Free chapter · Read without an account
KWAƊAYIN WASU IYAYEN Chapter 2
KWAƊAYIN WASU IYAYEN....!
*Chapter 2*
"Abban Nadeeya lafiya na ga fuskarka akwai alamar damuwa?" Umma Habeebah tayi tambayar tana zama kusa da mijinta Alhaji Muhammad Turaki,wanda suka sauke farali shi da Umman shekaru uku da suka gabata.Ya ɗago manyan idanunsa da duka ƴaƴan nasa biyu suka gada a wajensa ya sauke akan Umman,cikin matuƙar ɓacin rai yake faɗin, "Yanzu Habeebah har ta yaya aka yi Ruƙayyah ta fara soyayya da Yaron gidan Mallam Sulaimanu ɗan wajen Iya mai waina ba tare dana sani ba? Ko kuwa da ɗaurin gindinki hakan ya kasance eyim?" Umma tayi saurin dafe ƙirji tare da kama bakinta da ɗaya hannunta tana faɗin, "Wallahi bani da masaniya Abbansu Ruky,ko kaɗan bansan da wannan zancen ba sai dai idan ta waya suka ƙulla soyayyar tunda ka siya musu wayar hannu dake chat da komi." Abbah ya saki tsaki tamkar zai tsinke harshensa,kafin daga bisani ya labartawa Umman yadda suka yi da ƴan uwan Mallam Sulaimanu su Mallam Al-Hassan.Ya ƙare maganar da faɗin, "Sun cika mini idanu da kwarjininsu Habeeba,ta yadda na rasa yadda zanyi ince musu ban amince da buƙatar da suka zo da ita ba,amma amince masa zuwa zance bashi ke nufin na amince zan bashi auren Ruƙayyah ba,da zaran irin kalar mijin da ya dace da ita yazo zan sallama shi ya kama gabansa,amma a yanzu tunda babu tsayayyen da ke zuwa wajenta bani da hujjar da zan yi saurin dakatar dashi duba da irin mutanen da ya turo mini domin nema masa izini." Umma ta jinjina kai cike da gamsuwa kafin ta furta, "Hakane Abbbansu,amma baka ganin yin hakan kuskure ne? Da dai ka dakatar da shi tun a yanzu gudun kar su shaƙu da juna sannan daga baya irin mijin da muke fata yazo a koreshi rayuwarta ta shiga cikin wani hali." Abban ya ɗan yi jim! Kafin ya furta, "Babu wani damuwa Habeebah,domin ita kanta idan irin kalar mijin da muke mata fata da buri ya zo,ita da kanta ba za ta aminta ta auri wanda bashi da komi ba,don haka ki ƙyaleta tunda har ta amince masa ya turo neman izini to tabbas tana sonsa ne ta aminta dashi,yanzu dai kira wo mini ita domin inji daga bakinta da cewa saninta ne ya turo ko kuwa gaban kansa yayi?" Umma ta miƙe domin cika umurninsa tana faɗin, "Hakan shi ya dace kuwa,domin idan gaban kansa yayi kaga sai a dakatar dashi cikin ruwan sanyi,domin kuwa Ruky ba ajinsa ba ce wallahi!" Ta ƙare maganar tana fita a fusace domin zuwa ta kira Ruƙayyan.
"Ruƙayyah maza ki je Abbanku na son ganinki,ke kuma Nadeeya wani matsiyacin ne ya kawo miki wannan tsiyataccen yoghurt ɗin roba ɗaya tallin ƙwal! Me kika sha mai mu Iyayenki ki san mana muka sha? Ina rabaki da kula samarin da basu dace da rayuwarki ba amma kina nuna mini sam bakya ma jin maganata ko?" Umma ta furta kalaman cikin tsantsar ɓacin rai da takaici.Nadeeya tayi shiru tana jin zuciyarta na sake cika da ɓacin ran yadda iyayenta ke sake fiddo da maita da kwaɗayinsu a fili akan irin mazajen da suke musu fatan su aura,lamarin na matuƙar ɗaure mata kai da kuma bata mamaki.A tunaninta duk Iyaye na gari suna fata ne ƴarsu ta samu mai sonta tsakani da Allah,mai riƙo da addini kuma mai tarbiyyya da sana'ar da xai riƙa musu ita.Amma sai ta ga ita nasu Iyayen sam ba haka bane burinsu,fatansu kawai su samu masu kuɗi ko ƴaƴan masu kuɗin da idan suka auresu za a san cewa tabbas sun shiga gidan girma.Murya a sanyaye ta dubi Umman tana faɗin, "Umma bafa roba ɗaya bane guda biyu ne,na kai miki ɗaya roban ɗakinki ne na tadda kina ɗakin Abbah,wallahi Umma Khamis nutsatstse ne da ke sona tsakaninsa da Allah,kuma ya tabbatar mini da cewa aure ne ya kawosa ba wai wasa ba." Umman da ke saurarenta ta banka mata wata uwar harara tana faɗin, "Aifa sai aurenki zai yi,yanzu ke idan aka barki sai ki auri wanda bashi da komi,bai tara komi ba sai ya fita ya nema kullum sannan ya ciyar dake? Duk irin baiwar kyawun da Allah yayi muku ya yo ku da zubin matan manyan attajirai amma baku da buri saina bai wa ƴaƴan talaka fuska suna kawo kansu zuwa gareku har suna muku iƙirarin aure? To bari kiji wallahi Abbanku zan sanya ya taka masa burki tun wuri,ita ma Rukyn da ta jajibo ɗan gidan Iya mai waina wallahi sai naci mutuncinta." Tana kai wa ƙarshen kalamanta ta fice ɗakin a fusace ta bar Nadeeya da bin bayanta da kallo hankalinta a tashe.Tana son Khamis sosai da sosai,domin matashi ne nutsatstse da ke tsananin sonta tsakani da Allah.Yayi karatunsa har ya kammala deegree ɗinsa a fannin kasuwanci,sannan yana da sana'arsa daidai gwargwado dake kawo masa kuɗi na rufin asiri.Shago yake dashi na sayar da cusmetics,yana kuma sana'ar ɗinka manyan kaya yana siyarwa.Don haka ita bata ga abin kushewa a garesa ba tunda mai nema ai yana tare da samu,sannan bugu da ƙari ita bata taɓa yiwa kanta sha'awar auren Yaran masu kuɗi ko masu kuɗin kansu ba.Tuni Ruky ita ta fice zuwa ɗakin Abbansu domin amsa kiransa,ta same shi yana cin abincin dare da bai samu ci da wuri ba sakamakon zuwan waliyyan Ahmad nema masa izinin fara zuwa zance. "Abbah gani,Umma ta ce kana kirana." Ruky tayi maganar cikin wani irin cool voice mai sanyi da zaƙin amo da Allah yayi mata baiwarsa.Abban ya ɗago idanunsa ya sauke a kanta yana sake hasko tsananin kyawun ɗiyar tasa,cike da tsare gida ya sake ƙure ganinsa a kanta yana faɗin, "Hakane Ruƙayyatu,zo matso kusa dani ki zauna." Babu musu ta matsa zuwa kusa da shi ta zauna fuskarta a sake da murmushi.Abban ya aje kofin ruwan da ya shanye yana sake ɗaura ganinsa a kanta ya furta, "Ruƙayyah da saninki ne Yaron gidan Iya mai waina ya turo magabatansa akan a nema masa izinin fara zuwa zance wajenki?" Ruky take ta ji gabanta ya faɗi da wannan tambayar ta Abban,amma sai ta bai wa kanta ƙwarin guiwa ta furta, "Eh Abbah, da sanina ne,ya matsa ne akan gara a san dashi a gida hakan shi ne addini." Abbah ya jinjina kai yana danne ɓacin ransa ya furta, "Hakane kam,na sanar da wakilansa cewa na bashi izini,amma hakan ba yana nufin nayi masa alƙawarin zan bashi aurenki bane,da zaran wanda ya shirya aurenki ya zo zan sallamashi domin ko kaɗan baku dace da juna ba,na sha sanar daku cewa ni gidan hutu nake muku fata da sha'awar ku shiga,gidan ba za ku sha wahala ba sai ma dai ku samu daular da mu kanmu sai mun yi alfahari da haihuwarku,don haka ki sanya a cikin zuciyarki cewa na bashi dama ne domin ba zan iya watsawa waɗanda ya tasosu suka zo ƙasa a idanunsu ba." Ya dasa aya a kalamansa yana kallon yadda fuskar Ruky ta canza daga murmushi zuwa damuwa mai tsanani.Ta buɗe baki domin yin magana amma sai yayi saurin dakatar da ita ta hanyar faɗin, "Tashi ki je Ruƙayyah,babu abinda za ki faɗi mini yayi tasiri,domin ni Turaki ba zan taɓa aminta in aurar daku a inda za ku wahala ba." Ya ƙare maganar yana sakin tsaki yayin da ita kuma Ruƙayyah tayi saurin tashi ta fito daga ɗakin,bayan yayi mata inkiya da hannu akan ta fita ta bashi waje.
"Yaya Nadeeya kin ji abinda Abbah ke faɗi bayan zuwan wakilan Ahmad kuwa?" Ruƙayyah tayi maganar idanunta na tara ƙwalla.Nadeeya ta aje wayar hannunta tana maida hankalinta ga Ruky ta ce, "Me yafaru Ruky, bai amince masa ya dinga zuwa zancen bane?" Ruky ta share hawayen da suka sulmiyo daga kwarmin idanunta tana faɗin, "Cewa yayi bashi dama ba shi ke nufin zai aminta muyi aure ni da shi ba,wani na zuwa wanda ya dace dani zai kore shi,wannan wata iriyar magana ce Yaya Nadeey? Me yasa Abbah da Umma kullum burinsu sai dai mu auri masu kuɗi? Miye aibun Ahmad da Khamis da za a riƙa kushesu ana rainan rufin asirin Allah ya basu na sana'ar yi da kuma ilimin da suka samu? Wallahi na fara shiga damuwa da halayyar su Umma domin ya nuna a fili KWAƊAYI ne zalla a cikin zukatansu,ni kuma wallahi Ahmad nake so,shi zuciyata ta aminta dashi ko waye zai zo bayansa wallahi ba zan amshi soyayyarsa ba!" Ruky ta kai ƙarshen kalamanta fuskarta na sake yin jajir alamun takai maƙura wajen shiga ɓacin rai.A sanyaye Nadeeya ita ma ta sanar da Rukyn yadda sukai da Umman a ɗazu,ta ƙare maganar da cewa, "Addu'a za mu yi tayi Ruky domin nima lamarin su Umma ya fara bani tsoro Ruky,wallahi nima bansan ya zanyi ba idan aka rabani da Khamis mai ƙaunata da gaskiya." Suka haɗu ita da Ruky suna ta tattauna batun kafin kiran Ahmad ya shigo wayar Ruky.Ta janyo wayar samfurin Infinix mai kyau da Abbah ya siya musu,cike da narke murya take amsa sallamar da Ahmad ya doko mata.Ta sake komawa can ƙarshen gadon ɗakin nasu ta lafe,murya ƙasa-ƙasa suke yin wayarsu ba tare da Nadeeya na jin abinda Rukyn ke faɗi sosai ba.Soyayyarsu na birgeta matuƙa sabida ta laƙanci Ahmad irin social Ustaz ɗinnan ne da ya iya sace zuciyar mace da salon soyayyarsa,gashi kuma sun dace da juna da ƙanwartata bata ga wani makusa a tattare dashi ba ko ƙanƙani.
A washegarin ranar da misalin ƙarfe biyar na yamma Ahmad Sulaiman ya fara zuwa zance gidan su Ruky,Ruky ta ci ado cikin wasu riga da skat na atamfa dark gray mai mugun kyau.Indai batun saka sutura ne to tabbas sai an sara musu domin Abba bai gaza ta wannan fannin ba,yana ɗinka musu suturu kala-kala tunda sana'arsa ce sayar da atamfofi da lesuka.Ko bai ɗinka musu masu tsada sosai ba za ka gansu da masu matsakaitan kuɗi,suka kuma yi dace da telar da ta iya zuba musu ɗinki irin na zamani.Sosai kalar atamfar mai duhu ta haske farar fatarta,fuskarta simple makeup ne da iya powder da man leɓe kaɗai ta sanya.Ƙamshin sassanyar turarenta ke tashi a jikinta,ta ɗauki mayafin da ya dace da shigarta ta yafa tana jin zuciyarta cike da wani irin nishaɗi mara misaltuwa.Yaya Nadeey ce ta dubi ƙanwartata ta ƙara tana yaba kyawun da tayi,cike da tsokana take faɗin, "Autar Umma kinga yadda kikai mugun kyau kuwa?Irin wannan kyawun ai saiki ƙarisa rikita Amadun gaba ɗaya." Ruky ta dubi Nadeey tare da yin wani fari da idanu tana faɗin, "Wallahi Yaya Nadeey nama sassauta,kawai dai jikin nawa ne da fuskar basa raina ado,koya na ɗan raɓa abu kaɗan sai a ga tamkar zama nayi na musamman na tsara kwalliya,bari na je kar ya gaji da jirana tun ɗazu yana waje." Daga haka ta saka flat takalminta ta fice.Bata sanya takalma masu tudu sabida tana da tsayi mai kyau wanda bai cika yawa ba,hakan ya sanya duk takalmanta flat ne masu ɗan tudun kaɗan ne a ciki. "Umma zan fita Ahmad ya zo." Cewar Ruƙayyah tana daga tsaye jikin hannun kijeran one seater cikin jerin kujerun dake falon Umman.Umma ta ɗago idanunta daga danna wayarta ta sauke akan Ruky tana jin wani abu mai ɗaci na ratsa maƙoshinta,da wani irin murya mai kaurin amo ta furta, "Kaico! Ki rasa wanda za ki tsalawa wannan uwar kwalliyar ki fita sai ɗan gidan mai waina,yanzu Ruƙayyah ke kin ga cewa kin dace da ɗan talakan da bai aje ba bare ya bai wa wani ajiya? Mai na sama ya ci bare ya bai wa na ƙasa? Shi da kansa Ahmad ɗin ƙarya yake ya ce bai san cewa igiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa tsakaninsa da ke ba,kawai dai ya samu fuska ne daga gareki da kika ƙasƙantar da ajinki kika nuna cewa talaka kamarsa zai iya tunkaranki da batun soyayya har ki amince masa." Ta dasa aya a kalamanta tana sake watsawa Ruky da ta haɗe face harara.Ruƙayyah bata iya cewa komi ba ta juya ta fito daga ɗakin Umman tayi waje,sosai zuciyarta ke bugawa da matsanancin ɓacin rai da tsanar kalaman Umman nasu.A ginjine da jikin babur ɗinsa lifan ta same shi,ya gama ɗaukar wanka cikin wani yadi mai ɗan karan kyau kalar sky blue.Sosai kalar yayi masa mugun ɗinkin kuma ya dace da ƙiran jikinsa,Ahmad kyakykyawan gaske ne mai tsayi matsakaici.Yana ɗauke da manyan idanu masu haske da cikar gashin idanu gazar-gazar,pink lips garesa da ya ƙawata kyawun dark face ɗinsa kasancewarsa chocolate colour.Gashin kansa mai taushi da santsi kamar na fulani ya sha gyara ya kwanta luff! Bai sanya hula ba domin bai faye saka shi ba idan ba ɗaura aure zai je ko wani taro na musamman ba.Ƙamshinsa mai narkar da zuciyarta ne ya fara isa hancinta tun kafin ta ƙarisa isa inda yake tsaye,ta ɗan lumshe idanunta ta buɗe tana sake jin ƙaunarsa mai yawa na sake mamaye zuciyarta. Sallama tayi masa ya amsa yana sake zube manyan idanunsa a kanta,shigar ya birgesa matuƙa tare da sake zurfafa soyayyarta a cikin zuciyarsa.Ya sake harɗe hannuwansa a ƙirji yana jifanta da wani sassanyar kallo kafin ya furta, "Barka da fitowa gimbiyar matan Kano." Ruky ta saki wani ƙayataccen murmushi tana gaidashi cike da ladabi.Ya amsa da kulawa yana sake yaba nutsuwarta sosai a cikin zuciyarsa,muryarta mai matuƙar taushi da sayin amo ya sake ratsa kunnuwarsa time ɗin da ta furta, "Bimismillah! Mu ƙarasa ga kujerun zama can Yaya Ahmad." Ahmad sai da idanunsa suka ɗan lumshe sakamakon yadda idan ta kira yi sunansa yake jin zuciyarsa na kaɗawa,bai taɓa cin karo da macen da ta iya furta sunansa cikin karyewar harshe irin Ruks ɗinsa ba.Ita ta fara yin gaba zuwa wajen fararen kujerun da suke aje daga can gaban ƙofar falon Abbansu ta waje,ta ɗauki guda biyu ta aje musu tana janyo table ɗinsa ta sanya musu daga tsakiya ta yadda ya raba tsakaninsu ya zamana suna facing juna.A nutse suke zantawa cikin matuƙar nuna kulawa da soyayyar junansu,Ahmad ya iya amfani da kalamai masu taushi da sace zuciyar mace.Wanda kuma hakan ya samo asali ne daga zurfin da yayi wajen sanin ilimin sanin salon sarrafa harshe,wanda a larabce ake kira da ilimin(Balaga)
Sai wajen misalin ƙarfe shida na yamma yayi sallama da Ruky akan zai wuce,ta taka masa har zuwa bakin ƙofar fita gate ɗin gidan tana masa mita akan yadda bai sha ko ruwa da lemun da ta shiga cikin gida ta amso masa ba.Ya bata haƙuri akan cewa next time ba ruwa da lemu kaɗai ba,hatta abinci idan ta kawo masa zai ci matuƙar hannunta ne ya girka.Ta sakar masa wannan murmushin nata da ke tsumasa,tana yi masa bye-bye ta juya domin komawa cikin gida.Yana fita da mashin ɗinsa wajen gate ɗin gidan motar Abbah na danno kai cikin layin,sai ya faka mashin ɗin a gefe guda ya jirayi ƙarisowarsa domin ya miƙa gaisuwa kafin ya wuce.Shi ya buɗewa Abban gate ɗin gidan ya shigar da motarsa,bayan ya maida gate ɗin ya rufene ya ƙarisa gaban motar Abban da sauri yana yi masa sannu da zuwa.Alhaji Muhammad Kabeer Turaki ya tsurawa Ahmad ɗin idanu yana jin wani ɓacin rai na lulluɓe zuciyarsa,tabbas Yaron bashi da makusa a fannin kyawu da iya saka sutura, duk da cewa a kallo ɗaya da ya yiwa yadin jikinsa ya gano kuɗinta mai arha ce ba mai wata tsada ba.Da ladabi Ahmad ya rusuna ya gaida Abban cikin nuna tsantsar girmamawa,Abban ya amsa fuskarsa babu yabo babu fallasa.Har Ahmad ya juya zai tafi Abban yayi kiransa,sai ya dawo da baya ya tsaya yana fuskantar Abban kansa a ƙasa.Abbah ya buɗe baki a nutse yana faɗin, "To Mallam Ahmad,ba wai na baka damar zuwa zance wajen ƴata don ka samu kafar zuwa a duk sanda ka ga dama bane,domin bani ƙaunar wannan nacin zuwa zancen irin na samarin zamani da basu da abubuwan yi da suka sha gabansu,ban amince da zuwa zance ya wuce sau biyu ko sau uku a sati ba,sannan ban lamunci zuwa da dare ba sai dai da yamma,kafin magriba ka kama gabanka,don haka sai ka kiyaye." Ahmad ya jinjina kansa cike da gamsuwa yana jin wani abu na ɗan taɓa zuciyarsa kaɗan.Ya sake yin sallama da Abban ya fice daga gate ɗin gidan,yayin da shi kuma Abbah ya bishi da harara yana faman mitan bai ga abin so a takala da zai aurawa ɗiyarsa shi ba.Koda ya shiga cikin gidan ya samu Umma nata ma Ruky tsiya da gorin cewa tun a zuwan farkonnan da Ahmad yayi ya sake tabbatar mata da cewa bai dace da Rukyn ba,sabida bai ɗakko ko ƙwandala ya bata ba,bare kuma ya riƙo ƙatuwar leda cike da kaya ya taho mata dashi ba.Ita dai Ruƙayyah na durƙushe gaban Umman tayi ƙasa da kanta takaici na sake cika zuciyarta,muryar Abbah suka jiyo yana faɗin, "Ai nima yanzu muka gama gaisawa dashi yana faman wani sunkuyar da kai ƙasa,babu abinda ya ruɗeta a kansa sai kyawunsa da ƙyale-ƙyalensa irin samarin zamani da suka iya ɗaukar wanka da saka suturu masu arha,amma aljihu babu ko sisi,wallahi sam ba zan amince in bashi aurenki ba matuƙar ba wani buɗi ne ya sameshi kafin nan kafin ku gama diploma ɗinku in aurar daku ba." Ruƙayyah ta saki wani marayan kuka time ɗin da Abbah ya ƙarisa kalamansa,ta tashi a guje ta fito daga ɗakin Umman ta nufi nasu.Nadeeya na zaune saman gado tana duba wasu handout ta ga shigowar Rukyn tana kuka,koda ta tambayeta me yafaru? Sai kawai Rukyn ta sake sanya kuka tana samar da ita kalaman da Abban ke faɗi. "Wallahi Yaya Nadeey Ahmad shine zaɓina koda kuwa shugaban ƙasa ne zai zo gareni bayan shi,matuƙar da yardata ko amincewata za a bi wajen bani zaɓin abokin rayuwa to tabbas Ahmad shine nawa zaɓin,sai dai idan auren dole za a min sabida KWAƊAYIN abin duniya." Ruky ta furta kalaman tana sake sakin kukan mai cin rai.Nadeey ta shiga rarrashinta da kalamai masu daɗi har ta tsaida kukan tana share hawayenta, "Ruƙayyah ki godewa Allah ma ba koransa yayi ya ce kar ya sake zuwa ba,ni fa bayan fitarki mukai waya da Khamis ya sanar dani cewa Abbah ya ce kada ya sake zuwa ƙofar gidannan da sunan yazo zance domin bai tashi aurar damu yanzu ba,idan ma taƙamarsa da aure ya zo,na kuma san bakomi ya janyo hakan ba sai don bai fito daga gidan arziƙi ba,sannan kuma shi ba mai kuɗi bane kamar yadda suke da buri,don haka addu'a kaɗai za mu yi tayi amma tabbas ya tabbata Iyayenmu masu KWAƊAYI ne Ruky,kiyi fata Allah ya gaggauta bai wa Ahmad aikin yi da zaran ya kammala service ɗinsa ,tunda yana da sa a watakila idan Allah yasa ya samu aikin gwamnati Abbah ya amince zai iya bashi aurenki domin ina miki tsananin kwaɗayin mallakarsa a matsayin miji." Nadeey ta ƙare maganar cikin matuƙar sanyin murya,tana jin yadda zuciyarta ke sake cika da damuwar yadda aka dakatar da masoyinta daga zuwa zance wajenta sabida kawai bashi da abin duniya......✍🏻