Free chapter · Read without an account

39

by Fareeda Aliyu · KOWA DA ƘADDARARSA

Hankali na baya jiki na kammala girkin daren, a gurguje na koma ɗaki na na zaro waya ta tare da lalubo lambar shi a yayinda gaba yake faɗuwa cikin tsoron abinda zai wakana tsakanin mu.

Ganin mun gaisa ba abinda ya faru sai naji hankalina ya kwanta. Ɗan jim ɗin da nayi ne ya bashi damar magana "Ummu kin ji ni shiru ko? Tsoron faruwar wani al'amari ne ya sanya na ɗan ja baya da neman ki har ta waya."

Maimakon na amsa maganar da yayi sai nace "Don Allah wani abu nake son tambayarka."

Ya amsa "Ina sauraren ki, tambayi ko me kike so ni kuma zan ba ki amsa in shaa Allah."

"Yaran ka nawa ne? Ya sunan su?"

Duk da yayi mamakin tambayar amma hakan bai hana shi amsawa ba "Su huɗu ne, Amina, Zainab, Fiddausi da Imranatu." A raina nace ashe da gaske ne dai 'ya'yan na shi duka mata ne. Sai kuma na cigaba da tambayoyi na da "Don Allah 'yan mata nawa ka nema da aure kafin ni?"

Nan kam shiru yayi mai tsawo ni ma kuma ban katse masa shirun ba, sannan ya amsa "UmmalKhairi ban da na riga nace zan amsa dukkanin tambayoyin ki da ba zan cigaba da amsawa ba. Su tara ne, uku daga ciki muna tare don har maganar aurenmu ta fara ƙarfi na rasa su ta hanyar mutuwa. Babu ciwo babu komai aka wayi gari babu su. Ragowan kuma Allah ne bai yi auren ba. Assurance ɗaya zan ba ki, duka lamarinsu ya wuce, ke ce present and in shaa Allah future ɗina, kar ki bari zancen su ya shiga kan ki (ya ɗauka kishi nake yi shi yasa nake tambaya a game da su). Ragowan kuma baya-baya na ga sun fara ja da ni, ni kuma ina ganin mutum ya fara ja baya da ni bani da lokacin batawa."

Gaba na yana faɗuwa muka yi sallama. A halin yanzu na gama saduda akan komai, wallahi ba ni da wani haufi ita ce tayi mun abinda ya sanya nake ta masifar rama. Fuskata ba komai sai idon da tsabar rama har nema yake ya yi wa fuskata girma, sai kuma hancin nan nawa tubarkallah amma bakina kan shi yayi wa fuskata girma yanzu shi ma sai haƙora kawai. Watau ba domin Allah ya taƙaita mun ba, ranar da na fara mafarkin da za'a yanka ni, ban da Hassana na gida ta ganni ina juye-juye ta tashe ni da sai dai a tashi a ga gawa ta a gida kenan. Subsequent days ma ai su Mama ke zama da ni, ina farawa suke tashi na.

A ƙarshen sati Baba ya kirawo Alhaji Hamisu bayan yanke shawarar da suka yi, watau tsakanin Baba, Mama da yayyena. Baba yayi masa bayani dalla-dalla akan na samu rashin lafiya da ake tunanin asiri ne ko sammu ne (amma ba'a ce masa matar shi ake zargi ba), kuma ana kyautata zaton sabo kasancewarsa tare da ni ne ya ja aka yi mun, kuma rannan ya ga mai ya faru da muka gamu, Baba ya shaida masa nace idan na gan shi nace rikiɗa yake mun zuwa halitta mai matuƙar ban tsoro saboda haka bisa shawara ya kamata a dakatar da komai. Baba ya ɗauko kuɗin aurensa dubu ɗari biyu da hamsin ya dawo masa da shi, amma fafur ya ƙi karɓar kuɗin har yana faɗin zaman alherin da yayi da ni shi mai iya ba ni kyautar kuɗin ne ko da kuwa babu zancen aure a tsakanin mu, ya ƙara cewa dukkanin abinda ya ba ni gabaɗaya ba wanda yake buƙatar a dawo mashi da su. A faɗar Hussein da aka yi komai a gabansa cewa mun yayi idon Alhajin kamar zai yi kuka ya tafi, don idon shi sun yi jazur. Sannan yana tafiya domin fita daga gidan yana yi wa kan shi magana cikin matuƙar sanyin jiki.

Tsabar tausayin kan mu ya sanya na rufe kaina na sha kuka. Na kuma faɗawa kaina asirin ta ma kawai ƙaddarata ya tarar, da a ce Allah ya ƙadarto cewar shine miji na ba wani asirinta da zai yi tasiri a gare ni balle ya hana ni auren sa. Ni kaina na san ina son Alhaji Hamisu ko ba don komai ba ko don sanyayar soyayyar da yake nuna mun, ga rarrashi yanda zan yi shagwaɓa ta son raina kuma yayi indulging ɗina, bawan Allah!

Addu'a na dage da yi domin ba ni da komai da ya wuce ta. Cikin ikon Allah a sati uku da rabuwar mu na fara dangana da al'amarin Alhaji sosai da sosai, sai kuma na ɗau sabon hali.

Ranar Laraba da muka tashi daga wurin aiki ganin cewar ba abinda zan yi ko na koma gida, sai muka tafi tare da Rahina bikin wata 'yar uwarsu. Dama saboda ciwon rabuwa da Alhaji na maida kaina busy sosai, ko ma mene in dai zai zamo mun distraction yi nake yi, yana daga cikin abinda ke taimako na wurin rage tunani. Kuma kasancewar Rahina ce za tayi wa amaryar kwalliya sai zuwan mu ya zama da wuri.

Idona na buɗe ina kallon yanda take yin kwalliyar, ashe wanda nake gani a fuskar ta nafila ne. Mutum uku tayi wa, ni nake miƙa mata abubuwan kwalliyar, ita kuma tana mun bayanin amfanin abun, sannan ina gane yanayin yanda take amfani da kowanne kasancewar duka su ukun kalar fatarsu ta bambanta. Kamu ne ranar, muna nan har biyar da rabi.

Abin mamaki sai ga shi mun haɗu da Humaira a wajen da ɗan cikin ta da har ya fara fitowa. Cikin mamaki nace "Humaira? Me zan gani? Yanzu saboda Allah sai ki yi aure amma ko a waya ba za ki faɗa mun ba? Ko ban je ba, addu'ar Allah ya sanya alheri ma ai abu me kyau ne."

Tana murmushin kunya tace "Wallahi ba laifi na ba ne, Fa'izunmu nace ya faɗa maki kuma ya tabbatar mun ya isar maki da saƙon."

"Ni ba wani saƙo da ya faɗa mun. Shi yayi nasa auren ne yanzu?"

Tana ƙaramar dariya tace "Rana ɗaya aka yi ni da shi ai."

"Wace amaryar? Inye?" Na tambaya.

Sai kawai ta cigaba da dariya ba ta amsa mun ba, sai kuma ƙwaƙwalwa ta ta ɗau haske don haka nace "Wait! Kar dai ke ya aura?" Gyaɗa kai tayi ba ta amsa da baki ba, tana murmushi tana kallona kuma.

Nace "Wow! Maa shaa Allah! Abu yayi kyau! Wallahi naji maku daɗi!" Baki na sam ya ƙi rufuwa kuma har zuciya ta taya su murna nake don sun dace da juna sosai da sosai.

Shida saura muka baro wajen tare da Rahina don zan sauke ta a hanya kafin na wuce. Waya ta na hannunta tana ta game, in dai dama na lura waya ta babu chaji bana barin ta kusa da Rahina, don za ta iya kwana tana yin game ɗin nan ba tare da ta gaji ba kuma ta kasa sa shi a wayar ta. Naji shigowar text message amma sai na ɗauka na tallukan MTN ne da suke damun mutane da shi, don haka ko ta kai ban bi ba.

Rahina tace "Alert ne daga banki ki Hajjaju gidan kuɗi." Ihu ta fara yi tana cewa "Wannan ba miliyan biyu ba ce? Ko miliyan ba zero shida take da shi ba? Duk ta rikice.

Tsaki nayi nace "Ke ma dai ki ji Rahina, Ina naga wanda zai bani waɗannan manyan kuɗaɗen? Ƙila kuskure ne."

"Tsaya ki ji" ta fara karanta saƙon a fili kamar ya da aka turo shi "Your account 307****156 has been credited with NGN 2,000,000.00 on 20-AUG...." Ban bari ta ƙarasa ba na warce wayar gabana yana faɗuwa. Na yi parking na hau karantawa a gurguje amma ina ganin sunan wanda ya turo sai hankali na ya kwanta don nasan zai aika, Alhaji Hamisu ne. Don haka sai nace da Rahina "Au! Kuɗi aka turowa su Mama, ban ɗauka ta account ɗina za'a turo ba." Ko ta yarda ko bata yarda ba oho, mun dai share zance har na sauke ta.

Kafin na isa gida ruwa ya tsuge kamar da bakin ƙwarya, na ɗan daɗe a mota ta zaune ina jiran ruwan ya ɗan tsagaita kafin na shiga gida. Zuciya ta tana ta zuga ni na kira shi naji dalilin tura mun kuɗi maƙudai haka nan, amma sai na lallaɓi kaina da cewar na ɗan dakata sai na faɗawa Mama tukunna.

Ganin ruwan ba shi da niyyar tsagaitawa, sai kawai na zuba wayoyina cikin jaka ta sannan na sa jakar ta cikin riga ta na rufe, takalmina a hannu na fito daga motar a guje nayi cikin gida, don sai daga nesa na danna lock ɗin motar ma.

Hussein dariya yake mun ganin na jiƙe har ina ɗiga, na jefe shi da makullan motar tare da cewa "Me dariyar mugunta kawai, je ka shigo da motar, tana can waje don ba zan iya buɗe gate ga ruwa ba kuma dai kasan Yaro ya tashi daga aiki."

Sai da nayi wanka tare da sallah, na sa doguwar riga mara nauyi kafin nazo na nunawa Mama alert ɗin. Ita mamaki ne ya rufe ta har take tambayata ko na taɓa ba shi account number ɗina.

"Wallahi ko da wasa ban taɓa ba, saboda nasan zai iya tura mun kuɗi ta nan saboda ya san ba zan karɓa a hannu ba. Kawai dai yasan banki na First Bank ne."

Hussein da ke gefe yace "Sanin account ɗin mutum ai ba wani abu mai wuya ba ne, akwai abokanmu da suka yi redeploying daga garuruwan da aka tura NYSC zuwa Kano, so, alawi ɗin su na wancan garin bai zo ba saboda basu san account number ɗin ba. Customer care suka kira, sai aka ce su tura account name ɗin su da phone number, ko minti ashirin ba'a yi ba aka turo masu. Ba mamaki Alhaji tunda shi babba ne, ƙila Manajan ya samu tunda ya san sunan Yaya Ummu cikakke sannan yana lambar wayar ta. Sai dai ko ku kira ku ji kuɗin na menene ya turo. Wai ma nawa ne da kuka wani damu?"

Mama tace "Miliyan biyu ne fa."

Hussein kifowa yayi daga kan kujerar da yake kwance yace "Kan Uba!" Ni da Mama kuwa sai muka hau yi masa dariya.

Ko da na kira shi a waya cewa yayi ihisani ne na daɗin zaman da ya ji tare da ni, yana fatan zan yi amfani dasu na gina wani abu a rayuwa ta, ko kuma na ƙara girman business ɗina. Ya kuma yi mun fatan alkhairi tare da cewa wannan wayar ce ta ƙarshe a tsakanin mu. Sai da nayi kuka sosai a daren nan. Muryar shi kaɗai ta sanya naji kewar shi da yawa. Baba ma bai ce komai a kan kuɗin ba, da alama ya gaji sannan da ƙarin cewa shikenan an rabu gabaɗaya.

Washegari mun je bikin tare da Rahina, kamar jiyan ita ce tayi kwalliyar a take kuma sha'awar kwalliya ta kama ni. Komai take yi yau ma idona na kai don yau kafin ta faɗi abinda zan miƙo na miƙa, alamar cewa lesson ɗin jiya ya shiga kaina sosai. A kuma hanyar mu ta dawowa na roƙi Rahina akan gobe asabar ta raka ni na siyo kayayyakin kwalliya. Ita kam tsabar farin ciki kamar ta tashi sama don ta samu 'yar uwa.

Kafin sati biyu ba wani abu da za'a layance mun akan kwalliya, na zama gwana na gwanance. Shine kuma sabon halin da na koyo bayan rabuwa ta da Alhaji Hamisu.

*************************


Kafin shekarar nan ta ƙare na kammala NCE ɗina anan kwalejin Sa'adatu Rimi da wani matsanancin farin ciki sanin cewar ni da makarantar mun rabu har abada, don ina ga dana karɓi result ɗina shikenan ko ƙafa ba zan ƙara takawa zuwa ciki ba. Yanzu haka result nake jira kaɗai domin cike DE zuwa jami'a, finally Allah yayi lokacin zuwa jami'ar tawa yayi. Bana jin ko ɗar saboda a NCE 3 na maida hankali sosai akan karatu, da matukar wuya a samu course ɗaya da zan faɗi bare na dawo spill-over.

Kwalliya kam sai abinda yayi gaba. Haka da bikin Rahinatu nice na dinga yiwa mutane kwalliya. Sai da kaya na suka ƙare gabaɗaya sannan na haƙura, kuma a washegari naje na sake siyan wasu.

'yan biyu watanni kaɗan ya rage masu su kammala bautar ƙasa. Hassana ta zama 'yar Yola don ban ga alamar tana shirin dawowa Kano ba bayan ta kammala bautar ƙasar.

A irin leƙowar da take yi mana ne zuwa Kano, watarana na ritsata sai ta bari nayi mata kwalliya. Ita kuma ta dinga zamewa tunda a iya sanin ta ita ta fi ni iyawa ma. Har wurin Mama ta gudu wai ita ba zan ɓata mata fuska ba, Mama ita kuma dariyar mu kawai take yi tana cewa "Yau ga ikon Allah, tunda ba ta so a ƙyaleta mana."

Ni kuma nace "To Mama ta bari ta gani mana, idan ban iya ba zan bata abubuwan da za ta cire kwalliyar ko kuma ta wanke fuskar ma kawai."

Sai da muka gama ja-in-ja, ni naci, ita kafiya, kafin da ƙyar Mama sanya ta ta tsaya amma sai da na ajiye wipes, ruwan zafi da face wash sannan ta zauna na fara yi mata. Ƙwarewar da nayi yanzu tana sawa nayi sauri, cikin ƙanƙanin lokaci na kammala, na hana ta kallon mudubi sai an gama gaba-daya sannan.

Ihu kawai ta saka sannan ta juyo tana kallo na "Yaya Ummu?! Kai! Yaushe kika zama gwana haka? Bala'i!" Gabaɗaya ta sauya, na mayar da hancinta siriri sai ya koma kamar irin nawa. Hotunan da ta ɗauka yafi guda ashirin.

Ni ma sai yanga ta ta tashi nace daga yau nima ba zan sake yi mata kwalliya ba, har da durƙusawa ƙasa tana ba ni haƙuri, Mama kam na gefe tana ta dariya.

Nayi amfani da POP ɗin Hassana na tafi Yola gidan Yaya Muntari, kuma wannan zuwan nawa ne yasa na gano abinda yake maƙale da Hassana a Yola. Saurayi gare ta, kuma kallo ɗaya za ka masu ka gano irin ƙarfaffar soyayyar da ke tsakaninsu, ba ta shakkar idon Yaya Muntari bare ni da take gani kamar kan mu ɗaya. A jami'ar su Yaya Muntari yake shi ma, bai daɗe da fara aiki anan ɗin ba, a halin yanzu yana PhD ɗin shi ne. Da na tambaye ta yaushe za ta dawo Kano sai tace masters za ta ɗora a FUT Yola.

Yaya Muntari ma cewa yayi da a ce ɗaya daga cikinsu yana Kano da sun taimaka mun na buɗe gidan abinci. Da nace ai ga Hussein, dariya yayi yana faɗin ai ba wani bambanci tsakanin mu, don tsaf za'a cuce mu ni da Hussein ɗin, ya dai ce na adana kuɗina da kyau har zuwa wani lokacin sai a ga ya ya za'a yi.

A satin kuma aka kafe jarabawar mu, a kuma cikin satin naje makarantar domin yin clearance da tattara slips ɗina na mataki na ɗaya, biyu da na uku na kuma kai wa exam officer ɗin mu. Na kuma koma gida ina jiran tsammani, domin sakamakon kaɗai nake jira domin cigaba da karatu.

Auren Rahinatu bai hana mu yin kwalliya ba, jan bakin da aka sako mata a lefe biyu muka raba su ni da ita, irin mai kai wa awa ashirin da huɗu ne. Don haka kullum leɓenmu jawur yake. Sannan yanzu duk na maida turarukan da nake amfani dasu designers, akwai guda uku da kullum cikin turare sune favorites ɗina watau Acqua Di Gioia da Si na Giorgio Armani sai Black Opium na Yves Saint Laurent, sune na dindindin, ragowan kuma ina caccanza su lokaci zuwa lokaci, hakan ya sanya tun safe har dare cikin ƙamshi nake. Sannan ina da body gel na turare kala-kala da nake yawaita shafawa, a taƙaice zan iya kashe albashi na wata guda akan kwalbar turare ɗaya har ma fin kuɗin in dai ƙamshin yayi mun.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.