Free chapter · Read without an account
40
A kwana a tashi ba wuya ga mai yawan rai, sakamakon jarabawa ta ya fito ina da 13 points. Ni mamakin points ɗin ma nayi saboda wasan da na naɗa a makarantar, 13 points na nufin na gama da A, B da C a grades ɗina.
A satin da na karɓo kwalin a ciki na cike DE, kun dai san ba zan cike BUK ba. Da nayi tunanin ko na cike ABU Zaria amma yanda nasan daɗin samun kuɗi na kaina ba zai yiyu na koma Zaria da zama ba, haka ba zan iya jigilar zuwa Wudil da dawowa kullum ba, sannan ba ma yanda za'a yi nayi boarding a can ɗin. Don haka shawara ta ta tsaya akan makarantu guda biyu, Northwest University ita ce zaɓi na na farko sai ma saka FCE Kano tuna suna yin B. Ed watau suna its affiliated to ABU Zaria. Ina sane Sa'adatu Rimi sun fara B. Ed, amma ai ita kam na gama da babinta don ba abinda zai mayar da ni can da izinin Allah. Da yawan mutane ba wanda ya san nayi makarantar ma saboda ko da wasa bana maganar ta kuma bana son a yi mun.
Duk ƙiyayyar da nake yiwa SRCOE ɗin sai da na ba wa kaina dariya, tunda dai makarantar ita ce ta bani hanyar shiga jami'a yanzu haka, sannan duk ƙoƙari na sai da nayi carry overs da ɗan dama.
Abincin ma yanzu likkafa ta ci gaba kasancewar ni Ummu idona ya buɗe ƙwarai da gaske, riba sosai nake samu yanzu fiye da da, na daina cewa mutum ya bada abinda ya sauwaƙa a matsayin lada na, tsadancewa muke da kyau.
Wannan ramar har wannan lokacin tana nan duk da na cigaba da addu'o'in shifa da shan magunguna, amma shi sauƙi na Allah ne domin rashin ƙarfin da na sha fama da shi yanzu ya kau gabaɗaya, ragowan kuma ina ba wa kaina tabbaci we are getting there bi'izinillah.
Wurin aikinmu lafiya lau shi ma, Habiba ce har yanzu ba ta daina wahalar son Yaya Bash ba sannan ba ta daina ɓata ranta ba muddin ya zo gari yana tsokanata ko kuma idan ta ga mun yi waya, shi ke nan an shiga uku! Domin fushin da zata yi a ranar ba ni kaɗai yake shafa ba har kowa na ofishin mu. Rahinatu ma da kanta ta fuskanci hakan domin ni ko sau ɗaya ban taɓa nuna na fuskanci abinda take yi ba. Kwaɓar Rahina nayi da cewa kar ta kuma maganar idan ba haka ba mu ma sai mu zama ɗaya da ita watau wawaye. Amma ba za ka hana Rahina zama Rahina ba, kawai sai ta tsiri tsokanar Habiba a fakaice, haka rannan muna wurin da muka idar da sallah a ɗakin sallar mu, ni hoda nake gogawa fuskata saboda nayi alwala, sai Rahina tace "Oh Ummu! Wannan kwalliya kamar wadda za taga baƙo daga Legas?"
Har ga Allah bangane nufin ta ba don haka nace "Ka ji Rahinatu don Allah, ban da abin ki kwalliya har akwai ta ganin baƙon Legas da kuma na Kano?"
Tana dariya ta amsa "Ki cigaba da ɓoyewa, idan tayi wari kowa zai ji ne ma."
Ban kai ga amsawa ba sai kawai naga Habiba ta miƙe a fusace ta ja jakar ta ta fice, a take na gane ina zancen Rahina ya dosa, ita kuma Rahinar har tana kwanciya ƙasa saboda dariyar mugunta.
"Allah Rahina abinda kike yi ba kyau."
"Ƙyale ta dallah, so nake na kunna ta kaɗan shikenan kawai. Haushi ta bani ɗazu ne shi yasa na rama." Ta cigaba da dariyar ta.
Na girgiza kaina nace "Kunna ta fa? Ita sigari ce da za ki kunna ta?"
Sai ta ƙara ƙarfin dariyar ta tana cewa "Ummu akwai baƙar magana, bari na gudu ba za ki kashe ni ba."
Cikin ikon Allah kafin mu tashi sai ga Yaya Bashir ɗin ya duro, ina hango shi na gama sanin yau ko ƙur'ani zan haɗiya Habiba ba za ta taɓa yarda bansan da zuwan shi ba ko kuma maganar Rahina sara akan gaɓa ce ba, sai da gaba na ya faɗi na juyo ina hararar Rahina, duk da ita ma mamakin take yi hakan bai hana ta murmushin jin daɗin abinda tayi ɗin ba.
******************
Hassana ta fara masters ɗin ta a FUT kaman yanda ta tsara, tana ta fama da ɗan fulanin ta Izuddeen. Har ma ya fara maganar turo manya gida, don ma Yaya Muntari ya ɗan dakatar da shi akan cewa ya kamata su ƙara fuskantar juna shi da Hassana tukunna don abun yayi wuri da yawa.
Hussein ma ya fara nasa a BUK ɗin dai, Baba ne yace ya ajiye zancen neman aiki har sai ya kammala masters ɗin shi tukunna. Tunda ga Yaya Naziru nan tunda ya samu aiki sai ya zubar da zancen ƙaro karatu don gara ma Yaya Zainabu tunda ita mace ce.
Baba yayi ritaya daga aiki yanzu amma ya buɗe gidan kiwo kusan koyaushe a can yake yini. Don haka a wurin Baba nake siyan kaji idan zan yi wa mutane aikin abinci yanzu, amma fa har da ɗan wayo nake haɗawa wajen siyan kajin, duk da Baba yana sane sai yayi fuska kamar bai gane ba. Allah sarki Baba nawa!
Cikin ikon Allah na samu Northwest University level 2, sai a lokacin su Mama suka san na nema, kowa ya taya ni farin ciki. Na sanar da Manajan mu zancen makaranta domin a so na na bar aikin haka nan amma sai ya bani shawara naje na dubo time table ɗina idan ba chance shi kenan. Abu kamar wasa shekara ta guda kenan da kammala Sa'adatu Rimi College of Education.
Time table ɗina yawanci lecture ɗin safiya ce sai laraba kuma da nake kai wa huɗu, kuma kun san dai jami'a ba tsoro za ta bani ba, tunda na iya kai labari a BUK babu kuma wata jami'ar da za ta tsorata ni. Yawancin abubuwan da ake yi mana ba wanda ban iya ba, bambancin na yanzu akwai education, wancan na baya da nayi pure ne.
Tunda na riga na saba da ƙailula kuma naji daɗin ta shi yasa anan ɗin ma ba yanda za'a yi naje makarantar gabaɗaya ranakun. Har gara ma anan makarantar bana sanya liƙab, aikina na cigaba kawai ba tare da wata damuwa ba.
Alhamdulillah komai yayi sauƙi yanzu kam, ƙunci ya kauce daga zuciya ta. Samari gabaɗaya basa gaba na domin ban taɓa kai tsawon wannan lokacin bana tare da kowa ba, kuma bana sha'awar zama da kowan. Ko da muka rabu da Fa'izu nasan na daɗe amma ban kai haka ba a tunani na ko kuma ƙila don na daɗe da mancewa da shi da abinda ya dangance shi.
Rahina a satin ta tafi hutun haihuwa don haka in dai ba shift ɗaya muke da Anty Samira ba bana jin daɗin zama da Habiba, ban da ma ƙwaƙwalwar kifi gare ta yaushe rabon Yaya Bashir ɗin da Kano yanzu? Ya daɗe sosai bai zo ba sannan mai yawan tsokanar ta ta bata nan.
Lokacin da na fara jarabawa sai na ɗau break ɗon kwanakin exams ɗina, rabon da nayi karatun da na yi wa jarabawar nan na daɗe sosai da sosai don ba zan iya tunawa ba ma. Na kan maimaita gabaɗaya course sama da sau uku, har cikin dare yi nake duk da abinda na iya ne amma ba na fatan samun matsala ko ɗaya ce anan makarantar.
Shekara goma cif kenan tsakanin waccan jami'ar ta farko da na fara da kuma wannan ta yanzu da nake ciki a halin yanzu. Don ba zan manta ba, ina shekara sha bakwai na fara lokacin muna tare da Aliyu, abun ba wuya ga mai yawan rai.
Washegarin gama jarabawar kuma na dawo bakin aiki, cikin sa'a na iske motar Yaya Bashir a harabar ofishinmu, kusa da motar ta shi ma nayi parking. A hanzarce na hau benen don ba laifi na yi kewarsa ba kewar kuɗin da yake bani domin yi masa girki ba. Abokan aikina ma a gurguje nayi masu magana tare da cewa ina zuwa bari naje na ga Yaya Bashir it's been ages. Ina jin ana yi mun magana amma ban ji ba nayi gaba sai alamar ina zuwa da nayi masu da hannu.
Ƙwanƙwasa ƙofar nayi ban kuma jira izini ba na buɗe tare da shiga gabaɗaya, baki na a buɗe saboda murna. A gurguje na gaishe da yallaɓai tare da cewa "Ina Yaya Bashir ɗin?"
"Oga kuma? A ina kika gan shi?"
Sai murmushin da nake yi ya ragu na daɗa waigawa a ofis ɗin domin na tabbatar da cewar baya nan ɗin, wani na gani a zaune yana daddana laptop na amsa da cewa "Motar shi na gani a ƙasa fa sai na ɗauka ko ya leƙo mu yau ne."
Manaja yace "Au! In dai motar kika gani Nu'uman ne yazo da ita." Ya juya wurin mai danne-dannen laptop ɗin yace "Nu'uman ina ga wannan ce ta saura baku haɗu ba, Ummu kenan, yau ta dawo daga shortbreak."
Ya ɗago idanuwan shi ya kalle ni, a take gaba na yayi mummunar faɗuwa. Kallon da yake mani yayi kama da na wani mutum da na kasa tunawa, idan kuma ba haka ba ne to kuwa shi Nu'uman ɗin na sani a wani wuri. Tunda nake ban taɓa ganin mutum mai yalwar gashin ido irin na shi ba, kut! ji nake dama ni aka bawa.
Tsaki ya saki da ya dawo da ni cikin hankali na sannan yace "Oh!" A take jiki na ya mutu, ban ƙara cewa komai ba a sanyaye na juya tare da rufe masu ƙofar. Na ɗauki sakwanni a bakin ƙofar domin ƙoƙarin sai ta kaina. Na tsani tsaki! Mts! Da fara'ar ƙarya na dawo wurin abokan aiki na muka gaggaisa sosai sannan na fara aiki na da sanyin jiki. Har magriba jikina da raina babu daɗi saboda tsakin nan har yanzu ci na a rai yake yi. In taƙaita maku sai da na gudu banɗaki nayi hawaye, na wanke fuska ta na sake sabuwar kwalliya sannan na ji ɗan sanyi a raina.
A ranar bayan na gama komai na shirin bacci, ina kwanciya fuskar shi ta dawo mun, baƙi ne sosai irin waɗanda ake cewa coke, kamar yanda al'adar kasancewa baƙi take idanunshi farare ne kal hakazalika haƙoran shi da faratan yatsun hannayen shi. Nasan tabbas yana da ido don ko ni ba zan nuna mashi ba sannan hancin shi sosai ya dace da idanuwanshi yana da ɗan kauri sannan leɓen shi suna da faɗi amma ko ni da nake mace nawa sun fi na shi kauri don haka sai yayi kamar yanka wurin aka yi. Tsakin da na tuno ne ya sanya na watsar da abinda na gama tunowa yanzun nan, cikin jin haushin kaina na yi wa kaina tsaki.
Ko waye shi Nu'uman ɗin da zai yi mun tsaki? Allah ya isa! Sai hawaye ya zubo. Haushin kaina ya ƙara kama ni, yanzu haka yaran nan ne da suke zuwa ana nemar masu admission a ƙasashen waje ya sanya yake wani jin kan shi. Mts!
Ƙarar waya ta ce ta katse tunanin da nake yi, lambar Yaya Bashir ce don haka zumbur na miƙe zaune ina mamakin gain kiran shi a wannan lokacin.
"Hello? Yaya Bashir ina yini?"
"Lafiya lau Ummu. Don Allah ɗan turo mun account number ɗin ki yanzun nan, yi sauri please." Ya katse wayar.
Kaina a ɗaure nayi mashi text ɗin account number ɗin don ban san me zai yi da shi ba. Minti goma tsakani sai ga alert, na zaro ido ina kallon kuɗin don bansan ma'anar su ba, ban gama nazarin su ba ya sake kira na.
"Ummu na turo maki kuɗi yanzu, Nu'uman yana gari kuma ina ganin zai yi kwana biyu shi yasa na turo maki kuɗi masu ɗan dama. Direba zai dinga zuwa yana ɗauka, zan tura mashi lamba ɗin ki yanda za kuyi communicating a tsakanin ku na abin da yake so a kowacce rana."
Duk wannan bayanin da yayi ba wanda ya ja hankali na kaman sunan Nu'uman da ya ambata, don haka nace "Waye Nu'uman?"
Yana dariya yace "Brother ɗina ne, za ku haɗu a agency ai. Ina ga shikenan ko?"
Nace "Eh"
Ya amsa "To sai da safe and thanks a lot." Ya kashe wayar.
A fili nace "Don kawai shi ƙanin Ya Bashir ne sai ya raina wa mutane hankali? Mtswww! Shi yasa Yaya Bashir kirkin shi yawa ne da shi sannan darajar Yaya Bashir ɗin zai ci har nayi masa girkin, ɗan rainin hankali kawai.