka taƙaita mana wannan musiba, Allah ka ba mu juriya." Ta ɗago ta kalle ni sannan tace "Ummu ki dinga daurewa da dagewa da yawan addu'o'i, kin ji? Su ne kariyar ki, kar ki dinga wasa da shi."
Ashe ma wasa farin girki, domin ranar da ya zo bai faɗa mun ba aka ga abun mamaki a gidanmu. Hussein ya gani a bakin gate sai ya turo shi ya kira masa ni. Lokacin da ya shigo ɗakina wanka nake yi don haka sai ya ɗaga murya yanda zan jiyo shi daga bayangida yace "Yaya Ummu idan kin fito ana jiran ki a farfajiyar gida." Yayi ficewarsa.
Ko da wasa ban kawowa raina Alhaji Hamisu ba ne, don haka a hanzarce na sa kaya na fito. Sai da na zo kusa da shi na gane shi ne, a take na ji wata mummunar faɗuwar gaba da ban taɓa jin ta a rayuwa ta ba, don haka sai na yi ta maimaita 'innalillahi...' a hankali.
Ko da na ƙaraso cikin dauriya na yi masa sallama, amsar shi kam ban ji ta ba domin tunda ya ɗago ya kalle ni, a take na ga fuskarshi ta canza ta koma wani abu da ba zan iya misaltawa ba. Magana yake yi amma kunnena ba ya jin me yake faɗa, a take kuma na buga wata razananniyar ƙara na sulale a wurin na sume.
Ƙarar sai da ta sanya gabaɗaya na cikin gidanmu a lokacin fitowa domin ganin me ke faruwa. Hussein da aka yi abun akan idon shi ne yake yi wa su Mama bayani. Ruwan sanyin da aka dinga zuba mun ne ya farkar da ni, amma ina ɗaga ido na hango Alhaji a tsaye rungume da hannayensa cike da ruɗani yana nazari na, a take ya sake rikiɗe mun zuwa wata halitta da tafi wadda na gani ɗazu muni. Ƙarar da na saki wannan karon ma tafi ta baya na sake sumewa.
Hussein ne ya ɗauko ni zuwa falo saboda sun fuskanci me yake sumar da ni. Na farka na gan su sun zagaye ni suna ta tofa mun addu'o'i. Garas na miƙe kamar wadda tayi bacci ta tashi don ko kasala ban ji ba a tare da ni. A lokacin ne nake faɗa masu Alhaji rikiɗa yake yi, anya kuwa mutum ne? Daga haka kuma na kama sabgata na bar su suna ta jimami. Baba ya damu ƙwarai da halin da nake ciki, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar yana cike da damuwa. To amma ya ya zasu yi? Kowa da ƙaddararsa, ni ta wa haka take dole kuma sai ta same ni.
Kwana biyu tsakani sai ga Yaya Zainabu ta zo, daga wurin aiki ma take ta biyo gida. Ina kitchen ina masu girkin abincin dare ganin cewar na dawo da wuri. Daga kicin ɗin ina jiyo hirar da suke yi, a gigice Yaya Zainabu take cewa wai a wurin aikin su ne tana hirar halin da nake ciki shine ɗaya daga abokan aikin ta tace ta san matar Alhaji Hamisu. Har tana faɗin ko tayi rantsuwa ba zata yi kaffara ba akwai sa hannun ta a cikin halin da Ummu take ciki.
Duk da Mama ita ma zargin ta hakan ne sai da tace "A'a Zainabu, kar mu je mu kwashe mata alhaki garin yi mata zargi fa."
Yaya Zainabu tace "Tsaya ki ji abun Mama, shi Alhajin ya fi ƙarfin ta saboda dukkanin asiranta ba ya riƙe mata shi yanda take so saboda an ce bata isa ta juya shi ba don haka sai ta juya makaman yaƙin ta akan waɗanda yake nema. Sannan wadda ta bani labarin tace ba ƙaramin mamaki tayi da Ummu har yanzu tana da sauran hankalin ta. Domin kaf 'yan matan da ya taɓa nema da aure cikin biyu dole ɗaya ya faru, imma yarinyar ta rasa ranta haka kawai babu ciwo ba wani abu ko kuma ta haukace. 'Yan mata shida ta lissafa mun waɗanda suka hauka ce, yanzu a lamari irin wannan Mama kina tunanin coincidence ne? 'Yan mata shida fa! Kuma kowacce wadda mijinta yake son ya aura? Ai ba zai taɓa zana gamo da katar ba."
Mama cikin jimami take zabga sallallami tace "Chabdijan! Wannan mata me take son yi da duniya haka?"
Yaya Zainabu tace "Kin san basu taɓa haihuwar ɗa namiji da shi ba, kuma wai a wurin yawon tsubbun ta an faɗa mata amaryar da zai kawo mata ita za ta haifar masa yara maza kuma masu yawa sannan ita ce zata ja ragamar gidan. Shikenan ta haukace da kashe ko haukata matan da yake nema."
Mama tace "Ikon Allah! Ita a tunanin ta ta haka za ta kawar da abin da Allah ya ƙadarta? Besides ma ai zancen 'yan duba ai bogi ce, ba kuɗi suke nema ba?"
Yaya Zainabu tayi ajiyar zuciya tace "Allah dai ya sauwaƙe! Abokiyar aiki na tace na faɗa maki a dage da nemar wa Ummu maganin karya sammu da na kariya. A dage da addu'a sosai da sosai, idan ba haka ba ummu za ta iya kasancewa cikon ta bakwai ɗin."
Hankali na baya jiki na kammala girkin daren, a gurguje na koma ɗaki na na zaro waya ta tare da lalubo lambar shi a yayinda gaba yake faɗuwa cikin tsoron abinda zai wakana tsakanin mu.